FreeArewaPen original
MATAR SALMAN
- 1views
- 2chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample 路 Chapter One
*馃挮MATAR SALMAN馃挮*Daga Alkalamin: Hauwa Salihu鉃art OneP1馃尮 _TSOKACI_ 馃尮 ***Kasancewar jiya ban samu nayi bacci ba gabadaya, shiyasa ina idar da sallar Asuba ban san sanda bacci barawo ya saceni ba, daga zaunen nake bacci na sosai.Buga kaina da nayi a jiki drawer shi ya tashen na dafe kaina da yake mun ciwo dama ga damuwa ga rashin bacci .Kama kan nayi da karfi ina karanto addua.....Bansaki kan ba naji kamar horn din motarshi.Ban San sanda na saki kaina na mike da sauri na tafi window, kasancewar window din bedroom dina tana facing harabar gidan.Ina daga labule Rass! Zuciyata ta tsinke, lokaci guda mamaki ta lullubeni.Naji wani irin bacin rai da bakin ciki kamar na hadiye zuciyata.Da sauri na fita daga dakin na nufi harabar gida ko ganin gabana banayi da kyau tsabar bacin rai.Can na hangoshi ya fito gabadaya sojojin gidan sun zo suna kwasan gaisuwa.Da sauri na nufi can wurinshi a lokacin da ya juyo shi kuma bayan sun gama gaisheshi sun tafi. ya bude gaban motarshi.Bansan sanda na tsaya na saki baki ina musu kallon mamaki ba.Itama ni take kallo daga fitowarta fuskarta daukeda tsoro da fargaba .Ganin yadda muke kallon kallo yasa shi riko hannunta a hankali suka nufo inda nake ka min su karaso tuni na daga musu hannu ina kara tamke fuskata. Na kalleshi cikin tsantsar mamaki da 蓳acin rai nace" me zan gani kuma?Nafisa a gidana?Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace min "Haka ne, Nafisa ta dawone.鈥漀a zaro ido hade da fadin 鈥漺hat! ....Wlh bazai yiwu ba, wannan karon bazan dauki iskanci da rainin hankali da aka mini a baya ba bari kaji ni bazan zauna da Nafisa a gidan nan ba.鈥漀a nunata da yatsa hawaye na zubo min na kalleshi nace 鈥滽o ka mance ne in tuna maka? ....Wata daya da suka wuce aka kawota gidan nan a matsayin amaryarka, kawai daga shigarta daki ta yanki jiki ta fadi ta suma, 'yan uwanka suka sakoni a gaba da zagi ciki harda mahaifiyata da bataji ba bata gani ba, sukace mu mukayi tsafi don mu wargaza aurenka da Nafisa.鈥滺awayene masu zafi suka gangaro bisa kumatuna na ce "jiya jiyan nan aka kai maka ita a gidan ka na Abuja ta tare, mukayi sallama da kai ka tafi, sannan yau ka daukota kuyi sammako kuzo min gida kace ta dawo?鈥滽o kallo ban ishe shi ba ya kalleta yace 鈥漦e shiga ciki ina zuwa.Ta wuce sum sum jikinta a sanyaye na bita da kallo har ta shige cikin gidan.Sannan na dawo da kallona gareshi ina share hawayena nace 鈥漵hikenan tunda haka ka zaba ni zan bar maka gidan ka yanzu ba sai anjima ba, kaje ka zauna da matarda mahaifiyarka da 'yanuwanka suka zaba maka.鈥漌ucewa yayi ba tare da yace min komi ba.Kamar zan fashe don bakin ciki nayi ciki a zuciye ba 蓳ata lokaci dauki jakata da wayata da key din motata. Juyawan da zan yi sai ganin mutum nayi tsaye ya zuban ido fuska daure.Ban kulashi ba na saka takalmina na karaso bakin kofan ba tare da na kal...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.