NURI

THE NAMES WE STILL CARRY

by @saddiqahhh



Fita yayi daga bathroom din ya wuce can balcony din dakin ya tsaya yana kallon view din Dubai that was inviting, nature da yanayin weather din garin kawai yana kwantar da hankli ammn bai taba kwantar ma da Fu'ad da hankali ba. Tsayawa yayi sosai yana bin wajen da kallo hankalinsa gaba daya baya wajen. Shi kansa bai ma san me yake tunani ba lokacin. Har 12 tayi yana wajen a tsaye bai ma da niyyar komawa ciki iska sai kada gashin kansa take. Around 12:30 ya juya ya sake komawa bathroom ya daura alwala yazo ya tayar da nafila da bai san adadin da yayi ba. Kawai he found comfort in praying. Wata irin nutsuwa yake ji idan har yana yin sallah especially irin wannan na dare haka.

Bayan ya idar din ma addu'a ya zauna yana tayi which most of the prayer shine Allāh ya cire masa son NURI daga ransa. Kullum sai yayi addu'ar ammn it was almost as though he was praying for Allah to increase his love for her with each passing day maimakon ya ragu sai dai ya qaru.

2:30 ya samu ya kwanta da yake baccin yazo masa alokacin yana kwanciya ya daukeshi cike da tarin mafarkin sun hadu da Nuri, ba iya haduwa kawai ba sun hadu yama aureta. Lol. Dab da za'ayi kiran asuba ya farka, juyawa side din dama yayi yana yin addu'ar tashi daga bacci sannan ya miqe ya shiga bathroom ya daura alwala. Fitowa yayi ya sauya cikin wata white din jallabiya ya saka hula irin na larabawan nan akansa. Bai saka don yayi kyau ba amman yadda kasan dalilin sawar knn. Kan abin sallah da yake awajen constant a corner din dake dakin wanda akayi masa don Sallah ya hau. Raka'atanul fajr ya kabbara ya tayar daya daukeshi 3mins kamin yayi sallama ya fara addu'a kenan aka yi kiran sallah.

Azan na gama kira ya sake sabuwar addu'a sannan ya miqe ya fita kai tsaye ya nufi masallaci tare da Fa'iz dinsa da shima ya tashi. Bai dawo ba sai da gari yayi haske shima yana dawowa kayan ya sauya zuwa na gym kawai ya wuce yaje ya fara aikin motsa jikin nasa daya saba.

Around 7:30 ya gama shirya kansa cikin native wears namu na Nigeria saboda jumu'a ce. Shi kuma duk jumu'a ya maidashi qa'ida manyan kaya yake sawa duk da bai son garinsu ammn yana saka kayan garin nasu. Wani farin kaftan ya saka daya mugun yi masa kyau na wuce misali hular kanshi da takalmin qafarsa duk black ne haka ma rolex watch dake hannunsa. Bai damu da yayi breakfast ba ya fito ya shiga dakin da Fa'iz ya kwana ya tarar dashi akwance yana bacci hakan yasa kawai ya juya ya rabu dashi ya fita suka wuce Novebuild ltd........

JANNAH'S POV

Tana fitowa daga theatre room din tayi discarding mask da hand gloves dinta ta wuce office dinta da sauri tana ignoring guardians din patient din da suke tambyarta ya yake. Ba zata iya amsasu ba sam don aikin was not successful tun fara aikin ma ya rasu and she can't be the first person da zata fada musu mutuwar dansu da suke ji dashi. 

Hakan yasa tana shiga office din nata ta saka key ta kulle karma wani yayi gigin biyota. Kayan jikinta na surgery ta zare duka suma tayi discarding dinsu. Ta shiga bathroom ta dauki sanitizer ta wanke hannunta tas kamin ta dauraye fuskarta da fresh water ta fito tana yarfe hannunta. Kan office chair dinta ta zauna kawai ta zabga uban tagumi jikinta duk a sanyaye kamar tana da alaqa da wanda ya mutu haka.

Kawai the fact that patient din ya mutu a hannunta ya mugun kashe mata jiki, ba wai basu taba yin surgery wani ya mutu bane, no. Kawai yanzu anan itace head she's the CMO anan so hakan zaifi damunta. Kamar da wasa ta kalli agogon dake office din ya nuna mata 1:30, da sauri ta miqe tsaye ta nufi jakarta tunawa da sanyin idaniyarta da tayi.

Zuwa tayi ta bude office dinta tana dan daure fuska karma wani ya tare ta da zancen don she's afraid of yadda zasu ji mutuwar nan. Ta daya qofar asibitin ta fita ta wuce parking lot. Motarta ta bude ta shiga bayan tayi warming dinta tayi reverse ta fita daga asibitin gaba daya. Makarantarsu ta wuce ta tarar an dade da tashin yaran daga makaranta.

Tana yin parking ta fita tana dan yamutse fuskarta saboda ranar data daki fuskarta don ana yin rana ba laifi. Tana shiga makarantar taji an rungumeta ta baya. Murmushin da bata shiryawa ba ta samu kanta da yi. Kamin ta juya ta tsugunna gaba dayanta tana raba yaron da jikinta. Yaron ba wani fari bane yet he's not dark kana ganinsa kaga Jannah dake tsugunne gabansa. Ba buqatar bayani he's her son, one and only son. Yaron Zaid data haifa shekara biyu da suka wuce! Sai dai auren baiyi lasting ba, four months kawai auren ya mutu saboda matar Zaid din da ta mugun iya makirci.

"Mummy..."

Kai ta gyada masa tana kama kunneta ta furta "I'm sorry JR .. mummy is sorry..."

Murmushi yayi yana rungumeta da duka hannyensa ya furta "mummy rana..."

Miqewa tsaye tayi dashi ajikinta ta ta fita bayan ta gaisa da masu gadin dake wajen. Jr yana rungume da ita har sannan yana mata surutu. Yaron yana da mugun baki da wayo da suka zarta na shekarunsa that's why ma akayi deciding a sakashi a makaranta kodan Mamma ta huta da qiriniyarsa don mugun rashin ji ne dashi na gaske.

Passenger seat ta zaunar dashi ta rufe sannan ta zagaya driver seat ta shiga.

"Mummy..."

Kallonsa tayi ba tare da tace komai ba ya sake cewa "mummy gobe anje ba."

Kai ta girgiza masa tana kunna motar ta furta "there's no way Jr, idan ka zauna agida rashin jinka ba zai bar Mamma ta huta ba."

Pouting lips gaba yayi a shagwabe yana yin baya shi a dole anyi masa ba daidai ba.

Murmushi Jannah tayi kawai tana fara driving ta dan kalleshi kamin ta dauke kanta tana girgiza kanta.

"Jr din mummy.."

"Ni Mummy ba naci bane.."

"Haba na waye to?"

"Na Mamma da Abba ne.."

"To Mama da Abba ai na Mummy ne.."

"A'a ba naci bane su.. "

"to Jr din Mama da Abba.."

Shiru ya danyi yana zura hannunsa baki yana tsosa can ya cire hannun ya furta "Mummy aunty ace wai za'a jane ni ... "

"Halan kayi damben ko.. "

Baki ya turo gaba yana furta "a'a ba Aidar bane ya mincine ni shine a rama da.."

"Bance kake yin haquri ba Jr."

"Ni ba haqri ba.. a'a akwai jafi fa.. akkuka nayi. "

"Sorry Jr. "

Tunda suka shiga motar Jr yake ma Jannah surutu har suka qarasa gidan bakinsa bai mutu ba. Surutunsa na daya daga cikin abinda yasa aka sashi a makaranta yana dan two years kawai. Tun Jannah na amsa masa har ta gaji ta masa banza ammn still yaron nan sai ya koma magana da kansa shi kadai. Surutun Jr bai buqatar sai da wani da kansa ma yana yin abunsa that's one funny thing with the little boy, carbon copy din Dr Jannah.

Tana yin parking ta juyo tana kallon yadda ya juya baya yana zane jikin mudubin motar yana ta zabga magana. Binsa tayi da kallo kawai tana tunanin a ina yaron nan ya gado surutu.

"Anjo ba.. Mamma da Abba jacu jo.. muyi abcd a makalanta.. muci abinci na an bawa mummy ba.."

Hannu ta miqa ta jawoshi gaba dayanta tana murmushi ta dungure masa kai tana cewa "kasuwa zan kaika na siyar da kai Jr...."

Idan akwai abinda ya tsana bai wuce Mummy tace zata kaishi kasuwa ta siyar ba. Ko kowa zai fada baya damuwa amman har dai Mummy za tace zata kaishi kasuwa ta siyar sai yayi kuka.

Yanzun ma kukan ya fara yana birgima jikinta "ni bajaki ciyal dani ba... Allah bana co... Mummy ba jata ciyar da Jr ba... Allah mummy ba jata ciyar da Jr ba..."

"Ka ringa yin shiru to idan ko yaushe kana magana kuwa tsaf zan siyar da kai a kasuwa Kai na fasa ba kasuwa zan kaika ba a shara zan hullar da Kai..."

Ashe gwara kasuwar da shara, kukan gaske ya fara yanzu yana toshe hanci yace "Allah a'a. Jr a caya... U'um Mummy bana co... "

"Yimin shiru to if not muna fita yanzun zan ziraka a wancan."

Tsit yayi shiru don bil haqqi baya son irin wannan zancen. Da haka ta kashe bakinsa har suka shiga parlourn gidan bai sake cewa uffan ba.

Mamma sai oyoyo take masa yayi shiru yana satar kallon Mummy. Yana son yin magana yana tsoron shara da kasuwa. Wajen Mamma kawai ya wuce yana rungumeta bai ce qala ba.

"Waye ya taba Junior ne..."

Kai ya girgiza yana cusa kansa jikin Mamma.

Murmushi kawai Jannah tayi tana cewa "Mamma barka da gida."

"Me kika cewa yaron nan ne Jannah?"

Kai ta girgiza tana daga hannunta sama da murmushi afuskarta ta haye sama saying "u'uhm ba ruwana Mama yanzu kan wannan jikan naki zaki iya balbaleni tsaf better nayi shiru..."

"Yanzun ma baki tsira ba.. oya Junior tace zata kai ka kasuwa ko.."

Da sauri ya daga kai yana fara sabon kuka yace "arda caya wai jata kai Jr."

"Sorry Jr din Mamma da Abba muna nan ba zamu bar mummy ta kai Jr shara ba kaji good boy."

Da murmushi Jannah ta qarasa dakinta da kenan har ynzun yadda yake only few changes saboda Jr. Wanka ta sake ta daura alwala tazo ta tayar da sallar Zuhr bayan ta idar ta miqe ta koma kan gadonta ta kwanta tana son tayi bacci don yau a asibiti zata kwana.

Bata dade da kwanciya ba Jr ya shigo. Dagowa tayi ta kalleshi kamin ta furta "baka ce ba Jr.."

Hannu yasa yadan dafe kansa irin ya manta din nan ya koma waje ya sake shigowa yana cewa "Assalamu alaikum mummy.."

Murmushi tayi masa tana cewa "that's  my boy."

Wajenta ya qaraso ya kwanta jikinta don already Mama ta sake masa wanka ta sauya masa kaya.

"Mummy."

"Jr."

"Oya let's sleep kaji banda surutu ko kuma kasan sauran..."

Da sauri ya maqe kafada yana cewa "Jr baya co mummy ki dena.."

Cuddling dinsa tayi tana shafa bayansa da haka har yayi bacci ta tofa masa addu'a. Sai ta samu kanta da kallon fuskarsa. Komai na Jr irin nata ne only few differences. She always thanked Allah daya bata Jr. Yaron nan shine sanyin idaniyarta. Duk damuwar da take ciki tunawa da Jr kawai yana mugun sata cikin farin ciki.

Her life was never smooth past these two years amman Alhamdulillah. Ta aure Zaid da yace yana sonta amman rayuwa gidan Zaid was never good to Jannah. She faced many challenges because of her co-wife, who eventually framed her and caused Zaid to divorce her. Dama ba son Zaid din take ba ta koya ma ranta sonsa ne kawai.

Time din data tabbatar she's pregnant for Zaid hankalinta yaso tashi kamar cikin out of wedlock aka samoshi amman data kwantar da hankalinta sai taji she loves the child more than her life tun kamin yazo duniya, this is a mother.

Jr shine rayuwar Jannah Muhammad! Bata sani ba kodan an saka masa sunan wanda take qauna ne. Ammn ta tabbatar wannan sunan yana daya daga cikin abinda yake qara mata son Jr. Could you believe that even after all these years, Jannah still hadn't managed to get over her love for Fa'iz Aliyyu Ardo? Ta sakama danta sunan Fa'iz. Asalin sunan Jr Fa'iz Zaid!!!! This is Jannah for you....

To be continued...


like, comment and share