TASWIRAR KADDARA

Page 21

by @oumamani

*TASWIRAR KADDARA*



  DijahAM(Oum Amani)



Page 21



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM





  Shiru nai ganin manyan mutane a Palourn, sunkuyar da kai na nayi ina goge hawayen fuska ta.



Baffa ne yace "zo kinji jikata shigo ciki ba wanda zai rabaki da yarinyar ki."



Ajiyar zuciya na sauke haka kurin naji maganar tsohon ta ratsani, hannun Aisha na rike sosai muka shigo cikin palourn tsugunna wa mukai muka gaishe su, komawa gefe nai na tsaya ina kallon Mimi dake kare boye fuskar ta a jikin sa.



Abie ne ya kalle ni yace "ku zauna kunji"



Gefen carpet din muka samu muka zauna nidai banda ajiyar zuciya ba abinda nake yi, ina auna yadda zanyi kuli kuli da Mimi yau don ta kaini karshe sosai.



Kallona Abie yai yace "meye hadin ki da Azlan diyata"



Fashewa nai da kuka nace "ba abinda nai wa Mr Wicked wallahi, haka kurin ya takura min ya tsane ni so daya na taba zuwa da yarinya ta ya dauke ta ya tafi da ita office, yana nuna min fin karfi akan ta, ynxu kuma tsautsayi na sake zuwa da ita shine kawai yasa ta a mota, da badan mun shiga motar ba tafiya zaiyi da ita."



Duk mutanen palourn zuba min ido sukai suna kallona Jin sunan da na Kira Azlan dashi.



Da mamaki Azlan yake maimaita Mr Wicked a ransa, kasa rike wa yai sai da yace "Ke nine Mr Wicked din?"



Harara na galla masa ina murguda baki sannan na juya idona nace "kai ne mana da waye toh"



Baki ya bude yace "Ke ni sa'an kine naga alama kin raina ni wallahi"



Tabe baki nai ina juyar da kaina gefe nace "waye yace ka sace min yarinya"





Murmushi kawai Baffa yake yana kallon su wani abu na darsuwa a ransa, tabbas wannan yarinyar ita ce daidai Azlan da alama ba karamin drama zasu nayi ba.



Mummy ce da tunda suka shigo ta kalle su gabanta yake faduwa tace "ke baki da kunya kike ce masa Mr Wicked"



Sunkuyar da kaina kawai nai ina Kara damke jakata, don ni ba Zama ne ya kawo ni ba ana miko min yarinya ta Zan kama gabana.



Baffa ne ya daga mata hannu ya kalle ni yace "jikata meye sunan ki"



Dan dagowa nai na kalle sa sannan na sunkuyar da kaina kasa a hankali nace "Batul"



Murmushi Baffa yai ya kalli Aisha da tunda muka shigo kanta yake kasa gaba daya ta rasa ma tunanin mai xatai, da farko kamannin da Mimi take da Azlan ne ya kusa sata karamin hauka don brain dinta dena aiki yai sai dai kuma lokacin da suka shigo idonta ya sauka akan Junaid Wanda Batul bata lura da shi ba shine abin ya sake rikita ta.



Maganar Baffa dake tambayar ta sunan tane ya dawo da ita daga tunanin da take, Dan Murmushi tai mai kama da yake tace "Aisha".



Mai da kallon sa gun Batul Baffa yai yaga sai aunawa Mimi dake jikin Azlan harara take, girgiza kai yai yana murmushi yau ga wacce tafi jikansa tijara, gyaran murya Baffa yafara yi yace "ina mahaifin yarinyar nan yake Batul"



Da sauri na dago kai na kalle sa, ganin kallon da nai masa yasa baffa gyara maganar sa gurin cewa "ina nufin Ya sunan mahaifin ta, a yadda zaki ya ban labari yarinyar tace masa bata da baba bata son sunan saba ma."



Turo baki nai a raina ina fadin meye za'a tisani ana tambaya ta mahaifin yarinya ta, amma sbd girman mutumin daya mun tambayar yasa ni fadin "Ya rasu"



Dan tsura min ido Baffa yai a hankali yace "Allah ya jikansa," ba dan ya yadda da abinda tace ba.



Mami kuwa tunda suka shigo ta zuba wa Mimi ido tana kallon ta kamar su daya da Azlan lokacin da yana yaro sai kallon ta take daga sama har kasa.



Mama ma dai itama tunanin yadda yarinyar take kama da Azlan take, a zuciyar ta kuwa fata take a ce yarinyar Azlan ce ko ya daina damunsu da zancen budurci.



Mike wa Azlan yai ya janyo hannun Mimi, da sauri na mike nima har ina neman faduwa nayi sauri na rike dayan hannun Mimin.



Kallon sa nai nace "Ka cika min yarinya ta wallahi ba abinda kuka hada kai da ita, kuma baxa ku taba hadawa ba in shaa Allah"



Zuba min ido yai yace "zaki sake ta ko kuwa."



Zare masa ido nai kamar wani yarona nace" baxan sake ta ba sakar min yarinya ta," kallon Mimi nai ina hawaye nace "Mimi ni zaki yiwa haka koh Maa dinki kike gudu koh Mimi"



Fashewa da Kuka tai ta juya ta kalli Azlan sai ta juyo ta kalle ni tace "Maa kiyi hakuri baxan sake ba"



Girgiza kai nai nace "sakar masa hannu toh Mimi, sake shi kizo mu tafi gida ba Saida na miki fada ba akan ba ruwanki da shi ba Mimi, amma ynxu baki jin magana ta koh kin manta wace ni, Maa ce fah"



Fashewa Mimi ta sake yi da kuka da ihu tana fadin "kiyi hakuri Maa, juyawa tai ta kalli Azlan tace "sake ni Daddy zan tafi gurin MAA dita"



Tsawa na daka mata nace "baxa ki daina ce masa Daddy ba, a ta ina ya zama daddy wai me yasa kike so ki dinga bata min rai ne"



Yarfe hannu take tana kuka jikin ta yana rawa don yadda nake mata magana tasan da kyar in baxan dake taba, tsugunna wa Azlan yai ya rungume ta yana shafa bayanta kallona yai yace "baxa ki daina yiwa yarinya ta ihu ba"



Hannun mimi na saki na juya na kalli Baffa ina hawaye nace "kana ji yana cewa yarinyar sa wallahi ba yar sa bace"



Sudai su Baffa ido kawai suka zuba mana suna kallon mu, da alama kowa baya son saduda akan yarinyar.



Sungumar Mimi Azlan yai zai fita ban san lokacin dana janyo masa riga ba nace "sauke min ita don Allah kayi hakuri baxan sake maka rashin kunya ba Allah, kayi hakuri Baba Azlan"



Zaro ido yai yana yatsina fuska yace "nine baban?"



Da sauri na girgiza kai nace "Yaya Azlan zance Allah baxan sake ba nabi Allah na bika Ka sakar min yarinya ta"



Wani makircin murmushi Azlan yai yana Kara rike Mimi sosai yace "Kin yadda ta dinga ce mun Daddy knn"



Harara na watsa masa ina murguda baki nace "Wallahi baka isa ba kuma"



Baffa baisan lokacin da ya sa dariya ba Yana fadin "ikon Allah"



Juyawa yai zai fita da sauri nadaga kafa zan bisa bugewa nai da center table gaba nai Zan kife inda jaka ta ta fadi ta bude a tsakiyar palourn kayan ciki suka tarwatse, kafin na kai kasa naji an janyo ni na fada jikin wani.



Da sauri na dago dan ganin waye na fada jikin sa, zaro ido nai ganin mai kama da Mr Wicked sak sai dai shi ba irin kayan jikin Mr Wicked ne dashi ba amma kamar su daya banbancin kadan ne kuma shima ina hango kamannin Mimi a fuskar sa.



Kafin na dawo daidai naji an fizgo ni da karfi na fada kirjin wani, dago wa nai cikin tashin hankali don ganin kirjin wa na fada ynxu kuma ga wani irin bugawa da kirjina yake tunda yau kwallo ake dani a kirjinan kattai, Mr Wicked ne fuskar sa tayi ja da sauri na juya don ganin inda ya ajiye Mimi don nasan da a jikin sa take.





Hade rai yai yana sakar mata hannu yace "ai ni dashi daban banci ni daban Shi daban Abie"



Mummy ce da takaici ya gama cikata na iskancin da suke yi kamar ba manya agun tace "kai daka rike ta matar kace?"



Kankance ido yai yace "waya sani ko munyi aure"



Da sauri nace "Allah ya kiyaye"



Kallona yai yace "me kike nufi?"



Harara na maka masa ina dauke kaina daga kansa, Baffa da murmushi ya kasa barin fuskar sa gemun sa ya shafa kawai yana binmu da kallo yana karantar kowa.



Idona ne ya sauka akan kayana da suka watsu a kan carpet da sauri na kai hannuna don dauke bracelet din da na manta yana cikin jakar ma, nasa hannu Azlan yasa hannu shima da sauri muka dago muka kalli juna da wannan damar yai amfani ya dauke bracelet din yana juya Shi a hannun sa cikin mamaki.



Kallona yai yace "ina kika samu wannan abin?"



Dauke kai na nai kawai don na gaji da magana ma



Abie ne ya kalli hannun Azlan da sauri ya zo ya karbi abin kallon Junaid yai yace "zo Junaid"



Matsowa Junaid yai da mamakin ganin na biyun abin hannun sa a gurin yarinyar nn, don Abie ne ya siya musu Shi da Azlan wani zuwa dubai da yai yasa aka musu iri daya guda biyu aka sa AJ a jiki ma'ana Azlan Junaid.



Hannun Junaid Abie ya rike ya Janye hannun rigar sa zaro ido nai ganin irin sa sak a hannun Mai kama da Mr Wicked, da sauri na matso kusa da shi don na kara tabbatar wa AI kuwa shine har AJ din iri daya komai da komai wani irin bugawa gabana yai da karfi.



Abie ne ya kalli Azlan yace "ina naka yake in baxan manta ba bayan bikin Junaid na tambaye Ka ina abin hannun ka bana ganin sa kace ballewa yai Ka kai gyara kusan shekara biyar knn ynxu ina yake toh ban sake ganin Ka da shi ba" 



Dagowa yai ya kalli Junaid sai ya kalli Abie baisan mai zai ce ba hakan yasa shi fadin "barayi ne suka sace", jiri na soma gani da sauri nayi baya ina fadin Innanillahi wa innanillaihir raji'un a hankali idona ya soma rufewa kawai sai gani sukai na zube a gun.



Aisha da Mimi kusan a tare suka taho gurina da gudu suna kuka, girgiza ni Mimi take tana fadin "Maaa kiyi hakuri baxan sake ba ki tashi"



Mami da Aunty sarah ne suka zo suka dago ni akan kujera suka kwantar dani, kallon Junaid Mami tai tace "zo ka duba min yarinyar nan Junaid mai ya same ta"



Da sauri Azlan ya janyo Junaid baya ganin yana nufar inda take, kallon Mami yai yace "Maa a Kira likita mace tazo ta duba ta mana ba dole sai Shi ba"



Tsaki Mami tai tace "Azlan bana son shirme don Allah ceto rayuwar yarinyar nan za'a yi har sai an wani tsaya jiran likita mace bayan ga doctor muna tare dashi"



Girgiza kai yai yace "Mami baxa ki fahimta ba kawai ya fada min abinda za'a yi a ceto ta ni sai na mata amma gaskia shi baxai taba ta ba maman Yarinya tace fah"



Kallon sa Baffa yai yace "zaki bana son gardama, kai Junaid jeka duba ta"



Kallon Baffa yake idonsa na sheki sbd tsabar bacin rai, sai hadiyar zuciya yake ji yake kamar ana Kwara masa ruwan zafi a kirji.



Kallon Junaid yai yace "Junaidu, Junaidu, Junaidu kaga so uku na kira Ka koh wallahi ko hannun ta Ka rike sai na karya ma shi don iskanci taya zaka taba mamar yarinya ta........."









***