1
by @nanadiso10
GUGUWAR RAYUWA 🌪️
(...kowa da inda ta kaɗa shi!)
NA NANA DISO
PAGE 1
Sautin marayan kukan da ke tashi a cikin ƙaramin ɗakin mahaifiyar tasu ne ya daki ƙirjinsa, ya tilasta wa saurin takun ƙafafunsa tsayawa cak!
Umar ya ja wani dogon numfashi mai ɗumi da gajiyar rayuwa, ya ɗaga labulen ɗakin a hankali, bakinsa ɗauke da sanyayyiyar sallama.
"Barka da dawowa Umar... sannunka da ƙoƙari."
Wani gajeren murmushin ƙaƙa-ka-yi-kuɗi ya subuce a laɓɓansa, murmushin da bai iya ratsa ko maƙogwaronsa ba, balle ya kai ga zuciyarsa. Ya taka a sanyaye ya zauna dab da ƙaninsa Ahmad, wanda ke ta faman rera kuka yana sauke numfashi da ƙarfi. Umar ya ɗora hannunsa a kafaɗar yaron, yana buga bayansa a hankali cikin tsananin tausayi
"Ahmad... me ke damunka haka? Ba fa na son ganinka cikin wannan halin."
Kafin Ahmad ya iya buɗe baki, Mama ta zabura daga inda take, idanunta na zazzaro wuta a fusace
"Ka ga Umaru Wallahi zan ci mutuncinka idan ka biye wa wannan shashancin na Ahmadu! Yaro gaba ɗaya ruɗin zuciya da kwadayi sun gama jirkita masa lissafi! To idan ba ruɗin zuciya ba, wane irin babban hauka ne wannan yake shirin aikatawa?"
Shiru Umar ya yi, kansa a ƙasa yana sauraron huci da kalaman da ke fita daga bakin mahaifiyar tasu. Bai ce ƙala ba, kuma Ahmad bai fasa rera kukansa mai gunji ba.
Suna cikin wannan zazzafan halin ne sautin takalmin mahaifinsu ya dira a zaure; tun daga can waje faɗan matar tasa ke dukan kunnensa. Da sauri Baba ya turo ƙofar ɗakin, yana kallon Zainabu da idanu cike da tambaya
"Zainabu, lafiyarki lau kuwa? Tun daga zaure nake jiyo wannan bala'in, menene ya faru haka?"
Kallonsa ta yi a hasale, ta ja wani nannayan tsaki mai sauti har sai da ƙirjinta ya ɗaga, sannan ta nuna Ahmad da ɗan yatsanta
"Ka duba wannan yaron mana, babansu! Tun ɗazu yake kuka saboda ruɗin zuciya irin tasa, wai lallai sai na sa baki Umaru ya ba shi tallafin karatun (scholarship) da ya samu zai je can waje ya yi digirinsa"
Dumm
Wani wawan bugu zuciyar Umar ta yi, tamkar za ta fasa ƙirjinsa ta faɗo ƙasa!
Take numfashinsa ya sarƙe, jikinsa ya ɗauki karkarwa. Duk irin wahalar da ya sha? Duk daren da ya raba yana neman wannan damar don ya fita ya yi digirinsa? Duk uƙubar da ya dandana? Maganar ta doke shi a inda ba ya zato, har sai da idanunsa suka cika da ƙwalla, wani zazzafan hawaye ya zubo a kumatunsa.
Ganin yadda Umar ke mugun son Ahmad wata irin soyayya mai ban tsoro da za ta iya sa shi sadaukar da numfashinsa ya sa Baba ya dube shi da sauri, ya juya ga Ahmad a tsawace:
"Ahmadu! Abin da mahaifiyarku ke faɗa da gaske ne?"
Ahmad ya ɗago kansa da idanunsa da suka riga suka kaɗa suka yi jajur saboda kuka. Wani irin fushi da tsiwa suka ba shi ƙarfin gwiwar zazzago maganganu yana huci
"To Baba, tunda na taso a gidan nan sai dai a ce in yi haƙuri don ni ne ƙarami, amma duk da haka ni ake zalunta! Kamata ya yi ku tilasta masa ya bar mini wannan damar, amma saboda shi kuka fi so..."
"Ubanka ne zai bar maka!" Muryar Mama ce ta daki ɗakin a zafafe. "Kai dai wannan mugun hali naka Allah ya raba ka da shi, Ahmadu! Yanzu duk sadaukarwar da Umaru ya yi maka a rayuwa sai da ka nuna maƙiyinka ne? Ka manta don ka samu ingantaccen karatu Umaru ya haƙura da makarantar kuɗi aka biya maka, shi kuma ya tafi ta gwamnati ya sha wuya? Duk abin da ya yi maka ruɗin zuciya ya sa ka manta? To wallahi mu zuba mu gani! Yadda kake da ƙafa haka yake da ita, don haka ka tashi ka fita ka nemo naka!"
Baba ya sauke wani nannayan numfashi mai cike da baƙin ciki, ya zauna a gefen shimfiɗa yana kallon Ahmad:
"Ban san ka da wannan halin ba, babana. Wannan ba halinka ba ne. Ina so ka yi haƙuri, ka sa wa ɗan'uwanka albarka. Ni kuma zan dage in ga na samar maka admission a kwalejin fasaha (polytechnic) irin wadda Umar ya gama. Don Allah ku yi haƙuri, Allah ya haɗa kanku."
Shi dai Umar ya yi mutuwar tsaye. Zazzaɓin da ke jikinsa ya haɗu da baƙin ciki, wani zazzafan gumi ya shiga tsatstsafo masa ta goshi yana karyewa.
Wace irin baƙar rana ce wannan a rayuwata? abin da yake ta maimaitawa a can ƙasan zuciyarsa kenan.
Caraf Ahmad ya cafko hannun Umar, yana wani irin kuka mai karkarwa da riƙe hannunsa gam
"Yaya babba... yayana, ɗan'uwana kuma masoyina! Na san ban yi maka adalci ba, amma don Allah..."
Wani ɗaci Umar ya haɗiye a maƙogwaronsa, ya kalli Ahmad, sannan ya tilasta wa kansa wani murmushi na sadaukarwar rai da jini
"Babu komai Ahmaduna... Komai zan iya yi dominka a duniyar nan. In har a kan wannan tallafin ne, to ka kwantar da hankalinka, ka tafi. In sha Allahu a can za ka zama wani babban mutum a ƙasar nan. Na bar maka shi har abada, kuma yanzu zan je in samu Alhajin na roƙe shi a sauya sunan."
Ahmad ya ƙanƙame Umar a ƙirjinsa, yana sakin kukan murna da kiran sunansa cike da godiya
"Allahu! Yayana, wallahi ka gama mini komai a rayuwa!"
Mama ta zaro ido, jijiyoyin wuyanta suka fito radau saboda ɓacin rai
"Umaru, ba ka da hankali ne Wannan wace irin maganar banza ce kake yi?"
Murmushi ya ƙara yi a karo na biyu cikin sanyin rai
"Mama, ai ba ki koya mini son kai ba. Ba ke kika koya mana cewa mai buƙata shi ne a gabanmu ba? Ni zan ci gaba da jarrabawa a jami'o'in gida, idan rabo na ne zan samu; idan kuma babu, sai in dage da ƙaramar sana'ata."
Wani irin tausayinsa mai zafi ya mamaye ɗakin. Baba ya kauda kansa gefe yana wani busashen murmushi mai cike da jimami, ba tare da ya iya cewa komai ba.
Duk da yadda zazzaɓin jikinsa ke ƙoƙarin kayar da shi, Umar bai runtsa ba har sai da ya isa ƙaton falon Alhaji Wada. Ya yi sa'a kuwa aka yi masa iso.
"Barka da yamma, Alhaji."
"A'a, Umar, har an gama shirye-shiryen tafiyar ne?"
"A'a, Alhaji... wata alfarma nazo nema. Don Allah don Annabi, a sauya sunana daga cikin masu tafiya, a sanya sunan ƙanina Ahmad a maimakona."
Alhaji ya zuba masa ido cike da mamaki da nazari
"Amma Umar, anya wannan shawarar mai kyau ce kuwa?"
"Don girman Allah ka taimaka mini, Alhaji."
Alhaji ya ja wani dogon numfashi
"Babu matsala. To ya hanzarta ya yi fasfo da duk abubuwan da na gaya maka ya kawo. Amma..."
Sai kuma ya dakata, ya zuba wa Umar ido da wata irin fuskantar tausayi ba tare da ya ƙara magana ba.
Godiya sosai Umar ya yi masa, sannan ya fito. Yana shiga wani lungu a unguwar tasu, ya jingina bayansa da bango, ya kifa kansa a cinyoyinsa ya sha kukansa har sai da numfashinsa ya fara fita da ƙyar. Ya goge hawayensa ya nufi gida, inda ya tarar Mama ta sake cin mutuncinsa a kan dubu hamsin ɗin da ya ɗauka ya ba Ahmad don ya je ya yi fasfo. Ahmad kuwa a ranar ko gani ba ya yi saboda tsananin murna.
"Habu, wallahi ya amince fa!" Ahmad ya faɗa yana washe baki cike da murna.
"Ai dama na faɗa maka zai yarda! Yayan nan naka ai ɗan Aljanna ne."
"Amma Habu... wani lokacin idan na duba sai in ga kamar ban kyauta masa ba sam, kamar na zama wani..."
"Dalla daina wannan shiriritar Ahmad! Rabonka ne kawai. Babban abin da ke gabanka shi ne ka je ka dage ka yi karatu, shikenan."
"In sha Allahu! Ko don faɗan Mama ma sai na dage, don yadda take kallona ji take tamkar ta haɗiye ni ɗanye."
"Ɗan ubanki! Daga ina kike ne Kausar? Tun yaushe aka tashi a makarantar da har kika kwaso wannan daren? Ina kika tsaya? Ni fa ba na son fitsara da iskanci, dama na ga kuna shigewa da Hafsatu yanzu"
Kausar da duk unifom ɗinta ya sha datti, ita ma fuskarta ta yi ƙura fururu, ta turo baki gaba tana zumbura
"Ita Yaya Surayya ba ta laifi ne a gidan nan Inna? Na ga ita ya kamata ki tsaya ki tuhuma a kan daɗewar da take yi a waje ba ni ba, ni da da an tashi nake tahowa gida."
"Za ki yi mini shiru ko sai na fasa miki wannan tsinannen bakin naki marar kunya? To ai kece marar kamun kai! Duk layin nan wanene bai san rashin kunyarki ba da fitsara? Ita Surayya ai kowa ya san ustaziya ce mai hankali, ke kuwa kullum kina yawon gantali..."
***
***