GUGUWAR RAYUWAFree

ArewaPen original

Short StoryFreeOngoing

GUGUWAR RAYUWA

  • 1views
  • 5chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Writer ce

More from @nanadiso10

Sample · 1

​GUGUWAR RAYUWA 🌪️(...kowa da inda ta kaɗa shi!)​NA NANA DISO​PAGE 1​Sautin marayan kukan da ke tashi a cikin ƙaramin ɗakin mahaifiyar tasu ne ya daki ƙirjinsa, ya tilasta wa saurin takun ƙafafunsa tsayawa cak!  ​Umar ya ja wani dogon numfashi mai ɗumi da gajiyar rayuwa, ya ɗaga labulen ɗakin a hankali, bakinsa ɗauke da sanyayyiyar sallama.  ​"Barka da dawowa Umar... sannunka da ƙoƙari."  ​Wani gajeren murmushin ƙaƙa-ka-yi-kuɗi ya subuce a laɓɓansa, murmushin da bai iya ratsa ko maƙogwaronsa ba, balle ya kai ga zuciyarsa. Ya taka a sanyaye ya zauna dab da ƙaninsa Ahmad, wanda ke ta faman rera kuka yana sauke numfashi da ƙarfi. Umar ya ɗora hannunsa a kafaɗar yaron, yana buga bayansa a hankali cikin tsananin tausayi"Ahmad... me ke damunka haka? Ba fa na son ganinka cikin wannan halin."  ​Kafin Ahmad ya iya buɗe baki, Mama ta zabura daga inda take, idanunta na zazzaro wuta a fusace"Ka ga Umaru Wallahi zan ci mutuncinka idan ka biye wa wannan shashancin na Ahmadu! Yaro gaba ɗaya ruɗin zuciya da kwadayi sun gama jirkita masa lissafi! To idan ba ruɗin zuciya ba, wane irin babban hauka ne wannan yake shirin aikatawa?"  ​Shiru Umar ya yi, kansa a ƙasa yana sauraron huci da kalaman da ke fita daga bakin mahaifiyar tasu. Bai ce ƙala ba, kuma Ahmad bai fasa rera kukansa mai gunji ba.  ​Suna cikin wannan zazzafan halin ne sautin takalmin mahaifinsu ya dira a zaure; tun daga can waje faɗan matar tasa ke dukan kunnensa. Da sauri Baba ya turo ƙofar ɗakin, yana kallon Zainabu da idanu cike da tambaya"Zainabu, lafiyarki lau kuwa? Tun daga zaure nake jiyo wannan bala'in, menene ya faru haka?"  ​Kallonsa ta yi a hasale, ta ja wani nannayan tsaki mai sauti har sai da ƙirjinta ya ɗaga, sannan ta nuna Ahmad da ɗan yatsanta"Ka duba wannan yaron mana, babansu! Tun ɗazu yake kuka saboda ruɗin zuciya irin tasa, wai lallai sai na sa baki Umaru ya ba shi tallafin karatun (scholarship) da ya samu zai je can waje ya yi digirinsa"  ​Dumm​Wani wawan bugu zuciyar Umar ta yi, tamkar za ta fasa ƙirjinsa ta faɗo ƙasa!  ​Take numfashinsa ya sarƙe, jikinsa ya ɗauki karkarwa. Duk irin wahalar da ya sha? Duk daren da ya raba yana neman wannan damar don ya fita ya yi digirinsa? Duk uƙubar da ya dandana? Maganar ta doke shi a inda ba ya zato, har sai da idanunsa suka cika da ƙwalla, wani zazzafan hawaye ya zubo a kumatunsa.  ​Ganin yadda Umar ke mugun son Ahmad wata irin soyayya mai ban tsoro da za ta iya sa shi sadaukar da numfashinsa ya sa Baba ya dube shi da sauri, ya juya ga Ahmad a tsawace:"Ahmadu! Abin da mahaifiyarku ke faɗa da gaske ne?"  ​Ahmad ya ɗago kansa da idanunsa da suka riga suka kaɗa suka yi jajur saboda kuka. Wani irin fushi da tsiwa suka ba shi ƙarfin gwiwar zaz...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters5
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play