GUGUWAR RAYUWA

2

by @nanadiso10

GUGUWAR RAYUWA 🌪️
(...kowa da inda ta kaÉ—a shi!)

​NA NANA DISO

​PAGE 2

​"Yawon gantali dai! Allah ya shiryeki!"
​Muryar Inna ce ta daki zauren a hasale. Kausar da ke tsaye a bakin ƙofa ta turo baki gaba tana zumbura, ta amsa a tsiwace:
"Inna, Allah dai ya shirye mu za ki ce, ba ni kaÉ—ai ba!"  
​Cikin zafin nama Inna ta yo kanta gadan-gadan tana shirin sauke mata mari. Kausar ta zabura da baya a tsorace, sai dai kafin Inna ta iso, aka turo kyauren zauren da ƙarfi. Malam ne ya bayyana tsaye! Ganinsa ya sa Inna jan birki da sauri tana huci
"Zan gama da ke ne yarinya!"  
​Dariya ce ta kufce wa Malam ganin yadda Kausar ta lafe jikin bango, tana zare jajayen idanunta a firgice. Maimakon ya dake ta kamar yadda take zato, sai ya mika hannu ya janyo ta jikinsa yana shafa kanta
"Uwata... ban hana ki fitsara ba?"  
​Shiru Kausar ta yi tana sauke ajiyar zuciya a jere, har ya samu wuri ya zaunar da ita a kusa da shi. Inna kuwa ta É—ebo ruwa a kofi ta kawo masa, ta zauna dirshan a gefe tana watsa wa Kausar hararar da ke cike da Ć™una.  
​"Ina fata dai lafiya, Malam? Na gan ka da wuri haka yau?"  
​Malam ya yi shiru na wasu daƙiƙu, fuskarsa ɗauke da matsananciyar damuwa. Ya ɗago idanunsa da suka sauya launi, ya dubi matar tasa
"Innar Kausar... akwai babbar matsala. Malamin yaran nan ne ya kira ni a kan Surayya. Ya ce kusan sati biyu kenan ba ta zuwa makarantar Islamiyya! Tambayar da nake son yi miki shi ne: ko ke kika hana ta zuwa? Na san yarinyata da hazaka, Ć™oĆ™arin karatu, da son ilimi. Idan har ke kika hana ta zuwa, to ina tabbatar miki raina zai É“aci Ć™ololuwa a kan wannan maganar!"  
​Wani wawan bugu ƙirjin Inna ya yi, numfashinta ya kusan ɗaukewa saboda firgici! Sai dai da yake tana son rufa wa ɗiyarta asiri ko ta halin ƙaƙa, sai ta daure ta washe baki tana cewa
"Haba Malam! Ashe ban gaya maka ba ne? Kullum da yamma take dawowa da matsanancin ciwon ciki, ga wannan boko tasu da suke yawan tara su wai ana musu lissafin lesson, shi ya sa! Amma a ba Ustaz haĆ™uri, in sha Allahu yau yau É—in nan za ta koma."  
​Kausar da ke gefe, duk da shayin da take ji, sai da ta kasa haƙuri ta yi caraf
"Malam, ai Yaya Surayya ba wani lissafi da ake..."  
​Tas!
​Wani zazzafan dĹ«ka Inna ta kai wa bakin Kausar har sai da ta saki Ć™ara. "Tashi ki ba mu wuri mara mutunci!"  
​"Kar ki Ć™ara dukanta!" Malam ya daka mata tsawa yana miĆ™ewa da sauri, rai a É“ace ya fice ya nufi gonarsu.  
​Gaba É—aya natsuwar Inna ta É—auke tun daga lokacin da Malam ya sa Ć™afa ya fice. Mamaki da fargaba suka turniĆ™e zuciyarta, amma sai ta danne, tana jiran ganin ta ina Surayyar za ta É“ullo.  
​"Binta, wallahi mugun tsoro nake ji... Ba ki ji yadda hantar cikina ke kaÉ—awa ba!"  
​Surayya ta faÉ—a tana karkarwa, hawaye na silalowa daga idanunta tana gogewa da mayafi. "Duba fa, magriba ta kusa yi amma ban koma gida ba! Me zan ce wa Inna?"  
​Alhaji ne dai har yanzu bai fito daga ofis ba wai yana da baƙi. Binta ta watsa mata wata shegiyar harara
"Idan kina saka wannan tsoron na banza, wallahi ba za ki taÉ“a jin daÉ—in wannan harkar ba! Kin ga wannan tsohon akwalon gidan naku? Har shi sai kin sauya wa su Malam! Sau É—aya kawai zai É—an taÉ“a ki, ki ga maĆ™udan kuÉ—in da zai antaya miki. Ke za ki huta Ć™awata, dama ga ki da diri mashaaAllah!"  
​Kafin Surayya ta yi wani numfashi, Ć™ofar wani Ć™aramin ofis da ya sha tsatsa ta buÉ—e da Ć™ara. Wani alhaji ne ya fito mutumin da tsufansa ya kusa kai na Malam! Fuskarsa danye, baĆ™in bakinsa da ya sha taba ya sa Surayya firgita har sai da tsigar jikinta ta tashi.  
​Cikin wani irin shegen farin ciki mutumin ya buɗe baki
"Bintutu! Bintutu, ashe kin cika alƙawari?"
"To me zai hana, ranka ya daÉ—e? Ai dole ne a kawo maka abin raruma."
"Hahaha! Gaskiya ne Bintutu... Ina fata dai 'yar hannu ce?"
"Ina ranka ya daÉ—e, sabuwa ce fil-fil!"  
​Wani zabura Alhajin ya yi yana gyara zaman rigarsa, lafazin Binta ya ratsa shi har cikin É“argon jiki. Surayya ta kasa ko da É—aga idanunta ne ta dube shi saboda tsananin kunya da mamaki.  
​Muryarsa ta ji a kanta tana raɗa
"Baby girl... gobe sai kin zo, kin ga wurin ai ko?"  
​Jinjina masa kai kawai ta yi cikin rawar jiki. Suka miƙe zasu tafi, sai Alhajin ya ciro 'yan kuɗi masu kauri ya miƙa musu—dubu biyar cif! Idanun Surayya suka kusan fitowa waje saboda ganin wannan uban kuɗi a lokaci guda. Duk da razanar da ke zuciyarta, wani irin shegen daɗi ya ratsa ta
"Yanzu Bintu... dubu biyar fa ya bamu?"
"Ke ƙawata, ki saki jiki ki sha daɗi a duniya!"
"To me zan ce wa su Malam? Duba fa ƙarfe tara ta kusa yi!"
"Ki ce musu 'yan daba ne suka tare ku a hanya! Kinsan yadda Malam da Inna suka amince da ke, duk abin da kika faÉ—a musu gasgatawa zasu yi."  
​A bakin titi suka raba kuÉ—in Surayya ta riĆ™e dubu uku. Yana daidai Ć™ofar gida ta maĆ™ale kuÉ—in a can Ć™asan jakar makarantarta. Tana tura Ć™ofar gida, ta fashe da wani irin gigitaccen kuka mai ban tausayi! 
​Malam da Inna da ke zaune sukuku a tsakar gida suna jiranta suka zabura a tsorace
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Menene ya faru, Surayya?"  
​Ganin yadda suka tsure ya ba ta damar ƙara ƙarfin kukanta. Ta faɗa jikin Malam ta ƙanƙame shi tana rera kuka. Tausayin ɗiyar tasa ya sa shi ma Malamin hawaye ya wanke masa fuska! Sai da Inna ta tsawata musu sannan suka ɗan natsa, suna maimaita tambaya

"Malam... yau hanyar ba ta da kyau ko kaÉ—an! 'Yan daba ne suka tare mu, da Ć™yar muka shaĆ™u bayan sun lakaÉ—a mana dĹ«ka..."  
​Wani zazzafan tausayi ya turniĆ™e zuciyar iyayen nata. Malam ya shiga lallashinta yana kwarara mata addu'o'i. Saboda tsabar amincewar da suka yi mata, ko tantama É—aya ba su yi a kan Ć™aryar da ta shirya musu ba.  
​Ta sulale ta shige É—aki ta kwanta. Ko sallar da ba ta yi ba bai dame ta ba, domin kalaman Binta ne ke mata gizo a kunne: "Ke Ć™awata, ki daina damun kanki a kan sallah, ita fa rahama ta Allah ce." Duk tarin karatun hadisai da ta sani, kalaman Binta suka rinjaya, har ta ja mayafi tana faÉ—in wai sai gobe da safe za ta rama.  
​"Surayya! Ustaz ya kawo ƙararki!"
​Muryar Inna ta daki kunnen Surayya a lokacin da take saka takalmi washegari. Ta ɗago da sauri tana kallon mahaifiyarta, fuskarta ɗauke da dabara:
"Inna, Ć™yale rigimar Ustaz mana! Wai don ban kai masa hadda ba ne ya ce zai gaya wa Malam wai bana zuwa, saboda shi a ganinsa babu amfanin zuwa tunda na kasa haddar!"  
​Inna ta saki wata nannayar ajiyar zuciya, ranta ya yi fari sarai
"To ku dai dage da karatu! Don ba na son ku zama irin yaran unguwar nan da suka zama 'yan iska da jahilai!"  
​Kausar da ke tsaye gefe mamaki ya gama kashe ta, domin ita ce babbar shaidar cewa Surayya ba ta taɓa zuwa makarantar ba. Jin irin zagaye-zagayen da Inna ke yi ya sa Kausar cewa
"Wai Inna, shiriya a hannunki take ne da kullum kike zagin 'ya'yan wasu? Haba..."  
​Wani wawan dĹ«ka Inna ta kawo mata da nufin fasa mata baki, Kausar ta goce da gudu tana faÉ—in "A ba ni kuÉ—in littafi na tafi makaranta!"  
​Inna ta dafe ƙirji tana kallonsu
"Kausar! Kun san dai halin da ake ciki a yau ko? Ko abincin safe ba a samu ba a gidan nan, babu ko sisi! Malam tun É—azu ya fita wajen gari ko zai samo mana ko na kunu ne."  
​Wannan kalmar ta daki Ć™irjin Surayya. Wani irin ruÉ—i da shaiÉ—anci suka shiga raÉ—a mata a rai: 'Kin ga? Talaucin nan ya isa ya zame miki hujjar neman kuÉ—i ko ta halin Ć™aĆ™a!'  
​Ta daure ta kalli Inna cikin lallashi
"Inna, kada ki damu. Akwai 'yan canji a wurina, zan ba Kausar sai mu sayi abin karin kumallo a makaranta."
Albarka Inna ta shiga kwarara mata har suka fice daga gidan.  
​A kan hanya, Surayya ta kalli Binta cikin mamaki
"Wai Binta, ta yaya Principal yake barin mu muna fita a lokacin makaranta haka?"
Binta ta yi sheƙeƙe tana murmushi
"Ke Surayya, ai na hannuna ne! Shi ya sa babu wanda ya isa ya tsawata mana."  
​Surayya ta yi tsit, har suka isa Ć™ofar ofishin mutumin. Suna shiga, Alhajin ya miĆ™e jikinsa na karkarwa yana mika mata hannu!  
​Dasss!
​Zuciyar Surayya ta shiga bugawa a tsorace tamkar za ta fasa Ć™irjinta! Numfashinta ya tsaya cak. Anya ba halaka take tura kanta ba? Anya za ta iya jure wa wannan ruÉ—in? Anya ba baĆ™ar kaddara ba ce take shirin aikatawa? Anya...  
​Kafin ta ankara, ta ji mutumin ya cafko ta da Ć™arfi, ya maĆ™ale ta a bango yana Ć™oĆ™arin sumbatar bakinta!  
​Wani irin matsanancin firgici ya sa ta zabura ta yi baya da Ć™arfi, amma aikin gama ya riga ya gama! Daga nan sai ga Surayya a Ć™asa tana faman wani irin kuka mai karkarwa tana kiran "Na shiga uku! Na lalace!"  
​Mutumin ya fashe da wata muguwar dariya yana gyara rigarsa, ya ɗaga ta a hankali yana raɗa mata
"Kwantar da hankalinki baby girl... Yanzu ne ma kika fara ganin daÉ—in duniya! Wannan ganimar da kika kawo mini zan É—aukaka ki a kanta."  
​Ya ciro damin kuÉ—i masu kauri ya ajiye a gabanta dubu hamsin cif na sababbin kuÉ—i!  
​Ganin wannan uban kuɗi ya sa Surayya rikicewa gaba ɗaya! Ga wani zazzafan raɗaɗi da ƙuna da ke ratsa tsakiyar ƙashin ƙugunta, ga tsananin azaba, amma ganin damin kuɗin ya sa ta share hawayenta da sauri ta miƙe tana washe baki cikin rawar murya
"Duk nawa ne wannan, ranka ya daÉ—e?"  
​Mutumin ya kwashe da wata shu'umar dariya
"Wannan na É—anÉ—ano ne kawai! Har gida da mota kin kusa siya yarinya!"  
​Murmushi ta saki a gigice, ta kwashe kuÉ—in ta fito daga ofishin tana É—ingishi da Ć™yar saboda azaba.  
​Tana isa daidai Ć™ofar gidansu, ta kifa kanta a jikin kyaure ta kwalla wata gigitacciyar Ć™ara mai firgitarwa! Malam da Inna suka fito a guje suna salati, suka nufota a tsorace suna kallon yadda take takawa da Ć™yar tana dūƙewa...  
​Cikin wani irin kuka mai ban tausayi Surayya ta buɗe baki da ƙyar tana nishi
"Mai... mai mashin ne..."