GUGUWAR RAYUWA

Page 3

by @nanadiso10

GUGUWAR RAYUWA 🌪️
(...kowa da inda ta kaɗa shi..)


​NANANA DISO

​PAGE 3


​"Mashin ne... mashin ne ya buge ni!"
​Kukan da ke cin maƙogwaronta ya kufce a gigice, kafafunta suka gaza ɗaukar gangar jikinta, ta zube a ƙasa tana faman karkarwa.
​Malam ya zabura a ruɗe, ya tallafo hannayenta biyu ya miƙar da ita da ƙyar har zuwa kan tabarma, ya zaunar da ita yana sauke numfashi cike da fargaba. Inna kuwa, tuni hawaye ya gama wanke mata fuska sharkaf saboda gigita; jikinta na ɓari ta garzaya soro ta ɗora ruwan zafi a murhu, ta dawo tana mammatsa ƙafar Surayyar da zazzafan ƙyalle.
​Yadda iyayen nata ke tsaye a kanta suna faman nishi da jimami ya daki ƙirjin Surayya da wani zazzafan tausayinsu. Can ƙasan ranta, wata zuciyar na tsikayarta: ‘Kin ga irin muguwar yaudarar da kike tafka musu kuwa?’ Sai dai a take, wata shaiɗaniyar zuciyar ta buɗe mata wani sabon shafi ‘Wannan ita ce kaɗai hanyar samun ƴancinki da wadata, har ki share wa iyayenki hawayen talaucin da ke neman kashe su!’
​Muryar Malam mai rauni ce ta datse mata wannan saƙar zuci
"Daga yau... ni da kaina zan riƙa kai ki makaranta, kuma ni zan riƙa zuwa ɗaukarki da kaina! Surayya, ke ce babba fa a gidan nan, amma me ya sa kike neman yin wasa da rayuwarki haka?"
​Wani guntun murmushi mai cike da baƙin ciki da zubar hawaye ya subuce mata. Ita kaɗai ta san wane irin rami take haƙawa kanta tabbas, guguwar rayuwa ta riga ta gigita mata tunani! Ta ɗago idanunta da suka kaɗa suka yi jajur, ta kalli Malam cikin lallashi:
"Malam... ashe ba ka yarda da ƙaddara ba ne? Allah Yana iya jarrabar bawansa a duk lokacin da Ya so. Ni dai kawai addu'arku nake buƙata."
​Take jikin Malam ya yi sanyi lakwas. Wani irin alfahari da haushin tausayin ɗiyar tasa suka mamaye shi.
​Inna kuwa da ke faman huci, tana matse ƙafar Surayya, sai ta kasa haƙuri da abin da ke cin ranta ta ce
"Malam, wai ba ka ji labarin Larai ba jiya? Kai, ita dai Larai ko wane irin zunubi ta aikata a rayuwa oho, amma 'ya'yanta duk sun zama cikakkun karuwai! Jiya da idona na ga wani ƙasaitaccen alhaji a mota ya sauke ɗiyarta a ƙofar gida. Kai! Allah wadai da irin tarbiyyar da iyaye irin su Larai ke bayarwa..."
​Ranka ya daɗe, take ran Malam ya ɓaci ƙololuwa! Duk da tarin kyakkyawan halin matarsa, amma wannan mugun ɗabi'ar ta gulma da zagin 'ya'yan wasu tana matuƙar kona masa rai. Cikin ɓacin rai da tsawa ya daka mata tsawa
"Innar Kausar! Wai ke ba za ki taɓa iya kame bakinki ba ne ko sau ɗaya a rayuwarki?! Kullum ke a cikin tsinewa da aibata 'ya'yan wasu kike! Ba kya tsoron ranar da Allah zai iya jarrabarki da abin da ya fi wannan muni? Ko ke kika bai wa naki 'ya'yan tarbiyya da kanki, ba kika san duk daga Ubangiji yake ba?!"
​"Ji mini Malam da wata maganar banza!" Inna ta amsa a hasale tana murguɗa baki. "Don Allah wanene a unguwar nan bai san tsaftar tarbiyyar 'ya'yana ba, bama kamar Surayya? Kaf layin nan babu wadda ta kai ta natsuwa da kamun kai! Don haka ka daina haɗa mini zuriya da 'ya'yan karuwai, na dai gaya maka!"
​Surayya da ke kwance tana sauraron kalaman mahaifiyarta, wani irin sanyi ne ya ratsa mata kashin baya. Tabbas, yau ita ma ta riga ta tura ƙafarta a sahun karuwan! Kuma ta tabbatar gazawar buƙatun rayuwarsu da wannan muguwar dabi'ar ta Inna ta zagin 'ya'yan wasu na daga cikin abin da ya tura ta wannan muguwar hanyar.
​Bakin Ahmad ya kasa rufuwa farin ciki da annashuwa sun sa shi tamkar yana shawagi a gajimare! Yau zai bar ƙasar gaba ɗaya, zai tafi birnin Landan (London) domin faɗaɗa karatu! Wannan bawan Allah, Alhaji Wada, hakika ya gama masa komai. Ya gama shirya kayansa tsaf, ya fito tsakar gida inda iyayensa ke zaune jugum suna dakon fitowarsa.
​Umar ne ke riƙe da babbar jakar kayan Ahmad. Idanun Umar sun yi jajur, ƙwalla na ta sintiri a cikinsu, domin a ransa yana jin kamar wannan ita ce rabuwarsu ta har abada.
​Malam ya dube shi cikin fushi-fushi yace
"Umaru, menene haka sai ka ce wani ƙaramin yaro? Wannan kukan na meye kuma?"
​Mama da dama tun asali ba ta son wannan tafiyar ba, ta kalli Malam ta ce
"Ka bar shi ya yi kukansa don Allah!"
​Ahmad ya ƙarasa da sauri ya rungume Umar tsam a ƙirjinsa, yana sakin kuka da kwarara masa addu'o'in da ke fitowa daga can ƙasan zuciyarsa
"Ahmad... don Allah ka sa mu yi alfahari da kai," muryar Umar na rawa, hawaye na wanke masa kunci. "Ka dage ka yi karatu da gaske. Don Allah kar ka canza halinka Ahmad! Na fi kowa sanin zuciyarka; ina so a ranar da ka gama karatunka, ka dawo mana da murmushi a fuskokinmu a lokacin da muka ga shaidar kwalin karatunka."
​"Yaya, in sha Allahu ba zan ba ku kunya ba!" Ahmad ya faɗa yana share ƙwallar da ke idonsa. "Amma don Allah ka daina kukan nan Yaya, addu'a nake so ka riƙa yi mini. Kuma ina roƙon Ubangiji Ya haskaka rayuwarka kamar yadda ta sanadin sadaukarwarka tawa rayuwar za ta haskaka!"
​"Nidai babban burina ka riƙe mutuncinka, ka yi karatu kawai," Umar ya faɗa yana sauke nannayan numfashi.
​Nan take Baba ya shiga yi wa Ahmad faɗa mai ratsa jiki a kan kiyaye abokan banza da guje wa shashancin rayuwa. Mama dai tana gefe ta yi tsit, har sai da Ahmad ya duƙa ya damƙi hannayenta biyu
"Haba Mamana... kar ki yi fushi da ni mana! Idan kika yi fushi, ba zan taɓa samun albarka da jin daɗin karatun nan ba. Don Allah ki ɗauki wannan lamarin a matsayin ƙaddarar Ubangiji, ki sa mini albarka kin ji?"
​Murmushin ƙunar rai Mama ta yi, saboda tuna gargaɗin da Malam ya yi mata a kan cewa idan ta ci gaba da nuna Ahmad bai cancanta ba, za ta raba kan 'ya'yanta ne. Ta ɗago kanta, hawaye na silalowa a fuskarta tace
"Na yafe maka, Ahmadu. Allah Ya yi muku albarka gaba ɗaya, Ya kuma ba ka abin da ka je nema. In sha Allahu sai ka yi fice a duniya! Amma ina roƙon Allah Ya tsare mini kai daga sharrin fitinar matan duniyar nan..."
​"Ameen!" kowa ya amsa a tare, kafin suka dunguma aka nufi filin jirgi (airport) don yi masa rakiya.
​Bayan tashin jirginsu, duk yadda Umar ya so ya danne baƙin cikin da ke turniƙe a maƙogwaronsa, sai da ya kifa kansa a gefen mota ya sha kuka kamar ransa zai fita. Tabbas, komai rabo ne a rayuwa! Ya goge hawayensa, ya sa a ransa cewa shi ma in sha Allahu zai dage ya nemi admission a nan Jami'ar Ahmadu Bello (ABU Zaria), tunda Alhaji ya yi alƙawarin taimaka masa da gurbin karatu. Ya miƙe a sanyaye ya fice domin zuwa makarantar Islamiyyar da yake koyarwa.
​"Larai! Na ce ba me zai hana ki yi wa yaranki aure ki huta da wannan baƙin fentin da suke shafe miki a gari ba?"
​Larai da ta riga ta saba da halin Innar Kausar sai ta bi ta da dariya kawai ba tare da ta ce komai ba. Kwatsam, sai ga ɗaya daga cikin 'ya'yan Larai ta fito daga zaure a guje tana kwarara amai!
​"Oh ni 'yasu! Har kin kwaso wani cikin kenan?!"
​Inna ta faɗa da ƙarfi tana tofa tofin tsinuwa, sannan ta sa ƙafa ta fice daga gidan a guje domin ta kai gulmar cikin layuka. Haka kuwa aka yi; sai da ta bi gidaje bakwai cif tana watsa wannan labarin, kafin ta dawo gida ta tarar da su Surayya sun gama shiryawa tsaf.
​"Ke Surayya! Wallahi-wallahi idan na ƙara ganinki da 'ya'yan Larai... ko da yake ai ke ba irinsu ba ce! Na ma ba ki izini ki riƙa yi musu wa'azi, yanzu duba ki ga har ƙaramar ta kwaso wani shegen ciki a waje!"
​Kausar da haushin halin mahaifiyarta ya gama isarta, ta ja tsaki a ƙasan ranta ta sa kai ta fice daga gidan. Surayya kuwa, wani zazzafan sanyi ne ya ƙara ratsa mata zuciya, ta bi bayan Kausar a sanyaye.
​A aji, Surayya ta tarar Binta ba ta zo makaranta ba. Sai kawarta Hindu ce kawai ke zaune. Ganin Surayya shi kaɗai ya sa fuskar Hindu washewa da wani shegen murmushi. Ta tashi ta dawo kusa da Surayya ta zauna a benci ɗaya, ta kama hannunta tana matsawa a hankali:
"Ina son mu ƙulla ƙawance mai ƙarfi da ke, Surayya... Ina da manyan masu kuɗi a hannuna da zasu iya ba ki mota da gida na alfarma! Amma kafin nan... sai kin biya mini buƙatata tukunna."
​"Wace irin buƙata kuma?" Surayya ta tambaya cikin fargaba.
"Ina so ki zo mu kwana tare a gidanmu yau da daddare."
Surayya ta zaro ido tana kallonta da matsanancin mamaki:
"Ke ba kya da iyaye ne a gidan naku?"
Hindu ta saki wata shu'umar dariya:
"Kenan kina tsoron matsalar iyayenki ne?"
"Sosai ma kuwa!" Surayya ta amsa a tsorace.
"Ba ki da wata matsala yarinya! A yau ɗin nan za a rufe musu baki, su zuba miki ido ki ci karenki ba babbaka!"
​Wani guntun murmushin kwadayi ya subuce a fuskar Surayya, ta miƙe ta bi bayan Hindu har suka fice daga aji. Kai-tsaye ofishin Principal suka nufa. Yana ganin Hindu da Surayya, ya washe baƙin bakinsa da ya sha taba dama ya daɗe yana cizon yatsa da maƙwadaicin kallo a kan Surayya, ashe yau ita ma ta shigo tarkonsu!
​"Mutumina, mu za mu wuce wani wuri yanzu, akwai lokacinka da daddare fa," cewar Hindu tana wani lankwasa murya.
Principal ya lashe baki yana kallon Surayya da idanu cike da sha'awa:
"Kin ce an samu sabuwar leda kenan? Yaushe za a bar ni in ɗanɗana?"
"Sai ka zazzage mata account ɗinta mana! Ka ga oga, ba mu da lokaci yanzu za mu wuce. Amma ka tabbatar ka yi passing ɗinmu a wannan test ɗin!"
​Da wannan maganar Hindu ta janyo hannun Surayya suka fice.
​Suna fitowa waje, Surayya ta saki baki da hanci ganin yadda Hindu ta buɗe wata ƙaramar mota ta shiga! Wani irin tsoro da ɗoki suka turniƙe Surayya, har sai da Hindu ta daka mata tsawa "Shigo mana ki tsaya kina kallo!"
​Surayya ta faɗa motar tana waige-waige
"Wai Hindu, kina nufin wannan motar taki ce ta kanki?!"
Hindu ta ja wani dogon birki tana juya sitiyari da ƙwarewa
"Ke kanki za ki iya wuce haka wajen tara dukiya Surayya! Babban abin da nake buƙata a wajenki shi ne ki ba ni haɗin kai kawai."
‘Haɗin kai ai dole in ba ki shi!’ Surayya ta ayyana a ranta tana wani shu'umin murmushi. ‘Tunda wannan ita ce hanyar samun abin da nake buƙata, ni ma zan zama lamba ɗaya a bariki, in zama shahararriyar mai dukiya!’
​Ba su tsaya a ko'ina ba sai a wani lungu mai duhu da ban tsoro. Suna shiga wani ƙaramin ɗaki, suka tarar da wani tsohon boka a zaune, ƙasa a baje a gabansa.
​Hindu ta duƙa tana faɗin
"Malam, na kawo aminiyata ce. Ina so a ba ta maganin sa'a da daukaka, sannan ka rufe bakin iyayenta su daina ganin laifinta!"
​Bokan ya ɗago kansa da idanunsa da suka kaɗa suka yi jajur, ya gyara zama
"Aikinku zai ci naira dubu ashirin cif."
"Babu matsala!" Hindu ta amsa ba tare da fargaba ba.
"Ke... yaya sunanki da na iyayenki?" bokan ya tambayi Surayya da murya mai kwarjini da ban tsoro.
"Sunana Surayya. Babana Yakubu, mahaifiyata kuma Asma'u."
​Bokan ya miƙo mata wata ƙaramar laya da wata kwalbar ruwa mai launin ban-tsoro
"Ga wannan layar; ko da yaushe ta kasance a cikin kanki ko ɗaurin ɗankwalinki! Wannan ruwan kuma, ki tabbatar kin zuba shi a inda iyayen naki ke kwanciya barci! Ba za su taɓa iya jayayya da ke ba, kuma ba za su taɓa iya tsawatar miki a kan duk abin da kika aikata ba!"
​Godiya suka yi masa sannan suka fice. Kai-tsaye gidan su Hindu suka nufa. A ƙofar gida suka tarar da mahaifin Hindu a zaune, amma ko kallo ba su ishe shi ba, haka suka raɓa ta gefensa suka wuce ɗaki!
​Suna shiga ɗakin, Hindu ta rufe ƙofa ta fara janye mayafin Surayya tana mata kalaman da suka gama jirkita mata tunani... har sai da Surayya ta biye mata, suka tafka wata mummunar ta'asa ta luwaɗi da maɗigo! Duk da wani irin mugun ɗaci da amai da zuciyar Surayya ke yi mata, hakan bai sa ta fasa ba, domin son kuɗi ya riga ya toshe mata dukkan wata kofa ta tunani.
​Bayan sun yi wanka, Hindu ta ɗauko mota ta mayar da ita har ƙofar gidansu. Ta damƙa mata damin kuɗi dubu ɗari cif tana cewa
"Gobe ki fito da wuri, akwai wani hamshaƙin alhaji da zan haɗa ki da shi!"
​Surayya ta amsa da "To" tana rawar jiki saboda ganin dubu ɗari a hannunta, sannan ta tura ƙofar gida.
​Abin mamaki, duk da sallamar da ta yi, Inna da ke tsakar gida ko ɗaga kai ba ta yi ta kalle ta ba! A take Surayya ta gane cewa aikin boka ya fara aiki. Ta canza kaya da sauri ta ɗauki hijabin Islamiyya, ta fito tana cewa
"Inna, na tafi Islamiyya."
Inna ta amsa a sanyaye ba tare da fada ba:
"Allah Ya kiyaye... Idan kun taso, ki tsaya gidan Mairo ki siyo mana kuka."
"To Inna," ta amsa, ta fice tana murmushin mugunta.
​Tana isa makarantar Islamiyyar, sai ta ci karo da Ustaz. Wani kallo mai cike da tuhuma da ɓacin rai ya bi ta da shi, sannan ya yi mata nuni da hannu
"Biyo ni ofis yanzu!
​Suna shiga ya rufe ƙofa ya daka mata tsawa:
"Haba Surayya! Yaya za ki dinga wasa da karatunki haka? Kaf makarantar nan kowa ya san ke ce amirar ɗalibai, me ya sa kike neman ɓata tarbiyyarki?!"
​Surayya ta ɗaga kai ta dube shi da idanun da suka riga suka zama na cikakkiyar 'yar bariki, ta ja tsaki a gabansa
"Ustaz, na zo nan ne kawai don in ja maka kunne! Rayuwata daban, taka ma daban! Billahillazi idan ka ƙara samun Babana da maganar cewa ba na zuwa makaranta, sai na yi ƙaryar cewa fyaɗe ka yi mini a ofis ɗin nan..."