SECRETS OF THE PAST
by @saddiqahhh
NURI'S POV...
Yau kwana biyar da yima Inna aiki and Alhamdulillah, she's recovering fast. Nuri ta fara dan sakewa da mutanen dake around her, which are Maman Nabeela, Nabeela, sai Ammi, Abbie ne dai ta rasa me yasa kawai yana cika mata ido. Kullum ita ke kwana da Inna amman Nabeela is always with her. Maman Nabeela zata zao da safe ta dawo da yamma kuma hardai zata zo zata taho musu da abinci.
Ammi dake mugun tausayinsu especially Nuri itama tana zuwa though ita sau daya kawai take zuwa a rana sai dai sun mugun sabawa da hajiya Inna. Ko wani rana da abinda zata kawo musu data tabbatar zasu buqata. Inna ta tambyi Nuri ina ta sansu tace bata sansu ba. Ahaka sati ya zagayo Ammi da Abbie suka tafi bayan sun musu sallama sun bar musu kudin da zasu iya kulawa da kansu. Nuri har bakin mota ta rakasu tana yi musu godiyar da Ammi ta hanata amman ba taji ba.
Two weeks later...
An sallami Inna sun koma gida sannan Alhamdulillah akwai kudi sosai wajen Nuri wanda su Ammi suka bata yanzu dashi take amfani bata kuma yi gigin komawa wajen aikinta ba don tasan bama za'a amsheta ba. Nuri na dan sakewa da wanda ta fahimci suna da mutunci agidan wanda da duk ba tayi hakan ba. Duk da har sannan bata saba dasu ba dai Alhamdulillah akwai progress tanan fannin.
It was Sunday evening... Nuri na zaune a dakinsu daga ita sai Inna tana ninke musu kayansu data wanke. Inna kuma tana yanka lettuce don lafiya fa ta samu duk da ba komai take yi ba ammn Alhamdulillah.
"Nuratu kunyi waya da biyayyen naki kuwa jiya?"
Kai ta girgiza mata tana cewa "a'a tun wancan satin kamar he's been busy da karatu.."
"Kike yimin hausa zalla 'yarnan.."
Kai kawai ta gyada mata tana cigaba da ninke musu kayansu suka ji sallama a kofar dakinsu. Amsawa Nuri tayi tana dago kanta ta sauke kan dan labulen nasu daya mugun jin duniya.
Amsa sallamar da Nuri tayi ya bawa wanda suka yi sallamar damar shigowa.
Ammi ce da Safa! Dan waro idanu Nuri tayi ganinsu haka kawai tana jin far'a. Da sauri ta miqe tsaye taje ta dauko sallaya ta shimfida musu tana cewa "laaahhh Aunty kece..."
Kafadarta Ammi ta dafa tana cewa "uhmmmm tun shekaran jiya muka zo ma ammn sai yau na samu kwatancen gidan naku da kyar shima..."
"Ku zauna." Zama duk suka yi Inna sai maimaita "maraba lale" take kamar shine abinda tafi iyawa duk duniya.
Kallon Inna Ammi tayi tana cewa "Baba ina yini ya jiki?"
"Da sauqi 'yarnan naji sauqi wallahi. Allāh ya saka muku da alkhairi ya biya muku buqatunku na alheri.."
Da Aameen Ammi ta amsa tana yin murmushi Safa ma ta gaishe da Inna. Tana yin shiru Nuri ta gaidasu dukansu kamin ta miqe tana daukar hijab dinta ta zura ta fita samo musu ruwa mai sanyi. Bata jima ba ta dawo dauke da ruwa a leda taje ta dauko plate na roba da suke dashi ta zuba musu ruwan akai ta ajiye musu agabansu. Ammi banda kallon Nuri babu abinda take she's thinking of ta yanda zata yi convincing Nuri da Inna kan buqatar data zo musu dashi.
"Kusha ruwan Aunty me za'a dafa muku."
Kai Safa ta girgiza mata tana cewa "Alhamdulillah we're full karki damu kanki da girki kinji."
Qasa tayi da kanta tana wasa da gefen hijab dinta tayi shiru bata sake magana ba. Ruwan duk suka sha bayan sun ajiye Ammi ta kalli Inna.
"Baba don Allah alfarma nake nema awajenku.."
A tare duk suka kalle Ammi kowa cikinsu Inna yana dokin yaji wanne kalar alfarma ne wannan zasu so suyi musu shi.
"Ina so don Allāh ku dawo gidana da zama keda NURIYYA!!!" This was the last thing they expected to hear. Shiru duk suka yi suna kasa yin magana. Su koma gidanta as in how?
Ammi sai kallonsu take one after the other, hoping they would agree to what she'd just said. Jin har sannan sun kasa amsa mata yasa ta sake cewa "don Allah Baba... Banzo don na cutar daku ba. I just want to help, na fahimci yarinyarki bata makaranta I want to enroll her in a new school. I want to give you the best Baba, bansan labarinku ba Amman mijina yamin bayanin ranar daya hadu da ita yadda take kuka Kuma ban zo nan sai da izininsa ba.. "
Sai a sannan Inna ta rufe bakinta don tsabar mamki hangameshi tayi.
"Baki san mu ba, baki san komai akanmu ba kike mana wannan maganar."
Kai Ammi ta gyada mata tana "I work with human rights, so I don't know why I always feel this way whenever I come across people like you. Sannan Yallabi da kansa ya bani go ahead." Ammi ta samu cigaba sosai fannin aikinta har ynzu tana lecturing a base university ta samu offer din aiki da human rights ne last year.
Nuri dai bata iya magana ba sai sauraren Ammi da take yi. Kamar she'd been caught completely off guard. Su koma gidan Ammi forever ko kuwa? Wace matar da gaba daya da daga haduwa sati biyu da suka wuce har zata zo musu da zance irin wannan?
"Baba zuwa nayi na fada muku kawai. Kuyi tunani akai don Allāh akwai irinku da yawa da muke bawa shelter a humanitarian affairs dinmu amman I don't know why, with you people, I feel like I would rather have you stay in my house."
Kai kawai Inna ta gyada mata ba wai don ta fahimta ba tace "za muyi tunani akai."
Kallon Inna Nuri tayi da mugun mamaki. Yanzu ta sake tabbatarwa Inna ta shiryu, Innan da da gudu babu wani tunani zata amince da buqatarsu ammn wannan Innan tace za tayi tunani akai.
"Nagode sosai Baba." Sai ta kalli Nuri tana cewa "daughter kinyi shiru."
Qasa ta sake yi da kanta ba tare data amsawa Ammi ba don ita haka kawai taji tafi son zamanta nan akan binsu. Ita abinda bata fahimta ba shine daman har ynzu akwai wanda basu sanka ba zasuyi maka irin wannan tayin. Hakan yasa taji kawai bata yadda ba. Don't forget Nuri yanzu bata so ake taimakonsu. Har bakin mota suka rakasu duka bayan Ammi ta saka an shigo musu da provisions din data yi musu suna tayi mata godiya.
Bayan sun koma daki babu wanda ya sake tada maganar kowa abinda ta kama daban dukda zuciyarsu juya zancen Ammin kawai yake yi. Idan taimakon ne ma tayi musu shi ba tare da sun koma gidanta ba. She can sponsor Nuri's education here anan. That would make Nuri much happier.
It now dawned on her that, deep down, she still had a desire to pursue her education.
AMMI'S POV...
"Ammi me yasa baki fada musu gaskiya ba?"
"I don't know how they'll take the news Safa. Abbinku ya tabbatar she resembles the boy, sannan zaman da suka yi a asibitin we used her hair akayi carrying DNA test and they're siblings. Safa probably yaran nan jinin Fadimatun Abbu ne cousins dinku ne su din!"
Kai kawai Safa ta dagawa Ammi tana sake jinjina lamarin. Duk da ita har yanzu jin komai take ta kasa yarda kawai ita zata so Abbu ya fada nusu yadda ya san Fadimatu kuma har ya rabu da ita.
Ya akayi take nesa dasu basu santa ba jininta ma basu sansu ba. Uncle Farouk yayi ma Abbie maganar Afif daya kasa haquri dashi. Abbi take yaje Germany takanas saboda Afif and it turns out to him yaron nan jinin Abbu ne.
Basu boyema Afifi komai ba sun fada masa in fact har hoton Abbu suka nuna masa shi kansa Afif din yaga resemblance dinsa da Abbu. Bai boye musu komai na tarihin da Mami ta basu ba don ya tabbatar idan ma suna da alaqa bai wuce ta bangaren Mami ba.
Jikin Abbi sosai yayi sanyi da Labarin da Afif ya bayar yana sake samun tabbacin jinin Fadimatu ne. Don sunje har can Maiduguri nemanta amman an tabbatar musu yan boko Haram sun mamaye garin sun kashe wasu, wasu sun gudu.
Still, Abbu bai haqura ba yace don Allāh su cigaba da duba masa ita. Yace shi ko bai ganta ba yana son ganin jininta. Abbu yana warkewa aka wuto dashi Germany yaga Afif. Fadar kalar yadda Abbu ya kidime ma bata lokaci ne. Shi yace bama sai anyi wani test ba ya tabbatar wannan jinin Fadimatunsa ne.
Fadimatu matarsa wadda suka rabu tana da tsohon ciki sannan rabuwar nasu ma dai kawai qaddara ne da Allāh ya qadarta musu.
Duk da Abbu ya tabbatr haka su uncle Farouk suka saka akayi musu Grandparentage DNA test and it shows that they are related. Tun sannan Abbu yace akai shi yaga 'yarsa 'yar Fadimatunsa wadda aka sawa sunan Fadimatunsa. Afif ya basu address din gidansu. Basu gaji ba suka dawowa Nigeria kano. Sai dai basu samu su Mami ba bincike ya tabbatar musu sun tashi tunda shi Afif tsohon gidansu ya bada kwatance bai san kalar rayuwar da Nuri da Mami suka yi ba. Akayi musu kwantacen gidan Inna shima sukaje akace taun tashi. Basu fadawa Afif ba don sun fahimci wani abu daga cikin bayanin 'yan gulmar unguwar kusan na anan suka samu labarin kalar rayuwar da Mami da Nuri da kuma Innan ma suka yi.
Hakan ya mugun daga musu hankali aka satnu Afif da zancen. Atime din har kwatawa asibiti yayi bayan yaji sauqi yace ya haqura da karatun zai koma ya nemi Maminsa da Nuri. Abbie ya lallabshi ya masa alqawarin zai nemo masa su. That's the main reason da yasa Abbie yana ganin Nuri yaji yana sonta don ya tabbatar 'yar uwar Afif ce, bawai kama suke sosai ba amman jini yafi ruwa kauri so duk inda dan uwanka yake dan uwanka ne za'a iya ganeku especially idan family dinku irin family dinsu Abbu ne da duk kamarsu daya.
Bayan Nuri sunyi settling a Kaduna ta kira Afif shine ta kasa haquri ta fada masa Inna fa tayiwa Mami aure amman shi kadai ta fada masa wanda ya riga da yasan komai duk abinda suka ta boye masa. Duk kudin da yake turo mata Abbie ne yake bashi ya turi mata, duk da Abbi yaso ake tura mata mai yawa Amman Afif yaji tsoron ta titsiyeshi inda yake samun kudi mai yawa tunda sunce ba zasu fada mata komai ba sai sun hadu.
Layin da take yawan kiran Afif dashi suka saka akayi musu tracking ya nuna musu tana Kaduna. Zuwan Abbi kaduna har da wannan sai dai kamin ma su qarasa gidan nasu da aka binciko masa ya ganta a asibiti. Abbi yaso tun farko ya fadama Nuri gaskiya amman yace abari Inna ta warke. And now Ammi tazo da izinin Abbi zata daukesu ta kaisu can. Afif ya dan samu break sun dawo shida Suhana suna Abuja. Abbi yana so Nuri da Afif su hadu bayan shekara uku da rabi da sukayi basa tare.....
To be continued...
like, comment and share