BABI NA TALATIN DA SHIDA
by @zainabb
Zaren Rayuwar Mu
DA DARE Zaid ya shigo ɗakina. Naji daɗi sosai amma ban nuna a fuska ba se kallon shi da nake yana ɗauke da neutral face shi ba cikin farin ciki ba kuma ba cikin jin haushi ba ko fushi.
“Good evening” na fara gaida shi
“Good evening” ya amsa ni
Tsaye yayi ban san ko ya rasa abin faɗa bane ba. “Ka zauna” na faɗi mishi ahankali
Be zauna ba yana tsaye yace “Gobe zamu tafi Kaduna. Ki shirya cikin lokaci. Morning flight ne we take off by 10”
Tunda ya fara maganar nake kallon shi ban yi koda blinking ba. Zaid ze maida ni gidanmu ne fa amma kuma ina second thought akan zancen sakin nan saboda Yaya Hauwa tayi assuring nawa ba saki ze yi ba, Zaid ze ma sauko ne amma me ya kawo maganar zuwa Kaduna.
“Me zamu yi a Kaduna tunda safe? Wani abu ke faruwa ne?”
“A'a babu komai. Zamu tafi mu gaida su ne. Kwana biyu bamu je ba”
Shiru nayi ina ta tunanin the most obvious. Jiya nayi waya da Abba yace min ya tafi ganin likitan shi saboda mahaifi na yana da matsalar numfashi, to ko baya fuskantar matsalar at the moment yana zuwa ganin likitan shi ana duba shi akai-akai. Babu abinda ke cikin raina se abu biyu, ko de Zaid ze maida ni Kaduna ya rabu dani kenan ya sake ni ko kuma mahaifina ne bayi da lafiya zamu je duba shi ƙila ciwon nashi ya kwantar dashi a asibiti. Amma idan Abba ne bayi da lafiya, ba za'a kira ni a faɗa min ba?
“Are you letting me go or is my father sick he's on hospital bed? Please tell me”
Matsowa Zaid yayi wurina ya riƙe min hannuwa guda biyu “I'm not letting you go, Diza. Abba is fine we're going there to visit them”
Na yarda da abinda Zaid ya faɗa na farko na he's not letting me go saboda yace Diza, sunan da ya jima be min ba tunda ya fara ja da baya amma kuma ban yarda ba da yace Abba na lafiyar shi. Idanuna ne suka cika da hawaye saboda nasan wani abu ya faru a gidanmu. Wayata dake gefe na na jawo babu wanda ya min waya a gidanmu. Kafin nayi dialling number Gwaggo na Zaid ya amsa wayata a hannuna. Now I believe the latter.
“Wani abu ya faru a gidanmu. Ka faɗa min menene? Abba ne bayi da lafiya ko har ma bayi da rai?” na faɗa saboda nasan ɗaya daga cikin su se ya faru ga dukkanin mu.
Shiru Zaid yayi ya ƙara riƙe min hannuwa a cikin nashi.
“Is he alive or dead?” nace, idanuna suna bushewa ga hawayen da suka taru earlier on. Ji nake zuciya ta kamar jini ya dena gudana a cikin ta.
“I'm sorry Diza”
Shiru nayi nasan wannan ne ya farun. Iska na dena ji se na tashi tsaye na fara to and fro a cikin ɗakina. Zaid ya tare ni ya ƙara riƙe min hannuwa. “Me yake faruwa Hadiza?”
“Ji nake bana iya numfashi. Bana jin.....komai bana ji. Kamar zuciya ta zata dena bugawa kowane lokaci”
“Kina da athsma, Hadiza?” Zaid yayi saurin cewa
“Mu je Doctor ya gan ki, mu tafi” Zaid ya ja hannun Hadiza da ƙarfi suka fito gidansu.
A cikin mota kanta na sunkuye tana battling da numfashin ta yana jin yanda take ja da ƙarfi kamar zata yi hauka. Ƙara gudun mota yayi suka isa Cedacrest emergency. Doctor dake nan Zaid ya faɗa mishi abinda Hadiza ke ji.
A gado aka kwantar da Hadiza idanun ta na buɗe aka sa mata oxygen se kallon Zaid take tana blinking idanun ta a hankali. Gefen ta Zaid ya dawo ya riƙe hannun ta cikin nashi. Yana kallon ta se yanzu hawaye suka fara zubowa a idanun ta yasan tana tunanin abinda ya faɗa mata ne na rashin ta.
Duba vitals ɗin ta akayi komai lafiya lau. Kuma sun duba basu samu wani major organic disease a gare ta ba. Koda karfe goma tayi an gama stabilizing Hadiza numfashin ta ya dawo. Likitan yake ƙara jaddada musu acute grief ne ya haɗa mata da tsoro and it's completely normal to feel like she had lost her breath in common sudden overwhelming emotional shock. Haƙuri ya ƙara bata aka musu sallama.
A cikin mota babu me cewa wani abu har suka isa gida. Zaid na riƙe da ita suka shiga ciki. A ɗakin ta ta wuce Zaid ya bi bayan ta. Zaune tayi a gado ƙafafuwan ta duka na kan gadon.
“Na kawo abinci, Hadiza?”
Girgiza kai Hadiza tayi Zaid ya matso wurin ta “Baki jin yunwa ne?”
Ƙara girgiza kai Hadiza tayi. Tashi Zaid yayi ya shiga kitchen ya ɗauko mata hollandia da glass cup ya dawo dashi saboda yasan ba zata iya cin wani abinci ba.
Zuba mata hollandia yayi a cup ya bata amma Hadiza bata amsa ba se ya ajiye a jikin bedside lamp ya koma ya zauna a kujerar dake cikin ɗakin ta yana kallon ta. Jikinta ta ɗaura a jikin gado. Bayan wasu mintuna ta cire tasa kanta a cikin laps. Nan ma bayan wasu mintuna ta cire kanta tana dai zaune idanun ta da akwai ciwo a ciki. Ta zama shiru daga kallon ta zaka san akwai abubuwa da dama dake yawo a acikin ranta.
Babu wani abu wanda Zaid yake so game da ita yanzu se kukan da zata yi na rashin ta amma Hadiza ta kasa yin kuka. Damuwar da yake gani ɗazu ma akan fuskar ta ta fara gushewa yanzu fuskar nata yayi wani iri kamar me tunani kamar wacce bata cikin damuwa tayi surrender ga duk wani abu wanda ze faru da ita.
Kwantawa tayi ahankali bata rufe idanun ta ba. Zaid na kallon duk abinda yake faruwa da ita, motsi kawai take akan gado idan ta juya nan ta juya chan. Suna nan cikin ɗakin har ƙarfe daya tayi Hadiza bata yi bacci ba shima Zaid be yi ba yana zaune akan kujera yasa jikin shi a jikin kujerar. Suna a haka babu wanda yayi bacci har safiya ta waye.
A safiyan ma Hadiza na nan yanda take jiya, tayi wanka suka wuce airport tare da Zaid.
Koda suka isa gidansu Hadiza har an gama yiwa Abban ta sallah. Shiga cikin gida tayi shi kuma yana waje tare da maza.
Bayan an gama duk abinda ake aka tafi dashi. Ba mazan suka dawo gida ba se wuraren sha biyu. Nan aka fara gaisuwa ana shiga cikin gida ana yiwa matan gaisuwa har Zaid shima ya shiga.
Later in the day dangin su Zaid suka zo har Kaduna yiwa Hadiza gaisuwa daga Abba, Mummy, Yaya Hauwa, Muhammad da matar shi, Khalifa da Shahida duk sun zo.
A ranar suka koma Abuja amma ba tare da Zaid ba Abba yace ya tsaya wurin Hadiza.
Da dare take kiran shi tana tambaya ko yaci abinci yazo ya amsa an gama abinci a gida. Mamakin ƙarfin halinta yake amma yana son ganin ta se ya shiga cikin gidan aka mishi iso har cikin parlour daban da living room nasu, hannun shi na riƙe da leda ya siyo mata babban goran hollandia.
Kulolin abinci ne a cikin parlourn a tsakkiyar carpet. Yana nan zaune se ga Hadiza ta shigo sanye da abaya peach da ƙaramin hijab. Kallo ɗaya yayi wa idanun ta yaga sunyi jazir kamar wacce aka watsawa garwashin da ya ruru a wuta sosai a cikin idanu.
Tsugunnawa Hadiza tayi zata zubawa Zaid abinci yayi saurin cewa “Bana jin yunwa Hadiza”
Ɗago da idanun ta tayi tasa ana Zaid “Kaci abinci? A ina kaci?”
“Ke kinci abincin?”
Girgiza kai ta fara yi “Bana jin yunwa. Bani da appetite na cin abinci”
“Haka zaki zauna da yunwa? Ko baki da appetite yafi ki ci da ki zauna ahaka”
“Bana iya cin komai”
“And i bought this for you”
“i don't have appetite. Kai kazo kaci abincin”
“Bana jin yunwa Hadiza. Ki yarda dani”
Nodding Kai tayi tare da tashi daga tsugunnen da tayi ta zauna daura dashi kanta na sunkuye. Shiru Zaid yayi be san abinda ze faɗa ba. Gabaɗaya atmosphere gidan da na parlour ya chanja yana tuna lokacin da suka zo gidannan gaida mahaifin ta. Abban ta was so lively mutumin kirki ko a yadda yake magana ko bayan an ɗaura auren shi da Hadiza da Abban shi ya dawo gida yayi ta magana akan mahaifin ta babu ruwan shi dattijo ne na arziki.
Wani irin wave na sadness Hadiza ke ji a cikin zuciyar ta. Wannan zaman da take yi gaban Zaid bama son shi take ba. So take ta kasance ita kaɗai a cikin ɗaki ta cigaba da jin duk zafin da take ji ita kaɗai tayi kukan ta. Ba bata gaji da kuka bane ba. Kukan ne da kanshi yake zuwan mata a duk lokacin da yake so.
Tashi tsaye tayi zata wuce ba tare da ta cewa Zaid wani abu ba. Tashi tsaye yayi shima ya riƙe mata hannu ta sunkuye kanta yadda idanunta suka cika da hawaye har suna son zubowa.
“Hadiza?”
“I want to be alone” ta faɗa on the verge of crying
“I want to be with you in this your trying time, Diza”
Girgiza kai tayi “I want to be alone”
Ƙin sakin hannun Hadiza yayi yayi hugging nata a jikin shi ya ɗaura hannun shi a kanta. Ta fara kuka a cikin kukan tace “I want to be alone. Please Zaid”
“You can call me anytime” ya faɗi se ta tadda kanta a kirjin shi ta raba jikinta a nashi ta fita daga parlour. Tsaye Zaid yayi ya rasa abin yi amma yasan har cikin zuciyar shi yana son ya kasance tare da Hadiza to give her a shoulder to cry on but......Hadiza wants to be left alone and whatever Hadiza want, she gets it.
**********
But let's see Ibrahim and Maryam. Who misses them?