Zaren Rayuwar Mu

BABI NA TALATIN DA TARA

by @zainabb

Zaren Rayuwar Mu 

ƊAKINA NAKE JIN yayi min nauyi, ina jin yayi min ƙunci dayawa da shirun da gidanmu yake da a Kaduna. Ji nake kamar na ɓace gabaɗaya. Ina jin muryoyi mabanbanta da suke min taaziyya a gidanmu suke faɗa min nayi haƙuri. Wasun su an musu rashi sun san zafin shi da kuncin shi, ba zan ce basu san zafin rashi ba amma dai basu san irin ƙuncin da yake ɗauke a cikin zuciya ta ba. Wanda basu yi rashin ba, basu san menene shi ba. Basu san irin abinda ake ji idan aka rasa wani muhimmin mutum a rayuwa ba. Kun san mahaifina uba ne. Duk wani abu da ya rataya a wuyan shi nawa ya ɗauke min. Ya ɗauka duka responsibilityn shi ba tare da nuna gajiya wa ba. Na taɓa yin wata ƙawa wacce nake kira ƙawa wacce mahaifina yake haɗa muna sandwich tare da ita idan tazo gidanmu tun muna yara. Ya zamar min role na mahaifii da kuma mahaifiyya. Zan iya zama na tattauna dashi akan duka abinda ya shafe rayuwata ban zauna na faɗawa kowa ba har mahaifiya ta. Rashin shi, nasan wani abu ne a zuciya ta wanda zafin shi ba ze taɓa gogewa ba. 

Zaune nake akan carpet a gefen gado na. Na ɗaura hannuna ɗaya a jikin gado na na sunkuyar da kaina ina jin duk wani zafi me ciwo a zuciya. Idanuna a buɗe suke amma suna yi kamar su rufe. Nasan na zama me natsuwa sosai ba saboda komai ba, se domin na gano irin abubuwan da nake ji a zuciya ta kuma na bar kaina naji su ba tare da brushing nasu off ba. 
Sallamar Zaid naji yana shigowa cikin ɗakin. Ban amsa shi ba kuma ban motsa daga inda nake ba. 
   “Diza” ya fada yana zuwa wurina. Hannuna ɗaya ya riƙe tare da tsugunnawa daura dani. 
Shiru yayi be ƙara cewa komai ba se sa hannuwan shi da yayi a jikina ya tada ni tsaye muka zauna a gefen gado. Kaina tare da hannuwa na na ɗaura a laps ɗin shi hawayen da nake riƙewa suka zubo idanuna. “my Abba has left me all alone, Zaid” na faɗa cikin kuka 
Hannu Zaid ya ɗaura a bayana ba tare da patting nawa ba to and fro yace “You have me. You have me, Diza”
Kuka Hadiza ta cigaba da yi sosai bata ɗago kanta ba kuma bata ƙara cewa wani abu ba. Tausayin ta Zaid yake ji. Be taɓa rashin wani na kusa dashi ba sosai. Lokacin da ma ya rasa mahaifiyar sa bayi da wayon sanin ta bale ma yayi kewar ta se de yayi tunanin idan har da tana da rai, wani abu ba za'a mishi a gidansu ba saboda zata yi tsaye akan su shi da Hauwa akan matar mahaifin su. Duk da mahaifin su uba ne me kulawa amma wani abu duk yanda baka so se an maka shi wanda ba daidai ba. 

Ɗago da jikin ta yayi daga laps ɗin shi yayi hugging nata, hannun shi a bayan ta yana sauraren kukan ta be yi kusa da rarrashin ta ba saboda yasan tana buƙatar kukan da take. Idan ma bata yi yanzu ba, zata yi wani lokaci. 
Har ƙarfe biyu na dare suna haka tare da Hadiza. Ta dena kuka tun ɗazun amma ta kasa sakin shi, shi kuma da bata jenye jikinta ba be jenye nashi ba yasan tana buƙatar comfort a wannan lokacin. And she appreciates him not telling her not to cry. 

Kamar wacce akayi pinching, ta tashi daga jikin Zaid ta shiga bathroom. Tana ciki Zaid na zaune yana jiran fitowar ta. Ganin tayi minti talatin bata fito ba yasa ya tashi ya duba ta. Koda Zaid ya buɗe banɗaki ya ganta tsaye ta ɗaura kanta akan ginin banɗaki tasa hannun ta a goshin ta tana kuka. Rufe banɗakin yayi ahankali ya fito daga ɗakin ya koma nashi yana sanin cewa Hadiza needs her space amma be san ko kukan da take so tayi bata iya yi ne a gaban shi tafi so ta keɓe ita kaɗai ko kuma idan wani tragedy babba ya faru da ita bata so mutane su kewaya da ita tafi so ta kasance ita kaɗai wataƙila tafi gane kanta a haka ko kuma bata jin daɗi amma de tasan da cewa shi kam he'll always be beside her whenever she needs him yasan ba ze takura mata kasancewa tare da ita ba idan bata so amma tasan da cewa he's her shoulder to cry on and it pains him to see her in this situation but he can't do anything about it because it's part of life to be in this situation. 

Washegari ni na fara tashi daga bacci kafin Zaid. Da yake weekend ne na gama ɗan gyare-gyaren da zanyi har wanka nayi nasa doguwar riga na atamfa. Ɗaura ɗankwali nayi in a simple way na shafa kwalli a idanuna. Ƙarfe tara na safe naga tayi se na duba ɗakin Zaid naga ko ya tashi. Be tashi ba na wuce kitchen na haɗa mana breakfast; fries ne da omelette na dafa ruwan tea. A dinning table na jera kayan na koma dakin Zaid domin sake duba shi. Koda na duba baya cikin ɗakin nasan yana banɗaki yana wanka. Har na juya zan wuce na dawo cikin ɗakin na buɗe wardrobe ɗin shi na ɗauko mishi kayan da ze saka tukuna na fito daga ɗakin na koma dining table ina danna wayata. 
Ina nan zaune ya fito. Tun daga chan na hango shi yasa kayan da na ɗauko mishi ya min kyau in his blue light brown trousers and a white shirt. Tun daga chan na bashi thumbs up yayi murmushi which makes him look so handsome. 
   “Good morning, Diza” yace tare da zama daura dani a kujerar dining
  “Good morning” na faɗi tare da tashi tsaye na matso da jikina a nashi and gives him a peck on the cheeks. “How was your night?” 
    “Alhamdulillah” ya amsa cikin natsuwa yana kallon idanuna da suke jazir amma be ce komai ba. 
   “And you?” yace , be jira abinda zan faɗa ba yace “It'll be better. Trust me”
Murmushi nayi tare da tashi tsaye zanyi serving namu yace na bar shi ze yi. Komawa nayi na zauna. Zaid ya tashi yayi serving namu har tean da zan sha shi ya haɗa min. Bayan ya gama ya zauna be taɓa abincin shi ba ya tsaya yana kallo na naci abinci. 
  “Eat”
“You too, eat”
“Ladies first” Zaid yace. Murmushi nayi na fara cin abinci nasan duk damuwa ce yayi dani shiyasa yace na fara cin abincin. 
Har nayi nisa da abincin be fara cin nashi ba yana kallo na. Cewa nayi na koshi ya girgiza kai. Ban bari ya buɗe baki yayi magana ba na ƙara cin abincin. Tea nayi sipping nace “Na koshi, da gaske. Please don't make me eat more my stomach will explode”
  “I'll love to see that happen” yace. Murmushi muka yi mu biyu be ƙara matsawa na ƙara abincin ba ya fara cin nashi. 
Zaid na gama cin abinci yace “Do you want to go somewhere?”
  “Like?”
 “Any resting place or anywhere serene”
Shiru nayi ina nazari nasan bana so na tafi ko ina. Idan so samu ne zan so na rufe kaina a cikin ɗaki nayi zamana ba tare da naga kowa ba. Amma ganin yanda Zaid yake ƙoƙari akaina nace “Maybe Jabi Lake?”
   “We should go there?”
   “Yes, we should”
Hannun shi ya kai a nawa ya tada ni tsaye muka fara wucewa ɗakina. Da kanshi ya buɗe wardrobe ya ɗauko min mayafi na kuma ya ɗauko min takalmi. Sakawa nayi muka fito ya ɗauko makullin motar shi muka fito. 

Akwai rana ba me kaifi ba a waje. Motoci daban daban ne akan titi wasu da gudu wasu kuma ahankali. Juyowa nayi ga Zaid ina kallon shi yana tuƙi har muka isa Jabi Lake. Akwai mutane a ciki saboda mutane na son yadda Jabi Lake yake da nature ga ruwa. Mutane nata minding business nasu zaka ga wasu they look like family, some friends and some are not a couple and there's us, Zaid and I, a couple. 
Tsaye nayi a wurin ruwan ina kallon su da korayen itacen da suka zagaye wurin ana jin sanyi yana sauka na daga yadda wurin yake. 
   “You know, nature is beautiful” nace tare da kallon Zaid sau ɗaya na maida idanuna kan ruwan. 
Murmushi Zaid yayi na matsa wurin shi na ɗaura kaina a kirjin shi na cigaba da kallon ruwa. 
   “It is, Diza”
Dama akwai hadari ba sosai ba amma ya fara haɗewa har baƙi yayi duk da yanayi yana yi kamar lokacin sanyi na ƙoƙarin shigowa. 
  “My Abba use to tell me how he'd play in the rain when he was little. It's a story he tells me every rainy season. But you see, I have never stayed in the rain” na faɗi wa Zaid se kuma aka fara yayyafi 
   “The rain is.....” Zaid ya fara magana. Jin yadda ruwan ke ƙoƙarin ƙara ƙarfi yace “Lets get in the car”
Hannun shi na riƙe “Lets stay here like this. For today only. Please”
Zaid be ƙara cewa komai ba har aka fara ruwa sosai suka dake mu. Ganin ba zan ce mu tafi ba kuma ruwa sunyi ƙarfi ina jin sanyi sosai yasa Zaid yace, ahankali “I don't want you to be down with cold, Diza. Let's go home”
Kaina na cire a kirjin shi ya riƙa min hannu muka wuce cikin mota. A cikin motar muka zauna saboda ruwan na da karfi sosai se bayan sun fara ragewa muka tafi gida. Tun kafin mu isa na fara shivering ina jin sanyi sosai. Muna isa gida na wuce ɗaki na shima Zaid ya tafi nashi. 
Bathroom na fara wucewa nayi wanka da ruwan zafi sosai na fito duk ban bar shivering ba nasa doguwar riga na kwanta a gado tare da rufe jikina da duvet ina shivering. Nan take naji kamar bani da lafiya. 
Ban san lokacin da Zaid ya shigo ba amma naji hannun shi a cikin duvet ya taɓa wuya na domin jin temperature. “You are down with cold, Diza”
Hannun shi na riƙe sosai saboda nashi bayi da sanyi ni kuma duk jikina sanyi ne dashi. 
  “Should we get you a drug for the cold?”
Girgiza kai nayi “It'll come down later. Don't worry about me”
  “It has always come down on its own?”
“Just stay here with me. I don't want any drug”
Zaid be ƙara faɗin wani abu ba hannun shi na cikin duvet dai na riƙe sosai. 
Waya ta ce ta fara ringing. Ɗauko wa Zaid yayi ya bani. Idanuna na rufe nace “Wa yake kira?”
  “Umma”
Amsa nayi daga hannun shi na ɗauka. Gaisawa muka yi da Umma. Muryar ta cikin natsuwa ahankali take magana inaga yau ba zata min faɗa ba. 
   “Lafiyar ki? Are you cold, Hadiza?”
  “Eh Umma”
  “Menene to? Ya akayi?”
  “It was Zaid and I. We just stayed in the rain shikenan fa”
  “Stayed in the rain! You guys are still kids right?”
Murmushi nayi. Umma tace “Is that what your baby needs?”
Ina dariya jin abinda Umma tace nace “Umma bani da ciki fa. Wallahi bani da ciki”
  “To wayasani. Ko ke baki sani ba”
  “Umma da gaske nake miki”
 “Ya kuke keda mijin ki? Kuna lafiya dai ko?”
  “Muna lafiya Umma. Yana kusa dani, gashi ku gaisa”
Ba Zaid wayar nayi se na fito da kaina daga cikin duvet ina kallon shi yana waya da mahaifiyya ta. Bayan sun gama gaisawa Umma tace “Ku dinga haƙuri da junan ku. Allah ya ƙara baku zaman lafiya”
  “Amin Umma, mun gode. Allah ya saka da alheri” Zaid ya faɗa. Kallon shi nake ɗauke da murmushi akan fuska ta. Bayan sun gama magana ne ya bani. Nace “Umma har yanzu Gwaggo na nan?”
  “Eh, ba yanzu zata tafi ba”
  “To yayi Umma. Allah ya bamu haƙuri da juriya”
   “Amin Hadiza. Amin”