EP__________ 7️⃣
by @swrites22
🕊️ DESTINED MARRIAGE 🕊️
*HAUSA EDITION*
🕊️ QADDARARREN AURE🕊️
SWRITES
A-K-A
YOUNG WRITER✍🏻
EP__________ 7️⃣
"Yauwa, barkan ka da yamma".
"Ya kike? Hope all's well?". Mansur ya tambaya a hanzarce, dan ya san zuwa yanzu Aryan ya cika kaɗan yake jira ya fashe, ba kuma yaso aje matakin da zai fito daga motar.
"Eh, kun jefar da wallet ne a gidan mai ranar Thursday, shi ne dana duba ciki sai naga wannan address ɗin". Ta faɗa tana miƙa masa wallet ɗin.
Karɓa yayi ya buɗe sai kuma ya ɗago ya kalli Faryal ɗin da faɗin, "Kai Amman nagode sosai, you are such a kind hearted girl whl. Gani nan namu ma da kikayi yanzu tunanin zuwa muke mu yi report saboda IDs ɗin da ke ciki. Mun gode sosai whl, Ubangiji Allah ya saka miki da alheri".
"A'a, babu komai whl, dama ita ce na kawo, ni zan wuce, sai Anjima". Faryal ta faɗa tana juyawa zuwa ga motarta ba tare data jira amsar sa ba. Murmushi Mansur ɗin yayi ya sake juya wallet ɗin kafin ya juya ya koma mota cikin jin daɗin takaita musu wahala da Faryal ɗin tayi.
Yana shiga motar ya ce, "Aryan, ka ga wallet ɗin taka da ta ɓata, Alhamdulillah an same sh...". Maganarsa ce ta katse a dalilin ganin da yayi dukkan securities ɗin dake bakin gate sun iso wurin motar sun tsaya ta side ɗin Aryan.
Sai a lokacin Aryan ɗin dake ta faman cizon lips din sa ya ɗago ya kalli security ɗin da ya gani tsaye tare da Faryal lokacin da suka fito kafin ya ce, "Daniel, you are fired". Ya juya ga sauran securities ɗin ya sake cewa, "Ku kuma, duk wanda ya bari ko da wasa wata mace ta sake zuwa ko da kusa da gate ɗin wannan Company ne to whl ya tabbatar da ya kori kansa kafin ma in zo. I'm done, get lost". Ya Ƙarashe yana jan ƙwafa.
Shi kuwa Daniel dake durƙushe a kan guiwowinsa in banda roƙon Aryan ba abinda yake sai faɗi yake ba laifinsa ba ne dan Allah yayi haƙuri kar ya koreshi amma ko kallonsa bai sake yi ba, sai ma juyawa da yayi ga Mansur cikin fushi ya ce, "Idan ba za ka ja motar nan ba, to whl zan koma cikin Company, ka san ai ban rasa motar hawa ba".
"Me ke damunka ne Aryan? Me ya sa kake haka? A gsky wannan ba hali bane in faɗa ma gsky kenan".
"Ka san me? Idan ka sake yi min magana Mansur, za ka sha mamakin abin da zan yi maka whl".
"Ka daɗe bakayi ba". Mansur ɗin ya faɗa yana saka gear yaja motar, sannan ya miƙa masa wallet ɗin ba tare da ya kalle shi ba.
"Throw it away". Aryan ɗin ya faɗa a harzuqe.
Cikin rashin fahimta Mansur ya ɗan kalle shi kafin yace, "Ban gane ba, in jefar fa kace? ID's ɗinka ne fa da ATMs?".
"Na ce ka wurgar, naka ne ko nawa?".
"Kai to wallahi in kai mahaukaci ne, ni da saura na". Mansur ya faɗa yana maida hankalin sa ga tuqin da yake.
Nan fa Aryan yace da wa Allah ya haɗa shi, ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, shi dai Mansur bai sake cewa dashi uffan ba har suka isa gidan su Aryan ɗin. Ko parking bai bari ya gama yi ba ya buɗe ƙofar motar a fusace ya fice tare da banko masa ita kamar zai ɓalle ta.
Leƙo da kan sa ta glass ɗin motar Mansur yayi, cikin ɗaga murya ya ce, "Wallahi idan ka ɓalle min ƙofar mota, sai ka bani sabuwa, dan rainin wayo kawai". Ya ƙarashe yana gyara zamansa ya danna reverse ya fice daga gidan.
Ita kuwa Faryal tunda ta ɗau hanya in banda tunanin irin dokar Company su Aryan ba abinda take, daga ƙarshe dai ta tabe baki tare da ɗage kafaɗunta cikin nuna halin ko in kula.
Tana yin parking ɗin motarta a harabar gidan nasu ta buɗe ƙofar zata fita, sai wayarta ta fara ringing. Duba screen ɗin tayi sai ta ga sunan Fayyad.
Fasa fitar tayi ta gyara zama sannan ta amsa wayar, "Barka da yamma Malam Fayyad".
"Barkan ki dai salahar baiwa". Dariya Faryal ta kwashe da ita saboda sunan da Fayyad ɗin ya kira ta da shi, kafin ta ce, "Kai Malam Fayyad, daga ina ka samo wannan sunan kuma yau?".
Dariyar yayi shi ma kafin ya ce, "To ya kike? Ya hatsaniyar duniya?".
"Whl lpy kalau Alhamdulillah, Wby? Ya aiki?".
"Lpy lau Alhamdulillah. To, yanzu dai ya zan ce ne? Yaya ranar ki ta kasance ko kuma yaya ranar ki take tafiya? Tun da dai har yanzu yamma ce, so the day isn't over yet right?".
"Umm, yess. Ni ma ka ganni yanzu na dawo daga aiki, ko cikin gida ma ban shiga ba, ina parking space, gabaɗaya a gajiye nake whl".
"Oh my God, to ina ganin ya kamata in bar ki ki shiga gida ki samu ki huta yanzu. Ma yi waya anjima, sannan kar ki manta da cin abinci Okay? Kuma Karki biyewa magananniyar sister ɗin nan taki, hutu kike buqata yanzu. Ai kina ma ƙoƙari cox it's tough gsky, ai ku mata yan hutu ne, ku zauna kawai a gida sai dai in kun yi ra'ayi ku dan fita ku yi having fun haka, mu maza ai mu aka sani da wahala".
Faryal ta saki wani murmushi wanda ya fito daga kasan zuciyarta. Wannan shi ne karo na farko da wani ya taɓa faɗa mata irin wannan maganar. Ina ma mahaifinsu zai fahimci hakan, amma kuma ta san hakan abu ne me wuya, saboda shi a ganinsa mace da namiji duk ɗaya ne, su ma matan zasu iya yin duk abin da namijin zai iya yi.
Katse tunanin nata tayi ta hanyar sauke ajiyar zuciya kana ta ce, "Na gode Fayyad, ai bama zan biye ta ba, idan kuma ta dame ni to zan kira ka".
"Shikenan ma, ki gaya mata hakan kawai idan ta fara damunki, na san za ta daina, ai kin san yanzu tsoro na take".
Faryal ta yi dariya kafin tace, "Tabbas, naga alama kam".
"To shikenan, yanzu dai sai anjima, ki kula da kanki".
"In sha Allah. Thank you". Daga haka sukayi sallama ta kashe. Murmushi ta sake saki tana bin wayar da kallo, sai kuma ta ɗago da niyyar fita daga motar, idanunta suka sauka akan Manira da Hadiyyah, waɗanda ba ta lura da isowarsu wurin ba duk da kuwa ƙofar motar a buɗe take, tunda tana shirin fita ne kiran ya shigo.
"Kar ki ce min sake nemo shi kika yi?". Manira ta faɗa tana kallon Faryal ɗin da ta fito daga motar tare da tambayar, "Waye?".
"Hamdan ɗin mana". Tsaki Faryal ta ja tare da sauya zancen, ta hanyar tambayar ta ina zata.
"Hadiyyah ce zata wuce school shi ne nace muje ta sauke ni a gida, dan Ammi ta fara jero kira".
Faryal ta yi dariya cikin sigar tsokana ta ce, "Kitchen ne ya fara kewarki, oya maza wuce, karki bata lokaci".
Kwafa Manira taja tare da faɗin, "Zan yi maganin ki ne".
Faryal ta yi mata kallon gefen ido tana tabe baki ta ce, "Ai ni ba ni da magani, yadda kika san ciwon mutuwa haka nake".
"Okayyy, to za mu gani". Ta faɗa tana sake jan ƙwafa.
Gwalo Faryal ta mata sannan ta nufi cikin gidan tana faɗin, "Allah ya tsare, ki gaishe da Ammi".
*** *** ***
Haka lokaci ya ci gaba da tafiya, ranaku suka cigaba da wucewa kamar awanni. An shafe kwanaki goma yanzu tun bayan rashin arzikin da Hamdan ya mata, kuma har lokacin bai waiwaye ta ba. Sai dai tana ganin yadda yake liking post ɗin hotunan yan mata a Instagram, abin da ya ƙara tunzura ta kenan. Shikenan shi kullum ba zai canza ba, kullum cikin liking hotunan mata yake da wanda ya dace da wanda bai dace ba, shi ne har comment section. Haka dai wani lokaci zata ɓoye ta sha kukanta idan abun ya isheta. To yanzun ma hakance ta kasance, ai kuwa zuciya ta ɗibeta ta yi blocking ɗin sa ta IG ɗin. Haɗa kai da guiwa tayi ta shiga risgar kukan baqin ciki da nadamar yadda soyayya ta makantar da ita har ta ɓata lokacinta irin hakan. Ta san cewa a cikin shekaru biyar ɗin da suka yi tare, babu shekara guda da zasuyi ta cikakkiya tare, dan ya kasance kamar nepa ne a rayuwarta off and on amma duk da haka soyayyarsa ko gezau bata yi a Zuciyarta kamar ma ƙara mata ake yi, wanda ta ɗauki hakan a matsayin jarabawarta tun da ta kasa ɗaukan wani mataki akan hakan.
Tana jin motsi kamar za'a shigo, ta yi saurin share hawayenta, sai dai ta riga da ta makara. Dan Hadiyyar da ta shigo ta riga ta gan ta.
Zama tayi a gefen Faryal ɗin tare da faɗin, "Faryal me ya sa kikewa mutumin da bai damu dake ba kuka? Me ya sa za ki sadaukar da farin cikinki saboda shi? Ni whl ban ga laifinsa ba, duk ke ce kika jawo komai. Kuskurenki na farko shi ne yadda ke kika fara bayyana soyayyarki ga Hamdan, na biyu kuma yadda kika nuna masa cewa ba za ki iya rayuwa ba tare da shi ba. Shi kuma ya ɗauki hakan a matsayin damar da zai dinga juya ki, a ganinsa ai ba ki da zaɓi ne. Yana controlling ɗin ki yadda ya ga dama, ke kuma kina bin duk abin da yake so har aka kwashe tsawon waɗannan shekarun".
Kasa riqe hawayenta Faryal ta yi, dan haka ta bar su suna zuba, kafin ta ce, "Hadiyyah, mene ne laifina idan na fara nunawa Hamdan ina ra'ayin sa? Ki tuna Khadija bint Khuwaylid, matar Annabi Muhammad (SAW) ta farko, she proposed marriage to him, she was an affluent merchant and after being impressed by his character and business acumen. She initiated the proposal, and shi kuma Annabi Muhammad (SAW) ya amince da tayin nata, suka yi aure. Wannan yana nuna cewa there's nothing in Islamic teachings that prohibit a woman from initiating a marriage proposal Hadiyyah".
"Na yarda da hujjarki Faryal, amma batun qualities fa? Did you look at Hamdan's qualities before proposing to him?". Shiru Faryal tayi, domin ta san amsar ita ce NO.
Cigaba da magana Hadiyyah tayi, "Your silence says it all. Ba haramun ba ne mace ta nuna ra'ayin aure ga namiji kamar yadda kika ambata, amma abu mafi muhimmanci shi ne ta duba qualities ɗin sa, Religion, virtue da kuma characters. Sannan kuma ke da kika nuna ra'ayin sa, sannan kika fahimci cewa shi ba a shirye yake ba, me ya sa za ki ci gaba da jiransa kina ɓatawa kanki lokaci?".
"Ban fahimci cewa na yi kuskure ba sai yanzu Hadiyyah. Kin daɗe kina ƙoƙarin nuna min gaskiya amma na kasa fahimtar ki a wancan lokacin. Sai dai har yanzu ina da sauran lokaci, in sha Allah zan rabu da shi. I'm tired of one sided love, i won't keep trying to give love without getting it back. I will wait to experience how it feels to be loved". Faryal ta ƙarashe da muryar dake bayyana irin ciwon dake zuciyarta.
Hadiyyah ta yi murmushi tare da faɗin, "Haba Faryal, na san ki fa, yanzu da zarar ya neme ki shikenan za ki manta da duk waɗannan maganganun ki koma masa, abinda anyi wannan ba ɗaya ba ba biyu ba, ai ba yau ya fara ba".
Girgiza mata kai tayi tana ƙoƙarin fin ƙarfin Zuciyarta ta ce, "I promised. A wannan karon zan tsayawa kai na".
Ɗan ɗaga kafaɗu Hadiyyah tayi tare da share mata hawayenta sannan ta ce, "Shikenan, yanzu ki tashi ki je ki wanke fuskarki. Be happy Okay? Ina so ki sa Hamdan ya yi nadamar abin da yake miki, the regret that will never be corrected. I want you to make him feel jealous when you are already far away from him".
Faryal ta yi ɗan murmushin da bai kai zuci ba, ta jinjina mata kai cikin nuna alamun tabbatarwa. Martanin Murmushin ita ma Hadiyyah ta mayar mata yayin da Faryal ɗin ta miƙe ta nufi bathroom ɗin.
*** *** ***
A bangaren Fayyad kuwa, a yanzu Faryal ba ta da wani close friend sama da shi. Barkwancin sa da kuma yadda yake nuna mata kulawa kamar wani babban yayanta na daga cikin abinda ya sa ta saki jiki dashi sosai. Dan yanzu mostly every detail of their lives kowannen su ya sani, duk wani abinda ya faru da dayansu ko kuma plan na wani abun da suke shirin yi to sai sun sanar da juna. Dan in dai amincewa ne to Fayyad ya samo amincewar Faryal, kuma cikin ƙanƙanin lokaci.
Haka a bangaren Barr Hashim ma, duk da cewa Faryal ba ta saki jiki da shi kamar yadda ta sakewa Fayyad ba, amma shi ma yana ƙoƙarin amfani da damar friendship ɗin data bashi wurin ganin ya jawo hankalinta zuwa gare shi.
Kamar yanzu da agogo ya buga 5:30pm, lokacin tashinta daga aiki tuni ya wuce amma saboda yawan baƙin da suka samu a ranar da kuma kayayyakin da ake shirin fitarwa zuwa maqotan ƙasashen ya sanya ta kaiwa har wannan lokacin. Fitowa sukayi daga cikin store ita da Aysah da kuma accountant. Faryal ce ta ɗaga kai ta kalli sararin samaniya, wadda ke rufe da hadarin da ya gama haɗewa, alamun ako wani lokaci ruwa zai iya ballewa. Da muryar da ke nuna irin gajiyar da ke tattare da ita ta ce, "Ya kamata in wuce gida yanzu, ina ga a bar sauran ayyukan kawai zuwa gobe idan Allah ya kai mu".
A tare Aysah da account ɗin suka gyaɗa mata kai tare da faɗin, "As you wish Ma'am". Jinjina musu kai tayi sannan ta wuce zuwa office ɗin ta. Ta tattara yan kayayyakinta ta fito, wurin motarta ta nufa, ta shiga taja, ta fice daga Companyn.
Rage gudun motarta ta tayi saboda hango hold up ɗin dake gabanta, ta ɗan ciji lips ɗin ta na ƙasa kafin ta juya kan motar ta sauya hanya, duk da cewa ba ta son bin wannan titin saboda it's not safe ga mace gsky amma ba yadda zatayi dan wancan hold up ɗin data gani sai ta iya kaiwa sallah Isha a wurin. Shuru titin yake, dan ɗaiɗaikun motoci ne ma suke wucewa ta wurin, take accelerator ɗin ta tayi amma sai motar ta fara mata jerking, kafin ta mutu ma gabaɗaya.
Ƙoƙarin sake tada ta tayi amma ta ƙi tashi, fita tayi ta buɗe bonnet ɗin motar ta shiga duba abin da za ta iya dubawa, sannan ta koma ta sake mata key amma still ta ƙi tashi. Wayarta ta ɗauka ta kira number Malam Yusuf amma bata tafiya. Ta koma kan ta Hadiyyah, ita ma kiran baya tafiya, gabaɗaya ma network ɗin kan wayarta ta ya ɗauke. Dafe goshinta tayi cikin damuwa da rashin sanin abin yi, ta kalli titin da motoci suke wucewa jifa jifa, sai kuma ta kalli sama, wadda tayi duhu sosai kamar dare.
Yayyafi aka fara, wanda ya sanya ta yin surrender, ta shiga ƙoƙarin tsayar da motocin da ke wucewa amma babu wadda ta tsaya. Ta gama saddakarwa zata koma mota kawai ta zauna, sai ganin wata mota tayi ta yi reverse ta tsaya a gabanta. Duk da cewa taimako take buqata, amma sai da gabanta ya faɗi, ta ɗan yi baya kaɗan.
Glass ɗin motar aka sauke, wanda ya bata damar ganin mutanan ciki, Fayyad ne da wani mutum. Ajiyar zuciya ta sauke a yayin da Fayyad ɗin ya ce, "Faryal, me ya faru? Me kike yi a nan?". Ya tambaya cike da kulawa.
"Wallahi Fayyad, motata ce ta samu matsala".
"Meye matsalarta ta?".
"Ban sani ba whl, kawai ta fara jerking ne sai kuma ta mutu".
Buɗe motar yayi ya fito suka nufi wurin motar Faryal ɗin, ya shiga dubawa bisa kwarewarsa. Fitowa ɗayan mutumin ma yayi, suka haɗu wurin duba motar saidai duk ƙoƙarin su motar taqi tashi.
Fayyad ne ya ɗago ya kalli Faryal kafin ya ce, "Abinda za'ayi yanzu Faryal, ki shiga sai mu kai ki gida. Magriba ta kusa and it's rainy. Bugu da ƙari, wurin nan it's not safe. Ki rufe motar idan kikaje gida, sai a samu mechanic ya zo ya ɗauke ta".
Jinjina kai Faryal ɗin tayi, dan ta san ba ta da wani zaɓi. Jakarta ta ɗauka sannan ta kulle motar ta wuce motar su Fayyad ɗin, ta shiga suka ɗau hanya.
Ya tambayi address ɗin ta faɗa masa, sai gashi within 15 minutes sun isa. Yayi horn mai gadi ya buɗe suka shige. Saida suka yi parking sannan Faryal ta buɗe ta fito, a bangaren driver inda Fayyad ke zaune ta tsaya tare da faɗin, "Na gode sosai Fayyad, da ba dan kai ba, ai da ban san abin da zai faru ba. Ka sake taimaka min for the second time, you have really saved my life, thank you once again".
"Kai haba Faryal wannan ai ba komai bane. Kuma ba ga shi ba ma naga gida Umm? Yanzu dai ki shiga ciki kinga akwai yayyafa kar ya saki mura".
Faryal ta saki ƙayataccen murmushi jin daɗin yadda Fayyad ɗin ke nuna mata kulawa ako da yaushe, kafin ta ce, "To Allah ya kai ku gida lafiya. Mahmoud, na gode fa". Ta faɗa tana dagawa abokin Fayyad ɗin hannu, wanda ta ji Fayyad ɗin na kira da Mahmoud. Daga nan ta shige ciki su kuma suka yi reverse suka fice.
Sai da suka hau hanya sannan Mahmoud ya kalli Fayyad wanda yake ta faman sakin murmushi ya ce, "Shegen kaya, ka samo me maiƙo fa, ita ɗin ma kamar sauran ce?".
Fayyad ya yi saurin girgiza kan sa indicating NO to Mahmoud question kafin ya ce, "Ta bambanta da sauran, ita tsakani da ALLAH nake son auren ta, sai dai i haven't even proposed yet".
"Amma kana ganin ba za a samu matsala ba kuwa?". Mahmoud ya sake Tambaya.
Dan kallon gefen ido Fayyad ɗin ya masa kafin ya ce, "Na san taku na Mahmoud, dan haka kar ka damu".
"Shikenan tunda ka ce haka". Mahmoud ɗin ya faɗa.
*** *** ***
Tana shiga falon nasu, ta tarar da Appa, Maama da kuma sauran yan'uwan ta. Ƙarasawa tayi tana faɗin, "Yaushe ka dawo Appa?".
"Yanzu yanzun nan Faryal, na dawo ina ta tambayar ki, mahaifiyarki ta ce har yanzu ba ki dawo ba, nace to Maybe yau an samu aiki da yawa a Company".
"Wallahi kuwa Appa, kamar ka sani. Kuma abin da ya ƙara bata min lokaci ma motata ce ta samu matsala a hanya, i just got a lift fa".
"Oh no, gsky in haka ne dole a saka miki order wata sabuwar motar. Amma yanzu ya aikin? Ba dai wata matsala ko?". Appa ya tambaya ba tare da ya damu da batun lift ɗin data ambata ba.
"Alhamdulillah Appa, komai yana tafiya yadda ya kamata".
"Yanzu kin kira mechanic ne?". Maama ta tambaya.
"A'a, yanzu dai nake tunanin kiran nasa dama".
"Idan ya gyara ya kawo ta, ki ajiye ta ki ɗauki ɗaya daga cikin nawa ki riƙa amfani da ita kafin a kawo miki sabuwa".
"To Appa, na gode sosai. Allah Ya ƙara buɗi". Ta faɗa tana Murmushin jin daɗi.
"Ameen ya Allah. Ina fata dai babu wanda yake da wata matsala ko?".
"A'a Appa". Hadiyyah da Nasar suka amsa a tare.
"To ni zan ɗan shiga ciki in huta". Ya ƙare maganar yana kallon Beta wadda ke zaune a gefensa. "Beta, Appa zai shiga ciki ya huta, ya za'ayi kenan?".
"To Appa, a fito lpy". Murmushi yayi ya shafa kanta kafin ya miqe ya wuce ciki.
Tashi itama Maama ta yi ta bi bayansa, a daidai lokacin kuma suka ji kiran sallar Magriba. Faryal da Hadiyyah suka miƙe suka nufi ɗakinsu.
Hadiyyah ce ta fara shiga ta ɗauro alwala, sannan Faryal ta shiga, wanka ta fara yi kafin ta ɗauro alwalar ta fito.
Ko da ta fito, Hijab kawai ta sanya ta tada sallah, tana idarwa kuma ta jawo wayarta ta kira mechanic sannan ta tashi ta shirya ta fita neman abinda zata sawa cikinta.
Dinning ta nufa taci abinci, sannan ta koma ɗakin inda ta samu Hadiyyah zaune a kan gado tana aikinta na chatting, gefenta ta zauna tare da faɗin, "Ke kin san wa ya kawo ni gida kuwa?".
Hadiyyah ta ɗan kalle ta kafin ta ce, "Wa?".
"Fayyad".
"Fayyad? Dan Allah fa?".
"Eh, wallahi...". Nan ta bata labarin abinda ya faru da yadda suka haɗu.
Hadiyyah ta gyara zama tana ajje wayarta ta ce, "Ni kuwa Faryal, a fahimtata, sai nake ganin kamar Fayyad ɗin nan son ki yake kawai dai yana jin nauyi ne ko kuma yana tsoron faɗa miki".
Kafin Faryal ta yi magana, wayarta ta fara ringing. Tashi tayi, ta ɗauko ta amma sai ta tsaya ta zubawa screen ɗin ido kawai.
"Wa yake kira?". Hadiyyah ta tambaya ganin yadda tayi tsaye a wurin.
Ajje wayar Faryal tayi ta koma inda ta tashi ta zauna tana faɗin, "Hamdan".
"Au baza ki ɗaga ba?". Hadiyyah ta faɗa tana kunshe dariyarta. Faryal ta watsa mata wani mugun kallo ba tare da ta ce komai ba.
Haka kiran ya katse, wani ya sake shigowa shi ma ya katse, sai a na ukun Hadiyyah ta miƙe ta ɗauki wayar tana faɗin, "Ki sa ta a silent idan ba za ki ɗauka ba". Daidai lokacin da wannan kiran ma ya katse.
Tsayawa tayi duba missed calls ɗin kafin ta ce, "Hamdan two missed calls, Barr Hashim on...". Kafin ta ƙarasa maganar, sai ga wani kiran ya sake shigowa. Ta dubi sunan kafin ta kalli Faryal ɗin ta ce, "Fayyad ne".
TO MASU KARATU, ME KUKE TUNANIN ZAI FARU YANZU DA HAMDAN, FIRST LOVE ƊIN FARYAL YA SAKE WAIWAYOWA?
SHIN FARYAL ZA TA IYA RABUWA DA SHI DA GASKE KAMAR YADDA TA FADA, KO KUWA TSOHUWAR SOYAYYARSU ZA TA SA SU SAKE DINKEWA?
MEANWHILE, BARR HASHIM DA FAYYAD, WAƊANDA FARYAL ƊIN TA ƊAUKA MATSAYIN ABOKAI, SUN FARA ƘOKARIN NUNA MATA RA'AYIN SU A KANTA. ME KUKE TUNANIN ZAI FARU A GABA?
WANE NE FAYYAD?
ME YA SA ABOKINSA MAHMOUD YA TAMBAYE SHI GAME DA FARYAL DA CEWA "SHIN ITA MA KAMAR SAURAN CE?".
MENE NE RA'AYINKU READERS?
WANENE FAVORITE DIN KU A CIKIN SU UKUN?
WA KUKE FATAN FARYAL TA KASANCE TARE DA SHI?