Page 23
by @oumamani
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 23
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Murmushi wanda yafi kuka ciwo Abba yai yace "ba batul bace mahaifiyar mimi".
Cike da Mamaki su Baffa suke kallon sa, kasa jure wa Abie yai yace "ba ita bace mahaifiyar ta?"
Daga kai Abba yai yace "bara a takaice na baku labarin rayuwar ta"
*WAIWAYE*
Kamar yadda kuka sani haihuwa 3 ne Umma tai amma haihuwar ta farko ta haifi Yan biyu mata masu kama da juna inda aka sa musu suna Khadija da Fatima Batul sai ta biyu ta samu Aisha ta uku kuma ta kara twins maza Kamal da Khalil.
Sun taso kansu a hade duk da Khadija ta kasance mai sanyin hali da mutukar hakuri yayinda Batul kuma ta kasance Mai zafi da rashin daukar raini, kamar su daya sak don ta halayen su ne kawai ake banbanta su da kuma saurin maganar Batul.
Ajin su daya a makaranta komai tare suke basa boyewa juna komai, wannan hadin kan nasu ba karamin faranta ran iyayen su yake ba.
A lokacin da suke da shekaru sha uku wani mummunan abu ya faru da wannan ahalin wanda ya kasance sanadiyar tarwatsa musu farin cikin su.
Cikin sauri Umma ta fito daga kitchen ta daga kai ta kalli yadda garin ya hada hadari sosai gashi bata da magin da zata sa a girki ga kuma Magriba ta doso kai, kallon Khadija tai dake xaune tana bitar karatun Qur'ani.
Daki ta shiga ta dauko kudi ta mikawa Khadija tace "ungo Mamana yi sauri kije shagon Muntari ki siyo min magi na 200 da onga na 100 kinga magriba ta doso kuma gashi hadari ne a garin bana son aiken su kamal ne don wasa zasu tsaya yi."
Cikin nutsuwa ta mike tace "toh Umma" karbar kudin tai ta fita daga gidan tana tafiya cike da nutsuwa.....
Kusan minti 30 da fitar ta amma bata dawo ba, Batul da hankalin ta yaki kwanciya tun fitar Khadija ta kalli Umma da itama hankalin nata ba'a kwancen yake ba don har an Kira sallah tace "Umma bara naje na dubo ina ta tsaya, kinga har ynxu bata dawo ba kuma shagon Muntarin ba nisa ne da shiba"
Cikin fargaba Umma tace “kiyi sauri don Allah kema kar ki tsaya kinji”
Daga kai kawai tai ta sa hijab dinta ta fice daga gidan, shagon Muntarin ta fara zuwa amma yace mata bai ga Khadija ba, hankalin ta a tashe ta soma zagaye unguwar ko taje wani shagon bana muntarin ba amma duk inda taje sai ace mata bata zo ba.
Daidai wani uncompleted building dake kasan layin su tazo wucewa taji kamar muryar Khadija cikin kuka tana fadin "don Allah kayi hakuri ka kyale ni mutuwa zanyi"
Wani irin bugawa kirjin ta yai cikin sanyin jiki da kasalar data rufar Mata jikin ta na wani irin rawa ta zagaya cikin ginin da sauri ta runtse idonta ganin wani mutum dake sanye da bakaken kaya ya danne Khadija dake kwance tsirara duk ya yaga kayan jikinta ga ruwan sama dake dukanta..
Wani karfi ne yazo mata tasa ihu Wanda ya fargar da Mutumin da sauri ya daga Khadija ya juya da nufin guduwa batul ta maza ta cafki hannunsa dambe suka fara Yana son ya kwace kansa ita kuma tana kaimasa duka da karfi tana kokarin bude fuskar sa don ya rufe fuskar da hular rigar sa, karfin mace dana miji ba daya hankada ta yai da karfi Wanda ita kuma dake rike da hannun sa ta fincike abin hannun da taji.
Guduwa yai bata tsaya bin sa ba ta kwasa a guje gurin Khadija dake kwance cikin jini tana kuka, tana zuwa ta rungumo ta a jikinta tana fashewa da kuka, wani irin kuka Khadija itama ta kara fashewa dashi mai cike da tausayi da rauni.
Cikin rawar murya tace "Batul ya cuce ni ya raba ni da martaba ta"
Runtse ido Batul tai ta cire hijab dinta ta lullubawa Khadija, cikin karfin hali tace "Zaki iya tashi mu tafi gida"
Girgiza Mata kai kawai Khadija take idonta a rufe mike wa tai tace "ki tsaya kinji bara naje na Kira Umma"
Daga mata kai Khadija tai tana rufe idonta.
Cikin sanyin jiki Batul ta nufi gida a kofar gida ta tarar da Umma da Abba suna tsaye da alama Abban ya dawo ne.
Kallon ta kawai suke ganin tana tafiya tana kuka ga ba hijab a jikinta, da sauri Umma ta riko ta tace "lafia kin ganta Batul"
Fadawa jikin Umma tai tana fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro
Cikin tsinkewar zuciya Umma tace "ki min magana mana bana son iskanci"
Nuna musu hanya kawai take tana kuka, Abba ne yai dauriyar riko batul yace "Batul muje ki nuna min inda take"
Tana gaba suna binta a baya har suka isa kangon, a lokacin da suka isa Khadija bata numfashi tayi fayau kamar ba rai a tare da ita.
Umma da kafafun ta ke rawa ta isa kusa da Khadija ta kasa kuka ma cikin rawar jiki ta warware hijab din da batul ta yafa mata ta sama ta a jikinta, janyo ta tai gabanta na faduwa.
Abba daya fahimci halin da aka jefa yarsa ya juya da sauri yace "bara na samo mana abin hawa mu kaita asibiti,"
Umma bata iya magana ba idonta kuri akan Khadija da bata numfashi, bai dade ba ya dawo da adaidaita shida Umma ne suka shiga ni kuma Abba yace na koma gida.
Lokacin da na shiga gida da kyar na iya zama akan kujera Jin wani abu a hannuna yasa na bude shi, wani kyakkyawan bracelet na gani sai kwalli yake wani irin jifa nai da shi cike da tsanar ko waye mai shi don nasan shine silar lalacewar rayuwar yar uwata.
Kamal dake kallona yaje ya dauko ya kalle ni yace "Ya Batul me yasa kika yar da shi na waye ne wannan abin kingan sa mai kyau".
Ban basa amsa ba sai hawayena da nake sharewa kawai
Aisha ce ta kalle ni don itama tana da dan wayo shekarar ta 11 lokacin tace "Ya Batul ina Ya Khadija dasu Abba"
Cikin dauriya nace "sun tafi Kai Khadija asibiti bata da lafiya"
Fuskar tausayi dukansu sukai suka ce Allah ya bata lafia
**********
Lokacin da su Abba suka kai Khadija asibiti kin karbar ta akai wai sai an zo da dan sanda, dole Abba ya kira kawu Nasiru ya fada masa halin da ake ciki.
Cikin dimuwa Kawu Nasiru ya kira wani dan sanda dake unguwar su tare da shi suka zo asibitin sannan aka shiga da Khadija, numfashin ta aka soma samu ya dawo daidai sannan aka duba ta abin tausayi har dinki aka mata don Wanda ya mata fyaden karfi yasa Mata.
Sai da tayi sati daya a asibiti sannan aka sallame ta kuma tunda ta farka batai magana ba, batai kuka ba ko an mata magana sai dai kawai ta daga kanta ko ta girgiza kanta, Batul kuwa bata taba zuwa ba kullum tana gida ita ke kula da abincin su.
Tuni labarin abinda ya faru da Khadija ya karade Yan uwa da mutan unguwa, don tunda uwani taji da hama suka shiga barbadawa, inda Shamsiyya ma ta fada a makarantar bokon su da islamiyya cewa an kama Khadija tana iskanci shine aka fake da cewa fyade aka mata.
Ranar da aka sallami su Khadija, ina xaune a tsakar gida ina tankade garin masarar da zan mana tuwo anjima suka shigo Umma ce rike da Khadija dake tafiya a hankali sai Yakumbo a bayan su.
Dagowa nai muka hada ido da Khadija kawai ta ware min hannunta, cikin karyewar zuciya na mike da gudu naje na rungume ta itama rungume ni tai kawai muka fashe da kuka.
Umma itama da kukan yazo mata shigewa daki tai tana fashewa da kuka, Yakumbo ce ta goge hawayen ta ta shiga rarrashin mu.
Da kyar mukai shiru na rike ta muka shiga palour, sai dai me muna zama Uwani da Hama suka shigo.
Kallon Khadija Uwani tai tace "sannun yar nan ashe haka abu ya kasance toh Allah ya kiyaye gaba amma kam an cuce ki ynxu ke waye ma zai aure ki bayan wannan tabon da aka shafa Miki."
Hama ce ta cafe da fadin "ai abin tausayin ma in an samu wani ya aure ta tofa iyalan ta ne abin tausayi shiknn sai ana musu gori cewa Uwarsu ba budurwa aka same taba.."
Umma da ta fito daga daki tace "bakin ku ya sari danyan kashi , in shaa Allah ba abinda zai biyo baya sai alkhairi kuma kaddara ce tana kan kowa. Kuma kun yafi yaran nan"
Da sauri Uwani tace "dakata Sadiya ban gane mai kike nufi da kaddara na kan kowa ba badai fata kike ace muma yayan mu amusu fyaden bakoh?"
Hama tace "kyaleta Uwani inaga bakin ciki take mana mu ya'yan mu suna nan da budurcin su ita kuma nata gashi an dauke na daya saura biyu"
Umma zatai magana Yakumbo ta daga mata hannu, kallon su Uwani tai tace "xaku iya tafiya in kun gama fitsarar taku zan hadu da mazajen naku"
Cikin dan tsoro suka fita don sun san halin Yakumbo bata sakar wa sirika fuska kuma yayanta suna matukar Jin maganar ta, tabbas in ta fada musu sun kade..
Matsa hannun ta nai dago idon ta dake zubar da hawaye tai ta kalle ni, murmushi na sakar Mata ina goge Mata hawayen...
A daren ranar na nunawa su Abba abin hannun dana cire a hannun mutumin, naso yarwa Abba yace na ajiye wata ran zaiyi amfani.
Tun daga ranar rayuwar mu ta sauya koda muka koma makaranta gaba daya sai aka tsane mu duk inda muka wuce sai an nuna mu ana fadin gasu can waccan ce wacce aka kama tana iskanci, a islamiyyar ma bamu tsira ba gashi a unguwa duk kawayen mu sun daina kulamu.
Hakan yasa nima na Kara zama mara hakuri da farko in aka zage mu shiru nake amma daga baya daina shiru nai ana zagin mu ina ramawa in ta kama ma na zaune yan iska mu dambatu.
Dole Abba ya chanja mana makarantar boko da islamiyya, kawayen layin mu kuma duk na watsar da Yan iska, a unguwar ma da maman Hidaya kawai muke shiri don lokacin tana amarya.
Rashin kawayen da nai yasa muka Saba sosai da cilla, a gidan su ake mana markade kuma ni nake kaiwa, tun in nakai muna fada da shi sbd a lokacin yana ganiyar rashin jinsa duk da ya girme ni kuma in ya min abu ramawa nake har muka zo muka Saba sosai.
***