NI DA YA NABIL

008

by @swrites22

_ NI DA YAYA NABEEL _



  _YOUNG WRITER✍️




* 008 *




Ita kuwa Asum tana shiga daki ta samu wayarta na ruri 'Naela' shi ne sunan daya bayyana a kan screen ɗin wayar. Dauka tayi da murmushi akan fuskarta tace, "Kaga Matar habiby, shikenan kuma tunda habiby ya dawo aka watsar damu da karatun ma bakidaya".

"Ki bari kawai ke dai yar uwa in ana maganar aljannah wa yake kawo wani zancen yahudu tuba babu". Dariya Asum ta shiga yi kamar wata zararriya, ita kuma Naela ta sake fadin, "Ah tho kinga laifi na ne? In ban tsaya na Kula da mijina aljannatah ba wa zai Kula min dashi. Amma fa karki damu in sha allah gobe zan shigo".

"Ni kuma kinga goben zanyi tafiya ba". Da sauri tace, "Ba dai nigeria zaku wuce ba?".

 "Ah ah fa, Ya Nabeel zan raka Germany gobe da safe in Allah ya kaimu".

"Au tho da sauki ma ai. Ni fa kinga Assumi ina ma da magana dake, ya za'ayi ne?".

"Ummm, to ki bari idan mun dawo in sha allah, ko mu hadu a scul ko kuma ni in zo miki gida kawai".

"Keee ki rufamin asiri ina zaman zamana da mijina lpy na fito da matar Field Marshal guda, ahhh noo in kun dawo din dai ma yi magana, yanzu dai barin barki naga dare yayi".

"Ke fa matsalar ki kenan, ki tsaya mana ai bamu gama magana ba ko".

"Ai ba wata magana da zamu gama yanzu, dan nasan maybe ma kece da kwana mijinki na can na jiranki ke kina nan kina in tsaya bamu gama magana ba, wa ya gaya miki ana barin miji sakaka, to ni dai kinga nayi nan Allah ya bamu alheri". Tana gama fadin haka ta kashe. Zama Asum tayi a bakin gadon tana ɗan murmushin zantukan Naelan. (Naela ita kadai ce aminiyar Asum da ta jata a jiki sosai a universityn tasu, balarabiyar ƙasar saudiya ce, amma idan tana hausa Kai ka rantse haihuwar nigeria ce. Aure ne ya kawo ta Russia saboda mijinta dake aiki a nan)

Kayan jikinta ta tashi ta sauya zuwa na bacci kafin ta nemi wuri ta kwanta saboda wani ciwon kai da ya riqeta lokaci guda, ai kuwa ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita dan dama ranar gabaɗaya bata samu hutu ba.

A bangaren Nabeel kuwa sai 2am ya dawo gidan, bai samu kowa a ɗakin sa ba dama kuma bai tsammaci Asum ɗin zata zo ba kamar yadda yace. Wanka ya fara yi sannan ya dan harhada abubuwan da zai buqata a tafiyar tasu kafin ya haye gado ya kwanta.

Sai dai duk yadda yaso yin bacci kasawa yayi sai fama juyi yake from left to right. Tsaki yaja ya tashi ya zura bedroom slippers din sa ya fice, kamar zai nufi dakin Jumaymah sai wata zuciyar ta gargade sa da fadin satar kwana fa kenan? Tsaki ya sake ja yana mitar duk Baffah ne ya janyo masa wanna abun. A kofar ɗakin Asum ya tsaya yana tunanin ya shiga ko ya koma, ya rasa wani irin taurin kai ne da yarinyar kwata² ta raina shi, ba dan yau ɗin yace Kwanan ta bane yasan ai da Jumaymah sa ba zata barshi shi kadai ba, wani irin tausayin ta da kaunarta yaji ya sake huɗa zuciyarsa .

 Tura kofar yayi ya shiga, bai ganta kan gadon ba amma yaji motsin ta a toilet, kamar wanda akawa dole ya haye gadon ya kwanta, kamshin turarukanta da suka kama bedsheet din suka yiwa hancinsa sallama. Lumshe idanunsa yayi amma duk da hakan zuciyar sa zafi take masa wai yau shine da biyo mace daki, macen ma kamar wannan yar figigiyar yarinyar da in auren wuri yayi ya haifi kamar ta, tsaki yaja a karo na ba adadi yana gyara kwanciyarsa.

 Fitowa tayi daga toilet din tana hamma ba tare da ta lura da shi ba ta haye gadon ta kwanta, jin ta a jikin mutum ya sata waro idanunta da sauri ta bude baki zata zunduma ihu yayi saurin toshe mata bakin da hannun sa. Cikin takaici yace, "Whl kika sake kika min ihu saina babbalaki na wurgawa karnuka. Wato kece ma zan saka doka ki tsallake ko? To kije ki tambayi ita Jumayman banda zancen aurenki daya maidata abinda ya maidata ban taba jefar da kara ta ketara ba, ko ni na mata laifi ita ke bani hakuri, yau ma laifi na ne da nace Kwanan ki ne da yanzu ina dakina hankali kwance ban fito ina gararamba da tsakar dare ba, wato ke gaki yar gwal ko kinfi karfin ki kawo kanki".

Sosai maganar sa ta mata zafi ta buɗe baki zata mayar masa da martani sai kawai kuka ya kwace mata. Zare hannun sa yayi daga kan bakinta tare da jan tsaki. Da muryar kukan ta shiga faɗin, "Ni na saka ka raba kwanan ne, ai dama ba yau ka saba yin rashin adalci a tsakanin mu ba, yanzun ma kana iya zuwa ka taso ta ba sai kazo ka gayamin magana ba. Kuma ba za'a zo ɗakin ba karnukan sun daɗe basu ci abincin ba". Ta karashe tana yunqurawa da niyyar sauka daga kan gadon.

Fisgota yayi a zafafe ta fado kan kirjinsa, wani kukan ta sake fashewa dashi tana faɗin, "Ni ka sakeni, gwara in je in taso ma matar so ɗin taka abar bege, ni dama ai kabi ka tsaneni kamar ni na nemi a aura min kai. Gabadaya baka damu da jin halin da nake ciki ba ko dalilin da yasa banzo ɗin ba kawai zaka zo kana gasa min maganganu". 

Zubawa ɗan bakinta ido yayi a cikin guntun hasken dake ɗakin har tayi shiru. A nutse cikin wata irin calm voice yace, "I'm sorry to. To me ya hanaki zuwa?". Sake turo bakin tayi tare da faɗin, "Da ciwon kai fa na kwanta, kuma kuma". Sai kawai ta sake rushewa da kuka. Ɗan lumshe idanunsa ya sake yi cikin rashin sanin abin yi sai kawai ya haɗe bakin su wuri guda. 

Ƙoƙarin kwatar kanta Asum ɗin ta shiga yi amma yaqi sakinta har saida ya tabbatar kukan nata ya tsaya cak sannan ya raba bakin su yana gyara mata kwanciya a jikin sa yace, "It's Okay ai bansan baki ji daɗi bane. How are you feeling now?". Banza tayi dashi kamar bata ji ba sai wani mutsu mutsu take a ƙoƙarinta na gyara kwanciyarta, wanda shi kuma hakan ya fara affecting ɗin sa. Ɗan leqa fuskarta yayi, idanunta a rufe sai faman cuno ɗan bakinta take. 

Cikin wata irin sassanyar murya yace, "An baby talk mana, na san kina ji na kuma kin san bana so ina Magana ayi min shiru".

Ba tare data motsa ba ko ta buɗe idanun nata tace, "A'a ban sani ba, sai dai yanzu da ka faɗa na riqe. Amma na roqe ka dan Allah ka tashi ka tafi wurin matar Ka".

"Ba gaki ba, kema ai matata ce". 

"Eh, ni ma Matarka ce amma akwai banbanci tsakanin ni da ita". Ta faɗa tana waro idanun ta a kansa, harda wani zaro masa su.

"Okay akwai abinda take dashi ne wanda ke baki dashi, ko kuma akwai abinda zata iya wanda ke baza ki iya ba?". Marmar ta fara da idanu, yayi saurin faɗin, "Amma ai na yi apologizing ɗin ki ko. Ni bana san koke koken nan gsky". 

"Ni bazan haƙura ba, ayi min cin fuska sannan ace in yi haƙuri. Ka tashi ka tafi in da kake so ake son naka kawai". Jinjina kansa yayi kafin ya yunqura kamar zai tashi, sai kawai ya juyeta ya mata rumfa da faffadan kirjinsa yana sake haɗe girar sama data ƙasa. Zaro Idanu Asum tayi ta shiga ƙoƙarin ture shi amma ko gezau baiyi ba. "Kin hakura ko baki hakura ba". Ya faɗa yana wasa da harshen sa a cikin bakinsa.

 Muryar ta har wani sarkewa take wurin faɗin, "Na hakura Allah Hamma, na yafe ma".

"Ba hamma ba fadi wani sunan". Ya faɗa yana watsa mata wani kallon da ya sake hargitsata. Da sauri tace, "Yayanah, yaya Nabeel". 

"Basu min ba". Ya faɗa yana taɓe baki cike da iya shege. Yarfe hannu ta shigayi kamar zata fashe da kuka tace, "Dan Allah ka gyara, kar tsautsayi yasa ka fado kai na in mutu, kaga dai yadda kake". Sosai maganarta ta bashi dariya amma sai ya maze tare da faɗin, "In naki fa".

"Ai nasan baza ka so in mutu yanzu ba yayana, ko dan su Baffah ma dan Allah". Gyarawa yayi ya koma gefenta yana me jawota jikin sa yace, "Ga tsiwa ga raki, ya kamata ki rage ɗaya". Buɗe baki tayi zatayi magana ya ɗaura yatsansa daya kan bakinta tare da faɗin, "Shuru, bacci zan yi". Shurun kuwa tayi kamar yadda yace, amma a zuciyarta ta quduri niyyar whl yadda yazo yake yabon Jumayma a wurinta ita ma sai yaje ya yabeta a wurin Jumayma. Ai itama mace ce, dan haka zata tsaya ta fahimci likes da dislikes ɗin sa a hankali, sannan ta riqe masa wuya, ai da ashe kallon biri takewa ayaba, ashe dai yadda suke tunaninsa ba haka yake ba. Ashe yana da saukin kai har haka, to ai baza ma ta sha wahala ba wurin samo kansa. Da ire iren waɗannan tunanin bacci yayi awun gaba da ita.

Ko da suka tashi sallar asuba tare sukayi ta a ɗakin kafin ya fice, ita kuma ta tashi ta hau gyaran dakin, ta wanko toilet ɗin ta dan ita bata yarda ma'aikatan gidan su mata wani gyaran daki. Hijabin da tayi sallah ta dauka ta sanya kan kayan baccin dake jikinta sannan ta fita, part ɗin sa ta nufa kai tsaye sai dai baya ciki, nan take zuciyarta ta raya mata yana wurin Jumayma. Wani abu wanda ta kasa fahimtar kishi ne taji ya mata tsaye a wuya. Juyawa tayi zata fita sai kuma wani tunani ya zo kanta, wucewa tayi ta dauko kayan shara ta dawo, cire hijabin tayi, ta shiga gyara masa bangaren, saida ta kalkale ko ina ta sake sauya zaman duk wasu abubuwan da basu mata ba ta fesa room Freshener da taji kamshinsa ya mata kafin taje ta ɗauko turaren wutan da Umma ta saka mata a Kaya, tunda tazo ma batayi amfani dashi ba ta dai ɗauka ta adana. Tana saka shi kuwa gabaɗaya ɓangaren ya ɗauki wani kamshi na musamman me saukar da nutsuwa da sanya nishadi.

Tana kokarin fita sai ga mutum uku daga cikin ma'aikatan gidan na shigowa, dakatar dasu tayi tare da tambayar me ya kawo su, suka shaida mata sunzo gyara bangaren ne. Jinjina kai tayi kafin ta ɗago ta dube su tace, "To daga yau kar wanda ya kara shigowa bangaren nan ballantana har aje ga batun gyara, sai dai kuma in me gidan ne ya neme ku dan kansa to wannan kuma". Cikin girmamawa suka haɗa baki wurin amsawa da Okay Ma'am. "Kuje na sallame ku". Ta faɗa cikin bada umarni tana ƙara haɗe rai. Da sauri suka juya a ƙoƙarin su na fita sai ga Nabil ɗin ya shigo, binsu yayi da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ya amsa gaisuwar tasu, ya kauce ya basu hanya su fice.

Kasa tayi da kanta tare da faɗin, "Sannu da zuwa, ina kwana". Wucewa yayi yana amsawa da lpy.

Bin sa tayi da kallo tana shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka saboda ganin yadda ya basar da ita. Gani tayi ya tsaya cak, sai kuwa ya juyo a fusace yace, "Uban wa ya bawa masu aikin can izinin canja min tsarin falo?". Baya baya ta fara kafin tace, "Ni.. ni nice, ni na sauya da kai na basu bane. Amma in be ma ba bari in maida ma yadda suke da".

" Zo!". Ya faɗa yana tsaida idanunsa a kanta. Tsayawa tayi daga tafiyar da take da baya baya. A hankali kuma ta shiga takowa inda yake tana ƙoƙarin karantar yanayinsa. Tana Karasowa ya riqo tsintsiyar hannunta suka wuce ɗakin, tsayawa ya sake yi yana kallon dakin kamar wani bakon sa, sai kuma ya juyo yana mata kallon mamaki kafin yace, "Duk ke kikayi wanna aikin?".

"Whl duk ni nayi, ba wanda ya taba ma komai kaji na rants...". Katseta yayi da faɗin, "Ke dallah bance kimin rantse² ba. Tukunna ma wa ya saki, ko baki san akwai masu gyarawa bane?".

"Yanzu duk wannan uban aikin da nayi maimakon ka yaba min sai ka gwasale ni? To nace musu karsu Kara zuwa bangaren ka da sunan gyara, saboda turakar mijina sirri na ne, saidai kuma in kwanan Jumaymah ne ba yadda na iya in ta buqaci masu aikin su gyara mata, amma ni dai gsky a kwana na babu me shigo min". Ta faɗa cike da tsiwa tana cuno baki dan kar ma yace bai yadda ba. 

Shi kuwa zuba mata ido yayi kawai tunda ta fara maganar har ta gama, Murmushin gefen baki yayi mai sauti wanda ya sata saurin kallonsa ta kasan ido. "Jeki ki shirya kar lokaci ya kure, Allah ya miki Albarka". Yana faɗin haka ya wuce ya fara rage kayan jikinsa. Da sauri ta juya ta fice tana blushing cikin jin daɗi ta koma ɗakinta. 

 A gurguje ta hada abubuwan da zata bukata sannan ta fada wanka, tana fitowa ta shirya cikin wata dubai abaya green, tayi rolling mayafin, bata yi wata kwalliya sosai ba kwalli kawai ta sanya, ta murza lipgloss ta dauki handbag ɗinta ta fito janye da luggage ɗinta.

 A main parlour ta ajje luggage ɗin sannan ta wuce dining, takunsa ta jiyo a bayanta, da sauri ta waiwayo tana kallon sa, yayi kyau sosai cikin milk suit ɗin da ya sa, ga sajen nan da gashin kansa sai ɗaukan ido suke. Kujera yaja ya zauna yana fadin, "Kiyi abinda ke gabanki, bamu da time". Sai a lokacin ta lura ashe har ya ƙaraso ma bata sani ba, dan hararar gefen ido ta watsa masa saboda yadda yayi maganar kamar bashi ba. 

A plate ɗaya ta zuba abincin sannan ta zauna, ɗagowa yayi ya kalleta amma sai taqi yarda su haɗa ido, ta ɗauki spoon ta sanya masa a gabansa sannan ta sa nata ta fara cin abincin. Sai da ya kwashe kusan secs 60 kafin ya kai hannu ya ɗauki spoon ɗin ya fara cin abincin. Suna gamawa ya miqe ba tare da yace mata komai ba ya bar dinning ɗin ya wuce dakin Jumaymah.

Tashi tayi itama ta koma falo ta zauna tana waya da Adda Asmah har ya fito shi kadai da alama kuma ransa a bace yake, wucewa yayi ba tare da ya Mata magana ba, sallama ta yiwa Adda Asman ta tashi taja luggage ɗinta tabi bayansa, tana fitowa ɗaya daga cikin sojojin dake tsaron gidan ya karba sannan ya mata nuni da motar da Nabil ɗin ya shiga. Wucewa tayi aka buɗe mata ta shiga itama. Waya yake cikin harshen nasarar amma sai faɗa yake yana bada umarni gabaɗaya sai taga ya juye ya koma mata ainihin ya Nabil ɗin da suka sani. Rarraba ido ta shiga yi dan ita kanta da ba ita tayi laifin ba sai da faɗan da yake ya jefa Zuciyarta a firgici ballatana wanda ake wa. A haka dai har ta samu ya gama, ta ɗan saci kallonsa tana son tambayarsa abinda ya bata masa rai amma wata zuciyar ta gargaɗeta da faɗin Ke Asum kina zaune lpy ki raba kanki in dai baso kike ya huce a kanki ba. 

Juya fuskarta tayi side ɗin glass ɗin motar ta shiga kallon hanya, a hankali kuma ta fara bitar suratul Al Imran cikin ƙira'ar ta me dadin sauraro, ta kasan Ido taga ya kwantar da kansa jikin headrest ɗin motar ya lumshe Idanu, a haka har suka isa airport ɗin, anan ma wasu sojojin ne da yawa suka zagaye motar da alama kuma tare dasu suka taho ita ce kawai bata lura dasu ba.

Bude mata ƙofar akayi ta fito tana kalle² kai idan ana neman mazajen sojoji aka zo Russia an gama magana. "Ji wata lukutar masifa sai kace za'ayi yaqin duniya na uku?". Ta fada a Zuciyarta tana komawa gefen sa dan har ga Allah yadda ta gansu yau sai da Zuciyarta ta ɗau rawa. Tana ji yana wa wasun su bayanin data rasa ina ya dosa tunda ba aikinta bane, sai da ya gama sannan ya kalli agogon hannun sa ya wuce, da sauri tabi bayansa dan kar ya bace mata, wasu daga cikin sojojin kuma suka take musu baya har gaban jirgin kafin ya musu sallama ya shige. Mutum hudu daga cikinsu kuma suka bi bayansu zuwa cikin jirgin, da alama dasu za'ayi tafiyar.