Chapter 44
https://www.arewapen.com/book?id=6ab251c3cb0cfb2373811a7f
***
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
Chapter 44.
Wata baƙar dariya marar daɗin sauti mutumin ya yi, cikin muryarsa me tsoratarwa ya ce da ita.
"Wannan ta zama mallakina daga yanzu, tauraronta yayi daidai da wanda muka jima muna nema, yanzu aiki yabar kan mijinki ya koma kanta, ki gabatar min da ita a ranar bikin cikar shekara, kafin nan ki tabbatar da babu igiyar aure a kanta, munada ɓuƙatar mutane wanda tauratinsu keda hasken nasara irinta."
Ya faɗa yana ƙare min kallo.
Nan take Hafsa ta amsa da. "Umarninka abin bina ne, kariyar dodo ta tabbata a gareka, faɗa naka cikawa tawa."
Abin da ya biyo baya daga wannan ranar babban lamari ne daya ɗimauta rayuwa, cikin sati ɗaya kacal na fita a hayyacina, na daina tantance fari da baƙi, kwanyata ta rikice ta daina aiki da kissafi irina masu hankali, ni kaɗai haka nan sai inta sambatu da wasu abubuwa masu rikitarwa.
Sannu a hankali mu'amalata da mutane ta soma jada baya, cinikayyar kasuwancina bata tsaya ba taci gaba amma ta fannoni da dama da nike hagoranta an samu tazgaro.
Cikin wata ɗaya jal na rame na fita a hayyacina, saida takai ta kawo idan ba yarana Muhammad da Junaid ba, babu me iya raɓata, gani nan dai kamar ba mutum ba.
Haka rayuwata tacigaba da tafiya kullum wasu sababbin sauye-sauye na faruwa da ni, har takaiga kulawata kacokam ta tattara ne ta koma a hannun Hafsa, hatta da abinda zan ci ko zan sha daga gareta yake fitowa, zuwa lokacin na manta ko waye mijina Saminaka, kamar yanda shima nike da yaƙinin ya manta da ni, domin kuwa baya raɓar inda nike ko kaɗan ni da shi mun ɗauki lokaci bamu haɗuba, kuma koda mun haɗun bama magana a tsakaninmu yana yi kamar bai gane ni ba, nima haka ina mance ko wane ne shi a gareni.
A ranar da ƙaddara ta rabani da gidan mijina, ranace dabazan taɓa iya mantawa da ita ba, Hafsa ta gusar min da hankali, bayan sun lalata min tunani.
Bayan mun kwanta ni da Muhammad da Junaid a ranar ma harda Fahad wanda a yanzun yake liƙe min kamar me, ba zance kai tsaye lokacin da abin ya faru sunyi barci ba ko idonsu biyu.
Kawaide nasan nayi barci, kuma na farka a firgice cikin cikakken hayyacina har na tambayi Saminaka da Hafsa lafiya na gansu a kusa da ni sunyi cirko-cirko.
Wani sanyi da iska ne ya soma ratsani, bankawo komi a kaina ba na yunƙura da niyyar tashi tsaye, wani zazzafan mari da Saminaka ya sauke min saida na wuntsila ƙasa, kaina ya daku hancina ya fashe ya soma tsiyayar da jini.
Sai a sannan na gane ashe babu kaya a jikoni, bana iya gani da kyau danko marin har a idona sai da ya sauka amma a haka na soma ƙoƙarin kallon kan gadon.
Wani baƙi ƙirin ɗin ƙato na gani kwance tsirara haihuwar uwarshi sai minshari ya ke bugawa alamar yaji daɗin barcin.
Junaid da Muhammad kuwa sun ƙanƙame juna suna ƙananun kuka marar sauti.
Duka naji an rufe ni da shi tako ina babu ƙaƙƙautawa, dama kuma gani a suntule nan nahau ihun neman agaji cike da azabar raɗaɗin duka.
Ba dukan bane abin da ya razani illa kalmar sakin da ya ambata min, ya kuma bani umarnin fice ma shi daga gida a cikin daren.
A gaban yarana Hafsa ta furta min kausasan maganganu masu muni, sannan ta fice tana jaddada min in tbbatar dana fice tun kafin wanda ya aje ni ya dawo.
Ban iya ɗaukar komi ba illa rigar barcina na saka ina kuka me tsanani, na haye kan gado na rungume yarana su duka harda Fahad da shima ya farka, muka shiga raira kuka a tare.
Bansake tabbatar da Hafsa makira bace sai da ta zigo Saminaka ya koreni daga gidan shi a tsakiyar dare ya kuma kwace yaran shi, ina kuka suna kuka haka muka rabu, ya raba ƙauna tsakanin uwa da ɗanta, ɗanda bani da tabbacin sake samun wani bayan shi, yaronda shi kaɗai na mallaka a duniya da zanyiwa kallon jinina na kusa bayan mahaifana da suka rasu.
A wannan daren ƙaddarata ta sauya, rayuwata ta juye, lamurrana suka cakuɗe, duniyata ta yi zafi, komi nawa ya sauya.
Bayan na fito daga gidan Saminaka na jingina da jikin get ina kuka me sauti, kamar daga sama naga wasu mutane sun zagaye ni, suna saye cikin baƙaƙen tufafi, nayi fatan ace masu kisa ne, su ɗauki rayuwata a lokacin saboda tsabar yanda rayuwar ta fice min akai amma mi, ashe suɗin ƴan aike ne daga wata ƙaddarar dake jirana.
Sun ɗauke ni bayan nayi turjiya suka nuna min ƙarfi, sun tafi da ni a lokacin da nike neman taimako da agajin mijina ina kiran sunan shi akan yazo ya cece ni, suka nisanta ni da duniyar mutane, suka sauya min rayuwata gaba ɗaya da ƙarfin tsafi.
Na ɗauki lokaci me tsayi ina zaune a wani ɗaki cikin firgici da ɗimauta, babu ranar da ba'a zuwa ayi min wanka da jini, haka kuma babu ranar da zata zo ta wuce banga wani mummunan abu ba dangane da mutanen da ke rayuwa a gidan ba.
Bayan likaci me tsaye aka fiyar dani daga ɗakin aka kaini wani filli me girman gaske, aka zaunar dani akan wara kujera da wuta ta zagaye, wannan mutumin da nike gani tare da Hafsa kishiyata shine zaune a wajen, mutane na zuwa suna yi mashi sujjada wasu su aje ma shi jini, wasu kuma su soka jinjiran yara a jikin wani mashi, jininsu na kwarara zuwa ƙasa wajen wannan wutar data zagaye mu, tsoro gami da firgice da ɗimauta sune suka lulluɓe ni a baɗini a zahiri kuma ina nan zaune kamar gunki bani ko motsin kirki.
A gaban idona Hafsa itama ta zo, hannunta riƙe da jinjirin yaro akan idona ta ɗaga jinjirin, ta sauke tare da soke shi a jikin mashin, jinin jinjirin yayi tsartuwa ya sauka a kaina, har saida na saki ajiyar zuciya me ƙarfi, wani sanyi ya dira a zuciyata, na dinga jin sanyin jinin na baibaye ni yana mamaye gaɓɓan jikina, a kan idona jinin ya gangara cikin wutar ya soma ƙonewa, yanayine na shiga dana gagara tantacewa har saida na rintse idona na daina kallon wajen saboda dukan da zuciyata tashiga yi da sauri.
A ranar anyi abin da mutum marar imani da tsoron Allah wanda ya yarda akwai mutuwa bazai taɓa aikatawa ba, naga abubuwanda sosai na yi mamaki da ban haukace ba nan take saboda muninsu.
Daga ranar kuma rayuwata ta sauya, daga zamab ɗakin duhuwa da wankan jini zuwa tamfatsetsen katafaren gida na gani na faɗa, bansan yanda aka yi na wanzu a cikiba kawai na tsinci kaina ne a cikin gidan ina rayuwa, rayuwarda a zahiri komi ke tafiya daidai a baɗini kuma lissafina ya kuma kuncewa.
Abu ɗaya na riƙe shine, mutumin daya kawoni gidan wato Abdullahi Makafa ya kawoni ne a matsayin matar shi da muka yi auren tsafi, ya kuma killace ni ta yanda bazan taɓa iya fita ba, bayan ya tsaface gangar jikina gaba ɗaya, ya kuma ɗaure zuciyata da tsafinsa."
Nan Rimsha ta kwashe labarin komi ta bawa Noor daga yanda yake sadywa da ita shi da baƙaƙen Aljanun kan shi, har zuwa yanda yake gurmata ruwan gidan dudan ya shagaltar da ita tare da horar da ita akan ibadar daya gagara hanata yi, sai idan ya lalata ruwan gidan zuwa launin jini.
(To masu karatu nasandai yanzu kun gane ko wacece Rimsha wacce muka sani a baya matar Makafa, to wannan shi ne cikakken labarinta, yanzu zamu ɗora daga inda muka tsaya.)
****
Wata iriyar girgiza zuciyar Maryam ta soma yi tana cika tare da tumbatsa da kaɗuwa da jin labarin tarihin rayuwar Rimsha da irin baƙar wahala da gwagwarmayar data sha a hannun mijinta na bogi wato Makafa.
A hankali baƙin cikin ƙwayar idonta ya soma disashewa, wani haske me kaifi ya soma bayyana, wani yanayi da sam MARYAM bata san shiba ya soma lulluɓeta....
****
MUJAHEED.
A hankali yake takawa da Muhammad wanda sam jikin shi babu ƙarfin kirki, hatta da tafiyar sai a hankali yake iya yinta, har suka isa gaban motarda abokin shi Fawas yazo da ita don ɗaukarsu.
Back sit ya buɗe ya saka Muhammad ɗin, sai da ya tabbatar daya zauna sosai yanda bazai takura ba sannan ya rufe ya zaga ya shiga mazaunin me zaman banza ya daidaita zaman shi yana sauke ajiyar zuciya cike da gajiya.
"M.A." Fawas ya furta yana tada motar.
Kallon shi Mujaheed ya yi a ɗan gajiye tare da lumshe gajiyayyun idanuwansa sannan yace a taƙaice.
"What next?."
Murmushi Fawas ya yi tare da kallon Muhammad ta cikin miro ya ce.
"Muhammad ya ƙarfin jikin, fatan ka ji sauƙi sosai duda na lura alhamdulillah lafiya ta wadata ko?."
Sai da Muhammad ya yi tari meɗan tsayi, ya goge jinin daya fito ma shi sannan cikin disashiyar murya ya ce, "Alhamdulillahi sannunku da ƙoƙari Fawas Allah ya biya ku da lada."
"Mtswwww kana da problem Fawas na faɗa maka baya iya magana me tsayi amma kazo ka cika shi da surutu please stop it."
Ya faɗa yana ɗan ranƙwafowa zuwa baya kaɗan yace da Muhammad.
"Ka daina takura kanka sai ka yi magana kaga problem ɗin da hakan ke janyo maka ai."
Wani busashen murmushi Muhammad ya saki wanda ya sake fito da ramar da ya yi, har ƙasan zuciyar shi yana jinjina irin ƙyawun zuciyar Mujaheed ya bashi amsa da.
"Karka damu, bana jin daɗin yin shirun, da ace ina tare da ƙanwarka da yanzun haka ta cika ni da tarin surutai, kuma kaga ai dole zan biye mata ko?."
Ya ƙarashe zancen yana tare jinin da ke fesowa daga bakin shi, lokacin da yake maganar, yana kuma kallon Mujaheed da lokaci ɗaya ya haɗe rai kamar wanda aka aikawa saƙon mutuwa.
Gajeren murmushi Muhammad ya yi, yana mamakin yanda Mujaheed ke kishin abin da yake mallakinsa kuma halaliyarsa.
"Wai nikam yaushe dramer ɗin ku zata ƙare ni, kace min mijin Sistern ka ne amma kuma kana nuna wasu alamu kamar dai..." Fawas ya faɗa yana karya kwanar da zata sada shi da gidan da yake zaune.
"Kyale ni da wannan abokin naka, nasan matsalar shi ai." Muhammad ya faɗa yana jin gajiya da kasala na sake baibaye shi, tunawa da yayi da matar shi Zunaina.
Babu wanda ya sake magana a cikin su, duda kuwa Mujaheed nada abin faɗa amma hakanan ya shanye ya dake ya hana kan shi karya alƙawarin daya ɗauka tsakanin shi da zuciyar shi bayan Muhammad ya gama bashi cikakken labarin rayuwar da suka yi shi da Zunaina, idan dai ba son zuciya ba ya dace ace ya tausayawa Muhammad kuma ya haƙura ya kakkaɓe du wata soyayya da yake iƙirarin yana yiwa Zunainar....
AMANAR BILYN ABDUL CE....✍🏻