Chapter 3
by @hauwa3030
*💫MATAR SALMAN💫*
➡PART ONE
Page 3
Bayan sati daya da zuwansu Ya Salman, sai gahu sun kara dawowa wannan karon har da yayyen Mama. Naga sosai Mama ta dinga mamaki amma ta yi farinciki matuka. Sun dade suna tattaunawa, don ni Mama tace in tafi islamiya tun bayan da na gaishesu.
Har na fita ina tafiya ashe Ya salman ya biyo ni sai ji nayi ya kira sunans
”Rumaisah!”
Na juyo hadi da amsaawa ”na'am”
Ya karaso gabana sanye yake da kananan kaya sun matukar amsarsa yana sanye da bakaken glass wanda ya kara masa kyau da kwarjini.
Yace ”Muje na kaiki islamiyar a mota tunda akwai nisa ko”.
Na sunkuyar da kaina nace ”Nagode Yaya amma islamiyar mu in sunga an saukeni a mota.........”
Ya katseni da fadin ”Ce musu zakiyi Yayanki ne, ai zo muje.”
Ya bude min gaban motar, banda zabi don haka na shiga na tukure waje daya, muka tafi har muka isa bamucewa juna komi ba.
Ya sauka ya zagayo ya bude min ina fita sai ga Kulu da Zainab sun taho zasu shiga suma, sake baki sukayi suna kallommu har da tsayuwa.
Yace "Nasan kamin ki dawo mun tafi. Don haka ki kula da kanki, kiyi karatu sosai kinji?”
Kai na daga masa nace ”To Yaya ku gaida gida Nagode.”
Aljihunsa ya lalubo ya ciro five hundred yace ”Gashi kiyi kudin break....”
Na girgiza kai nace "Aah nan bama break na gode.”
Ya bata rai yace ”Zamu bata fa, waya gaya miki ana maida hannun kyauta baya ko kin raina ne?”
Nayi saurin girgiza kai sannan na karba hadi da yi mishi godiya baice komi ba ya shiga motar yaja ya tafi.
Su Kulu suka karaso wurina kallonsu nayi na dauke kaina na wuce gaba.
Da sauri suka sha gabana Zainab tace ”Ke Rumaisa waye wancan mai motan da ya saukeki?”
Na harareta nace ”Ina ruwanki?”
Kulu tace "Kar ki yadda ki fada mana maganar banza yanzu anan muyi miki shegen duka.”
Murmushi nayi babu shiri nace "Au Allah, to ko zaku gwada, hmmm bismillah mana.”
Zainab ta harareni tace zaki fada in muka tare ki a lungu yasin kuwa. Taja hannun Kulu tace ”Kulu mu tafi.”
Kulu ta harareni tace ”Karuwa kawai uwarki karuwa kema karuwa Allah wadaran zuriarku tir!”
Binsu nayi da kallo har hawaye ya taru a idona sai kuma na goge na shiga islamiyya.
Bayan an taso daga islamiyya canza hanya nayi don bana son in kuma haduwa da su Zainab, don abinda zai biyo bayan haduwar tamu bazatayiwa kowa daɗi ba nasani.
Bayan na idar da sallar isha nayi shirin kwanciya mama ta kirani don haka naje na sameta ta nunan tabarma tace ”Zauna.”
Na zauna tace "Rumaisa yayyena sun yanke shawarar daukeki a kauyen nan ki koma can birni gidansu Salman.”
Na dago da sauri fuskata sake cikeda murna nace ”Kai Alhamdulillahi Mama dama zaman garin nan ya isheni kwanan nan.”
Jikinta a mace tace ”Hmmm Yaro kenan, Rumaisa ba don kar suce na kara bijire musu ba wannan karon da nace su barki kawai, domin gidansu Salman zamanki a can akwai matsala Innar su Salman bata da kirki ko kadan.”
Nace ”Mama ba tare Zamu tafi ba?”
Ta girgiza kai tace ”Ni aure zanyi kwanan nan Rumaisa, dama saboda kece nakiyin auren to yanzu tunda zaki koma hannunsu Yaya zaman ne zan zauna yi?”
Cike da mamaki nace ”Aure kuma a ina Mama?”
Tace ”A birnin, gara nayi aure kawai da in koma zaman gidan yaya da matarsa, ke kanki naso ace gidan Ya Kasim wato mahaifin Salim aka kaiki don matarsa mutumiyar kirkice amma kamar Salman naga ya fi so ki zauna a gidansu tare da kannensa don duk mata ne.”
Nayi shiru na rasa me zance can nace ”Mama to ki tafi dani gidanki mana in kinyi aure.”
Murmushi tayi tace ”Bazai yiwu in ɗora mishi dawainiyarki ba alhali ba shi ya haifeki ba.”
A raina nace ”To ni ki kaini gidan Babana mana kawai ba shikenan ba.”
Ta lura da yanayinda na shiga sai tace ”Karfa ki daga hankalinki, ke dai kiyi taka tsan tsan ki zauna da kowa lfy kinji?”
Haka ta dinga kwantar min da hankali har bacci ya daukeni.
Sati biyu akai sai ga Ya salman ya dawo daukana. Wannan karon shi kadai ne, na tambayeshi Ya Salim yace min ya koma Abuja.
Dama na shirya kayana tuni kuma na sallami kowa, wasu na min fatan alheri wasu ko kallon ban ishesu ba.
Haka muka sallami Mama ta rakomu har waje tace "to Salman ga Rumaisa ka kula da ita sosai kasa ido, kar ka sassauta mata idan ta kauce don bana son ka shagwabata ba gata bane.”
”To.” Kawai yace yayinda yake saka kayana a mota. Ta kalleni tace ”Ke kuma kiyi taka tsan tsan da kowa domin birni ba kauye bane ki maida hankali ki nitsu banda rawar kai ki girmama kowa ki mutunta kowa kuma sai kiga kin zauna lafiya da mutane, sannan ki maida hankali wurin karatunki sosai banda wasa kinji?”
Nace mata ”to mama.” Hawaye ya ciko min ido na sunkuyar da kaina kawai, ina jin babu daɗi rabuwa da mahaifiyata, domin tunda na buɗe ido muke tare bansan kowa ba sai ita......
Ya Salman ya katse ni ta hanyar ce min in shiga mota mu tafi, ya bude min gaban motan na shiga sannan ya rufe. Ya sallami mama sannan ya zagayo ya shiga ya tashi motar Mama ta daga mana hannu ta yi ciki kayanta.
Na goge hawaye da ya gangaro min ya kalleni sai kuma yace ”daura belt.” Bansan me yake nufi ba na shiga dube dube.
Bai ce komi ba naga ya ɗan kwanto yasa hannu ya jawo igiya ya zagayeni hannunsa na taba jikina nayi saurin janye jikina.
Ya ɗan kalleni sannan yace "sorry belt din zai taimaka miki sosai saboda yanayin hanyar kauyen naku sai a hankali.”
Naga shi ma yaja ya daura daga nan muka fara tafiya. Sanda muka isa gidansu a Gadon Ƙaya rana ta yi sosai. Don haka ya sami inuwa a kofar gidan yayi parking na motar ya fita sannan ya bude min yace ”Sauko ga gidan nan ki shiga ciki.”
Na kalli gidan da ya nuna mun gaskiya babban gidane kam. Wata ce ta fito daga cikin gidan zamuyi sa'a da ita, tana ganinmu cike da fara'a ta karaso tana min sannu da zuwa.
Ya Salman yace ”Yawwa Sakina zo ki tayata ku dauki kayan nan ki kaita dakin Inna tayi wanka taci abinci sannan ta huta.”
Rass! Naji zuciyata ta tsinke jin an ambaci ɗakin Inna, bansan sanda na tsaya ina kallonshi ba har Sakinan ta dauki kayana tana mu tafi ma banjita ba.
Ya karaso gabana yana kallona yace ”Me ne ne?”
Girgiza kai nayi da sauri na sunkuyar da kai nace ”ba komi.”
Yace ”To ku shiga ciki.”
Na dauki ragowar kayana na bi bayan Sakina zuwa cikin gidan. Abinka da ɗan kauye sai kalle kalle nake ta yi abuna. Har muka isa ciki a tsakar gida naga wata mata tana wanke shinkafa, sai wata yarinya kuma na daka tattasai.
Na hangi wata kuma can tana wanki sai wake waken ta takeyi.
Matar ne data ganmu cike da fara'a tace ” Rumaisa har kun iso sannunku da zuwa, lallai kun shawo hanya Sakina ki wuce da ita dakin Innarku.”
Na ɗan russuna na gaisheta da fara'a take amsawa har tana tambayata Mama na. Wancan da take wankin ta dago a yatsune tace min ”Sannunki da zuwa.”
Na amsa sannan na gaisheta ta amsa min a wulakance.
Sannan matar ta kalli wacce take daka tace ”Zainab baki ga yayarki ba?”
Wacce aka kira da Zainab ta kalleni cike da fara'a tace ”Sannu da zuwa ina wuni?”
Na amsa mata ina murmushi sannan muka shiga dakin Inna nida Sakina, da yake ciki da Palo ne mun sami wata kuma kwance akan kujera da kyar ta amsa mana sallama Sakina tace mata "Raihana kicewa Inna ga bakuwa.”
Ta dago ta kalleni a yatsune itama sannan tace ”Ki zauna mana Innan zata fito yanzu ai.”
Na zauna sannan na gaisheta. Sakina kuwa tana ajiye kayana tace ”Ina zuwa Rumaisa Mama ta aikeni shago.”
Na ce ”To ko in rakakine ?”
Tace ”Aah Ya Salman yace ki huta tukunna ai.”
Tana faɗin haka ta fita da sauri. Muna nan zaune shiru da Raihana. Sai ga wata mata ta fito daga dakin kyakkyawar mace fara sol, jikinta dai dai batada tsawo sosai, ga gashi har gadon baya, kuma bakinta baki kirin leben kasa irin dai na 'yan kamaru, ko daga gani ma 'yar kamarunce babu tantama, kamanninta da Salman yasa na fahinci itace Innarsu. Sam bata tsufa ba har matar wajen nan ta fita girman jiki, wanda na lura kamar kishiyoyine. Kuma na fahimce waccar itace mahaifiyar Sakina da wacce ke daka a waje wato Zainab, don suna kama da Mamansu.
Da sauri na sauko daga kujeran nace ”Ina wuni?”
A wulakance take kallona kamar bazata amsa ba sannan daga bisani tace ”Lafiya lou sannunki da zuwa.”
Na amsa kaina a sunkuye gaba daya na tsorata na kuma sha jinin jikina da irin karban da yan dakin suka min ni wlh da dakin su Sakina ma aka kaini mamarsu tafi fara'a da kirki.
Munfi minti talatin zaune ba wanda yakara cewa komi har waccar mai wankin ta gama ta shigo ta na cewa ”Inna nifa sabulu na ya kare tass, naga wani a leda na dauka na karasa wankina dashi.”
Inna tace "ke dai Sadiya kin iya almubazaranci duk girman sabulun har ya kare? To babu ruwana wanda kika dauka kuma na Salman ne, ba ruwana ki tanadi amsa in ya tambayeki don yace in yaron nan mai masa wanki yazo a bashi sabulun.”
Raihana ta mike tana cewa ”tab! Yarinya kin taro aradu sabulun Ya Salman? Lallai yau zamu sha kallo a gidan nan, Wallahi tun wuri ki nemo masa sabulunsa kafin ma yaron nashi yazo.”
Sadiya ta harareta tace ” Ke dallah malama babu abinda zaiyi ai wanki nayi kuma sabuluna ne ya kare......Inna ina akwai wani sabulu a karkashin gado wanda su Nenne suka kawo miki daga kamaru?
Inna ta harareta tace ”ba duk ya kare ba ko Maman sakina ma ban basu ba, kwaya daya ya rage na baiwa Salman shine kika dauka. Dama ai abu a dakin nan baya dadewa ko man shafawa abbanku ya siyo ya raba sai na dakin nan ya kare, amma na su Sakina na nan, sabulun wanka, haka man goge baki ma haka kafin ace me wnn ya kare tass a dakin nan sannan kuce na fiye korafi kuna dai ganin su Sakina a dakinsu yadda suke tattalin kominsu, alhalin ba yawa muka fisu ba daidai muke.”
Sadiya tace ”wallahi Inna ba wani tattali da suka fimu, mako ne na tsiya.”
Inna ta tabe baki tace ”Ai shikenan ku kuka Sani gashi yanzu mun karu kuma, tunda ga wannan yarinyar ma a dakin nan zata zauna.”
Raihana ta kalleni da sauri sannan tace ”Kai wannan ƴar kauyen a dakin nan zata sauka?”
Inna tace ”Aah to ga dai kayanta nan kun gani.”
Sadiya tace ”Tabdijam, to wallahi sai dai ta kwanta palo a kasan kafet.”
Inna tace ”Oho muku kunfi ni kusa da ita.” Nikam duk naji ba dadi na kara takurewa wuri daya. Sakina ce ta shigo da sallama tana rikeda kulan abinci ta ajiyae tace ”Inna wai ga abincin Yaya Salman.”
Inna tace"Baya nan ne Salman ɗin?”
Sakina tace ”Eh abokansa sunzo sun tafi tare.”
Sannan ta kalli su Sadiya tace ”kuzo muci abinci, Rumaisa zo muje waje.”
Da sauri na mike kamar jira nake, nabi bayan Sakina waje ta shimfida tabarma an saka abinci a babban tire da miya a roba sai ruwan a katon jug me sanyi.
Sakina ta kalleni da fara'a tace ”Bimillah Rumaisa muci abinci su Sadiya kam sai sun gama yangansu zasu zo.”
Munacin abinci suka fito bayan sun wanko hannu suka karaso Sadiya kalleni a kyamace tace ”Ke Sakina da 'yar kauyen nan zamu ci abincin?Allah ma ya sawwaka.”
Ta wuce kitchen ta dauko plet tazo ta diba tuwon gefe gefe har zata saka miyar sai ta yatsuna fuska tace ”Hmm miyan duk ta jagwalgwala bari inje in dibi na tukunya, bazan iya wannan kazantar ba.”
Ta wuce kitchen tana gunaguni. Raihana ta kalleni tace ”Ke wallahi kar ki kuskura ki taba min gabana don naga baki iya cin tuwo ba, kuma ki rage loma da kiketa yankowa kato sai kace an sakoki daga igiya haba dan Allah, ko da yake baki saba da jar miya ba babu a House”
Nidai bance komi ba. Sakina ne tace ”wallahi duk abinda kuka fada a kunnen ya salman ko Abba, don sun hana mu wulakanta ɗan Adam ko yaya yake, bare ma wannan ƴar'uwarmu ce.”
Sadiya dake zaune can tace ”To munafuka annamimiya ai sai ki fada din tunda karya aka mata.”
Ni dai har ga Allah naji gara min zaman kauyen namu kuma. Don zama da wayan nan kam sai anyi da gaske!
*Muje zuwa!*
*RUMAISA SALMAN BY MAMAN KAUTHAR*