MATAR SALMAN

Chapter 4

by @hauwa3030

*💫MATAR SALMAN 💫* 


➡PAGE ONE
Page 4

Satina biyu a gidan na fara zuwa makaranta da Islamiyya, ajinmu ɗaya da Sakina da Raihana, Sadiya ce na gabanmu don yanzu zata zana ssce ma ita kam.

Gaskiya rayuwa bata min daɗi a birni sai dai godiyar Allah, a inda nake samun sassauci shine idan na tafi makarantar ko islamiyya. Amma in muka dawo gida ko motsi kwakkwara ban isa inyi ba, Inna da Sadiya sun sakoni gaba sosai, har gara in Abba na gida, gashi ya Salman tun randa ya kawoni washe garin yayi tafiya, ni a bakin Sakina ma naji tace min ya koma aiki a Lagos.

Bazan manta wata rana muka wayi gari ana ruwan sama kamar da bakin kwarya, duk muna zazzaune a palon Innah su Sakina ma suna dakinsu. Inna ta kalleni tace ”Niko Rumaisa ina son in miki wata tambaya tun tuni.”

Nace ”To Innah.”

Tace ”Ko Mamanki ta taba baki labarin inda mahaifinki yake kuwa?”

Na girgiza kai zuciyata ta shiga bugawa nace ” Aah bata taba bani labarinsa ba.”

Da mamaki take kallona tace ”Hmm Amina kenan, ai bazata gaya miki ba domin labarine mara dadin ji Rumaisa, sam bakida kykkyawan tarihi, mahaifiyarki ta cuceki ta sameki ta hanyarda bata dace ba.”

Na dago da sauri na kalleta zuciyata na tsinkewa, lokaci guda naji kamar kirjina ya fara toshewa......Sadiya ce ta yi farat tace ”Inna kenan Rumaisa shegiyace kike nufi?”

Raihana tace ” Tabdijam hmm! kuma shine a rasa inda za'a kawota sai nan don aja mana abun kunya da faɗe ayita nuna mu?”

Sadiya ta kalleni sannan tace ”Don haka ni dai kar ki kuskura ki nunani matsayin 'yar uwarki koda wasa kuwa.”

Sunkuyar da kaina nayi bansan sanda na fashe kukan bakin ciki ba. Me yasa Mama tayi min haka ta sameni ta hanyar da be dace ba, tunda in na fahinci Inna tana nufin ni Rumaisa shegiya ce banida Uba....Ya Salam! dama shine dalilinda yasa Mama batason in tambayeta waye mahaifina kuma ta na yawan kebe kanta tayita kuka a daki?”

Inna ce ta katseni da fadin ”Ke dallah bama son kukan munafurci anan tashi kije ki hura wuta maza ki daura mana abinci, da kin dauka bamusan komi bane, kokuwa kina nufin a bakina kika fara jin irin wannan kalmar, ai kedai Uwarki ta cuceki, tsakaninki da ita kuwa sai dai ku haɗe a gaban Ubangiji.”

Sadiya tace ”Wallahi kuwa...... a tashi aje a ɗora mana girki don mukam 'yunwa mukeji.”

Raihana ta karba tace ”Bare ma anyi ruwa kam dama sai a slow, a tashi aje a ɗaura maza.”

Na mike idona tuni har yayija, ina jin wani irin zafi a zuciyata, na fita na nufi kitchen a tsakar gida, sai ruwa ake tayi kamin na isa kitchen din har na jike sharkaf ashe itacen ma sun bari a waje ruwa ya gama jikawa.

 Haka na kai kitchen na hada murhu na hura wuta, na nemi wuri na zauna naci gaba da kuka sosai ina bakin cikin kasancewata a raye dama mutuwa nayi kawai da na huta da wannan bakin ciki da takaicin rayuwa.”

Na kai awa daya ina kokarin hura wuta amma ina yaki kamawa ga hayaki ya turnuke kitchen ko gani banayi da sauri nayi waje a gigice idona duk yayi ja sai kwalla ke zubo min, numfashina kuwa na barazanar ɗaukewa wanda rabon da naji irin yanayin har na mance.

Sadiya ta fito zata ban daki har zata wuce ta leka kitchen taga hayaki, ta shiga tafe hannu tana salati tace ”Yanzu tun fitowarki baki dora ba muguwa so kike ki kashe mu da yunwane yau?”

Shiru na mata tace ”Au ina miki magana kina tsaye ko? to wallahi kamin na fito daga bandaki ki fifita wutan nan ya kama, bayan yunwa har horo zaki mana da hayaki ki cika mana ciki muguwa kawai anyi gadon mugunta.”

Ta wuce bandaki, zuciyata kamar zata fashe hawaye kuwa yaki yankema idona. Har ta fito daga bandaki ta sameni zaune a wurin. 

Tace ”Kan ubancan lallai ma yarinyan nan taurin kai zaki min ko? zan nuna miki na fiki danyan kai.” Ta rufe leman hannunta ta wuce randa fuuu! ta debo ruwa cikin botiki ta nufi kitchen da isarta tajuye ruwan tsaf cikin murhu. Zaro ido nayi ina kallonta na tuna irin wahalar da nasha akan hura wutan nan. Murmushin mugunta ta yi tace ”Duk sanda kika gama hutawa kyaje ki hura wani don bazaki kashemu da hayaki ba.”

Ta shige ɗaki na bita da kallo sannan na fashe da kuka. Durkusawa nayi a bakin kitchen ina ta rusar kuka kamar raina zai fita bakin ciki goma da ashirin Ya Salam!

 Kawai sai ga Ya Salman kamar an jefo min shi, ashe tuni ya dawo ruwa ya hanashi shigowa shine yanzu da ruwan ya ɗan tsagaita ya shigo. Yana ganina cikin wannan yanayin yace ”Subhanallah! Ke me kikeyi a ruwan nan haka duk kin jike, me ya sameki?”

Ban kulashi ba kukana kawai nakeyi ina jin bakin ciki na na karuwa.

Ya karaso bakin kitchen ya riko hannuna yana kallona yace ”Rumaisa taso taso muje ciki kar mura ya kamaki.”

Na mike har sannan kallona yake yace ”Me ya faru dubi yanda kika jike, don Allah tafi ciki ki cire wayannan kaya.” Yana faɗin haka ya sakeni.

Inna ce ta fito daga daki tace ”ba wani canza kaya da zatayi.... don Allah sabar munafurci ba wuta nace ki hura ba? Shine kika barmu da yunwa, kika zauna cikin ruwa kika jike don munafurci ko?”

Na girgiza kai nace ”Inna har na hura wutan sadiya tazo ta ɗebi ruwa ta zuba a murhun kuma dama itacen sun jike.”

Tace ”Madalla tayi min daidai, ai tun lokacinda hadari ya hadu nace Ki shigar kitchen kikayi banza da maganata don ba uwarki bace ni ko?”

Nace ”Aah Inna Raihana ce kika ce ta shigar bani ba.....”

Ta katseni da fadin ”Zaki wuce kije ki hura wutan ko zaki tsaya kina min musun rainin naki?” 

Sai lokacin yayi magana yace ”Inna ai gaskia Rumaisa bazata iya hura wutan nan ba saboda murhun ya jike, kawai suje da Raihana su sayi ko gawayi ne don gaskia ina jin yunwa, bazan iya jiran wani icce sai ya kama ba.”

Inna batayi magana ba ta wuce ciki fuskarta a ɗaure. Ya kalleni yace ” Maza jeki cire kayan kice Sadiya da Raihana su zo yanzu ina jiransu anan.” Na wuce ciki ina goge hawayena, ya bini da kallo duk kunya ya kamani saboda yanda rigan ya kama jikina da ya jike.

Bayan na kirasu sai hararata suke na wuce ciki don canza kayana.

Ko da suka fita yacewa Sadiya maza ta wuce kitchen ya bata minti. ashirin ta hura wutan da iccen da ta jika in ba haka ba zata ci duka bana wasa ba. Ya baiwa Raihana kuma kudi yace ta wuce taje ta sayi gawayi maza tazo ta daura girki. Kowacce ta tunzura baki, babu halin yin rashin kunya, sun san halinshi don ya cire belt ya lallasa su ba matsalarshi bane.

Shigowa palon Innah yayi ya zauna suka fara gaisawa. Nikam bayan na canza kayana sai naji bugun zuciya ta ya canza kirjina ya toshe numfashina ya fara fita sama sama har wani barazanar daukewa yakeyi, ganin babu sassauci bansan sanda na fara kiran Inna ina zan mutu wayyo Allah na a taimakeni, ina dafe da kirji.

Da gudu suka shigo suka sameni cikin wannan yanayi Inna kam sai salati ya Salman bai tsaya wata wata ba ya fita waje da sauri kamin ya dawo Inna kam har ta fara kuka tana ta shiga uku, cak! Yayi dani ya tafi ya sakani a mota sai asibity emergency aka karbeni nidai bansan inda kaina yake ba banda azaba da kokuwa da numfashi babu abinda nakeji.

 Lokacin da na dawo hayyacina sai kalle kalle nake ina maida numfashi a hankali doctor ne ya shigo da Ya Salman a bayanshi

Ya sake duddubani sannan yace ”Yanzu kam ba wata matsala ko Rumaisa?”

Shiru na masa nidai. Yayi murmushi yace ”Gaya min me kike ji yanzu?”

A hankali nace ”Babu komai jikinane bana jin karfinsa.”

Yace ” Sannu kinji, ba wata matsala a hankali zaki warware inshallah.”

Sannan ya juya wurin Salman yace "don Allah a kula da ita sosai ciwon athsma nada hadari sosai.”

Ya Salman yace ”mu bamu san tana da athsma ba sai yau data sami attack.”

Doctor yace ”To a kiyaye pls.”

Da kai ya amsa masa docton yaci gaba da fadin ”kuma akwai ulcer ma don haka a sayi magunguna da aka rubuta mata duka Allah ya bada lfy kuna ita tafiya gidama.”

Anan suka fita da Ya Salman. babu jimawa ya shigo ya kalleni yace ”zaki iya tashi?” Na daga mishi kai alhalin inaji jikina ba karfi sam. Ganin yadda nake ta kokarin tashi na kasa yasaka shi isa bakin gadon ya dagoni, ɗan kwalina ne ya zame ya fadi, gabadaya gashi na ya baje har fuska dama ga tsawo ga cika ga kuma yauki gashi ban iya parking ba na saba da kitso ne.

Kallon gashin yakeyi da mamaki har ya shagala da sauri na fara lalubo dan kwalin zan ɗaura. Sai naga ya kai hannu ya tattare gashin gabadaya ya ce ”Ina rivon dinki?

A kunyace nace ”bani dashi.”

Ba zato ba sammani naji yace ”Dama an taba budurwa ba rivon ashe? Ke dai 'yar kauyece kawai.”

Na girgiza kai nace ”Mama tana saya min amma sun bace ne duka wasu kuma sun sake.”

Baice komi ya tattare min gashin sannan ya kawo hijabi ya sakamin ya riko hannuna yace ”Taso mu tafi.”

Yana rike da hannuna har muka isa bakin mota.

Muna isa gida muka tarar Inna har ta shirya da Mmn Sakina zasuje asibityn don dubo ni.

Suna ganinmu cike da mamaki Maman Sakina tace ”har an sallamota? Ikon Allah sannu Rumaisa.”

Inna ta karba tace ”Mu fa har mun tsorata yarinya kamar baza ta tashi ba?”

Salman ya kalli Sakina yace ”Sakina zo ki rike hannunta kuje ciki ta kwanta.”

Sakina tazo ta rike min hannuna duk sai sannu suke min, mun shiga palon inna na kwanta Sakina ta kawo min pillow. Nan naji ya Salman yana cewa "Inna Rumaisa athsma take dashi likitan yace a kula da ita sosai don ciwonta bai son sanyi baison hayaki ko kura da makamantansu don Allah a kiyaye.”

Sannan ya kalli Sadiya yace " Ke kuma Wallahi Wallahi ki kiyayeni don idan kika kuskura kika shiga hannuna sai kin yabawa aya zakinta!”

Ya kalli Raihana yace ”Ke kuma ci gaba biye mata zakusha mamakina.”

Ya juya ya fita fuska ɗaure Innah ta bishi da kallo sannan ta taɓe baki tace ”Kai dai jeka masifaffe, mutum ne baza a taba maganar arziki da kai ba kullum cin magani, naga matar da zata aureka da wnn uban zuciyar taka Salman.”

Maman Sakina tayi dariya tace ”Shi da akace ƴanmata na mutuwar sansa.”

Raihana ta karba tace ” Hmm Mama don ma bakiga yanda 'yan matan ke binsa yana ta gwalesu bane.”

Inna tace ”A hakan?mts***

Maman Sakina tace ”Ai inajin takaicin yanda ya nace akan Salima alhalin ba bashi aurentama zasuyi ba.”

Inna tace ” To saboda sun ganshi ɗan talaka ne mana kekuwa, ai sunsan shi ba ɗan kowa bane, bai da komi sai uban zuciya da miskilanci.”

Sadiya tace ”Aah fa so suke suyi mata auren dangi ne, Yaya kuma sai dagewa yake yi akanta, to itama fa sonshi take kamar ranta.......

Shigowarsa ne ya katseta, gabadaya shiru sukayi suna binsa da kallo suma su Innan. Sarai ya ji su sai dai baiyi magana ba ya wuce dakin Innan ya sameni ina kwance yace min ”Kinci abinci?”

Nace"Aah.”

Dan tsaki yayi sannan ya fito ba jimawa ya shigo da plet guda biyu da cokali.”

Ya dauko kular abincinshi ya saka mana, jalof ne da wake da manja.

Ya tura min gabana yace ” To tashi kici bari in gama sai inje in sayi maganinki.”

Na mike a hankali na jingina da kujera na ɗauki plet din na fara ci kadan kadan ina ware wake gefe guda don bana cin wake tun tasowa ta.

Yace ”Ba kya son wakene?”

Nace mishi ”Eh banaci.”

Yace ”Lallai ke dai 'yar kauyence da gaske.”

Bance komi ba har ya karasa cin abincinshi zai tashi Inna ta shigo tace "yawwa Salman zauna inada magana.”

Ya koma ya zauna ba tare da yace komi ba. Inna tace ”Su Sadiya sun kawo min kararka akan in suna tsaye da samarinsu kana zuwa ka musu wulakanci ka koresu hakane?”

Kai tsaye yace ”Inna korarsu nake yi......

Inna ta matukar kulewa tace ”To meyasa jika su zamuyi musha ne?”

Yace ”Ba haka nake nufi ba amma karatu zasuyi sai sun gama makaranta.....

Inna ta harzuko ta kama bala'i ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, tana ”Makarantar banza makarantar wofi, baza suyi ba wallahi, makaranta indai irin wacce Goggonku Amina tayi ne Allah wadarai wallahi, domin ni tun kan Amina naga illar nitsa a karatun boko don haka ni ƴaƴana suna gama wannan secondary aure zasuyi shine rufin asirinmu baki daya, don haka kar in kuma jin ka sake Koran musu samari, ba ruwanka kai da kake zuwa naka zancen wa ya Koreka? To ka kiyayeni kafita a idona na rufe.”

Baiyi magana ba mikewa yayi ya fita kayanshi. Nikam na kasa cin abinci saboda maganganun Inna, na dade ina juya maganar a raina.

Tunda na gama shan magunguna na na warware tass kamar babu abinda ya taɓa samuna.

Rannan nashiga ɓangaren Kawun naje gaisheshi sai na tarar kawuna na Abuja ma yazo suna tare, na gaishesu duka cike da fara'a suke amsa min.

Abbansu Salman ne yace ”Rumaisa Mamarki ta ɗaura aure fa, daurin auren ne mukayi dazu a masallacin unguwar nan.”

Kaina a sunkuye nace "Allah ya bada zaman lafiya ya sanya alkhairi.”

Sukace amin suna dariya sannan Abien su Ya Salim yace ”Sai in ta tare za'a kaiki gidanta kinji?”

Nace ”To Abie.” Daga nan na mike na musu sai anjima. Ina fita muka tafi aike shago ni da sakina.

Muna dawowa a kofar gida na hango ya Salman zaune kan kujerar roba da wata da bazata wuce saarmu ba ko Sadiya, tana tsugunne gefensa kanta sunkuye, abin mamaki fuskarsa daukeda murmushi yana kallonta alamar ita ke magana yana sauraronta.

Naja hannun sakina da sauri mukayi baya kadan tace min ”Lafiya?”

Nace ”Ke gulma ajali Ya Salman na gani da wata ko itace Salimar ne naga har murmushi yake tayi dama yana fara'a?”

Sakina ta yi dariya tace ”Kiji sharri Rumaisa, Yaya fa baida matsala kawai fahimtarshi ne har yanzu baki ba, amma duk da haka Yaya yana son Salima sosai shiyasa anfi ganin fara'arshi in yana tare da ita, amma sai iyayenta basasonshi sunfi so suyi mata auren dangi da danuwanta, kuma ma gidansu sai sunyi jami'a tuku......

Na katseta da fadin ”dama bata gama secondary ba?”

Sakina tayi dariya tace ”Kin ganta tafi mu girman jiki ko? Yarinya ce jin dadine kawai da hutu amma fa ta fimu don sa'ar su Sadiyane yanzu zasu gama secondary, kinga zasu bamu shekara daya.”

Tabe baki nayi nace ”Hmm sun dace kuma da Yayan, kinga mu tafi.”

Mun iso kofar gida har zamu shige ya kirani Sakina kam ta yi ciki abinta.

Na dawo nace "gani Yaya.”

Yace ”In babu abinda kikeyi a cikin gidan je ki share min dakina don Allah.”

Nace "To.”

Salima ce ta dago ta kalleni tace ”Wacece wannan kuma ban santa ba?”

A takaice yace mata ”kanwatace itama.”

Haka kawai na tsinci kaina da jin haushinta nidai, amma kam kyakkyawa ce yar gayu ga kwalisa. Fakar idonshi nayi na watso mata harara nayi cikin gida abuna.

Kallonshi ta yi cikin mamaki tace. "amma dai ba 'yar gidanku bace naga fa harara na tayi.”

Yace ”Rabu da ita ƴar kauyece.”

Tace ”wai kaga wata uban hararan da ta buga min, duk kannenka suna respecting dina amma ita ko gaisheni fa kaga ba ta yi ba.”

Murmushi yayi yana kallon fuskarta sannan yace ”Zan ja mata kunne kinji dear, yanzu ki tashi kije gida kar su Abba su fito su sameki kiji kunya.”

Ta turo baki a shagwaɓe tace ”Ai na gaya maka yau nazo ne don ka kaini in gaida Innahrmu.”

Ya mike yana fadi ”To bismillah muje cikin gidan.” Anan ta ɗauki ƙatuwar ledanta suka shigo cikin gida, har dakin Inna ya kaita suka gaisa da fara'a Inna ta karɓeta har ta ma rasa inda zata sakata. Ƙatuwar ledan ta direwa Inna wanda cike yake da sabulan wanka ne da trurarrruka masu tsada sai wanda ya gani, dayan ledan kuma juices ne kala kala da cookies sai cupcakes hmm. Inna sai wasahe baki take tana zuba godiya. Ya kai ta dakin Maman su Sakina ma suka gaisa sannan ya rakata har gidan ya dawo ya sameni har na gama sharar daki ina tsaye ina kallon hoton Salima kato manne a dakin nashi fuskarta ɗaukeda murmushi kyakkywace gaskia gata 'yar gayu.

Ko da ya shigo baimin magana ba ganin na shagala kallon hoto, ya wuce abinsa ya fara cire shirt din jikinshi.”

Motsin da naji ne yasa na juyo da sauri sai ganin mutum nayi da vest ba riga yana kokarin cire belt din wando ma. Zaro ido nayi a tsorace don ban taba ganinshi haka ba. Gashi kirar karfi ne da shi hannun nan a murde, dama Sakina tace min yana dukansu Sadiya da belt, don haka duk zatona zai cire belt ne ya jibgeni nima tunda nasan budurwarshi zata gaya mishi na harareta.

Naja baya na ajiye hoton zan gudu kawai sai naci karo da stool zan kife, da zafin nama ya taroni don saura kiris in kai kasa. A tsorace na rikeshi gam, baice komi ba sai da na dawo hayyacina na ga yadda na masa kyakkyawan riko kunyane ya kamani sosai na sassauta masa a hankali na cire hannuna da kyar na iya fadan ”Kayi hakuri.”

Sakeni yayi yace ”Zauna.”

Na zauna a kasan kafet kaina a sunkuye har sannan gabana bai daina faduwa ba, yace min ”Gobe zan koma Lagos, don haka ki fada min abubuwanda baki dashi sai na siya miki don in na tafi zanyi watanni biyu a can.”

Ji nayi kamar ince kar ya tafi don ko ba komai su Sadiya suna raga min in yana nan. Hawayene ya taru a idona har ya fara zubowa ba tare da na ankare ba, nayi saurin gogewa nace ”Babu komai.”

Shiru yayi sannan daga bisani yace ”Aah ki tuna dai?”

Na girgiza kai nace ”babu.”

Yace min ”kina da man shafawa da sabulu?”

Nace ”Aah.”

Yace ”Menene sunan manki?”

Nace ”cocoa butter”

Yace ”turarenki fa?”

Nace "babu ya kare”

Yace ”wanne zan siya miki?”

Nace ”Smart collection ne Mama ta ke saya min ko Sure.”

Ya gyada kai yace ”pad fa....

Da sauri na sunkuyar da kai cikin jin kunya na kasa dago kaina.

Yace ”ko baki sanshi ba?”

Nace ”Mama tana siyamin......

Baice komi ba
Shiru nayi nimakaina a kasa.
Har na cire tsammanin zaiyi magana sai kuma yace min ”Under wears fa kinadasu, ki fa bude baki ki min magana duk kannena mata ne nike siya musu komi.”

A hankali nace ”Mama ta na saya min suma din, inada sabbi ma.”

Yace ”Lallai Maman nan tana kokari wurin kula dake duk da a kauye kika taso, don haka in kinyi sallah ki dinga mata addu'a sosai.

Ni dai duk na kosa yace in tafi, na dai daga mishi kai kawai.

Can kuma ya dauko maganar makaranta yace ”Malaman ku suna yabon kokarinki a makaranta ki kara kinji kanwata ina son gaba daya dis year ku rubuta ssce ku tafi jami'a.

 Wani irin dadi naji har nayi murmushi don babu abinda nake buri irin naganni a Jami'ar Bayero da nake jin labarinta.

Yace ”Shikenan kince ba wani abu ko?”

Nace ”Eh Yaya sai dai dama inaso in anyi hutu inje gun Mamana.”

Ya girgiza kai yace ”Waya gaya miki ana zuwa gidan amare kawai kije ki takurata. za dai kije ki dawo amma in kina so in anyi hutu zan yiwa Salim magana yazo ya daukeki ya kaiki Abuja.”

Wani dadi naji zanje Abuja birnin tarayya naji ance garin 'yan hutu ne da jin dadin rayuwa.

Nayi murmushi nace "Na gode Yaya.”

Hannu ya daga min snn yace ”Is ok kina iya tafiya.”

Na tashi na fita ya bini da ido, ya rasa dalili haka kawai yakejin tausayina tun randa ya fara ganina, don haka yake kokarin jawoni jiki yaji matsalolina mu dinga tattaunawa, amma shi matsalar shi bai iya sakin fuska irin na Salim ba, duk yadda yaso ya sakar min fuska abin ya gagareshi.

Ina shiga gida na tarar duk suna tsakar gida kowa da goran juice a hannunsa ana sha ana zuba zance Sadiya sai washe baki ake tayi.

Da shigata Inna ta kalleni tace "Ke ina kike tuntuni sai yanzu kika gama sharar dakin Salman din kenan? Kinga har na gama rabiya na manta dake ungo ragowar nawa ki karasa sai kizo ki min kitso.”

Na kallesu nace ”Baki akayi a gidan ne aka kawo abinsha?”

Sadiya tace ”bakuwa ce Aunty Salima matar da Yaya zai aura itace ta kawo mana.”

A take fuskata ta sauya a raina nace shine suke ta rawar jiki.....mtswww.

Inna ta katseni da fadin ”ungo amshi mana.”

Na girgiza kai nace ”A'ah Inna na koshi bari in dauko comb in zo muyi kitson.” Na wuce ciki fuskata ba fara'a. Muna kitson Ya Salman ya shigo Inna ta kalleshi tace yaje ya dauki juice ta ajiye mai a fridge din palon Abba yace ”Ni bazan sha ba aba Rumaisa rabona.”

Inna tace ” Wace Rumaisa ai na bata taki karɓa, ban sani ba ko ta rainane don na bata kadan to in mun gama kije fridge din palon Kawunki ki dauki na Salman din.”

Nace ”Inna ni na koshi ne fa.” Zata fara fada ya katseta da fadin ”Rabu da ita Inna 'yar kauyece fa bata wani san juice bane.”

Sannan yace ”Inna gobe fa da sassafe zan koma in akwai wani abu a gaya min zan shiga kasuwa yanzu.”

Ta danyi shiru sannan tace "ni bana bukatar komi kudi zaka bani.”

Yace ”To zan turo muku Abba zai baku.” Shiru ta yi kamar bata so. Shi kam tashi yayi ya tafi.


 *RUMAISA SALMAN BY MAMAN KAUTHAR*