BAYAN HANZARI

PAGE ONE

by @khadijahsulaiman406

BAYAN HANZARI
KHADIJAH SULAIMAN
  



*Labarin "BAYAN HANZARI kirkirarren labari ne,idan yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne.*

*Bismillahirrahmanirrahim*


*Page 1*

    Tsaye take a gaban dogon wardrobe ɗin gabanta,gyara kayan ciki take a tsanake,a nutse take aikin nata ba tare da wani gaggawa ba.
Ta share a kalla mintuna kusan goma kafin ta maida murfin wardrobe ɗin ta rufe.
Ƙara bin ɗakin nashi ta ke da kallo ko da akwai wani abin da yayi saura da za ta yi,ganin babu wani abinda ɗakin ke bukata yasa ta shiga takawa a nutse ta fita.
Tana fitowa parlourn idonta ya sauka a tangamemen agogon dake manne mai zanen adon ɗawisu daya ƙarawa parlourn wani kyau da haske.
A hankali ta buɗe baki tace
"subhanallah,ashe lokaci ya tafi haka?"
Da ɗan sassarfa ta wuce nata d'akin,kayan jikinta ta cire ta d'auro towel ta shige toilet.
Ta ɗan jima a ciki kafin ta fito ta jawo stool dake gaban mudubin ɗakin ta zauna.
Sosai take ƙarewa kanta kallo cikin madubin,kasa haƙura tayi da abinda take gani ta ɗago hannunta na hagu tana taɓa kashin wuyarta.
Fashewa tayi da wani kuka mai cin rai,saida ta shafe a ƙalla mintuna goma tana abu ɗaya kafin ta sarara ta mike tare da kokarin barin wurin.
Jirin dake shirin zubar da ita yasa tayi saurin komawa ta zauna tana dafe kanta.
Saida ta d'an huta na wasu mintoci kafin a hankali ta kara miƙewa ta karasa ta buɗe wardrobe ko gani ba tayi sosai ta jawo wasu silk kayan bacci armless riga da dogon wando.
Komawa jikin madubin tayi ta shafe jikinta da turare ta haye gado ta kwanta don wani azababben ciwo kanta keyi tamkar zasu fad'o.
Cikin bacci taji horn dinshi tare da buɗe gate ɗin kusan lokaci ɗaya.
Juyo da fuskarta tayi ta jawo wayarta dake gefen bed side lamp ta kunna press button tare da kokarin duba lokaci.
Karfe sha ɗaya da minti sha takwas lokaci ya nuna mata sai kawai ta maida wayar ta ajiye tare da lumshe ido.
Da ƙyar ta miƙe ta zauna tana jin kanta tamkar  zai rabe biyu.
A daddafe ta fito daga ɗakin tana ƙara gyara hular kanta.
Ɗakinsa ta nufa ganin babu kowa a parlourn illa kamshin turarensa da ya gama cika wurin.
Tana murɗa ƙofar tayi sallama a hankali tare da maida shi ta rufe.
Yana tsaye yana ƙoƙarin cire links ɗin rigarsa da wayarsa dake dafe da kafaɗarsa dake nuni da magana yake a wayar ya juyo ya mata kallo ɗaya ya kauda kai.
"Idan na fito daga wanka zan kira ki".
shine kawai abinda yace ya kashe wayar tare da  ajiyeta saman gadon dake shimfiɗe da white bedsheet ya cigaba da abinda yake.
Bahiyya tayi kokarin danne abinda ke tokare saman kirjinta tace "Sannu da zuwa".
Da kyar ya buɗe baki tamkar wadda akayi wa dole yace
"Yawwa".
Zama tayi gefen gadon ba tare da ta ƙara cewa komai ba har ya gama cire kayan ya wuce toilet, ta bishi da kallo hawaye na kara gangarowa daga kyakywar fuskarta.
Ƙarar shigowar sako yasa ta ɗaga kai ta dubi wayar nasa,bata so karanta abinda ta gani ba amma idonta ya riga ya sauka akan rubutun.
"Kar fa matar ka ta mantar da kai ina nan ina jiran ka don ka san ba zan iya bacci ba har sai na ƙara jin muryarka".
Kauda kai tayi ta miƙe ta bar masa ɗakin.
Dining ta karasa ta dafe ɗaya daga cikin kujerun dake wurin tana ƙoƙarin daidaita numfashinta.
Ƙirjinta wani irin zafi da ciwo yake mata,cike da ƙoƙarin bai wa kanta ƙwarin gwuiwa ta koma ɗakin nasa ta tarar dashi zaune a bakin gado yana danna waya.
"Abinci na saman dining".
Ɗago kai yayi a takaice ya ɗan kare mata kallo tare da kauda kai yace
"Ba na jin yunwa".
Ringing ɗin wayarsa yasa ya gyara zaman towel dake d'aure saman ƙugun shi yana sakin murmushi ya ɗaga wayar ya kai kunne, Bahiyya bata ƙara ko minti dt'aya ba ta juya ta bar masa ɗakin.
Ko da ta koma nata ɗakin zama tayi bakin gadonta ta cigaba da sana'ar nata wato kuka,ganin kukan dai ba shine mafita ba yasa ta miƙe jiri na ɗibarta tayi ƙoƙarin dafe bango ta shige ta d'aturo alwala ta dawo ɗakin.
Ta kai kusan karfe biyu tana faɗawa Allah damuwarta kafin bacci barawo ya ɗauke ta a nan zaune ba tare da ta shiryawa hakan ba.
Hasken ranar da ya kashe mata ido yasa tayi saurin tashi zaune a rikice tare da janyo wayarta.
Ganin karfe bakwai har da mintuna kusan biyar yasa ta miƙe da sauri sai dai komawa tayi ta zauna riƙe da kanta.
Hawaye na sauka a idonta tace
"Innalillahi wainna ilaihi rajuun, innalillahi wainna ilaihi rajuun,Allah ka kawo min ɗauki".
A daddafe ta karasa shigewa toilet ,wanka tayi gabadaya tare da ɗauro alwala ta fito ɗaure da towel,jallabiya kawai tasa da dogon hijabi ta ta da sallah.
Shiryawa tayi cikin wani sharaton atampha da aka yiwa d'inkin dogon riga daya matuƙar karbar  fatarta,bayan turare da ta shafa babu wani abinda data shafawa fuskarta da sunan kwalliya amma ba karamin kyau tayi ba sai idanuwanta da suke a kumbure,ta ɗauko baƙin mayafi da baƙin takalmi tasa a kafarta.
Black bag ta d'auko sai wayarta da ATM card ɗinta ta rufo d'akin.
As expected ya riga ya fita,sai kawai ta ɗan zauna ta shiga dialing numbern shi sai dai har kira uku babu wanda ya samu damar ɗauka,hakan yasa kawai ta tura masa sakon za ta je asibiti ta maida wayar jaka ta mike ta fita.
Koda ta fito ɗan madaidaicin farfajiyar gidan mai gadi ta tarar zaune saman benci yana jin radio,ganinta yasa shi saurin mik'ewa yace
"Barka da fitowa Hajiya".
"Barka dai Mal Tasi'u,ka yi hakuri yau ba ka ga abin kari ba bana ɗan jin daɗi ne zan je asibiti".
Cike da girmamawa yace"Allah sarki Hajiya  Allah ya baki lafiya,babu damuwa wallahi na siyo koko a waje".
"To ba laifi sai na dawo".
"A dawo lafiya Hajiya".
Da kyyar ta samu abin hawa saboda yanayin anguwar nasu ta tsaida shi suka karasa asibitin da suke da file.
Mutane biyu kawai ta tarar sai ta nemi wuri ta zauna tare da ciro wayarta dake jaka ko za ta tarar da saƙon shi sai dai kamar yadda ta zata ɗin dai babu wani reply,maida wayar jaka tayi tare da lumshe ido.
Layi na zuwa kanta ta miƙe da kyyar da zuwa lokacin har wani dishi dishi take gani ta shiga consultation room d'in.
Dr Ismail dake zaune saurin mik'ewa tsaye yayi ganin yanayinta yace
"Subhanallahi,yi sauri ki zauna".
Tana zama ya d'yan mata tambayoyi tana bashi amsa,kafin ya shiga gwada BP dinta.
Ɗago kai yayi ya fuskance ta da kyau yace 
"Mallama Bahiyya kamar ba kya amfani da shawarwarin da ake baki kwata kwata,u know ur issue bai kamata ki na sawa kanki damuwa ba,yanzu dai dole sai mun ɗan ajiye ki saboda mu yi monitoring BP ɗin ki ko da zuwa yamma ne,ke kaɗai ki ka zo?"
Gyad'a mishi kai tayi ba tare data buɗe baki ba,sai kawai ya girgiza kai tare da jawo telephone dake saman table ɗinsa yana cewa
 "Allah ne kawai ya karaso dake lafiya,bari in kira nurse da zata tafi dake".
Ko minti biyu cikakke nurse dy'in ba ta ɗauka ba ta shigo ta kama hannun Bahiyya suka fita.

*****

Sai karfe huɗu Bahiyya ta buɗe idanuwanta tare da da sauke su saman agogon bangon dake ɗakin.
Jinta take wani fresh ko ciwon kan da ya matsa mata babu sai kawai ta tashi zaune ta janyo jakarta dake gefen pillow tayi saurin ciro wayar da nurse ta bata umurnin sa shi a silent.
Ganin babu misscall ko ɗaya ko sako yasa kawai ta maida wayar ta ajiye ta koma ta jingina da jikin gadon.
Buɗe kofar da akayi yasa ta ɗago kai a nutse ta sauke akan Dr Ismail da wata nurse ɗin daban.
Da murmushi saman fuskarsa ya karaso inda take yace
"Patient ɗina ta farka,ya jikin?"
Tana ƙara gyara mayafin jikinta tace 
"Na ji sauk'i".
"Masha Allah,haka muke son ji,akwai wani abu dake damun ki ne?"
Girgiza kai tayi sannan ta buɗe baki tace 
"Babu".
Dr Ismail yace"Alhamdulillah,za ki iya tafiya gida yanzu,ga magungunan da za ki tafi gida dasu,please a kula a dinga sha kuma a din ga bin doka dan Allah don babu yadda za'a yi magani yayi aiki idan har ba ki daina sawa kanki damuwa ba".
Ya karasa maganar tare da waiwayowa wurin nurse dake gefen shi ya karɓi ledar maganin ya miƙa mata.
"Allah ya k'ara sauk'i".
A hankali ta amsa addu'sr na shi ya juya ya bar ɗakin nurse ɗin na bin bayan shi ta bi su da ido.
Wasu siraran hawaye suka gangarowa saman kumatunta,a hankali tace 
"Dr,damuwa dole in shigeta amma Allah yana ji kuma yana gani".

Daga haka ta miƙe zaune ta gyara jikinta tare da ɗaukar jakarta ta bar ɗakin.
A bakin hospital ɗin ta samu adaidaita sahu, faɗa mishi inda zai kaita tayi tare da maida idonta waje tana bin kowa da kallo a zahiri amma a baɗini wani tunani daban take.
A gaban wani ɗan madaidaicin gida ta tsaida mai napep ɗin ta ciro kuɗi ta miƙa masa tare da shigewa cikin gidan bakinta ɗauke da sallama sai dai babu lallai mutanen gidan sun ji sallamar tata.
Wata mata dake zaune tsakar gidan tana gyara allayahu ta ɗago jin tafiya.
Ƙura mata ido tayi har ta karaso inda take ta zauna saman tabarmar dake shimfiɗe a gefe tace
"Umma ina wuni".
Ba yabo ba fallasa matar data kira da umma ta ɗauke kai tace
"Lafiya kalau, daga ina haka da yamman nan?"
Ɗan sauke ajiyar zuciya tayi tace
"Daga asibiti nake Umma,nace bari in biya in ganku,kawo in yanka miki".
Ɗan dakatawa Umma tayi da yankan da take ta buɗe baki tace
"Allah ya sawwaƙe."
Bahiyya tayi saurin maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata tace
"Umma kawo in yanka miki".
Ba tare da umma ta kalle ta ba tace
"Ki bar shi,ke da kika dawo daga asibiti."
Bahiyya bata kara cewa komai ba ta dinga bin Umma da kallo harta gama yanka allayahunta ta mik'e ta shiga kitchen ɗin dake tsakar gidan.
Tashi tayi ta d'auki butan dake tsakar gidan ta d'auro alwala ta rama salloloin dake kanta.
Tana zaune a wurin umma ta gama abinda take a kitchen ta fito ta ce mata 
"Ke yaushe zaki tafi gida ne? yamma tayi fa".
A sanyaye tace"umma yanzu zan tafi,Baba fa?"
Umma ta kauda kai daga dubanta tace"da yana nan da kin ganshi ai,kiyi kokari ki tafi kafin dare ya miki a hanya".
Da toh ta amsa tare da sunkuyar da kanta,har umman zata wuce ta shiga ɗaki sai kuma ta juya ta koma kitchen ta zubo mata tuwon shinkafa miyan kabewa ta ajiye mata a gabanta ta shige parlour.
Bata wani jima ba ta dawo ɗauke da pure water mai sanyi guda biyu ta ajiye mata tare da barin wurin.
Jiki na rawa Bahiyya ta miƙe ta wanke hannunta ta dawo ta janyo plate ɗin ta hau cin abincin don tun safe babu abinda ya shiga cikinta sai maltina da doctor yasa nurse ta bata kafin a mata treatment.
Umma dake kokarin kammala ayyukanta ta dinga satar kallon ta harta gama cinye abincin.
Bata ankara ba ta jiyo muryar umma tana cewa
"Ko a ƙaro miki ne?"
Girgiza kai kawai tayi kafin ta mike tare da ɗaukar plate ɗin ta wuce dashi kitchen.
Za ta fito tayi saurin dakatawa gabanta na faɗuwa jin muryar wanda ya shigo gidan.
Da ƙyar ta janyo kafafuwanta ta fito daga kitchen ɗin tare da sauke idanuwanta saman wani dattijo dake zaune saman tabarmar data tashi yana kokarin ɗaukar pure watern da umma ta ajiye masa.
Kauda kai yayi ya shiga shan ruwa bayan sun haɗa ido.
"Baba ina wuni".
Saida ya gama shan ruwan ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba,sai kawai ta karasa saman tabarmar ta ɗauki hand bag ɗinta ta juya tana kallon umma idonta cike taf da hawaye tace
"Umma zan tafi sai da safe".
"Allah ya tsare, Allah ya bamu alheri".
Juyowa tayi tana fuskantar baban tace
"Baba sai da safe".
Ko amsata bai yi ba ya ciro wayarsa a aljihu ya shiga dannawa.
A sanyaye ta fita daga gidan umma ta bita da kallo,tana fita umma ta sake tsintsiyar hannunta ta koma ta zauna gefen baba ta fashe da kuka.
Da sauri ya ajiye wayar hannunsa yace
"Lafiya Fatima,akwai wanda ya rasu ne?"
Sai da umma tayi kukarta mai isarta duk da rarrashin da Baban ya dinga mata da tambayan abinda ya sa ta kuka.
Haɗa hannayenta duka biyu tayi tana fuskantar Baban da kyau tace
"Dan Allah Babansu ka taimaka ka shiga lamarin yarinyar nan,dan Allah ba don halinta ba,don Allah".
Wani dogon tsaki Baba ya saki tare da miƙewa ya shige ɗaki cike da takaici,shi da yasan dalilin kukanta kenan babu abinda zai sa ya zauna yana rarrashinta.








✍️