DAƊIN HARAM

SUDDEN IMPACT

by @missnasiraouther

🚬 (DAƊIN HARAM🚬
By Maryam sulaiman 
Miss Nasir ✍️
Complete book 📚 
Page 15-16

 Yana ta tafiya a cikin baƙar motarsa kirar Rolls-Royce Ghost wadda ta yi wani irin sheƙi saboda tsananin tsafta. Gudun da yake yi a titi ba ƙaramin tsoro yake ba wa sauran masu ababen hawa ba, domin a wurinsa, titi na kowa ne amma shi ne sarkinsa.
Yana cikin tafiya yana sauraron sautin waka mai tsuma zuciya a cikin motar, sai ga wata yarinya ta fito ba zata ba ta shiga tsallaka babban titin da ke kusa da unguwar ta Maitama, tana ta sauri saboda wani dalili na rayuwa. Hankalinta ba ya kan titi sosai, kuma ta yi mugun sakaci wajen dubawa.
A daidai lokacin da ta zo tsakiyar titin, idanun Rameez suka sauka a kanta ba zato ba tsammani. Da gudu ya taka burkin motar, amma nauyin motar da kuma tsananin gudun da yake yi ya sa ba zai yiwu a dakatar da ita a take ba!
SKRRRRRRT!
Wata razananniyar ƙara ta fita yayin da tayoyin motar suka gugar kwalta, amma kafin su tsaya ƙyam, gaban Rolls-Royce ɗin ya buge yarinyar da wani irin karfi!
Ta fasa wata matsanciyar ƙara "Wayyo Allah na!" kafin ta gurzu ta fadi gefen titi, jikinta na rawa yayin da jini ya fara zuba daga goshinta, inda ta fadi a sume ba tare da ta san inda kanta yake ba.
Rameez ya zauna a cikin motar, idanunsa sun yi ja, sannan a hankali ya cire tabarous ɗinsa yana kallon abin da ya faru ta madubin mota. A karo na farko a rayuwarsa, zuciyarsa ta buga da wani irin yanayi na mamaki da kuma tashin hankali—amma nan take ya dawo da miskilancinsa, yana mai cewa a ransa:
"Damn it... Me ya kawo wannan yarinyar a gabana a yanzu?"
Ya kashe sigararsa, ya buɗe kofar motar ya fita domin ganin abin da ya aikata.
karar da tayoyin motar suka yi ta dakata, sai wani irin shiru mai cike da ban tsoro ya biyo baya a kan titin Maitama. Rameez ya tsaya a kusa da gaban motarsa ta Rolls-Royce, fuskar nan tasa ta murtuke da miskilanci da baƙar damuwa. Ya kalli yarinyar da ke kwance a wajen tana fitar da numfashin karshe na rashin sani, jini na fita daga goshinta tare da wanke fari da baƙin kayan da ta sanya.
Ba a dauki sakan biyu da faruwar hakan ba, sai ga wata budurwa daga gefen titi tana tafe a guje tana ihu da kuka mai cin rai. Ta zo ta fada a kan gawar ko kumaace sumaffiyar jikin yarinyar da ta bugu, tana girgiza ta da wani irin tsananin tashin hankali.
"Ayla! Ayla! Wayyo Allah na, Ayla ki tashi! Kar ki mutu ki bar ni!"
Kukan kawar ta da yadda take ta kiran sunan Ayla ya cika wajen, tana jajjefa hannayenta sama cikin tsananin rudani da zafin zuciya. Tana kallo ta ɗago da idanunta da suka cika da hawaye, ta kalli Rameez wanda ke tsaye yana kallonsu da sanyin jiki da miskilancinsa, ba tare da ya nuna wata fargaba a fili ba.
"Kai! Wane irin mutum ne kai?! Ka kashe min kawar ta! Ka kashe Ayla!" Kawar ta fasa wata razananniyar kara tana nuna Rameez da yatsa, yayin da mutane suka fara taruwa a wajen suna nuna mamaki da tsegumi kan abin da ya faru.
Rameez ya lumshe idanunsa, ya mayar da hannunsa cikin aljihun wandon ripped jeans ɗinsa. Duk da cewa a zuciyarsa akwai wani irin yanayi da bai saba gani ba, bai nuna tsoro ko danasanji ba. Ya kalli yarinyar da ake kira Ayla dake kwance sumamme, sannan ya kalli kawar tata da wani irin kallo na kasaita.
"Shut up!" Rameez ya fada da muryarsa mai tsoratarwa, wadda ta sa wajen yin wani irin tsit duk da hayaniyar mutanen da suka taru. "Ba wanda ya ce ta zo gaban motata. Kukan banza ba zai dawo da ita ba!"
Ya juya a hankali, ya dauki wayarsa daga aljihu, sannan ya kira Zayyad wanda ke kan hanyar zuwa. "Zayyad, change of plans. Akwai babban abin da ya faru a nan. Ka zo yanzu nan!"

Bayan mintuna kaɗan, Zayyad ya iso wurin da gudu a cikin motarsa, yana zuwa ya ga yadda mutane suka yi wa Rameez da kuma yarinyar da ta sume (Ayla) kawanya. Ba tare da ɓata lokaci ba, tare da taimakon wasu mutanen wajen, suka ɗaga jikin Ayla da ke ta zubar da jini, suka sanya ta a motar Zayyad, yayin da kawar tata ta bi su a baya tana kuka da rusa ihu. Rameez kuwa, ya bi bayan motarsu a hankali da nasa Rolls-Royce Ghost ɗin, fuskarsa ba ta nuna wata alamar tsoro ko fargaba ba, sai dai wani irin shiru mai cike da miskilanci.
Sun isa wani babban asibiti na alfarma da ke birnin Abuja. Da gudu Zayyad ya shiga da ita cikin sashin gaggawa (Emergency Room), yana kiran likitoci da ma'aikatan lafiyar asibitin da su kawo dauki maza.
Amma da fitowar babban likitan da ke kan aiki, ya tare su yana nuna cewa ba za a iya shiga da marar lafiyar ɗakin gaggawa ba tare da an kawo rahoton ‘yan sanda ba (Police Report), la'akari da cewa hatsarin ya faru ne a waje kuma akwai jini da raunuka a jikinta.
Zayyad ya fusata sosai, ya kamo kwalar rigar likitan da karfi, fuskarsa a murtuke. "Wai kai wane irin likita ne?! Yarinya tana neman mutuwa a hannunka kana wani zancen 'yan sanda? Ka shiga da ita emergency room yanzu kafin na sa a rufe asibitin nan gaba ɗaya!"
A daidai lokacin ne Rameez ya tura ƙofar asibitin ya shiga ciki da wata irin takama da sarauta. Sanye yake da ripped jeans ɗinsa da kuma baƙar hoodie, tabarar idanunsa a murtuke a fuska.
Yana zuwa kusa da su, ya cire tabarar a hankali, ya kalli likitan da wani irin wulakantaccen kallo mai cike da izza.
"Ka saurari abin da abokina ya gaya miki," Rameez ya fada da muryarsa mai sanyi amma mai tsoratarwa. "Idan wani abu ya sameta a nan saboda wani banza police report naku, zan sayi asibitin nan gobe da safe in mai da shi wurin shakatawa na karnuka! Ka shiga da ita ciki nan da sakan biyu!"
Likitocin da ma'aikatan asibitin, ganin irin yadda Rameez yake magana da kuma tsantsar kasaitarsa, suka tsorata matuka. Ba tare da sun kara wani baki ba, nan take suka gaggauta karbar Ayla suka fada da ita ɗakin gaggawa (Emergency Room) domin ceton rayuwarta, yayin da Rameez ya tsaya a waje yana hura sigararsa ko a jikinsa!



Miss Nasir ✍️