Chapter 4
by @queenmeemi
HABIBULLAH
BY
Meemi Basheer
4
Bayan mahaifiyata ta tare sai Yakumbo ta sako mata ido, saboda ta ga mahaifina na kula da ita. A lokacin baya ɗaukan rainin ta tunda ya samu lafiya.
Allah ya yi mahaifiyata da kauda kai, ko abu ta gani ya ɓata mata rai ba za ta nuna ba.
Wataran haka nan Yakumbo za ta zo ƙofar ɗakinta tana wanki, babu damar ta yi magana ta ci mata mutunci. Wani lokacin sai ta dace daidai lokacin da mahaifina ya kusa dawowa za ta tsiri kuka. Idan ya tambayeta sai ta kaɗa baki ta ce ai Rukayya ce wato mahaifiyata, ta yi mata rashin kunya ta uwa ta uba ta zagi iyayenta da yake ya san halinta, sai dai kawai ya bi bayanta dan a zauna lafiya ya bata haƙuri, ko ƙala ba zai ce wa mahaifiyata ba saboda ya san halin kowa.
Ga laɓe da take musu, kullum dare takan kai shabiyu na dare tana sinturi mahaifiyata na kula da ita amma ta share, ba ta taɓa gayawa mahaifina ba, domin ta sha ganinta tana leƙe. An fi wata ɗaya tana hakan, abinda ya ishi mahaifiyata, ya sa ta samowa kanta mafita. Sai da ta daidaita lokacin da take leƙen ta watsa mata ruwan data garwayashi da barkono ƙara Yakumbo ta saki tana yarfe hannu idonta yaji Mahaifina ya tashi da sauri cike da diriiricewa ya ce, "Me nake ji ne?"
"Ni kam ban sani ba," cewar Babata da ke dariya a ciki-ciki. Buɗe ƙofar dakin ya yi don gasgata ihun da ya jiyo, nan fa idonsa ya sauka kan Yakumbo ido a rufe tana laluben hanya dan saurin shiga ɗakinta. Jinjina kai ya yi yana dariya domin lokacin sanyi ne, dole ko ruwan ya shigeta
Watan mahaifiyata huɗu ta samu ciki, murna gun mahaifina kamar an biya masa hajji da umara Yakumbo kam kamar mahaukaciya ta dawo, kullum bala'i, da habaici tare da aibata cikin a fakaice sam ba sa sauraron ta.
Lokaci ya ja, watanni sun shuɗe, har ciki ya isa haihuwa mahaifiyata ta haihu, ranar suna aka sa Habibullah domin sunan da mahaifina ke so ke nan.
Ganin yadda na ke samun kulawa ni da mahaifiyata, ya kuma ɓacata ran Yakumbo, hakan ya sa ta ƙara tashin hankalinta, ko ganina ba ta son yi, ba ta taɓa ɗauka na ba. Ta ƙi jinin son da mahaifina ke mini. Cikin fusata ta sadakar a ranta zuwa wajen tashi boka. Nan da nan bayan shudewar makwanni mahaifiyata ta rasa gane kan mahaifina domin sai ya zama sai abinda Yakumbo ta ce shi yake yi, ko kallona ba ya yi. Idan baƙin-ciki ya ishi Mamana sai ta shiga ɗaki ta yi kuka har ta gode Allah.
In taƙaita maka labari, sai da ta hana mahaifina ya bama Mamana abinci, haka za ta zauna da yunwa, sai dai Yakumbo ta fito tsakar gida tana ciye-ciye kala-kala.
Da ƙyar ake ba ta ƙanzo, shi ma sai ta yi mata aiki. Mahaifina kam komai ya yi idan ya fita waje ya yi ta kuka, ya rasa yadda zai yi da Yakumbo, kai mugunta iri-iri.
Ana haka ƙyanda ta kamani ni, mahaifiyata ta yi masa zencen asibiti ya ƙi kulata. Da ta ga ta dame shi da maganar sai ya ce ta yi jik'e-jik'e. Da yake rayuwa a gun Allah take, da kamar ba zan rai ba ALLAH ya sa na warke.
Ganin hakan ya sa Mamana ta sayar da kayan ɗakinta ta fara sana'ar sayar da shinkafa da miya. Farko Yakumbo ba ta sako mata ido ba, amma ganin yadda Allah ya buɗa mata kasuwar sai hassada ta shiga zuciyrta har ta yi gulmar da sai da mahaifina ya hana sana'ar, domin cewa ta yi wai gardawa na shigowa suna mata ɗauke-ɗauke. Da yake mahaifiyata na da haƙuri haka ta haƙura ta fawwala wa ALLAH.
Ina da watanni goma, Mahaifiyata ta fara zuwa gidajen masu kuɗi tana musu aikatau, a hakan take samu ta kula da ni da abinci da komi, sam ba ta shiga shirginsu. Anan ma ganin hankalinta ya kwanta sai da ta zuga mahaifina ya hanata zuwa. To tun daga lokacin ba ta ƙara marmarin yin wani sana'a ba, haka take zaune.
Shekarata ɗaya a duniya Yakumbo ta sa mahaifina ya sallami Mamana da ya ce ta tafi har da ni baya son ganina, amma Yakumbo ta buɗe ido ta ce ba za a tafi da ni ba. Ba yadda Mamana za ta yi ta ajiye ni ta tafi gidan su. Mafarin shigata uk'uba da raunanniyar rayuwa ke nan.