Chapter 11: A long day, a longer night
Washe gari haka ta wuni a lounge ita kadai, sai da yamma Ahmad da Rayyan suka zo wanda a karshe daga Rayyan har Ahmad sai da suka b’ata mata rai tayi alkawarin ko magana ba zata musu ba
Ranarsu ta biyu a Lagos…
“Madam, kin shirya?”
Rahama ta ɗago kai daga wayarta, ta kalli Ahmad wanda yake tsaye a bakin ƙofar lounge, hannunsa riƙe da key ɗin mota
“Ka ga wani abu a hannuna da zai nuna maka ban shirya ba?”
Ahmad ya sauke idanunsa zuwa jakarta da take a gefen kujera, sannan ya dawo da kallonsa gare ta sai ynx ya fahimci zafin da Rayyan yake mata“Madam, ni dai tambaya na yi”
“To ni kuma na amsa maka. Or do you want me to write it down for you?”
Ya yi murmushi yana girgiza kai “Madam, Allah ya ba ki haƙuri”
“Ameen oo Allah ya ƙara maka haƙuri, ya kuma ba ka promotion sbd juriyar da kake yi da ni”
Kallonta kawai yake da mamaki
“Kar ka manta kamar ka saka sadaka ne dan wannan juriyar ba ƙaramin ibada ba ce”
Ahmad ya fashe da dariya, ita kuma ta miƙe tana ɗaukar jakarta “Yanzu me ya sa ka dariya? Na faɗi gaskiya ne fa”
“Mu je Madam, Rayyan yana jira”
Murmushin da ke fuskarta ya gushe “Rayyan? What has he got to do with my life this morning?”
“Shi zamu biya mu ɗauka ynz”
“Ya Ahmad ka tabbatar dani kake magana? Ko dai akwai wata Rahama da kake mgn ban sani ba?”
“Madam please kada ki fara”
Ta ɗora jakarta a kafaɗarta, ta bi shi zuwa waje tana girgiza kai
“Wlh Ya Ahmad, duk wanda ya ƙirƙiro wannan workshop ɗin, idan na gan shi sai na tmby shi ko me ya sa bai sa a yi ta online ba. Mutum ya zauna a gidansa, ya sha tea, ya gama aikinsa, Instead sai an haɗa mutane da ba sa son ganin juna a wuri ɗaya”
Ahmad bai ce komai ba, ya buɗe mata ƙofar mota
Rahama ta tsaya kafin ta shiga “Ka ji ni ko?”
“Na ji, madam”
“Good! At least wani yana sauraron complaints ɗina a wannan Lagos ɗin”
Ta shiga motar, Ahmad ya rufe ƙofar sannan ya zagaya ya shiga driver’s seat
Ba su daɗe da barin wajen ba, Rahama ta jingina da kujerar tana duba wayarta. Ahmad kuwa yana tuƙi cikin nutsuwa, lokaci-lokaci yana kallonta ta madubin mota
“Madam, please ki yi min alƙawari ɗaya mana?”
“Wane irin alƙawari kuma?”
“Ki yi ƙoƙarin kada ku yi faɗa da Rayyan yau”
Rahama ta ɗago kai a hankali “Me?”
“Na ce ki yi ƙoƙarin ku zauna lafiya a wurin workshop”
Ta kalli Ahmad na ƴan mintuna, sannan ta ɗan gyara zamanta “Ya Ahmad, ina son ka saurare ni da kyau, shin ka taɓa ganin na je na nemi Rayyan da faɗa?”
“A’a, madam”
“Exactly!!! To, idan mutum yana tafiya a hanya, wani ya tsaya a gabansa yana neman ya taka masa ƙafa, me kake so ya yi? Ya durƙusa ya ba shi haƙuri sbd yana da ƙafa?”
Ahmad ya yi ajiyar zuciya “Madam, ban ce ki ba shi haƙuri ba”
“To ka bar ni in yi rayuwata, ni ban zo Lagos don in yi masa biyayya ko nayi shiri da shi ba”
“Ban ce kuyi shiri ba, madam”
“Good! Kada ka ƙara kawo maganar shiri a cikin wannan conversation. My blood pressure is still normal, and I intend to keep it that way”
Ahmad ya yi murmushi, ya ƙyale ta, ba da daɗewa ba suka isa hotel ɗin da Rayyan yake
Ahmad ya kira shi a waya, ya ce masa yana saukowa. Rahama kuwa ta ci gaba da zama a cikin mota, tana kallon mutanen da suke wucewa a wajen hotel ɗin
Da ta ga Rayyan ya fito, ta juya kai ta koma duba wayarta
Ya buɗe ƙofar, ya shiga motar, sannan ya rufe ƙofar da ƙarfi fiye da yadda ya kamata
“Morning sir” Ahmad ya gaishe shi
“Morning. Let’s go”
Rayyan ya ɗaura seat belt, ya jingina da kujerarsa
“Madam, good morning” Ahmad ya ce, yana kallon Rahama ta madubi hakan wai a fakaice yake tuna mata ta gaida Rayyan
“Ya Ahmad?”
Rayyan ya ɗan ɗaga idanunsa ta madubi ya watsa mata wani kallo “Some people still know how to greet”
Rahama ta daina motsa yatsunta a kan wayar, a hankali ta leka ta kalle shi “Some people too know how to mind their business”
Ahmad ya gyara zamansa a gaggauce
Rayyan ya kalli Rahama daga sama har ƙasa a kaskance, sannan ya karkatar da kansa “Was I talking to you?”
“Ka yi magana ne a cikin motar da nake ciki. Ko sai an rubuta sunana a jikin kowace magana kafin in amsa?”
“Then learn to stay out of conversations that don’t concern you”
Rahama ta buɗe baki, ta sake rufewa, sai ta yi murmushi wanda bai kai ciki ba “Of course sir. Anything for your highness”
Rayyan ya yi tsaki
Rahama ta juyar da kanta “Allah ya shirye ka” ta faɗa a ƙasa-ƙasa
“What was that?” Rayyan ya tambaya
Rahama ta juyo tana murmushin mutanen kirki ta ce “Nothing fah”
Ahmad ya yi saurin kunna motar “Madam, sir, let’s go, we don’t want to be late”
“Exactly” Rayyan ya amsa, yana kallon agogonsa
Rahama ta koma kallon window, ta ɗauki earpiece ɗinta ta saka a kunnuwanta, Idan har akwai wani abu da za ta iya yi don ta guji jin muryar Rayyan, to za ta yi shi
Wurin workshop ɗin ya cika da mutane tun kafin su isa, hall din an gama tsara sa, da wajen zaman guest harda masu gabatarwa
Rahama ta sauka daga mota tana gyara mayafinta, ta ɗauki jakarta, ta bi Ahmad zuwa wajen shiga
Rayyan kuwa ya tsaya yana duba wayarsa
“Madam ga ID ɗinki” Ahmad ya ce, yana miƙa mata katin da aka ba shi
“Thank you, Ya Ahmad” Ta karɓa ta rataya a wuyanta
“Rayyan your ID” Ahmad ya ce
“Give it to me”
Ahmad ya miƙa masa katin, Rayyan ya karɓa ba tare da ya ɗaga kai daga wayarsa ba
Rahama ta riga ta shiga cikin entrance kafin ya ƙarasa
Ta zaɓi kujera a gefe, ta ajiye jakarta, sannan ta zauna tana duba takardun da aka ba ta. Ba ta damu da wanda zai zauna kusa da ita ba, muddin ba zai dame ta ba
Sai ga Rayyan ya bayyana a gefen kujerarta “Move your bag”
Rahama ta ɗago kai “Excuse me?”
“Your bag, Move it”
Ta kalli kujerar da ke gefenta, sannan ta kalli jakar tata “Yau naga ta kaina, Is this seat reserved for you?”
Rayyan ya zuba mata ido “I don’t have time for this”
“Neither do I” Ta ɗauki jakar ta ɗora a cinyarta, sannan ta juya ta ci gaba da duba takardunta
Rayyan ya zauna a kujerar sannan ya fara danna wayarsa
Rahama ta gyara zamanta ta yi kamar babu wanda yake kusa da ita
Sai da aka fara gabatar da shirin ne ta mayar da hankalinta gaba ɗaya kan aikin, ta dinga jotting na muhimman bayanai, sosai tayi concentrating, kuma ta yi tambayoyin da suka shafi abin da ake tattaunawa
Rayyan ma ya mai da hankali, dukda wayansa yake kallon, ita kuma duk da rashin jituwarsu, ba ta ga dalilin da zai sa ta yi sakaci da abin da aka kawo ta yi ba
A lokacin da aka ba mahalarta damar tattaunawa a group, Rahama ta juya zuwa ga mutanen da suke tare. Suna nazarin wani batu ne da aka ba su, kowannensu yana bayar da ra’ayinsa
“Ni ina ganin idan za a yi amfani da wannan method, ya kamata a fara da tantance abin da ake son cimmawa” Rahama ta faɗa, tana nuna wani sashe na takardar
Wani daga cikin mahalarta ya gyada kai “That makes sense”
Ta ƙara bayanin yadda za su iya aiwatar da shawarar cikin sauƙi, sannan suka rubuta abin da suka samu
Bayan ɗan lokaci, aka nemi kowane group ya gabatar da sakamakonsu
Rahama ta tura takardun zuwa ga abokin aikinsu wanda zai gabatar. Yana gab da tashi sai wani ya tambayi wani abu da ya sa suka sake komawa kan aikin don dubawa
Rayyan, wanda yake wani group a kusa da su, ya yi magana daga inda yake “Your conclusion doesn’t address the main issue”
Rahama ta ɗago kai daga takardunta
Abokin aikinta ya kalli Rayyan “Which part?”
Rayyan ya nuna wani part na takardar “This part. You’ve explained the process, but you haven’t shown how it solves the problem”
Rahama ta yi shiru tana kallon takardar. Ta fahimci abin da yake nufi, amma yadda ya faɗa ya sa ta ji kamar ya ɗauka su ba su iya aikin ba ne “Actually, we were just discussing that” ta ce
Rayyan ya juya yana kallonta “Then discuss it properly”
Ta rufe pen dinta “Thank you for your professional advice”
“You’re welcome. Try to use it”
Mutumin da yake zaune kusa da Rahama ya sunkuyar da kai yana ɓoye murmushi, bcos ya lura kamar suna da ‘yar sama ne
Rahama ta ɗauki takardar ta juya tana kallonsa
“Ka ga? Wannan shi ne dalilin da ya sa nake son a yi duk wani workshop online. At least, mutum zai iya kashe microphone idan ya ga irin wannan”
“Miss” abokin aikinta ya faɗa a hankali, yana ƙoƙarin kada ya yi dariya
“I’m serious. Some people need a mute button in real life”
Sai dai wannan karan mutumin ya kasa danne dariyarsa
Rayyan ya ɗago kai “Do you have a problem?”
Rahama ta kalle shi “No sir, I’m just appreciating technology”
“Then focus on your work”
“I’m doing that already”
“Clearly not enough”
Ta yi murmushi ta juya baya “Mr arrogant and Na’iya ba”
Sai ta koma kallon takardunta, ta gyara abin da suke tattaunawa a kai, corrections din suka gyara hadi da kara wasu bayanai, while presenting gabatarwarsu ta kasance mai kyau
Bayan an kammala wannan ɓangaren, an ba su ɗan hutu
Rahama ta fita zuwa wajen da ake samun ruwa, ta ɗauki bottle ɗaya ta buɗe. Tana tsaye tana sha sai Rayyan ya fito, ta ɗan matsa gefe domin ya wuce
Sai ya tsaya “Your group should have checked that conclusion before presenting it”
Rahama ta sauke bottle daga bakinta “Mun gyara shi, ko ba haka ba?”
“After I pointed it out”
“Thank you for the reminder sir, zan rubuta sunanka a certificate ɗina”
Rayyan ya kalle ta ba tare da murmushi ba
“You really don’t know how to talk with manners”
Ta rufe bottle, ta ɗaga gira “Ni kuma ina ganin wasu mutane ba su san lokacin da ya kamata su yi shiru ba. I guess we all have our weaknesses”
Ya yi tsaki, ya wuce ta, Rahama ta bi shi da kallo na ɗan lokaci, sannan ta juya zuwa entrance din “Tsaki kamar ana ƙoƙarin kashe sauro a cikin hanci” ta faɗa a hankali, ta koma ciki tana dariya ita kaɗai
Bayan an kammala workshop ɗin, Ahmad ya jira su a wajen parking space
Rahama ta shiga mota ta zauna a gaba, ta cire ID ɗinta ta saka a jakarta, sannan ta jingina da kujerar
Rayyan ya shiga, yana duba wayarsa
“Madam, how was the workshop?” Ahmad ya tambaya yayin da ya fara tuƙi
“Alhamdulillah Ya Ahmad, It was good”
“Kin amfana?”
“Sosai! Na koyi abubuwa da dama, na rubuta notes, kuma ina ganin zan iya amfani da wasu daga ciki, Overall it was productive”
“That’s good, madam”
“Eh fah! Sai dai akwai ɗan matsala”
Ahmad ya kalleta ta madubin motar “Wace irin matsala?”
Rahama ta kalli Rayyan wanda yake zaune a wajen mai zaman banza “Some people think they’re the only ones who understand everything”
Rayyan ya ɗago kai daga wayarsa “Say it with your chest, stop making indirect comments”
Rahama ta leka ta kalle shi sosai “Okayyy Kai ne nake magana a kai?”
Ahmad ya yi saurin tari, idan har shine Rayyan ko kulata ba zai yi, sosai dariya ke cinsa
Rayyan ya ajiye wayarsa a cinyarsa “You need to learn some manners idan ba haka ba wlh kafin mu koma gida sai na ɓaɓɓallaki”
“Ka fara koya min da misali sir”
“Don’t test my patience”
“Ban taɓa neman gwada ta ba. Kai ne kake kawo ta gabana kullum”
“Enough!” Muryar Rayyan ta fito da kaifi wanda ya sa Ahmad ya yi shiru nan take
Rahama ma ta yi shiru, ta juyar da kanta gefe, ta haɗa hannayenta a kan jakarta
Bayan ƴan secs, sai ta ce a hankali, “Thank you”
Ahmad ya kalle ta window ya ce “For what?”
“Ka ga yadda yayi shiru? Na ji daɗi sosai”
Ahmad ya ce “Rahama!”
Ta yi saurin kallon window “I’m quiet now!”
Ahmad ya girgiza kai yana murmushi, amma bai ce komai ba
Ragowar tafiyar ta kasance cikin nutsuwa. Rahama ta ɗauki wayarta ta ci gaba da chatting abunta, Rayyan kuma ya koma nasa duniyar
Lokacin da suka isa airport, Ahmad ya taimaka musu da saukar da kaya
“Thank you for everything, Ya Ahmad” Rahama ta ce
“Ba komai madam, Allah ya kai ku gida lafiya”
“Ameen”
Rayyan ya karɓi kayansa daga hannunsa “Thanks, Ahmad”
“Sir”
Rahama ta ɗauki jakarta ta bi hanyar shiga, Rayyan yana bayan ta
Bayan da aka kammala dukkan shirye-shiryen tafiyar, suka shiga jirgi, Rahama ta zauna a kujerarta, ta ɗaura seat belt, sannan ta mayar da kanta kan kujerar
Ta yi wa kanta alkawarin ta huta har sai sun isa Abuja
Ba ta da niyyar yin wata mgn da Rayyan fiye da abin da ya zama dole, kuma da alama shi ma ba shi da wata niyya ta daban
Da suka isa Abuja, dare ya riga ya yi sosai
Driver ne ya iso airport, ya ɗauki kayansu ya saka a mota, Rahama ta shiga baya
Daga ita har shi babu wanda yayi mgn, Driver ya tambayi Rayyan ko akwai wani wuri da yake son su tsaya kafin su wuce gida
“No, take us home”
“Okay sir”
Rahama ta jingina da kujerar tana kallon fitilun tituna ta window, gajiyar tafiyar ta bayyana a fuskarta, kuma ba ta da sha’awar buɗe baki sai idan akwai abin da ya zama dole
Da suka isa gidan, mai gadi ya buɗe gate, motar ta shiga har cikin harabar gidan
Rahama ta sauka, ta ɗauki jakarta, sannan ta bi Rayyan zuwa cikin gidan
Da suka shiga falo, Mommy da Daddy suna zaune, da alama dai jiransu suke
“Ah, ga matafiya sun dawo!” Mommy ta faɗa tana miƙewa
“Welcome home, my children” Daddy ya ƙara da fara’a
Rahama ta yi murmushi ta ƙarasa gabansu “Good evening Mommy, Good evening Daddy”
“Good evening my dear. How was the journey?” Mommy ta tambaya tana kallonta
“Alhamdulillah Mommy, although it’s stressful”
“Allah ya kawo ku lafiya, Alhamdulilah!” Daddy ya ce “Ya workshop ɗin?”
“Alhamdulillah Daddy, It was very educative. Mun koyi abubuwa da dama, especially a ɓangaren yadda za a tsara aikin da kuma yadda ake gabatar da ideas cikin tsari”
Daddy ya gyada kai cikin jin daɗi “That’s good! Na yi farin ciki da kika amfana, wannan shi ne abin da nake so”
“Thank you Daddy”
“Kin yi amfani da damar da aka ba ki kenan” Mommy ta faɗa tana murmushi
“Kaii Mommy, ai har na rubuta notes da yawa zan sake duba su idan na huta”
“Very good”
A lokacin ne Hajiya ta fito daga ɗakinta, tana riƙe da carbi “Su waye suka dawo haka a daren nan?”
“Ga su nan Hajiya” Mommy ta amsa tana murmushi
Rahama ta juya da sauri “Good evening Hajiya”
Hajiya ta yi murmushi “Ah, Rahama ta dawo, sannu da zuwa jikalle na”
“Yawwa, Hajiya”
Ta ƙarasa ta gaishe ta, Hajiya ta tambayi yadda tafiyar ta kasance, sannan ta zauna a kujerar da ke kusa da su
“Ya workshop ɗin?” Hajiya ta tambaya
Rahama ta fara ba ta labarin yadda suka yi, daga yadda aka shirya wurin zuwa yadda aka raba su group-group. Ta yi bayanin abin da suka koya, da yadda suka yi aiki a matsayin group din, har ta kai ga yadda aka yi gabatarwa
Daddy yana sauraro cikin kulawa, yana tambayar wasu ƙarin bayani time-time
“Na ji daɗin yadda kika mai da hankali” ya ce “Mutum zai iya zuwa irin wannan taro ya dawo ba tare da ya ɗauki komai ba. Amma idan kin rubuta notes kuma kin fahimci abin da aka koyar, to kin yi amfani da lokacinki yadda ya kamata”
Rahama ta yi murmushi “Thank you Daddy. In sha Allah zan sake duba su”
“Allah ya taimaka”
A lokacin ne Rameez ya shigo falon da sallama a bakinsa “Assalamu alaikum”
“Waalaikumus salam” suka amsa
Rahama ta juya tana kallonsa “Good evening, Ya Rameez”
“Evening Rahama, sannu da zuwa”
“Yawwa, thank you”
Rameez ya zauna, ya kalli ƙaninsa sannan ya kalli Rahama “Ya Lagos?”
“Alhamdulillah Ya Rameez mun yi tafiya lafiya kuma mun dawo lafiya”
“Workshop ɗin fa?”
“Ya yi kyau sosai, na amfana”
“That’s good”
Rameez ya ɗan yi shiru, akwai tambayar da yake son yi mata sai kawai ya fasa, ya kalli Rayyan da yaki kallon kowa a parlon yana danna wayansa ya ce “Ka gaji ne?”
“I’m fine” Rayyan ya amsa a taƙaice
Rameez ya ɗan ɗaga gira, ya san ɗan’uwansa sosai, kuma ya san wannan amsar tana nufin kada a ƙara tambayarsa
Ya sake kallon Rahama. Ya so ya tambaye ta yadda ita da Rayyan suka yi tafiyar, musamman yadda suka kasance a Lagos tare ba tare da wata babbar matsala a tsakaninsu ba, amma da ya kalli fuskarta, sai ya yanke shawarar barin tambayar a ransa
Wataƙila wata rana zai samu damar jin labarin daga bakinta
Bayan sun ɗan ƙara hira, Rahama ta kalli agogo “Daddy dan Allah, zan so a kira driver ya kai ni gida, dare ya yi sosai”
Hajiya ta juya tana kallonta ta nan take “Gida? Wane gida kuma a wannan daren?”
Rahama ta yi murmushi “Hajiya, na san dare ya yi ne, shi ya sa na ce a kira driver”
“To, ai ba inda za ki je, za ki kwana a ɗakina yau kawai”
Rahama ta buɗe baki kamar za ta yi magana, amma Hajiya ta riga ta katse ta “Ba na son jin gardama. Kin dawo daga tafiya, kin gaji, kuma dare ya yi, za ki huta a nan, gobe sai a ga yadda za a yi”
Mommy ta yi murmushi “Ki kwana mana Rahama, baƙunci ne wannan? Ai ba yau kika fara sanin nan ba”
“Na sani Mommy, thank you”
Daddy ya gyada kai “Hajiya ta yi magana, ki huta kawai”
“Okay, Daddy”
Hajiya ta miƙe “Zo ki ɗauki kayanki, bari ki je ki shirya wajen da zaki kwanta”
Rahama ta ɗauki jakarta, ta bi Hajiya zuwa ɗakinta
Da suka shiga, Hajiya ta nuna mata inda za ta ajiye kayanta, sannan ta nuna mata inda za ta ajiye kayan jikinta idan ya cire
“Ki ji sake sosai kamar gidanku Rahama, kada ki ji wani baƙon abu”
Rahama ta yi murmushi “Thank you Hajiya Allah ya saka da alkhairi”
“Ameen, jikalle”
Hajiya ta bar ta ta shirya, ita kuma Rahama ta ɗauki wayarta ta kira Mammy.
Kiran bai daɗe ba aka ɗaga “Hello, Rahama?”
“Assalamu alaikum, Mammy naaa”
“Waalaikumus salam, my love kun iso?”
“Eh Mammy, mun iso lafiya, Alhamdulillah”
“Alhamdulillah! Ya tafiyar? Kun gaji sosai ko?”
“Ɗan gajiya kaɗa Mammy, amma Alhamdulillah, yanzu ina gidan su Ya Rameez ne”
“Gidan su Rayyan?”
“Eh Mammy, dare ya yi sosai wai Hajiya ta ce in kwana a kawai, gobe zan dawo gida, in sha Allah”
“To madalla ki kwana lafiya, ki gaishe su Mommy da Daddy, sannan ki gaishe da Hajiya”
“In sha Allah, Mammy”
Rahama ta katse kiran, ta ajiye wayarta a kan ƙaramin teburin da ke gefen gado
Ta cire kayan jikinta, ta cire kayan da idan tayi wanka zata saka, sannan ta zauna na ɗan lokaci tana danna wayanta
Can a hankali gidan ya fara yin shiru. Muryoyin da suke fitowa daga falo suka ragu, ana rufe ƙofofi, kowa na komawa ɗakunansu
Rahama ta kalli agogo 10:07 PM.
Ta dafe cikinta “Yanzu kuma me nake ji haka?” ta tambayi kanta a hankali
Cikinta ya sake ƙara
Ta zaro ido ta kalli ƙofar ɗakin Please ba yanzu ba, ba ni da ƙarfin zuwa parlon”
Can taga ba zata iya ba, ta miƙe, ta gyara vintage dinta, sannan ta buɗe ƙofar ɗakin a hankali
Falon ya yi shiru, a haka ta fito, ta bi hanyar dining tana kallon ko akwai wanda yake wurin
Sai ta ga Rayyan zaune a dining table yana cin abinci, hade da shan tea
Ya ɗago kai da jin motsinta
Rahama ta tsaya na ɗan mintuna, sannan ta ci gaba da tafiyarta ba tare da ta kallesa ba
Rayyan ya ajiye kofinsa “Can’t you greet when you see someone?”
Rahama ta tsaya ta juya kaɗan “Good evening”
“It’s past ten”
Ta kalli agogo a bango “To, good night kenan?”
Rayyan ya zuba mata ido “Do you always have to be difficult?”
Rahama ta ɗaga kafada “Ban san kana son gaisuwa ta musamman ba. Next time, zan zo da microphone”
Ya yi tsaki ya koma shan tea ɗinsa
Rahama ta juya tana tafiya zuwa kitchen “Tsaki ɗin nan fa…” ta faɗa ƙasa-ƙasa “Ya riga da ya saba”
“What?”
Ta tsaya a ƙofar kitchen, ta juya masa fuska “Na ce tea ɗin ya yi zafi ne?”
Rayyan ya kalli kofin da ke hannunsa, sannan ya kalleta “Stop talking nonsense”
Rahama ta ɗaga hannayenta biyu “Okay sir, I’m leaving”
Ta shiga kitchen, ta ɗauki abincin da aka ajiye mata, ta kai shi parlon ta zauna ta fara ci
Bayan ta gama, ta kai plate inda ya kamata, ta wanke hannunta, sannan ta koma ɗakin Hajiya
Da ta shiga, ta rufe ƙofar a hankali, ta cire dankwalinta ta ajiye a gefe
“Alhamdulillah” ta furta tana kwanciya a kan gadon