MATAR SALMAN

Chapter 5

by @hauwa3030

*đź’«MATAR SALMAN đź’«* 


 âžˇPART ONE
   Page 5

Kafin Ya Salman ya koma Lagos sai da ya tabbatar babu abinda muke bukata. Sannan ya bani dubu biyar yace in ajiye in wata bukata ta taso in dauka in kashe kuma ya gargade ni yace banda yawace yawace, kar in biyewa su Sadiya. Naji kewa sosai duk da ba magana mai tsawo ke shiga tsakaninmu ba. Munyi exams an bamu hutu har na tsawon wata daya.

A cikin week din ya Salim yazo ya sauka a dakin ya Salman, ranar raba dare mukayi a dakinshi muna hira saida Maman Sakina tazo ta kira mu tace mu bar shi ya huta haka nan dare yayi.

 Washe gari kuwa muka shirya ya kaimu gidan Mama dake borno avenue. Babban gida ne tsarin ginin zamani ga kayan alatu. Alhaji Aminu shine mijin Mama shahararren É—an kasuwa ne, matansa uku Mamace cikon ta hudu, yaransa goma sha shidda yawanci sunyi aure wasu kuma na makaranta a kasashen waje. Kuma abin birgewa ko wacce mace da sashinta da kuma masu aikinta.
Wallahi ko da naga irin jin dadi da Mamana ke ciki ji nayi kamar nayi zamana anan kar na koma gidan su Ya Salman, sai dai nasan ba karamin dalili bane ya saka Mama taki in zauna a gabanta ba, ko ba komai naji farin cikin ganin mahaifiyata cikin jin dadi da kuma walwala, Alhamdulillah.

Ta kawo mana kayan ciye ciye kala kala ga 'ya'yan itatuwa da lemon kwalba ga abinci iri iri. Muka bude ciki mukayita ci muna santi nida Sakina da Zainab Raihana na taya mu. Sadiya nata yatsune yatsunen fuska, har wani kallon banza take bin Mama dashi in taga ta wuce duk ina lura.

Bayan munyi azahar ne ta kaimu dakunan kishiyoyinta muka gaggaisa har palon Alhaji ta kaimu ya karbemu da fara'a kamar yaran cikinsa, na lura yana ta ji da Mamana.

Ban samu na kebe da Mama ba sam saboda su Sadiya har dare karfe 7 ya Salim yazo yace mu tafi gida. Gaskia kishiyoyin Mama suna da kirki ko wacce sai da ta cikamu da kaya. Shima Alhaji ba'a barshi a baya ba kudi ya raba mana dubu goma goma, munata murna.

Anan mukayi sallama da kowa kamar ince zan kwana, don ban gaji da ganin Mama ba, kuma ina son muyi hira. Ganin yadda na bata fuska hawaye na kokarin zubowa yasa ya Salim yaji tausayina yace ”Goggo Amina Rumaisa kawai ta kwana jibi zanzo in dauketa......”

Kafin ta yi magana har Sadiya ta yi farat tace ”To muma zamu kwa......

Tsawa ya Salim ya daka mata ”dallah wuce mota malama, in kun zauna anan suwaye zasu yi aikin gida?”

Na lura sam Ya Salim baya son maganar Sadiya. Haka suka shige mota nikam tuni na tafi cikin gida.

Yace wa Mama ”Goggo kamata yayi ma Rumaisa ta miki sati saboda kun jima baku hadu ba, amma zatayi kwana biyu kawai don ina so ranar Sunday mu wuce Abuja da ita tayi hutunta acan.”

Cike da fara'a Mama tace ”babu komai Salim na gode sosai Allah ya kaimu rai da lafiya kuma.”

Daga haka ya mata sallama suka tafi tana daga musu hannu har saida motarsu ta bace. 

Nikam dama bedroom na wuce na fada gado ina birgima ga AC. Mama da ta shigo kallona tayi sai ta yi murmushi tace ”to meye hakan kuma?”

Nace ”wallahi Mama rabona da in kwanta kan gado tun a kauye, a dakin Inna fa a Palo nake kwanciya ni kadai akan kujera in ta jin tsoro kuma da asussuba take tashina in ran girkintane ta yi ta sakani aiki ga zagi da gori kam kala kala inasha.”

Nan na tsinke da bada labarin su Inna. Tun Mama na tsaye
har ta gaji ta zauna ta na kallona bata katseni ba, har na gaya mata ma athsma na ma ya tashi rannan sai da aka kaini asibiti

Ta numfasa tace ”Hmm! To Allah shi kyauta, Shatu dai bata canza hali, wallahi ni dama ɗakin Rabi (Maman Sakina)kika zauna.”

Nace ”ai Yaya Salman ne ya kaini dakinsu Inna nima bana so.”

Tace ”kar ki damu ke dai kici gaba da musu biyaiya kiris ya rage ai idan kika tafi jami'a hostel kawai zaki zauna, tunda Salman yace zakuyi ssce dinku a ss2 koh?”

Nace ”eh haka yace.”

Hira mukeyi har sha dayan dare yayi bamu sani ba. Mama ne ta kalli agogo tace ”tashi kije kiyi wanka mu kwanta.”

Nace ” To, amma Mama sai kin nuna min yadda ake yin komi fa a bandakin naki, ni ban gane komi ba, dazu ma Sakina na kira ta nuna min nayi alwala.”

Dan dariya ta yi tace "Wayyo Rumaisa muje to.” Muka shiga ta nuna min komi sannan ta fita ta barni. Bayan nayi wanka ta ban zaninta da t shirt na saka ina ma kaina dariya a madubi. Itama ta shiga ta yi ta shirya sannan muka kwanta. Bacci na rika yi da kyar na tashi nayi asuba na koma Mama kyaleni tayi nayita sharar baccina har sha daya yunwa ya tasheni. Nayi wanka nayi brush na shirya sannan Mama tace in tafi dining inje in karya.

Habawa nayita zuba kauyanci nan ma.

Kwanana biyu a gidan Mama Ya Salim yazo ya daukeni don gobe zamu wuce Abuja dashi.

Mama ta bani waya Karama Nokia tace in rike zamuna gaisawa, kuma ta bayarmin kaya kala bakwai amin dinki, ga cosmetics data haÉ—a min harda takalmi da jaka irin na en matan birni irin su Saleema. Dadi kamar zai kasheni.

Mun dawo da daddare ina haɗa kayana Inna ta shigo ta sameni a dakin. Tace ”Wai ke shirin me kike yi hakane?”

Nace ”Inna gobe ne tafiyar tamu Abuja ai.”

Tabe baki tayi tace ”Shiyasa kike ta rawar jiki haka, wato kinje kun gama kulla munafurci da uwarki sai shigewa Salim kike, to me zaiyi dake waye yasan asalinki?”

Kaina a sunkuye tuni hawaye ya fara zubowa a idanuna. Saida ta kare min zagi tass sannan tace ”Ki tashi kije kiyi wanke wanke tunda sammako zakuyi, ga kuma zanin gadona guda biyar na jika ki wanke tass sannan ruwan kumfan ki je ki wanke ban daki dashi, In kin gama na daura pepper soup na ganda a wuta ki hada komi ki jira ya nuna ki sauke sannan ki kwanta, gobe da ssassafe kuma ki tashi ki hura wuta ki dora ruwan shayi saura ki kuskura in tashi in sami ba kiyi min yadda nace ba kiga abinda zan miki.”

Ta na gama maganganunta ta fita nasan dakin Abba zata tafi don yau girkinta ne. Na kalli agogo karfe goma har yayi da sauri na tashi na fita wanke wanke nayi na gama na kama wanke bedsheets inayi ina duba girkina har na gama wankin naje na karasa parking ina zaune a Palo har saida na sauke pepe soup din sannan na kwanta a gajiye sosai.

Asuban fari na riga kowa tashi naje na hura wuta na daura ruwan tea sannan na wanke ban dakin don jiya naga dare yayi ina tsoro, wanka nayi nayi brush hade da alwala. Kamin dai Inna ta fito har na shirya tsaf don har É—akin ma da tsakar gida na share. Shidda saura ta shigo ta sameni a shirye tsaf.

Na gaisheta harara ta watsa min tace ”kina ta rawar jiki zaki Abuja wai har kin gama aikin ne?”

Nace"I na gama Inna.”

Tabe baki ta yi ta shige ciki naji tana tashin su Sadiya daga bacci sai fada take musu don ko Sallah basuyi ba.

Bayan mun karya karfe bakwai muka dauki hanya da Ya Salim. Mun isa Abuja lafiya
nikam sai kallon kauyanci nakeyi lallai Abuja babban birnine gaskiya ba karya.

Gidan Kawu Kasim kam ba magana don ya tsaru iya tsaruwa kai gabadaya anguwan haka gidajen suke sai ka rikice ka rasa wanne yafi wani, to kamar gasa fa sukeyi, lallai kudi suna inda suke.

Muna sauka mota sai ga Fa'iza wacce take bin Ya Salim, amma sa'ar muce da Sakina. Sai kuma É—an karaminsu Hakim.

Da fara'a suka mana sannu da zuwa, Fa'iza ta rumgumeni babu kyama.

Sannan ta dauki kayana mukayi ciki, anan naga Ammeensu ita ma da fara'a tace min ”mutanen Kano oyoyo marabanku da zuwa.”

Na ɗan russuna nace ”Ina kwana aunty.....”

Cike da fara'a tace ”Aah kinga 'yata kuje ciki kiyi wanka ga breakfast na shirya muku a dining in kun gama kije ki kwanta ki huta tukunna......

Ta dafa kafadana ta na murmushi tace ”In yaso sai mu gaisa a nitse ko?”

Naji daɗin yadda suka karbeni sosai. Faiza ta kaini dakinta ta nuna min ban daki nayi wanka na canza kaya na fito dining tuni ya Salim da hakim kam suke jira. Anan fai,za ta musu serving ta kalleni tace ”Rumaisa me zan saka miki?”

Nayi murmushi nace ”komi ma na inaci.”

Tace"wow ya Salim na sami 'yar uwa fa, mu komi ci muke.”

Dariya yayi yace ”Sai kuyi ta ci ai.”

Itama dariyar ta yi sannan ta sakamin dankali soyayye da kwai sai pepper soup na kayan ciki, sannan ta tura min kayan tea itama ta hada nata 

Mun fara ci tace"wayyo ya Salim na manta ban gaya maka abinda ya faru a BEYHAD ba.

Ya salim yace ”Aikuws an wuceni sosai ko?”

Haka suka dinga hiran series har muka gama breakfast, muka dawo Palo. Ya salim kam yana da saukin kai don hira yake da kannensa sosai ba kamar Ya Salman ba.

Nan da nan na sake Fa'iza ta dinga koya min kwalliya iri iri na wayayyun en matan Abuja, yayinda mummy kuma take koya mana girki zamani kala kala. Kafin kuce meye wannan nima na goge, har wani kyau na kara haskena ya fito sosai saboda hutu, nima sai É—ana magana da turanci nakeyi abuna lol!

Yauma bayan mun fito daga kitchen wanka mukayi, bayan mun gama shiryawa na kalli Fa'iza ina murmushi nace ”Fa'iza shigarki tana burgeni wlh naga ke baki damu da saka wasu riga da siket ko da zani ko wando ba, sai dogayen riguna kawai.”

Tayi murmushi tace ”Aini sam kinga banson abinda zai takurani ne Rumaisa, don nafi feeling free a cikin dogayen riguna shiyasa duk kayana sune.”

Ta karaso kusa dani ta zauna tace ”Kema ai in kina so sai ki fara sakawa.”

Na tabe baki nace ”Ina na ga kayan ma tukun dududu dogayen rigunana basu wuce uku bane fa.”

Ta yi dariya tace ”Kar ki damu ina da sabbi na zaman gida guda biyar zan baki kuma nasan zamuje shopping in Abbie ya dawo zai bamu kudi sai ki zabi iya son......

Karar wayar ta ne ya katseta ta dauko sai naga ta saki murmushi ta daga hade da limshe ido tace ”Hello Yaya.”

Ta danyi shiru sannan a shagwaɓe tace "Yaya munyi missing dinka sosai fa Allah yaushe zaka zo Abuja?”

Ta sakeyin shiru sannan tace ”Gata nan muna tare a bata ne?”

Da sauri ta mika min waya hade da fadin ”Ya Salman ne.”

Na karba da nasa a kunne nace ”Yaya ina wuni?”
”Lafiya lou.” Ya amsa sannan yace ”Me ye full Name dinki da kike amfani da shi a school?”

Nace ”RUMAISA IBRAHIM AHMAD.”

Yace ”OK.”

Sannan ya kashe na mikawa Fa'iza, nace ya kashe ta karba tana murmushi tace ”gaskia wannan guy din zai kasheni da sonsa, ba karamin wahalar da zuciyata yake ba.”

Zaro ido nayi da mamaki ina kallonta nace ”waye kuma Fa'iza?”

Ta mika min wayar ta ina dubawa photon Ya salman na gani cikin kakin sojoji. Rass naji gabana na faduwa na mika mata da sauri nace ”Innalillahi Fa'iza ai Yaya Salman wannan, me kuma ya hadashi da kayan mugayen nan?”

Dariya ta yi ganin yadda na rikice ta zauna tace ”kina nufin baki san Yaya soja bane?”

Na girgiza mata kai sannan nace ”Ko kusa ko da wasa ban sani ba wallahi.”

Tace ”To soja ne shi ki sani daga yau .

A tsorace har jikina na rawa nace ”Ya rasa abinyi ne ya shiga aikin soja?”

Dariya ta yi tace ”Ahh kamar yaya ra'ayinsa ne kawai in faɗa miki.”

Shiru nayi ban kuma cewa komi ba nidai.

Taci gaba da fadin ”Wallahi Rumaisa son Ya Salman nake kamar zan mutu Allah, ko Rumaisa ni inaga zan fada masa kawai duka abinda zaiyi ma yayi na gaji da noke noke nidai, tunda yaki ya gane shi.”

Nan da nan annurin da ke kan fuskata ta gushe, na rasa dalilin da yasa maganar ta ya ban haushi nan take, har ta gane tace min ”Lafiya Rumaisa?”

Nayi ajiyar zuciya nace ”Hmm Fa'iza zanso ace ke ce matar Ya Salman amma kinsan Ya Salman ba wacce yake so kamar Salima to ya zakiyi ki cusa kanki? Kuma Inna ma dasu Sadiya sonta suke kamar zasu hadiyeta tsabar alherinda take musu.”

Jikin Fa'iza a mace tace ”Hmm ai Rumaisa ni kaina nasan labarin wannan Salimar tashi, bansan ya zan yi ba Sakina tace min yana sonta sosai gaskiya.”

Nace ”Kuma abin takaicin ma kuma ma naji ance iyayenta sunce baza su bashi ita ba amma sai dagewa yake ko me ya gani a jikinta nema ni oho.”

Fa'iza ta danyi shiru sannan tace ”Ni fa inaga Ya Salim kawai zan fadawa, bazan cuci kaina ba, Allah ya gani ina sonshi, kuma banjin akwai wanda zan so ko anan gaba, domin Ya Salman kaɗai ne a gabana, na koyi sonshi tun ban gama mallakar hankalina ba, a zatona shakuwace ta ƴan'uwantaka, tunda kinga shi a gidan nan ya tashi tun suna ƴan shekara bai fi takwas ba.......

Saboda yadda nakejin maganar nata na damuna sai kawai na katseta don in kawo karshen hiran nace ”Eh kin kawo shawara kuma wallahi in su Abba sunji zasu amshi maganar hannu bibbiyu sabida zumunci ya kara dorewa, Allah dai ya sanya alheri.”

Tana murmushi tace ”Amin sis na gode da kulawarki gareni.”

Gaskia Fa'iza ba karamin so takewa Ya Salman ba na lura hmm.

Nayi wata na daya a Abuja, sai kunga yadda na murmure nayi kyau abuna, dama ana saura one week a bude school Ya Salim yace in shirya Ya Salman zaizo daga Lagos mu wuce Kano tare.

Kawu Kasim ya bama Aunty Zuwaira kudi masu yawan gaske yace akaini shopping na sayi duk abinda nake so. Murna na dinga da godiya, nan muka shirya da Fa'iza muka tafi da Ammie gaskia nasha siyayya kam masha Allah, waya Ammie ta siya min babba, Wayyo Allah nima na shigo gari, Su Sadiya sai dai bakin ciki ya kashesu

Ko da muka dawo Fa'iza ne ta koya min yadda zan dinga amfani da wayar, nan da nan na gane komi. Wai sai ga Rumaisa a Facebook,WhatsApp.har da Instagram
Tunda na sami waya bana komai sai aikin danne danne......

Yau ma ina ta sana'ar kallo a wayata Fa'iza ce ta shigo dakin da sallama ban ma jita ba har ta wuce bayi wanka ta yi ta fito ta zauna gaban mirror ta fara kwalliya, kamshin turare da na fara jine ya sakani ajiye wayar nace ”to fa sabon salo sai ina haka da wannan kwalliyar yammaci ko zamuje shan ice cream ne.”

Ta harareni ta cikin madubi tace ”wani ice cream kinaga har Ya Salman ya kusa shigowa Abuja ban mishi kwalliya ba.”

Dariya nayi nace ”To fa yanzu wannan adon duk na Yayan ne?”

Tayi fari da ido tace ”Kwarai da gaske.

Nace ”Yayi matar Soja.”

Ta tashi ta dauko dogon riganta na atamfa tasaka ta zauna ta murza daurin ɗan kwali har gaban goshi ta zubo da gashi kan kafada. Nikam dariya nayi nace ”abin naki fa da gaskene, to wai ni sis ya sunan daurin dankawalin nan?”

Tayi fari da ido sannan tace ”sunanshi ture kaga tsiya”.

Na sake tinsirewa da dariya nace ”aikuwa na gani matar soja.”

Ta daga min gira hade da fadin ”yessss”

Sannan ta dauko turare ta fara fesawa, yamutsa fuska nayi jin kamar turaren ya min karfi, don haka da sauri na tashi gudun kar ya shige min hanci in sami matsala..... Aikuwa cikin rashin sa'a ina mikewa ta fesa setin hancin nawa, Wayyo nan da nan na rikice numfashina ya sauya kirjina ya fara toshewa na fara kokuwa da numfashi na, na durkusa a wurin. Jifa ta yi da turaren da sauri ta kamani tana ”Na shiga uku Rumaisa kar dai kinada athsma..... sorry ina inhaler dinki?”

Da kyar na nuna mata jakana ta je ta dubo amma babu. Kawai babu ɓata lokaci ta kira Ammie, itama ganin halinda na shiga yasa tace kar a bata lokaci mu tafi asibity kawai

Muna zuwa aka min taimakon gaggawa sai da sukaga komai normal sannan muka dawo gida.

A harabar gida muka ga ya Salim da wani sanye da kayan soja. Nan naji zuciyata ta tsinke don tsabar tsoro don mu a kauye ko police ma gudunsa muke bare kuma soja.

Muna fita suka karaso wurinmu kuwa na kalli Yah Salman cikin kakin Sojoji hmm. Da kyar na iya dagowa na É—an saci kallonshi yana gaisheda Ammie.

Aikuwa ina dagowa muka hada ido da sauri na sauke idona nayi ciki da sauri.

Ammie da ya Salim har hada baki suke ”Ke lafiyarki rumaisa?”

Fa'iza ne ta yi dariya tace "Tsoron ne fa taga Ya Salman da kaki, kunsan a kauye police ma na basu tsoro.”

Dariya sukayi gabadaya banda ya Salman don shi haushi ma yaji.
Ammie tace ”Aikuwa gara ta cire wannan tsoron yanzu kam tunda ta zama ƴar birni.”

Salman yace ”Ammie ina kika je ne haka?”

Ammie tace ”Kaga tsautsayi ne Fa'iza ta fesawa Rumaisa turare a hanci shine ciwonta ya tashi, ba bata lokaci muka tafi asibity don dazun da kyar take numfashi ma, amma da sauki yanzu.”

Ya Salim yace ”Subhanallah! Allah ya bata ya kiyaye gaba.”

Sukace ”Amin.”

Daga nan suka nufi Palo duka Fa'iza ta kalli Ya Salman murmushi tayi tace ”Yayana na shirya maka abinci da abinsha kala kala.”

Ba tare da ya kalleta ba yace ”nagode.”

Bayan sallar isha muka hadu a dining gabaɗaya. Da kyar na iya kallon Ya Salman ashe ya cire kakin nashi ma tuni. Muka hada ido da sauri na sauke idona nace ”Ina wuni Yaya?”

A takaice ya amsa min da lafiya kawai yaci gaba da abinda yake.

Daga nan naja bakina nina nayi shiru sai Fa'iza da Hakim suke ta zolayata yau dai na kasa sakewa bare in basu amsa.

Muna gamawa na tashi zan wuce daki Fa'iza tace ”ke za'a fara BEYHADH yanzu ko kin manta ne?”

Nace ”Ah ah ni bacci zan yi.”

Ya Salim yace ”Ko dai har yanzu ba kya jin dai dai ne?”

Na ɗan yi murmushi nace ”A'ah Alhamdulillahi naji sauki so nake inje in karasa parking inyi bacci da wuri saboda in tashi da wuri.”

Yace" OK to Allah ya tashe mu lafiya.”

Nace " Amin.

Hakim yace " aunty Rumaisa ki tsaya ki gani mana.”

Harararsa nayi sannan na shigewata ciki.

Fa’iza kam na gefen Ya Salman akan kujera ko da muka hada ido ma gwalo ta min. Da safe kuwa muna gama breakfast muka je muka sallami Abbie anan na kara yi masa godiya. Yace min ”babu komai Rumaisa, in Allah ya kaimu wani hutun ma kizo don munji dadin zuwanki kinji.”

Ammie ma tace ”Kwarai kuwa, wani hutu ma kizo.”

Murmushi nayi nace ”Inshaa Allah zanzo, nagode sosai Allah saka da alkhairi.”

Mun fito harabar gidan, Na gaisheda ya Salim sannan na kalli Ya Salman shima ni ya zubawa ido na rasa dalilin yawan kallona da yake tun jiya.

Nace ”Yaya ina kwana?” Ya amsa kamar kullum a takaice.

Ammie tace ”Kai Salman ban yarda da kallon nan da kake mata ba fa.”

Murmushi yayi yace ”Ammie to na ga 'yar kauyen ce ta canza ne gabadaya.”

Sukayi dariya Ammie tace ”Hmm ai tukunna ma, kai dai in kana yi ka shigo daga ciki muyi 'yar gida gida kawai.”

Nan da nan ya tsuke fuska yace ”Allah ya sawwaka ni me zan yi da 'yar kauye kuma Ammie, sai dai ko Salim.”

Ya Salim yace ”Ai bani aka yi alkawarin aure tsakanin mu ba.....

Ammie tayi dariya tace ”Kwarai kam, don nice ma nayiwa Salman kamu tin tana er shekara biyu, kuma nace Amina ta rike wannan alkawarin, gashi Allah yayi lokacin cika shi, don haka kaje ka tara kudin aure malam.”

Faiza ko kunya babu tace ”Ammie to nifa?”

Murtuke fuska Ya Salman yayi yana kallon ta yace ”Ke ni sa'anki ne koni abokin wasanki ne, kifa shiga hankalinki?”

Da sauri ta koma bayan Ammie, ganin kamar zaizo ya daketa, tasan kuma tsaf zai aikata.

Salim yayi dariya yace ”Soja mai farin jinin ƴan mata, kai dai kaje kayi tunani duk wacce kaga tafi dacewa da kai acikinsu.

Ammie ma cikeda zolaya tace ”Duukkansu ma zamu iya baka ai, kuma munsan zaka iya rikewa.”

Fuskarshi a ɗaure yace ”Ammie kuna magana a gaban yaran nan sai su dauka da gaske su rainani fa, don Allah ku bari nidai.”

Ya kalleni yace ”Ke ƴar kauye shiga mota mu tafi.”

Dariya suke ta masa.

Daga nan Ammie ta mana addua, Fa'iza kam har da kuka nima sai da hawaye ya ciko min ido sam bana son mu rabu da Fa'iza.

Har mun ɗauki hanya ya kalleni yace ”daura belt ƴar kauye.”

Na fara lalubowa ganin zan bata masa lokaci yasa ya dan kwanto jikina yaja belt ya daura min, cikin rashin sa'a hannunsa ya taba bakina sai ga Jan baki a hannun shirt dinsa ya fitar da shape din bakina mai kyau a jikin rigan abunka da farin abu.

Ya kalli hannun rigar sai kuma ya kalleni tsaki yayi yace ”dubi yadda kika batan riga da jan bakinki anya ba da gangan ma kikayi ba?”

Saura kadan dariya ya subuce min na matse nace ”Kayi hakuri ban sani ba ne Yaya.”

Baice komi ba ya ci gaba da tuku aikuwa gudu yake kamar zai tashi sama nikam kamar na saki fitsari don tsoro kai ya Salman bai da dadin sha'ani, Ranar da muka zo da ya Salim a hankali yake tafiyarshi munata hirarmu har muka isa.

To yau tsabar gudu sai gashi mun iso da wuri ni dai sai hamdala nake ganin mun isa lafiya.

Kawai sai ganin Salima mukayi ta fito daga cikin gida. Nikam yana gyara parking na fita,na bude booth na fito da kayana ko kallo bata ishen ba. Shine ma yana hangota ya saki murmushi kamar ba shi ba.

Ta karaso cike da fara'arta tace ”oyoyo dear.”

Da murmushin shi mai kyau yace ”Ranki ya dade gimbiyar mata yaushe kika dawo?”

Tace ”hmm nima fa dazu na dawo ai bansan kana Abuja ba da mun taho tare.”

Yace "waya gaya miki ina son ki yi taravelling by road ki wahala.”

Murmushi ta yi tace ”to kaima ka daina.”

Murmushi yayi ya harde hannayensa kan kirji yana kallonta anan ta ga jan baki a hannun rigarsa nan da nan yanayin fuskarta ya sauya. Sai ta kalleni harara na watsa mata naja akwatina, ashe karaf akan idonshi. A fusace ta juya zata tafi yace ”Zo kiji Salima.”

Bata ma saurareshi ba tayi tafiyarta. Har zan shiga gida ya tsaida ni ya karaso yana kallona fuska ɗaure yace ”me yasa kika harareta?”

Nace ”Ni ban mata komi ba.”

Hade fuskarsa yayi yace ”Makahone ni ko? Na lura da irin kallon banzan da kike mata wallahi zan mugun bata miki rai. Kuma daga yau in kinganta ki girmama ta ki gaisheta kina jina ko.”

Cikin jin haushi na amsa masa ”Eh.” Sannan nayi cikin gida.


 *RUMAISA SALMAN BY MAMAN KAUTHAR*