GARWASHI

Chapter 20

by @gidaniko422

*Duk inda mai gaskiya yake sai ya wahala a rayuwa, mafi yawan yan Aljanna mabarata ne a duniya, sun rayu Suna masu shan wahala ana musu kallon kaskantattu, amma imanin su ya isa a mizani sai Allah yayi musu alfarmar shiga aljanna, Ku bar kaddara tayi aikin ta, ku bar ikon Allah a inda ya sauka, shiga hurumin Ubangiji daidai yake da cewa Allah bai iya ba, daidai yake da cewa Allah baiyi daidai ba, As'tagfurullah*



*_Wannan Page yabawa ne ga MARYAM IBRAHIM LITEE MALUMFSHI marubuciyar KISHIYA TARA,_*  

*Complete na littafin garwashi 1k ne, ****



..............Salla nake Amma hankalina Yana bayana don ban San Wanda ya shigo ba don ban Kuma Jin wani motsi ba na Kuma San mamakin ganin na kalli gabas ne ya Hana Wanda ya shigo din ya tanka don bana ma zaton wani zai iya shigowa Kai tsaye in ba yarima Gibson ba shi Kuma banji Zan iya boye mishi ko Ni wacece ba don ya hutawa Ranshi Akan dora Ran da yayi akaina domin kuwa mun Sha banban Kuma tazarar mu tana da tsayi don tamkar nisan sama da kasa ne
Na sallame sallar Ina waigowa don Inga Wanda ya shigo sai Naga babu kowa sai iska dake kada kofar tana lilo inda Naga Ashe hadari ne ya Soma tasowa don Haka na yi saurin cire hijabina na mayar a cikin jakata na zauna Akan kujerar falon na zabga tagumi Ina hango ta inda Zan samu mafita  wadda zata fitar Dani Amma na Rasa gano ta nayi shiru Ina tunani sai naji karar waya ta nayi maza na jawo ta inda Naga sunan Umar nayi murmushi naga tare da sallama cikin wata siririyar murya ya amsa Yana tambayar inda na shige Bai ganni ba bare na Kai mishi fauziyya Yar Amana 


"Kayi hakuri tafiya ce ta Kama Ni Amma Zan kawo maka ita alkawari nayi maka . Muka ci gaba da fira Yana Kara fada min hanyoyin da Zan bi don Kara inganta addini na da Kuma ADDU OIN da Zan Rike Wanda zasu Kara taimaka min. Muna cikin wayar ne Ruwan sama ya Soma saukowa Wanda yayi daidai da shigowar yarima Gibson ya shigowar shi Kuma Bata sa na fasa wayar da nake ba saima bin shi da kallo da nayi shima Kuma ya bini shanyayyun idanun shi Wanda basu boye tsantsar kaunar da Yake min ba fuskar shi dauke da murmushi da Kuma jin Dadin gani na a dakin nashi . Jin da hausa nake magana yasa ya zare wayar daga kunne na Yana duba sunan Wanda ke Kan Kiran yayi maza  ya hade fuska tare da kashe wayar gaba Daya ya saka ta aljuhu

Bai nemi ba asin ko waye Wanda muke maganar dashi ba Haka Kuma baiyi min tsegumin komai ba sai dai yadda ya nuna ba zai bani wayar ba kenan dai iko zai gwada min irin na matar Auren shi wadda Yake Aure

Nayi zaton ko zai nuna min bacin Ranshi ko yayi min fada Amma Kuma sai baiyi hakan ba sai ma murnar zuwa na dakin shi da Yake 
Kan kace me? Sai ga nau ikan abinci ana shigowa dasu ana tsube su a Gaban mu tamkar za ayi wani party ko dinner

Ya tsura min ido Yana kallon tsakiyar idanu na Wanda ban San me Yake Shirin hangowa ba wata Kil tana zai iya fuskantar yadda nake Jin shi a zuciya ta sai naji wani sashe na zuciya ta Yana tausaya mishi akan son da Yake min Wanda Ni ba Haka bane a wurina sai Kuma na Gane a yanzu Ni din musulma ce su Kuma musulmai an San su da kyautatawa don Haka sai nayi nufin kyautata mishi ko don na tabbatar da Ni din a yanzu Ina daga cikin masu kyautata wa

Na Riko hannun shi na Runtse a nawa Nima na zuba mishi ido inda na gano tsantsar farin cikin da yayi da wannan Yar kulawar da na nuna mishi sai kawai naji Yana hada tsinin hancin shi da nawa Yana  Kuma Riko kuturi na Yana son dauko Ni ya daidaita Ni da tsayin da ya zarta Ni zuwa fuskar sa

Sai dai Kuma abinda bana so kenan don Umar ya fada min babu kusantar mace da namiji su Biyu don na ukun su zai iya zamowa shaidan Amma Kuma Dole ne nabi hanyar da zamu Rabu lafiya da Gibson Amma Kuma Rabuwa lafiya yana nufin na bishi yadda yake so yayi min ciki Wanda dama saboda Haka Amaka ta tako takanas ta Kano ta kawo Ni ita da kawayen ta suna Kuma alfahari da hakan

Ban San yadda akayi ba sai naji ya sake kwata min abinda yayi min lokacin da yazo gidan mu wato hada bakina da nashi a wannan karon kuwa cikin wani salo yakeyi abinda ya ganar Dani manufar da Yake nufi wato kudirin su Amaka yake kokarin cikawa wadda har kudi Amakar ta Kai a coci Wai ayi Mata addau a na shigo da kafar dama gidan Gibson Ina shigowa nayi tuntube da ciki wats Kil Kuma ADDU AR tace ta karbu

Nayi saurin zare jikina don dai na tabbatar da ADDU A R Amaka Bata karbu ba ba Kuma zata karbu ba da ikon Allah

Na nuna mishi abinci yace nayi service din shi muci tare. 
Na zuba abincin Wanda ya zamo na Alfarma Kuma na gidan sarautar igwai  sai sai Ni ba najin cin abincin Amma Dole ya SHIGA bani a Baki Yana bani Kuma Yana fada min kalaman nuna kauna da tarairaya har naji tausayin sa sosai don yayi nisa a cikin bege na Ni kuma Bai San munyi hannun Riga ba Ni Ina gabas shi kuma Yana kudu

A Dole Nima na ciyar dashi abincin har yaji Ashe dai shima Yana da wani matsayi a gareni ko Yaya ne

Wasu Mata daga bangaren mah suka shigo suka zube a gaban mu suna gaisuwa inda suke da dauke da sabbin kayan shimfidar gado komai Kuma na shimfidar farine tas ban kawo komai a Raina ba a zato na ma tunda gidan cike yake da hadimai ai komai yi musu ake musamman yarima Gibson don Haka suka nufi Uwar dakin suka sabunta sabuwar shimfidar suka fito suna Mana bankwana

Bayan mun Gama cin abincin ne yace zaiyi wanka Kuma nice Mai hada mishi Ruwan wankan Dole Kuma na SHIGA na hada Ruwan wankan na fito na sanar dashi ya SHIGA da ya fito ne Nima na shigo Amma fa zuciya ta fal zullumi da tsoro tsoron Kar yayi nasarar samun abinda yake muradi akaina ganin daga Ni sai shi a daki Kuma indai karfi zai gwada min to Babu abinda ba zai faru ba sai dai ko in Bai so bane

Na fito ne cikin Rigar da na SHIGA da ita maimakon na dauro tawul ga Kuma sallar Isha I da ban samu zarafin yi ba

Ban gan shi a falon ba sai motsin shi da najiyo a uwar dakin don Haka na kasa motsawa

Ina tsaye ya fito cikin Rigar bacci Mai madaurai a gaba ya taje sumar kanshi inda Ni da kaina na yarda na Kuma Amince Gibson Mai kyaune Amma kuma kyan da sai dai na yabawa wata Amma bani kyan ya amfanar ba. Ya Ruko hannuna ya Runtse Yana Yana Rungumo Ni a kirjin shi zuwa Uwar dakin inda ya nuna min wani mirro da aka tsube kayan kwalliya na Mata Wanda na tabbatar dama Ni aka shiryawa shi. Yayi min Rada a kunne Wai na tsara mishi kwalliya wadda zata kayatar dashi wadda zata Hana shi bacci a yau din 

Ya koma Kan gadon ya kwanta Yana zubo min ido Amma Kuma na Rasa abinda zanyi a gaban mirror din don Sai hikima ta ma ta kubuce na kasa ko da shafa cream ne bare kwalliyar da Yake magana wadda zata gigita shi

Lokacin da na dauka A zaune ne ya fahimtar dashi bani da niyar tashi don Haka shi Kuma Ni din kawai yake jira don Haka ya Miko ya taho ya Kama kafaduna ya dago Ni Yana fadin Wai ko Babu kwalliyar Yana Sona a Haka 

Da na fahimce shi sai Naga Akan gadon yake kokarin kaini kafin ma nayi tunanin mafita sai jinayi yayi sama Dani ya Dora Akan gadon Yana Kuma yi min abinda ya ganar Dani manufar shi na Kuma Gane bani da mafita sai wadda na samowa kaina don Haka Yana farawa da Kai bakin shi a nawa sai kawai na yanke shawarar tada aljanun karya  sai na kurma uban ihu Ina furje furjen yawu Ina tuma Ina faduwa abinda ya dakatar da yarima Gibson daga nufin shi da kudirin shi ya koma yadda Zan dawo daidai Amma har dab da safiya ban Daina gurnanin karya ba tamkar wata damusa ................


Kar ku Bari ayi Tafiyar nan Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran



Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI💃🏿