Chapter 21
by @gidaniko422
*Yau fari gobe tsumma haka rayuwar ta koma, abubuwa da yawa Wanda bama so kaddara ta bamu su, abubuwa da yawa da muke so kuma kaddara bata bamu su ba, Ku lura ba komai ne kaddarar Ku tazo dashi ba, wani Abun duk yadda kake son shi in kaddara bata baka shi ba dole ka hakura, wani kuma duk yadda baka son sa in kaddara ta baka shi dole ka jure, Allah ya Allah! Ka zama gatan mu*
Complete din littafin 1k ne, ***
_Gaisuwa ga makarantan wannan littafi a duk inda suke, Allah yasa rubutun ya amfane mu mu duka baki daya_
...........Sai dab da Asubahi naji Ni kaina na gaji da wannan furje furjen don da gaske bacci ne Yake neman lullube min idanu don Haka na sulale Nan inda na tada borin karya ta na kwanta Kan kace me? Sai bacci ya sureni inda Kuma yarima Gibson ya bini da shanyayyun idanun shi cikin tunanin abinda ke faruwa akaina don shi Kam ai Bai bukaci Nazo don ya zuba min ido ba ya sanar da igwai ne cewa Yana son a kawo Ni dakin shi don ya gama ganin abinda Yake so a tare Dani sai Kuma nazo Yana ganin ya Kama Kuma sai wannan abin ya sameshi ba don ya tsara hakan ba?
Yana tsugune a Gabana Yana kallo na Ni Kuma Ina sharar bacci har dai ya kalli lamarin a matsayin lalura don Haka ya Mike ya shige ban daki ya saki shawa Akan shi kafin shima ya dawo ya Kuma dauko Ni daga kasa ya mayar akan gadon ya na kankame Dani ya Rufe mu da blanket shima tuni baccin ya sure shi
A can dakin mah kuwa ta matsu a Zo a daukar Mata zanin gadon da aka shimfida Mana Mai kalar fari don Wai Ashe Suma fararen shimfidun da aka shimfida Mana hikimar itace don a su Gane wani Abu ya faru don su Soma lissafi
Misalin Sha biyu mah ta turo da kayan break Amma Yar Aiken ta sanar Bata ji motsin mu ba wata kil bamu tashi ba don Haka mah ta saurara
Sai misalin dayan Rana har da Rabi na Fara farkawa don kuwa ai kusan mukayi zaune tuna hakan da nayi yasani murmushi na Kuma dubi yarima Gibson shima baccin Yake ta Shaka na tashi na SHIGA bandaki na saki Ruwa kafin nayi Alwala ta na fito Ina tunanin inda Zan SHIGA nayi salla wani Bai ganni ba
Ina fitowa Kuma shima ya farka Yana kallo na Yana murmushi Yake fadin shine na tashi ban tashe shi ba? Nace Nima yanzu na tashi
Ya Riko Ni Yana kaini jikin shi har Yana shafa min Gashin fuskar shi a tawa fuskar inda Kuma nake tambayar kaina Wai shi duk cikin son ne Yake son hada jikina da nashi?
Ya SHIGA bandaki wanka Ni Kuma na fito falo cikin sauri nayi salla ta ta Asubahi da azuhur na maida hijabin jakata nayi mursisi kamar ba Ni ba
Yar Aiken mah ta shigo inda take fada min ta kawo Mana abin Kari tun dazu bamu tashi ba nace Mata to mun gode ta juya ta fita
Ina zaune jiran ya fito daga wankan don Ni kaina yunwa nakeji Kuma har yanzu baccin nan Bai ishrni ba sai kuwa gashi ya fito cikin wata Riga jallabiya Mai Ruwan goro orange kenan wadda Bata boye gashin dake kwance a kirjin shi ba irin tasu ta princess
Ya ga har yanzu kayan da nazo dasu ne jikina ya Kama hannu na muka koma dakin inda ya bude wadrop ya fito min da wata Riga shigen ta jikin shi sai dai ita ta Mata ce Kuma gabanta ya Sha adon duwatsu Amma fa gaban ta bude Yake sosai don Haka ya Soma kokarin sauya min Amma na Rike hannun shi da ke kokarin cire min Riga
Yayi murmushi ya sakar min Rigar Yana kallo na inda Kuma naji ko Zan iya sauya Rigar ai ba a gaban shi ba shi Kuma ya kasa ya tsare a Dole sai na cire Rigar a gaban shi abinda kuma na tabbatar ba me yuwa bane don Haka na nufi toilet Amma ya kirani Yana fadin nazo zai bani wuri tunda kunyar shi nake nifa matar shi ce
Ya fada Yana ficewa Amma ko da na saka Rigar kunyar na tunkare shi a haka ma ta hanani fitowa sai da yazo ya fito Dani nayi service din mu Yana dab Dani Yana cin abincin cikin nutsuwa Yana Kuma fada min kalaman da Yake yawan furta min na so da kaunar da Yake min tun a cikin barcin shi ya Soma ganina ya kumayi yawon nemana Amma Bai ganni ba sai gashi ya sameni a bikin kanwar shi onye shine ma dalilin da ya daga Ni sama Yana juyi don marna
Bance mishi komai ba har muka gama kafin ya jawo Ni jikin shi Yana tambaya ta abinda ke damu na Akan abinda nayi jiya Mai Kama da shafar aljanu. Kadan ya Rage dariya ta kwace min Amma nayi fuska nace mishi dama bani da lafiya Ina fama da matsalar aljanu na Fadi hakan da fatan yace ba zai iya Auren Mai matsalar aljanu ba Amma sai Naga Akasin hakan har Yana min albishir din zai sama min magani don Haka muje mu kwanta shi fa bacci yakeji
Ba don naso ba na bishi shi Kuma manufar ba ta bacci bace kawai har da muradin zuciya Yake son cikawa Kuma muradan su Amaka har ma da mah dake jiran zanin gadon mu don ta Soma lissafin watan dake kaina
Shima dai a yanzun aljanun karyar na sake tadawa ya Kuma zuba min ido wani Abu na mintsinin zuciyar shi don har ga Allah yanzu dai bashi da buri sai nawa inda Kuma Ranshi ya Soma sosuwa Amma Bai bi ta kaina ba ya koma gefe Ni Kuma naci gaba da furje furjen yawu har zuwa lokacin da na gaji nayi shiru azatona bacci Yake shiyasa Nima na hutar da kaina Ashe ba bacci Yake ba
Ya Aiken mah suka Zo daukar zanin gado suka kwasa suka tafi ban San ya sukayi ba sai ga Kira tana neman yarima Gibson ya Kuma tashi ya tafi inda mah ta nemi ba asi ganin zanin gadon Babu wata Alama da take son gani shi Kuma Bai boye Mata komai ba inda ta daki kirji tana fadin Kai me kace? Me aljanu Kuma? Ba zai yuwu ba
Don Haka sai ta nufi igwai ta sanar dashi abinda ke faruwa shima ya kadu da Jin hakan don Haka amma sai yace babu matsala sai Akira min Mai magani yazo ya Raba Ni da aljanun Amma ita mah ba Haka taso ba yadda taso akwashe Ni a mayarwa su Amaka da Maazi Nkem Amma igwai yace ba Haka za ayi ba Mai magani za a Kira min
Ban San abinda ake ciki ba sai gani nayi an shigo min da wani mutum Wanda suffar shi kadai abin tsoro ce kuma irin shigar shi ta nuna min yafi Kama da matsafa sai Kuma Gibson ke fada min shine zai min maganin aljanuna .................. ...
Kar ku Bari ayi tafiyar nan Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran
Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI🖤
Masu Neman labarin garwashi daga farko su shiga cikin channel din mu zasu samu lanarin daga farko