Chapter 26
*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*Ba ni da Madogara*
(Sai Allah...)
026
Da matuƙar ƙarfi Abdul ya riƙe kan motar don tana niyyar ƙwace masa. Wani sauti motar ta bada ji kake Ƙiiiiiiiiiiiii!!! Ƙiris ya rage motar da haɗu da trailer. Kai tsaye daji motar ta nufa sai kuma ta haɗu da wata bishiya, tana haɗuwa da bishiya ta kama da wuta. Cikin zafin nama Mas'ud da Abdul suke buɗe kofarsu da matuƙar sauri suka taimakawa su Prof suka fito daga motar, hayaƙi ya turnuƙe cikin motar inda wutar bata kai ba. Fitarsu Prof daga motar keda wuya, ko'ina na motar ya kama ta wuta. Allah ya ƙaddara babu wani abu mai muhimmanci a cikin motar. Ƙarasawa wurin wata bishiya su ka yi inda ta yi ɗan nesa da motar. Babu wanda ya ji ciwo a cikinsu kasancewar kowannansu ya saka seat belt wanda hakan ba ƙaramin taimaka musu ya yi ba a lokacin da motar ta bigi bishiyar. Tari sosai mahaifin Abdul yake wanda da ƙyar ya lafa masa kasancewar mutum ne mara son hayaƙi ko ya yake. Kowa kana ganinsa a wurin za ka san yana cikin tsantsan firgici gami da tashin hankali,ba kamar su Prof da mahaifin Abdul. Daga inda suke suna hango yadda motar take ci da wuta bal-bal. Wani Sabon tashin hankali da ya sake riskansu yanzu shi ne wasu ƙattin maza ne har huɗu suka iso inda motarsu Mas'ud take suna duddubawa, kowanne a cikinsu riƙe yake da bindiga ƙirar A.K 47, basu rufe fuskokinsu ba, hakan yasa su Abdul suka iya ganinsu da kyau. Sosai gabansu ya shiga tsananta bugu kenan turosu aka yi idan ma basu mutu ba sai ƙattin su Ƙarasu. Da sauri Mas'ud ya ciro wayarsa da ke cikin aljihu,bai jira komai ba ya fara yin Video ɗinsu, wanda basu san da akwai wasu a cikin dajin ba kasancewar inda su Mas'ud suke ya ɗanyi tudu kaɗan daga inda motar su take. Sai hakan ya basu damar kallon duk abin da ke faruwa a wurin motar. Wani daga cikin ƙattin ya ciro wayarsa ya kira wata numba. Ring uku ta yi aka ɗauka. Daga can aka ce
"Sun mutu ko?"
Kasancewar wutar har yanzu tana ci sosai, sannan ba za a ji shi da kyau ba, sai ya ɗan matsa daga inda motar take don ya ji daɗi amsa wayan, wanda kuwa bai sani ba hakan da ya yi sai ya ba su Mas'ud damar sauraron duk abubuwa da suke tattauna a cikin wayar da kyau gashi a hands free mutumin ya saka. Gyara tsayuwansa mutumin ya yi sannan ya ce
"Ya sheikh babu Wanda ya tsira daga cikinsu, don muna biye dasu har lokacin da motar ta bugu da bishiya"
A can Sheikh Munnir ya ce
"Good job ka tabbata babu wanda ya tsira daga cikinsu ko, don kasan bana son kuskure"
Cike da tabbatarwa mutumin ya ce
"Na tabbata mai girma Sheikh"
A can aka ce
"Ku juyo tunda babinsu ya shafe, Ni zan ji da sauran ayyukan. A tunaninsu za su zo wurina su tafi ba tare da na cika ƙudirina a kansu ba"
"Hakane the Boss of all boss Mai girma Demon king"
Daga haka ya katse kiran tare da komawa inda ƴan uwansa suke suka bar wurin. Kai tsaye motarsu suka hau sannan driver ya taba suka bar dajin. Daɓas! Mas'ud ya zauna a ƙasa. Kowa a cikinsu ya cika ta tsantsan mamaki jin Sheikh Munnir ne ya turo waɗannan ƙattin su ƙarasa su.
*Waiwaye*
Abin da su Mas'ud basu sani ba, a lokacin da suka shiga ɗakin masaukin baƙi, sai Sheikh Munnir ya yi amfani da Wannan damar ya saka a kwance birkin motar da kuma lalata bututun mai. Tun lokacin da mai gadi ya wangame wa su Mas'ud gate, wani daga cikin masu yi ma Sheikh Munnir aiki ya ɗaga waya ya kira sheikh munnir tare da sanar da zuwansu, kasancewar ya san Abdul tun lokacin da suka zo da mahaifiyarsa wurin sheikh Munnir kwanakin baya. Murmushin gefan baki Sheikh Munnir ya yi ganin mugunta ƙarara. Nan take ya umurci mai aikin da ya kwance birkin motar yadda babu wanda zai gane sannan ya tabbatar da ya lalata bututun mai yadda koda sun sake shan mai nan da nan zai ƙare. Hakan kuwa aka yi don mai aikin ya ƙware a wannan harkar. Daman saboda hakan ya ɗaukesa aiki, saboda idan mutum ya zo wurin sai suka ɗan samu hatsaniya. Kai tsaye yake saka wannan mai aikin ya yi aikinsa. Da zarar mai motar ya hau ya bar Layin. Cikin tafiya zai ji motar tana niyyar ƙwace masa wanda a ƙarshe zai yi hatsari ya mutu. Idan kuma bai mutu ba sai yaran Sheikh Munnir da suke biye dashi su ƙarasa shi. Wanda hakan ta sukan faru dasu Mas'ud sai dai haƙar sheihk Munnir bata cimma ruwa ba domin Ubangiji ya tsaresu saboda suna da sauran kwana a duniya. Allah ya toshe wa yaran Sheihk Munnir ƙwaƙwalwar tunanin duba ko'ina na dajin ko su Mas'ud sun fita daga cikin motar. Sannan ya bawa Mas'ud damar naɗe maganarsu ba tare da yaron ya ankara akwai wani a wurin ba don kafa hujja idan an buƙata.
*Cikin labari*
Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya kowanne a cikinsu ya sauke kamar waɗanda suka yi tseran gudu. Prof ya dubi ɗan uwansa ya ce
"Alhaji ka ji komai ko?"
Gyaɗa masa kai mahaifin Abdul ya yi yana cewa
"Na ji komai Abdulrahman, idan na fahimci tattaunarsu kenan wannan hatsarin da muka yi akwai sa hannun Sheikh Munnir. Ba Allah ne ya ƙaddara ba"
"Tabbas Hakane wannan hatsarin shiryayye ne, don alamu sun nuna hakan" cewar Prof.
"A gaskiya Sheikh Munnir kura ne mai lulluɓe da fatar akuya. Mutumin nan ba mutumin arziƙi ba ne, sunan malunta yake amma zuciyarsa ta yahuwa ce. Yaso mu mutu sai kuma Allah bai nufa ba, muna da sauran shan ruwa a duniya. Sai gashi ko ciwo babu wanda a cikinmu ya ji " cewar mahaifin Abdul.
Ɗan wani tunani Mas'ud ya yi sannan ya dubi mahaifan nasa ya ce
" Abba ina da tantama akan wannan mutumin, Ina ganin zan Kai report ɗinsa office Zuwa jibi Idan mun koma, domin a bani damar bincike akansa "
" A'a Mas'ud kar ka saka ranka cikin hatsari, akwai wanda zan kira ya yi mana bincike akansa" faɗin mahaifin Abdul.
Murmushi Mas'ud ya yi sai ya ce
"Abba daman bani zan yi aikin da kaina ba, sai dai ni zan jagoranci aikin"
"To ai shikenan, gaskiya koni ina da ayar tambaya akan Sheikh Munnir, don malamin Allah ba za a taɓa samunsa da irin wannan mummunan aikin ba, Yanzu bari na kira Alhaji Tanimu ya turo mana mota mu koma cikin Maiduguri kar mu ɓata lokaci. Mafi sauƙi mu yanka ticket ɗin jirgi" cewar Prof yana ciro wayansa tare da kiran ɗan uwansu wanda ya ce ba za a jima ba za a kawo musu mota kasancewar basu bar Maidugurin ba. Ko awa ɗaya ba a yi ba aka kawo musu motar da yake har sun fito daga dajin kowannansu jikkunansu na yi musu ciwo saboda jijjigar da suka sha a cikin motar. Suna hawa suka koma Maiduguri. Tun a hanya suka yanki ticket ɗin jirgi na ƙarfe 5:00om a yamma ta online . Suna isa gidan ɗan uwan nasu suka sake sabon wanka tare da mai da kayansu kasancewar basu zo da wasu kayan ba.Zuwa yamma aka kaisu Airport lokaci na yi jirginsu ya Lula sararin samaniya... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Ƴan Majalisu, Unguwan Dosa, Kaduna state. Nijeriya*
Bayan saukansu Mas'ud daga jirgi,ɗaya daga cikin dribobin mahaifin Abdul ya zo ɗaukarsu, suna isa gidan kai tsaye suka nufi masallaci sai da suka jira aka yi isha'i kafin suka fito. Abdul ya shiga gida wurin mahaifiyarsa daga bisani ya wuce part ɗin matarsa a can ya ci abinci. Mahaifin Abdul da prof suka ci abinci tare kasancewar bai koma cikin gida ba. Yana so su gama tsara yadda auran zai kasance daga bisani su san matakin da ya dace su ɗauka akan sheikh munnir, Mas'ud ma ya ci abinci.
A babban ɗakinsa na taro suka zauna, akwai kujeru masu yawa a ciki, Alhaji da prof suka zaune a saman kujera mai cin mutum biyu, sai Mas'ud ya zaune a one sitter, basu daɗe da zama ba Abdul ya shigo. Shiru ɗakin ya yi daga bisani Alhaji ya katse shirun ta cewa
"A idon kowa komai ya faru, da ba don Allah ya nufa muna da sauran shan ruwa a gaba ba da yanzu ana can ana nemanmu domin ban tunanin ko gawarmu za a iya gani sai dai toka"
" Hakane ɗan uwa ta Allah na tashi ba" cewar Prof.
"Mas'ud shin abokinka da gaske yake yana son Halima?" Alhaji ya ce yana kallon Mas'ud.
Ɗan ƙasa da kai Mas'ud ya yi, shi dai a yadda yake tunani gaskiya Mahmoud yana ƙaunar Halima sosai domin labarin zuciya aka ce a tambayi fuska. Babu ranar da za su zaune tare koda kuwa aiki suke bai ambaci sunan Halima ba ko kuma ya yi misali akanta. dan nisawa ya yi sannan ya ce
"Abba bani da tantama ko haufi akan Mahmoud yana son Halima da aure sannan a shirye yake, kwanaki da muka zanta dashi yake faɗamin ya kammala akwatinsa da gidan da zai zauna da ita. Mahaifinta ne cikas ɗinsa"
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke sannan ya ce
"Alhamdulillah faɗuwa ta zo daidai da zama sannan an yi sara akan gaɓa, abin da nake so da kai Mas'ud kiransa za ka yi idan ka koma masaukinku ka faɗa masa idan har da gaske yake yana son Halima da aure to zuwa gobe ya turo da magabatansa a yi maganar aure domin bana so a wuce nan da jibi ba a yi auran nasu ba, idan kuma yaƙi turo iyayensa, Ni da kaina zan zaɓa mata miji zuwa jibi a ɗaura musu aure."
"ina komawa masaukinmu zan kirasa, nasan ba zai yi wasa da wannan damar ba in shaa Allah" cewar Mas'ud.
Gyara zama Prof ya yi sannan ya ce
"Ɗan uwa bayan maganar auran Halima sai maganar shi Sheikh Munnir akan abin da ya yi mana don ba zai ci ɓagas! Ba, dole mu ɗauki tsattsauran mataki akansa"
"Wannan haka yake, kasan commissioner of police na can Maiduguri aminina ne sosai, tun lokacin da muke University, zuwa gobe zan kirasa na sanar dashi komai, nasan zai taimaka mana in shaa Allah" cewar Alhaji.
"Nima zan kira aboki mai gidansu Mas'ud zan sanar masa komai, don gwara mu yi wa tufkar hanci" faɗi Prof yana gyara zamansa.
"Abba nima ina kokwanto anya ba Sheikhul Munnir ya turo yaransa su kasheni cikin dare ba, Allah ya nufa a daran ranar Hassana ta tashi da naƙuda, cikin dare muka bar gidan zuwa asibiti. Bayan mun iisa na kira mom kafin ta zo nurse ta ce ana buƙatar kayan haihuwa wanda na manta ban zo dasu ba. Na tafi ɗauko kayan haihuwar kafin na isa gidana na tarar da motoci har biyu a wurin gate ɗin gate gidana. Ganin salsalin dare ne sai naƙi yarda da motocin, kai tsaye na shiga App ɗina na duba CCTV camera da ke farfajiyan gidan. Ƙatti na gani masu kalar kayan mutanan ɗazu hannun kowannansu riƙe da bindiga amma ba kalar tasu ba, sun tsare mai gadina suna tambayarsa. Ganin haka na juya kan motana na bar Layin" Cewar Abdul wanda sai yanzu ya saka baki a zantawarsu, daman bai faɗawa mahaifinsa abin da ya faru dashi ba.
Sauke ajiyar zuciya kowannansu ya yi sai Prof ya ce
"Biri ya yi kama da mutum, No wonder lokacin da muke falon Sheikh Munnir ya tsareka da idanu kenan he wasn't happy seeing you alive, lalle Sheikh Munnir"
"Dole a tsananta bincike akansa don akwai tantama akansa sosai wallahi" cewar Alhaji.
Daga haka suka ci gaba da zantawa akan yadda za su yi maganin Sheikh Munnir tare da tsananta tsaro a gidansu da iyalansu saboda kar Sheikh Munnir ya sake tunanin farmakarsu idan ya ji labarin suna raye, da kuma yadda auran Halima zai kasance. Kowa na bada ra'ayinsa har daga bisani suka samar wa kansu lafiyayyar mafita mai ɗorewa, daga haka kowa ya nufi makwancinsa... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Kwanar Faru ƙwai, Kaduna state. Nijeriya*
Kamar yadda Hannatu ta ce zuwa gobe za ta dawo, a washe garin ranar ta dawo gidan, ba tare da Faisal ta dawo ba da yake Muntari zai canja masa makaranta ganin ba wani karatun kirki ya iya ba. Bayan ta sauka daga mashin ta sallamesa sai ta ƙarasa cikin gidan bakinta ɗauke da sallama. Murja ta iske a tsakar gidan tana bakacen masarar da ta ɓarzo, jikarta na kusa ta ita. Kallon hadarin kaji Murja ta yi wa Hannatu ba tare da ta amsa mata sallamar ba. Hannatu bata ji haushi ba a tunaninta ko bata ji ta ba ne. Sake kwaɗa wata sallamar ta yi tana ƙarasowa cikin gidan fuskarta ɗauke da murmushi. Cike da harzuƙar Murja ta miƙe daga zaunan da take tana faɗin
"Wai Innar Harira dole ne saina amsa miki sallama! , Kin wani cika wa mutane kunne da shaƙakƙiyar muryarki wacce ko daɗin sauraro babu"
Taɓe baki Hannatu ta yi don ita yanzu bata da lokacin cece-cuke, abin da zai amfaneta shi ta saka a gaba ba kishi ko mugunta ba. Koda Alhaji Zakari ya yi mata saki ɗaya akan Zaliha bata ji haushinsa ba don tasan giyar asiri ke jansa. Sannan bata yi kishi ba don tana sunan zaman aure ne amma ta canja komai na rayuwarta. Kullum cikin ibada da neman yafiyar Ubangijinta take, masamman haɗasa da wanin da ta yi a baya. Koda ta koma Giwa ta ƙara samun damar ibada da neman gafarar mahaliccinta. Takan tambayi ƙaninta Muntari akan abin da ya shige mata duhu na game da addininta. Sosai yake fayyace mata komai. Baka samun kowani video a wayarta sai wa'auzzukan malamai maza da mata wanda ta tura daga wayar ƙannenta. Daman a cikin familinsu ita ce ta fita zakka amma yanzu ta dawo kan hanya. Ɗan nisa wa ta yi tare da sakin ƙasaitaccen murmushi ta ce
"In banda abin ki Innar Balki lada goman ne baki so?"
Haushi Murja ta sake ji don bata yi zaton amsar da Hannatu za ta bata kenan, ta so a ce haushi ta ji amma kuma sai ta ga akasin haka. Girgiza kai Murja ta yi sannan ta ce
"Idan har sai na amsa miki sallama kafin zan samu lada goma ko ki riƙe kayanki. Ni ba shashasha bace ko mahaukaciya, Ina sane da haɗin kan ta kika yi da Zaytuna har da Fatsima, ke ga munafuka annamimiya ko, naga ai da tare muke komai da ke amma yanzu sai kika yi ɗan waken zagaye kika koma ɓarayin Zaytuna bayan kinsan bana ga maciji da ita. Wato kuna so ku ga ƙarshena ko! to ta Allah ta taku ba. Ni Murja !! "
Da ƙarfi da buga ƙirjinta sannan ta ci gaba da cewa
" Kainuwa ce dashen Allah, sannan muruccin kan dutse ce ni ban fito ba sai da na shirya, duk wanda ya ce zai ga bayana to ya shirya ganin kansa a makushewa,ni buhun barkono ne nafi ƙarfin danna"
Dariya maganganun Murja suka ba Hannatu, sai da ta ɗan dara sannan ta ce
"Kin ga Innar Balki shigowana kenan ko ɗakina ban shiga ba, kibari idan na kammala komai na ci abinci sai in fito ki ci gaba da bani labarin don babu ƙarya kin iya bada labari mai ƙayatarwa ga saka dariya. Ni kinga tafiyata zuwa anjima zan zo ci gaba da bani Labarin."
Tana ƙarasa maganar ta ci gaba da tafiya ba tare da ta jira cewar Murja ba. Murja ta ƙulu iya ƙuluwa kenan mahaukaciya ta maida ta, Zaytuna ma haka ta maida ta kamar mahaukaciya jiya. Lallai da Murja suke, kwanan nan zata fara gasa musu aya a hannu, ba dai Hannatu ta dawo ba, habawa za su san sun taɓo Murja. Ta daɗe a tsayan hannunta a ƙugunta tana kallon hanyar da Hannatu tabi, daga bisani ta ja tsaki sannan ta koma saman tabarmar tare da ci gaba da bakacenta, jikarta na wasa a gefanta bata san wainar da ake toyawa ba. Bata daɗe ba ta kwashi kayanta ta koma sashenta don zuciyarta na mata zafi, gwara ta watsa ruwa ko ta ji sanyi a jikinta.
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Ƙarfe 6:39om na yamma*
Hannatu bata fito daga sashenta ba sai bayan magrib, sai da ta gyara komai ta yi girki kasancewar har yanzu da sauran kayan abinci wanda bata yi amfani dasu ba, Alhaji Zakari bai ɗauka ba. Wanka ta yi sannan ta yi sallah, sai fito zuwa ɗakin Kakulle don ta gaisheta. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin ɗakin,Kakulle da ke aikin gyaran saiwarta wanda ta yanko a daji ta amsa mata cike da kulawa. Wuri ta samu ta zaune sannan ta shiga gaida Kakulle. Cike da fara'a ta amsa mata tana tambayar ya ta baro ƴan gidan, Hannatu bata lura da little Zakari da ke kwasar abincinsa hankali kwance, da yake ta ɗan juya masa baya kaɗan.
"Tanta yuwa" cewar little Zakari.
Sai a sannan ne ta juyo jin muryar yaro a bayanta. Ras! ƙirjinta ya bada ganin ɗan yana kama da mijinta sak! Kamar an tsaga kara. Cike da mamakin da ya kasa ɓoyuwa Hannatu ta tambayi Kakulle da cewa
"Innayi ina muka samu mai kama da Zakari?"
Murmushin takaici Kakulle ta yi sannan ta ce
"Lokacin da bakya nan aka kawo shi"
Kakulle bata ɓoye wa Hannatu komai ba akan abin da ya faru bayan bata nan, komai ta faɗa mata,har da abin da amaryar Alhaji Zakari ta ce akan baza ta riƙe shege ba. Sosai Hannatu ta shiga tsantsan mamaki, wato mugayan halayar mijinta ba a nan ya tsaya ba har da zina 'Innalillahi wa'inna ilaihi Rajiun' ta shiga maimaitawa a ranta don ta yi matuƙar gigita da jin wannan labarin, lallai Zakari ya yi nisa baya jin kira. Cikin ruɗu wanda bata san maganar ta suɓuce mata ba ta ce
"Ka kuwa shiga uku Zakari, abu goma da ashirin, wanne za ka fara, gaba kura baya damisa"
"Mai ya haɗun ma ɗan yaya haka Hannatu, meke faruwa dashi ne, ko ya nemo magana ne?"
Sai a sannan ne ta tuna shirman da ta so yi, Ashe gaban Kakulle take fa, cike da in-iiina Hannatu ta ce
"Nii ba abin da kike tunani nake nufi ba Innayi, ganin babban kuskure da ya aikata wanda har ya mutu ba za a daina jifansa da shi ba, Zina fa! Zina fa Inna! Bayan haka ga tsarabar shege ɗa da ya samu, ai abun ya ƙazanta Inna"
"Hakane Hannatu, raina ya yi matuƙar ɓaci gashi mahaifiyar yaron ta ce ba za ta sake waiwayo nan ba. Alamu dai sun nuna mu za mu riƙesa" cewar Kakulle fuskarta ɗauke da damuwa.
"Allah kasa mu dace, amma Zakari bai kyau wa kasan da makusantansa ba, ai wannan abun kunya ne babba wallahi" faɗin Hannatu tana gyara zama ta.
Matsar da kayan aikinta Kakulle ta yi tare da gyara zama tana duban Hannatu da kyau, don maganar da za ta yi mata mai matuƙar muhimmanci ce.
"Hannatu wani taimako nake so ki yi min kar ki duba Ɗan yaya, da a tozarcin da ya yi miki kwanakin baya, don Allah za ki yi ki samu lada"
Ɗan nisawa ta yi Hannatu bata katseta ba ta ci gaba da cewa
"mai sunan ɗan yaya nake so ki riƙe duk da babu daɗi amma naga kin fi da cewa da ki riƙesa, na yi tsufan da bazan iya riƙe ƙaramin yaro ba. Ba zan takura miki ba idan kinga bazaki iya riƙesa ba ban ga laifinki ba"
Tun lokacin da Kakulle ta fara magana annurin fuskar Hannatu ta ɗauke gabaɗaya.a ranta tana faɗin 'Wato ni aka raina shiyasa za a bani riƙon shege, naga ga amaryarsa wacce yafi so da ƙauna hasalima akan ya min saki ɗaya, ita ba a takura mata ba sai ni, to bazan riƙe ba' Katse mata tunanin Kakulle ta yi da cewa
"Hannatu nasan ranki ba zai yi daɗi ba"
"Innayi zan yi shawara a kai" cewar Hannatu tana sauke ajiyar zuciya.
"Allah yasa mu ji alkhairi"
"Ameen Inna" Tana faɗin haka ta miƙe ta bar ɗakin.
Da kallo Kakulle ta bita har ta bar ɗakin, ko Hannatu ta ce bazata riƙe little Zakari bata yi laifi ba, laifin Alhaji Zakari ne, shi da ya yi aika-aikar. Hannatu na fitowa daga ɗakin Kakulle ta shiga sashensu Fatsima da mammin Hujayrah suka gaisa daga bisani ta fito daga sashensu za ta buɗe ƙofar sashenta ta ji motsin buɗe ƙofa. Juyawan da za ta yi ta haɗa ido da Zaliha a hasken lantarki tana niyyar fitowa daga sashenta. Da sauri Zaliha ta fito daga sashenta tana wa Hannatu kallon uku saura kwata. Kallo ɗaya Hannatu ta yi mata za ta buɗe ƙofarta ta ji Zaliha na cewa
"Uwar gida ran gida an dawo kenan"
Bata kulata ba sai ma ƙoƙarin buɗe ƙofarta take don bata da lokacin waɗannan shirman. Maganar da Zaliha ta yi yanzu ya sakata tsayawa cak tare da juyowa jin tana cewa
"Da ba dan na umurci Zakari ya dawo da ke ba, da baki isa ki shigo gidan nan ba"
Murmushin takaici Hannatu ta yi don bata ga laifinta, babu masu laifi sai mijinta da Murja, bayan haka tana sane da asirin da ta yi wa Alhaji Zakari na mallaka, ita yanzu ta daina zuwa wurin boka ko malamin duba, da a ce a baya ne ƙarya take ta saka Alhaji Zakari ya saketa, idan ma bata yi wasa ba ita za ta bar gidan. Barin ƙofarta ta yi Hannatu tare da gyara tsayuwanta tana kallon Zaliha da kyau, sake sakin wani kasalallan murmushi ta yi sannan ta ce
"Yaro yaro ne, idan banda abinki Zaliha ke a a tunaninki ke kika umurci Zakari ya dawo dani kuma na dawo saboda shi, Hmmmmm! Idan ma ƙaramar ƙwaƙwalwarki haka take raya miki to ƙarya ne don ba domin Zakari na dawo gidan nan ba, saboda girma da darajar Innayi yasa na dawo, da kuma yarana"
Taɓe baki Zaliha ta yi sannan ta ce
"Ni kuwa na isa, don idan na gadama a yau ɗin nan zan ƙara umurtarsa ya sakeki"
Tintsirewa da dariya Hannatu ta yi sannan ta ce
"Allah sarkin daɗi wai inji ɓarawon dakanɗa, idan kinsa haƙuri ni Zakari baya gabana, na bar miki shi halak malak ki jiƙa Ki sha,saboda yarana na dawo gidan nan ba don Zakari ba. Magana ta ƙarshe ki bi duniya a sannu, asiri baya dawwama a jikin wanda aka yi wa shi, ki guji randa asirin da kika yi wa Zakari ya karye, a ranar za ki kwashi kashinki a hannu. Tun wuri gwara ki tuba ki koma wa Allah, Ni kin ga lafiyata".
Tana gama faɗar mata hakan ta buɗe ƙofarta ta shige ba tare da ta jira cewar Zaliha ba. Taɓe baki Zaliha ta yi a fili tana cewa
"Uhmmm ita ala dole ustaziya, to Allah ya karɓa, zuwa wurin boka yanzu na saka ƙafa, idan ta saka haƙuri na kusa barin mata gidan"
Juyawa ta yi ta koma saahen ba tare da ta je inda ta yi niyyar zuwa ba. Cikin dare Zakari ya dawo, kai tsaye ɗakin Zaliha ya nufa, bai samu tarba ba ya koma sashen Hannatu, bai ma san ta dawo ba, koda ya shigo har ta yi bacci. Wanka ya je ya yi sannan yabi lafiyar gado ya kwanta duk da ransa baya masa daɗi akan abin da Zaliha take masa musamman idan ya zo amsar hakƙinsa, sai faman juyi yake a gadon daga bisani bacci ya yi awon gaba da shi. Cikin dare Hannatu ta farka sallar dare, mutum ta gani a saman gadon yana sharar baccinsa hankali kwance, wani tuƙuƙin baƙin ciki ne ya taso mata, wani wawan tsaki ta ja sannan ta miƙe zuwa bayi ta ɗauro alwala. Daddumarta ta shimfiɗa tare da kabbarta sallah. Ta daɗe tana sallah daga bisani ta sallame tare da hayewa gadon ta yi kwanciyarta... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Gidan Alhaji Sambo Dala*
Zaune Akmal yake kusa da mahaifiyarsa suna hira, tun lokacin da Sabrin ta rasu basu keɓe su biyu sun zanta ba sai yau. Zaune Hajiya Mariya take a saman two seater, Shi kuma Akmal yana zaune a saman carpet, a gabansu fruitsalad ne suna sha. Sosai suke hira cikin nishaɗi da annashuwa, cikin hirar Hajiya Mariya ta dubi shalelan ɗan nata ta ce
"Ni kuwa Akmal yaushe za ka fiddo da matar aure ne? Na ƙagara naga jikokina"
Duƙar da kansa ya yi tare da sosa ƙeyarsa yana murmushi. Zuciyarsa babu wacce take hasko masa sai Hujayrah, idanunta masu ɗaukar hankali, shagwabanta mai nakar da zuciya haɗi da saka kasala, zazzaƙar muryata da shegen daɗi kamar ana busa sarewa.
"Akmal da kai fa nake"
Firgigit! Ya dawo daya kogin tunanin da ya lula, wani sabon murmushin ya saki sannan ya dubi mahaifiyarsa ya ce
"Mom ina da wacce nake so amma ban riga da na zanta da ita ba, mutuwar Sabrina ce ta tsayar da komai amma idan na daidaita ta yarinyar zan sanar miki"
Lokaci ɗaya fuskar Hajiya Mariya ta faɗaɗa da murmushi,har haƙoran makkanta guda biyu na gwal suna bayyana. Cike da farin ciki Hajiya Mariya ta ce
"Alhamdulillahi, wace mai sa a ce haka ta yi wuff da zuciyar yarona, a gaskiya ta yi babbar sa a a rayuwarta"
Wani murmushin mai ƙayatarwa Akmal ya saki sannan ya ce
"Don't worry Mom very soon za ki santa, Ni dai ki tayani da addu'a Allah yasa ta Soni because I'm madly in love with her"
Zaro ido Hajiya Mariya ta yi tana cewa
"Tooooo, daman baku daidaita ba Akmal, don't worry za ta soka har sonta ya fi naka, kai fa kyakkyawa ne, ga kuɗi ga boko, to wace mace ce a duniya za ta sameka har ta yi wasa da damarta, ai kawai ka saka a ranka mallakinka ce. Kaga idan kun daidaita sai kawai a haɗa bikinka dana Sakhiyya"
"Mom Sakhiyya ta samu Miji ne?" cewar Akmal.
"A'a, akwai dai yaro ƙawata wacce nake so mu haɗa zuri'ah da ita, suna da kuɗi sosai "
"Amma Sakhiyya tasan da auran? "
Gyara zama Hajiya Mariya ta yi tare da kai cokalin fruitsalad a bakinta sannan ta ce
"A'a bata san da auran ba, mahaifinku ba bai san da auran ba, muna jiran yaron ya dawo daga Scotland ne sai ya zo su daidai daga bisani na faɗawa Alhaji"
"Allah ya kaimu, zance gym room ɗina, Kwana biyu ban motsa jiki ba, duk jikina ciwo yake min"
Yana maganar yana miƙe zuwa sama inda ɗakinsa yake. Ita kuma Hajiya Mariya ta ci gaba da shan fruitsalad ɗinsa tana latsa waya... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*New G.R.A Bauchi State Nijeriya*
A ɓangaren Hajiya Ramla washe gari da safe bayan sun karya senata ya wuce office sai ta kira Tahseen zuwa ɗakin. Bayan ta shigo ta samu saman gado ta zauna sai Hajiya Ramla ta dubi ɗiyarta ta ce
"Tahseen mahaifiyar Arqam bata da lafiya"
"To ni ina ruwana da rashin lafiyarta, dama Arqam ne yake rashin lafiya shi ne zan damu"
Matsowa Hajiya Ramla ta yi kusa da Tahseen don taga alama yau ƴan faɗa ne a kai, ita kuma tana so taje ta dubota. Cike da rarrashi gami da ban baki Hajiya Ramla ta fara magana da cewa
"Dady's princess nasan babu ruwanki da rashin lafiyarta amma ai yaronta kike so and idan baki je kin gaisheta ba Arqam will be angry with you, zai ce baki son mom ɗinsa, amma idan Kika shirya zuwa gobe muka je gidan da ke kika gaisheta zai ji daɗi a ransa, ƙila ma ya koma sonki tunda kin nuna kulawarki aka mominsa, how did you see it my angel"
Murmushi Tahseen ta yi tare da cewa
"OK mom zan je na dubata and I will be friendly to her, Amma ni mom tsoron wanna yarinyar nake mai green eyes"
Tana maganar tana ɓata fuska, shiru Hajiya Ramla ta yi don ita ma tsoron Hujayrah take, ɗan tunani ta yi tana duban sama sai can ta ce
"Great! Nasan abin yi, Kin san me za ki yi Tahseen?"
Girgiza mata kai Tahseen ta yi tana faɗin
"Aa mom"
Gyara zama Hajiya Ramla ta yi sannan ta ce
"Idan mun je gidan kar ki kula yarinyar, koda tsokanarki ta yi kar ki kulata, kar ki nuna fushinki a gaban mutane kin ji My gurl, trust me Idan kin yi haka Arqam sai soki sosai, haka mom ɗinsa"
"OK mom I will, yaushe za mu tafi "
Ɗan tunani ta yi sai can ta ce
"Before na ce yau amma mu bari zuwa gobe around 11:00am sai mu je,amma zan bar ki gidan don ina so daga can na wuce gidan Yayana Ayyub"
"OK zani goben ƙila na yi kwana biyu ma"
Daga haka ta miƙe ta bar ɗakin zuwa ɗakinta. Bayan fitar Tahseen Hajiya Ramla ta kafa wani wawan tagumi tana tunani mafita, tsoronta ɗaya tsoron Hujayrah kar ta karya asirin don da alamu yarinyar ba ita kaɗai bace, tana tare da iskokai, Hajiya momma na samun lafiya za ta sa a yi kidnapping ɗinta kawai to Hutu, idan yaso daga baya sai su sake sabon asirin a yi auran. Daga haka ta miƙe zuwa banɗakinta don ta yi tsarki...✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Gida-dubu, Gubi Housing Estate, Bauchi State Nijeriya*
A ɓangaren Hajiyan Sama bayan ta dawo gidan, kai tsaye ta wuce kitchen ita da masu aiki, girki take shirya wa ƴan matanta na gani na faɗa domin Fauziyya ta kira ta ce suna hanya. Cikin ƙanƙanin Hajiyan Sama ta kammala girkin tare da taimako masu aiki har biyu. Dayawa ta yi girkin saboda ita take da kwana, ga kuma Khalil shima. Kai tsaye bedroom ɗinta ta koma, toilet ta shiga ta watsa ruwa sannan ta fito, wani sabon shiri ta yi kamar mai shiri fita unguwa, sai ta dawo falonta ta zauna.
A can gidan Prof. Hajiya Zinatu ta shiga ruɗu iya ruɗu ta rasa inda za ta saka ranta ta ji daɗi,sai safa da marwa take amma ta kasa samar wa kanta mafita. Tafi awa tana tunanin yadda za ta magance komai, idan ta ɗaura can sai can ya warware, sai saƙa da warwara take, data miƙe sai ta zauna can ƙwaƙwalwarta ta harsaso mata Hajiya Izzatu, ita kaɗai ce aminiyarta wacce ta yarda da ita, sannan suna bayyanawa junansu matsalolinsu tare da nemawa kansu mafita. Da wannan tunanin Hajiya Zinata ta ɗauko wayarta ta kira Hajiya Izzatu.
Lokacin data kira Hajiyan sama na riƙe da wayarta, bugu ɗaya ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta tana cewa
"Aminiya ƙwarai"
A can Hajiya Zinatu ta ce
"Aminiya na shiga uku na lalace, tawa ta sameni"
"Toooo! Meke faruwa ne aminiyar kar dai kiran da Prof ya yi ɗazu ya haddasa miki tashin hankali "
A can Hajiya Zinatu ta girgiza mata kai kamar tana kallon ta ce
"Idan dan wannan ne ai mai sauƙi ne Aminiya, cikin bala'i da tashin hankali nake dumu-dumu"
Dafe ƙirji Hajiyan Sama ta yi tana faɗin
"Subhanallahu antassalamu, me ya faru Aminiya"
A can Hajiya Zinatu ta ce
"Prof ya gane Rayyan na asibitin mahaukata, yanzu haka ya ce idan ya dawo zai ɗaukesa su wuce India a duba ƙwaƙwalwarsa a can"
Sauke ajiyar zuciya Hajiyan Sama ta yi sannan ta ce
"Ai wannan mai sauƙi ne Aminiya, Haba don Allah har kin tayar min da hankali"
A can Hajiya Zinatu ta ce
"Inaaaa! Aminiya ai idan wannan ne ba saina kira ki ba, tashin hankalin da nake cike ya ci uban wannan Aminiya, ciki fa Nadiya keda shi"
Da sauri Hajiyan Sama ta miƙe tare da dafa ƙirjinta da ƙarfi ta ce
"Cikiiii! Aminiya?"
Maganarta ta yi daidai da shigowansu Fauziyya da Zahriyya, da sauri suka ƙaraso inda take hankalinsu tashe ganin yadda ta dafe ƙirjinta kamar zai burma.
A can Hajiya Zinatu bayan ta share hawayenta sai ta ce
"Nadiya ciki ne da ita, bayan haka wannan ba shi ne cikin nata na farko ba, ta yi ciki har sau biyu tana zubarwa sai a na uku ne likitan ya ce idan ta zubar mahaifarta za ta samu matsala, amma haka Nadiya ta ce ta yarda. Yaron abokin Prof ne ya nasar wa mahaifinsa shi kuma ya sanar wa Prof, shi ne kiran da ɗazu ya yi min, Aminiya ban san yadda zan yi da rayuwata.... "
Bata ƙarashe abin da ta yi niyyar faɗa ba ta fashe da matsanancin kuka. Sosai Hajiyan Sama ta tausayi wa aminiyarta dole ta shiga tashin hankali, abin kunya fa kuma ga ɗiyar mace. Komawa ta yi ta zauna sannan ta ce
" Aminiya kibar kukan in shaa Allahu za mu samu mafita, kuka ba naki ba ne yanzu, neman mafita shi ne abin da ya dace mu yi. Ki bari zuwa gobe mu haɗu don maganar tafi ƙarfin waya. Mu san me ya dace mu yi amma gaskiya bazan ɓoye miki ba Kema kina da laifi a wani ɓangaran, kina tare da yarinya har ta yi ciki fin sau biyu amma kin kasa ganewa, Yaran yanzu ba ababan yarda ba ne Aminiya. Zuwa gobe sai mu haɗu ki kwantar da hankalinki za mu samu mafita kin ji"
Lallashi gami da ban baki Hajiyan Sama ta shiga ba wa Hajiya Zinatu har ta tsagaita da kukan da take yi daga bisani suka yi sallama.
Wata nauyayyar ajiyar zuciya Hajiyan Sama ta sauke, fuskar babu annuri, sosai ita ma hankalinta ya tashi.
"Mom mun dawo"
Sai a sannan Hajiyan Sama ta fahimci su Fauziyya sun dawo. Cikin sanyin murya Hajiyan Sama ta ce
"Sannunku da dawowa, ku je ku yi wanka, abincinku yana dining area"
"OK mom, lafiya naga fuskarki dauke da damuwa mom" cewar Fauziyya.
Sake sauke ajiyar zuciya Hajiyan sama ta yi sannan ta ce
"Ku je ku watsa ruwa Fauziyya zuwa anjima na sanar daku komai"
Daga haka bata sake basu ƙofar tambaya ba, miƙewa suka yi zuwa ɗakinsu. Bayan sun ci abinci sun huta sai Hajiyan Sama ta kira su Fauziyya falonta na sama. A saman carpet suka yada zango, zaune take a saman kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗara tana girgizawa, shiru ɗakin ya yi daga bisani Hajiyan Sama ta katse shirin da cewa
"Nasan ɗazu kunji abin da nake tattaunawa da Aminiya akan ciki. Ku yaran zamanin yanzu ba a yarda daku, ba kamar lokacin mu ba, kunada shegen son maza a ƙashin jikinku. Ga irinta nan Nadiya ta je ta yi cikin shege bayan haka ta zubar da ciki har biyu a baya"
Waro ido Fauziyya da Zahriyya suka yi, Fauziyya har da dafe ƙirji don maganar ta yi matuƙar girgizata, ya aka yi Nadiya ta yarda ta yi ciki har sau uku kamar ba wayayya ba, ga tablet tasha na hana haihuwa ko kuma a saka mata roba a hannu karta ɗauki ciki. Oohhh God! Hajiyan Sama ta katse mata tunani da cewa
"Kin yi shiru Fauziyya ko kisan da cikin ne?"
"Niiiiiij!!!! Fauziyya wallahi tallahi na rantse da Ubangijin sammai da ƙassai wanda ya yi kowa ya yi komai bansan komai akan cikin Nadiya ba. Mamaki ne kawai ya cikani shiyasa kika ji na yi shiru"
Gyara zama Hajiyan Sama ta yi sannan ta ce
"Duk ba wannan ba Fauziyya abin yasa na ce ku zo shi ne, maganar akan ki ne Fauziyya kin san kafin ku tafi na ce zan yi wa Alhaji maganar auranki da Arqam ko"
Gyaɗa mata kai Fauziyya ta yi sannan ta ce
"Bayan na samesa na sanar masa batun haɗi auranku, sai ya ce ya riga da ya yi wa mahaifiyar Tahseen alƙawarin aure. Kasancewar Tahseen na mutuwar son Arqam. To na yi iya abin ƙoƙarina akan ya amince da auran amma yaƙi, har abin ya bani haushi na haƙura na yi wa Hajiyan momma asirin ƙuraje, babu laifi asirin ya kamata amma kuma wannan sheɗaniyar yarinyar ta lalatamin aiki, yanzu haka muna neman yadda za mu kawar da ita ne"
Tun lokacin da Hajiyan Sama ta fara maganar Fauziyya ta duƙar da kanta tana hawaye, sosai take son Arqam son irin na ko a mutu, taya za ta ga samu taga rashi, bayan har iyayanta ta sanar musu da takusa aure amma yanzu a ce ba za ta aureshi ba.
"Kuka kike Fauziyya?"
Da sauri Fauziyya ta girgiza mata kai ba tare da ta ɗago ba still hawaye na zuba a idanunta. Cikin natsuwa Hajiyan sama ta ce
"Fauziyya nasan kina son Arqam sosai kuma nima ina goyan bayan haka amma Hajiya Ramla ta rigamu"
"Mom Arqam ba son Tahseen yake ba hasalima baya son magana da ita tun muna yara, yafi magana sani akan Tahseen. Lokacin muna yara cewa yake nafi Tahseen hankali" cewar Fauziyya tana Share hawayenta.
Murmushi Hajiyan Sama ta yi sannan ta ce
"Hmmmm Fauziyya kenan nasan bazaki iya rabuwa da Arqam ba, tunda ke mace ce kuma mu mata an san mu da kissa da kisisina, sai ki mai da hankalinki har ki janyo ra'ayina ya dawo kanki, duk da kwanakin baya na sanar miki da haka. Su maza da kike ganinsu suna son masu iya maganar da rangwaɗa, sai ki dage ki sace zuciyarsa, idan kika yi haka so abin da zai biyo baya mai sauƙi ne, daga gobe ki fara kai harinki har Allah ya baki nasara "
Sai yanzu Fauziyya ta ji sanyi a ranta, faɗaɗa murmushinta ta yi sannan ta ce
" In shaa Allah mom zuwa gobe-goban nan before son days za ki ga results "
Murmushi Hajiyan Sama ta sake yi sannan ta ce
" Da kuwa na ji daɗi Fauziyya"
"Mom ina Yaa Khalil ne naga tun ɗazu da muka dawo ban gansa ba" cewar Zahriyya wanda ce yanzu ta saak baki a maganarsu.
"Yana tare da Akmal a can gidansu ni na manta ban faɗa muku Sabrin ta rasu"
Salati suka shiga tare da yi mata addu'a daga bisani suka ɗan taɓa hira, sai kuma koma ɗakinsu... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A ɓangarensu Hujayrah tana zaune da su Nazima, Razina da Halima suna hira kasancewar sai zuwa gobe su Nazima za su koma gidansu. Suna tsaka da hira Mami ta shigo ɗakin da sallama, ido kowa ya zuba mata ba tare da sun ce komai ba can kuma suka ɓarke da dariya , Hujayrah ce ta yi ƙarfin halin amsa mata sallamar tana riƙe dariyarta, su Nazima dariya suke sosai ganin shigar da ta yi. Wani Sabon wanka Mami ta sake yi bayan ta farka daga gajeran baccin da ta yi, tare da sake sabon kwalliya irin na mutan da, ɗaurin ma irin na da ta yi, bakin nan ya sha baƙin kwalli raɗau. Sallamar Arqam suka ji a bayan Mami, suna dariya suka amsa masa, abin da suke wa dariya ya nema jin ba'asi Haba Yana arba da fuskar Mami ya kwashe da dariyar da bai shirya ba. Sosai Mami ta ƙulu iya ƙuluwa tana bin kowa da kallo. Hujayrah kaɗai ce bata yi dariya, miƙewa ta yi zuwa wurin Mami take tsaye tana cewa
"Mami duk baƙin ciki suke kinfita su kyau, shiyasa suke miki dariya karki gane, Ni baki ga ban yi miki dariya ba ai saboda bana baƙin ciki da kyawun da kika yi ne. Kin ga har Yaa Raqamqam dariya yake miki saboda yana jin haushin budurwarsa bata kaiki kyau ba, kalla yadda kwalliyar ta yi miki kyau kamar wata sarauniyar a cikin fadar sarki, Kin fi ɗawisi kyau, ɗawisun ma idan ta yi arba da ke dole ta sallama miki.kinga yadda ɗaurin ɗankwalin ya yi miki kyau Kakulleta. Hmmmm! Allah ki yarda Mami baƙin ciki suke miki"
Sosai Hujayrah ta koɗa Mami sai faman ɗadɗaga kai take ita ala dole ta yi kyau kamar yadda Hujayrah ta ce, nan da nan Mami ta washe guraguran haƙoranta wanda basu fi a ƙirga ba ta ce... ✍️
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***