MATAR SALMAN

Chapter 6

by @hauwa3030

*đź’«MATAR SALMAN đź’«*



➡ *PART ONE*
 *Page 6*

Washegarin ranar da muka dawo Abuja na tafi gidan Mamana. Nice ban dawo ba har ana gobe Monday sannan ta saka driver din gidansu l ya dawo dani har kofar gida. Na sami Ya salman a waje yana zaune shi kadai.

Nan da nan nan murtuke fuskana don tun randa muka dawo Abuja da ya min faÉ—a akan Salima nake jin haushinshi.

Da kyar ma na iya kallonsa hade da fadin ”Yaya ina wuni?” Kai kawai ya daga
min shima yana ji da miskilancinsa inaga, hmm nashiga cikin gida, daga Inna harsu Sadiya ba wanda yace min ci kanki, nima ban ce musu ba É—akinsu Sakina na wuce munata hirar school da ita.

Tun a wannan lokacin na daina kulasu Sadiya, in dai na gama aikina ciki zan koma inyi kwanciyata wayana nane abokin hira ta a yanzu, in dai kaga fara'ata to na tafi makaranta ne ko islamiyya. Har ya salman ya koma Lagos bana kulashi shima, dama ba wani kula juna muke ba, aikene dama kuma ya daina aiken nawa, sai dai Sakina ko Raihana.


A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, sai gashi har mun kusa mu fara WAEC da NECO, don haka Abba ya biya mana JAMB dukanmu mukayi kuma duk munyi sa'a Sadiya ce kawai ta fadi Fa'iza ma munyi waya tace ta haye, murna a wurin mu ba'a magana. Haka nan WAEC and NECO nida Sakina da Fa'iza munci amma Sadiya da Raihana duk sun fadi.

Bakin ciki gun Abba da Ya Salman ba'a magana Inna dai ko ajikinta zugasu ma take suyi aure wai su huta, don har ta sami Abba da maganar auren nasu ma. Yace shikenan tunda haka suka zaba ko wacce ta turo wanda zata aura ko cikin satin zai musu aure, kuma da abinda Allah ya hore masa zai kai kowacce gidan mijinta, bazai yi musu abinda yafi karfin shi ba, tunda sunki su tsaya suyi karatu shikenan.

Inna kam farinciki ma take sosai abinta. Da farko Ya Salman yaso ya roki Abba akan kar ya auradda su amma da ya tuna irin kwashe kwashen samarin da suke, bama Sadiya kam nata daban ne don har suka barta gaba kadan zata iya janyo musu abin kunya. Don haka ya shafawa kansa lafiya.
Nidai ina shan hutu gidan Mama, har ma na sami admission na BUK Sakina kuma ABU a tare da Fa'iza, can suka zabi mass communication, nikuma Accounting.

A haka aka saida maganar auren su Sadiya ma, yanzu sati biyu ya rage. Dole na tattara na dawo don mu fara shirye shiryen bikin don mune kawayen Raihana, Fa'iza ma tazo don haka a tare muke ta tsula tsiyarmu.

Mamana tazo sai dai a sashin Kawu Kasim dake cikin gidan ta sauka tare suke da Ammin su Ya Salim, na lura sam sam Mama basa shiri da Inna sai dai Maman Sakina.

'Yan uwan Inna na kamaroo duk sun zo sun cika gida, Inna sai fulatanci ake ta yi, kyawawan mutane kuwa wallahi, gasu farare sol abinsu sannan na lura ko wacce mace bakinta baki irin na Inna ko me suke shafawane oho.

Ranar walima a wani katon filinsu Ya salman da Salim muka shirya zamuyi kuma kusa da gida ne sosai aka zo aka mana decorating din wurin yayi kyau sosai. Kawaye munsha ankon material mai kyau.

Salima ma tazo anci adon nan kam harda na hauka, to wani uban make up da tayi ni sam bata burgeni ba, sai ji da kanta kuma take tana zuba yanga, ta fito da blackberry É—inta don shi ake yayi a wannan lokacin sai hotuna take ma amare.

Ni da Fa'iza kam duk mun cika da haushinta Fa'iza ma ta ciro nata Blackberry din tace ”Rumaisa zo muje muma muyi photo.”

Na tashi muna rikeda hannun juna har muka isa inda Salima take Fa'iza kam sai da tasan yadda ta yi ta bangajeta. Da sauri Salima ta juyo tace ”Malama ya haka, ba kya ganine kika tureni?”

Faiza ta juyo ta kalleta sama da kasa kuma a wulakance tace ”Oh! Ashe mutum na ture sorry.”

Wani irin kallo tayiwa Fa'iza ma sannan tace ”Nasan da gangan kika tureni........

Bansan sanda na sakar mata harara nace ”Ke DaAllah yiwa mutane shiru aje an tureki din sai me ko zaki rama?” Na kuma balla mata harara kamar idanuna zasu fadi, cikin tsiwa na ja wani dogon tsaki.....

Ta yi saurin fadin ”Ke ki kiyayeni banyi magana dake ba kija bakinki ki mana shiru don na lura sam bakida kunya.”

Na tako na isa gabanta na kalleta nace ”Ashe kin gane, gaskiane banda kunya kam ko kadan, kuma kika kuskura kika yi magana anan zaki ga yadda zan yi dake.”

Faiza ma ta harareta tace ”Fatan kinji ai?”

Shiru ta yi tana kallonmu fuska É—aure.

Nace ”kuma wannan da kike gani itace matar da Ya Salman zai aura don haka ki daina mafarkin kece matar Ya Salman daga yau don yafi karfinki fatan kin fahimceni?”

Naja hannun faiza muka yi gaba muka barta a tsaye sororo. Dariya muka koma gefe muka dinga yi harda rike ciki nace ”Fa'iza wallahi ta tsorata.”

Faiza ta sake kwashewa da dariya tace ” Yo ba dole ba? Ke koni ma na tsorata kinga yadda kika dinga buɗa mata wuta ashe haka kike da tsiwa, amma duk ki dinga barin su Sadiya suna miki iskanci, ke ko faɗa zakuyi ba abinda zasu dauka jikinki.”

Mukayi dariya nace ”Kyalesu, nida naci gabza, ai da zamanmu zai dade watarana sai dai gawansu, amma kinga yanxu kowacce tayi aure, suje can gidan mazajensu kowacce ta girɓe abinda ta shuka, ba shikenan ba?”

Tace ”Hmm hakane kam wallahi.”

Nace ” Ni yanzu kinsan me wallahi tsorona waccar banzan Salimar idan ta fadawa Ya Salman abinda mukayi mata ne zamu fuskanci hukunci sosai.”

Fa'iza ta zaro ido tace ”Billah ban ko tunashi ba.”

Nayi dariya na ce ”Koni wallahi ban tunashi ba sai da na gama zuba rashin mutunci, ke dai kawa Allah ya dubemu, in ba haka ba akwai matsala wlh.”

Washe garin daurin aure an kawo 'yan kidan kwarya a tsakar gidan, ana ta cashewa, kowa ya saka anko, dama mu namu na kawaye daban ne.

'Yan matan kamaroo sai rawa sukeyi suna juyi.
Koda muka shiga har mun ma fisu iyawa don haka kowa mu yake kallo.

Ammie da Mamana harda spray suka mana don É—aurewa karya gindi.

Muna cashewa bamu san Ya Salman ya shigo tsakar gidan ba Inna tayi kiranshi, suka koma gefe tana mishi magana, shikam shiru yayi yana sauraranta amma idonsa akan mu nida Fa'iza, don Sakina tuni ta zame ta gudu daki bayan sunyi ido huÉ—u, mukam ina muka sani, Nida Fa'iza har da compotition na juya mazaunai mukeyi muna dariya.


Da yamma tuni 'yan daukar amarya Raihana sunzo don ita a zoo road za a kaita Sadiya kuma dama a cikin unguwar tamu amma can gaba kadan gidan mijinta yake har ma da dangin sa kaf.

Don haka muka fita don ganawa da abokan ango sai janmu suke da hira sunga Ć´an mata mu kuma muka karkace aka yi ta yi har da dariya in ka ganmu zaka dauka mun shekara tare hmm

Nan ma sai ga Ya Salman ya dawo cikin motar Abie, mu bamu san shi bane sai hirar mu muke, Sakina tuni ta ganshi don ita komi tana yinsa da lura da taka tsan tsan, don haka ta sake zamewa ta yi cikin gida ta barmu.


Bayan an kai Amarya mu a can aka barmu sai washe gari aka sallami kawaye. A motar abokin ango muka dawo su biyu ne dayan yace yana sona daya kuma wai Sakina yakeso, Fa'iza kam dama da an tabota sai tace ai ita an mata miji (wai Ya Salman take nufi)

Mun dawo sai na tafi dakin inna na shiga na sameta da yan uwanta suna ta filatanci na gaishesu, Inna tace ”Rumaisa har kun dawo?”

Nace ”Eh Inna an sallame mu.”

Tace ”Ti ina kayan da nace ki amso min su zanin gado da bargo?

Nace ”Inna taki badawa, wai ki bar mata duka bedsheets dinta tana so.”

Tace ”Ai Raihana bata dama, duk zata hada ta bata gashi ba wanki take so ba, shiyasa nace ta rage a ajiye mata wasu anan.”

Nace ”Inna ai gidan Raihana ba irin gidan nan bane, mai wanki mijinta zai samo mata dama.”

Ta washe baki tace ”To dai Allah yasa.”

Nace ”Amin”

Tace" Kije ciki ki dauko flaks din Salman da kofinsa ki kai masa can dakinsa, nasan baya son shiga gidan cike da mutane ne.”

Ai sai da naji kirjina ya buga dam! a sanyaye na tashi na shiga na dauka na tafi dakinsa. Nayi sallama bakin kofar jin ba'a amsa ba yasa nace to ko yana waje don haka kai tsaye na shiga ina murna har da 'yan wake wake na.

Ina dagawa bayan na ajiye flaks kawai karaf ba sai muka hada ido ba. Bansan sanda nace ”Wayyo Allah na Yaya kayi hakuri na dauka ko baka nan ne.”

Na russuna nace ”Ina kwana?” Kallona kawai yake baice min ko kala ba.

A tsorace nace ”Dama Inna ce tace in kawo maka tea dinka.”

Na tashi zan fita ya danyi gyaran murya yace "dawo ki zauna.”

Zaro ido nayi a tsorace nace ”na'am?”

Wani uban tsawa da ya daka min har sai da hanjin cikina suka kaÉ—a. Da sauri na isa gabanshi na durkusa babu shiri.

Bai kuma ce min komi ba naga dai yana daddana waya can yasa a kunne naji yace ”Ammie pls Fa'iza tazo min da bottle water guda biyu ina dakina.”

Nikam na kara zaro ido jikina ya shiga rawa, aikuwa shikenan Salima ta haɗa mu da Yaya. Ba jimawa kuwa sai ga Fa'iza ta shigo da alamu har ta soma bacci ma. Ajiye ruwan tayi tace ”Yaya ina kwana?”

”Zauna.” Yace mata babu musu ta zauna tana zazzare ido ta kalleni, sunkuyar da kaina nayi nikam.”

Kallonmu kawai yake mun dauki kusan minti biyar a haka, sai kawai muka ga mutum ya janyo belt dinsa na sojoji, Jikinmu ne ya fara rawa nan take..,. Fa'iza zata fara magana ya cafko kunnenta daya ya murda da karfi ta saki ihun azaba. ”Wayyo Allah Yaya kayi hakuri bansan me nayi ba.”

Tsawa ya daka mata shut up before I bonce on you!”

Sannan yace ”Salima ta gaya min duk rashin kunyan da kuka yi mata da rashin mutunci keda wannan ƴar kauyen, don haka nake ja miki kunne akan Salima wallahi Salima ta kuma ce min ko kallon banza kika mata kinsan saura.”

Ya kara murde mata kunne da karfi ta saki ihu tace ”Bazan sake ba Yaya pls kayi hakuri kunnena zai cire.”


Yace ”Dama ina son ya cire ne ai, kuma bari kiji duk irin abubuwanda kika dinga yi a bikin nan duk a kan idanuna, kuma zan gayawa Abie idan auren kikeso kema ki fito da miji ai miki, kar ya ɓata kudinsa wurin sakaki jami'a.”

Kuka Fa'iza takeyi ya saki kunnen ta yace " Tashi ki bar nan nonesense.”

Ta mike da sauri ta fita tana hawaye. Sannan ya ka kalleni yace ”Ke kuma na dawo kanki.......

A tsorace na rike kunnuwana duka biyu naja baya, ina runtse idona kam!

Jin yayi shiru yasaka na buɗe idon a tsorace mukayi ido hudu na sunkuyar da kai jikina na rawa nace ”Yaya don Allah kayi hakuri wallahi na tuba wlh......

Katseni yayi da fadin ” ”Ke me na gaya miki a baya akan Salima?”

Nace ”Yaya wallahi Fa'iza ce tace mu........

Ya katseni da tsawa ”Shut up my friend an gaya miki bata fada min irin rashin kunyan da kika mata bane? To wallahi tun wuri ki kiyayeni kece baki sanni ba dama, kuma kar ki kuskura ki kaini bango don wallahi bazai miki dadi ba.”

Hawayene ya fara zubo min nace ”Kayi hakuri Yaya bazan sake ba.”


Yace ”Kima saken in kinga dama, na riga na gaya mata duk randa kika mata rashin kunya ta nemi bulala ta zaneki.”

A zuciyata nace ”Tabdijam! Ai ko bacci nake Salima bata isa ta tabani ba bare idona biyu.”


 Ya kuma ce min ”Kuma daga yau idan na kuskura na kara ganinki da wani kuna tsaye ko a bayan idona naji labari zan mugun saba miki. Naga sai wani rawar kai kike a gaban wasu Ć´an iska......to bari Kiji yadda Mamanki tace karatu za kiyi to karatun zakiyi kuma dolene ki cire tunanin aure a ranki ma don ba yanzu zakiyi ba, don haka ki maida hankali kamin ki kureni mu saka kafar wando guda.”

Kaina a sunkuye nace ”Kayi hakuri Yaya, Allah bazan kuma ba.....”

Ya katseni da faɗin ”Tashi ki bar nan!”

Ai tun kan ya karasa har na ɓace..


Biki ya kare an watse gida sai mu. Ni da Sakina tuni mun fara shirye shiryen tafiya makaranta don har ya Salman ya mana komi na registration da hostel.

Rannan ina kwance cikin dakin Inna, ya shigo a Palo ina jin yana cewa Inna.

”Inna ina rumaisa ne?”

Inna tace ”ina zaka ganta a waje kuwa tsabar bakin hali a daki take zama kamar mayya.”

Yace ”ai ki daina damun kanki Inna 'yar kauyece ba wani wayewa takedashi ba.”

Tabe baki ta yi tace ” To kai ɗin neman me kake mata?”

Yace ”Ba wani abu bane so nake su shirya itada Sakina suzo mu tafi suyi siyayya kayan bukatarsu na makaranta a kasuwa kinga a satin nan zasu tafi ai.”

Tace ”Yawwa zauna dama ina son magana da kai.”

Ya zauna yana kallonta
Tace ”Salman na lura sai faman kashe kudi kakeyi akan karatun wannan yarinyar anya lafiyan ka kuwa? yaushe ka fara aikin ma dududu harda zaka dinga kashe kudinka a banza?”

Yace ”Inna naga ya dace ne in tsaya mata ta yi karatu ta cikawa Mamanta burinta na son taga yarta ta yi karatu me zurfi kuma in kin lura Rumaisa tana da ilimi uwa uba kwazo da kokari kinga ai bai kamata ace an barta a banza ba.....

Ta katseshi da fadin ”Kaji min zancen banza, to uban me karatun nata zai amfanar maka kai kuma?.....Hmmm ina jiye maka tsoron wannan shishigi da kake wa wannan shegiyar yarinyan. Salman bari kaji in fada maka wallahi inde Rumaisa ce to bazata taba yin abin kirki ba, in kun kaita jami'ar ma lalacewa zatayi domin halin uwarta tayo kaf! dama zaku gane ku lallaba ku mata aure zai fiye muku sau dubu!

Ya danyi shiru sannan yace ”Inna in Allah ya yarda ba abinda zai faru da ita ki mata fatan alheri.”

Tace ”Ai shikenan, amma ka daina kashe kudinka akan ta domin bazan zuba maka ido ba gaskiya, in kudin ne da kai ka fara gininka ka min nan in mahaifin Salima ya amince kuyi aurenku. In ba haka ba kuma ka bawa Sadiya da Raihana jari su fara sana'a a gidajensu yafi maka alheri akan wnn asaran da kake yi, makarantar Rumaisa bazai amfanar mana komi ba naga Abbanku da Alhaji Kasim ma sai wani dagewa suke akanta suna ganin zatayi abun arziki hmm Allah dai ya kyauta, ai muna nan!”

Yace ”Amin inna ina son ki daina damun kanki don Allah, gini kam zamu fara in kudi yazo tunda ga fili mun siya ai, dama akwai kasuwancin da Abie yace zai daura mu akai mu gwada, kinga in anyi nasara shikenan, sannan batun Sadiya da Raihana ma Abie yace zai basu jari. kuma duk abinda kike ganin nake kashewa Rumaisa ba duka kudina bane Goggo Amina tana turo min kudi, don yanzu ma ita ta turo min dubu ɗari biyu tace ayima Sakina da Rumaisa siyayya....

Inna ta ɗan zaro ido tace ”dubu har dari biyu! Aminan? me takeyi haka?”

Kai tsaye yace ”Kasuwanci mana Inna, kinsan ta na da kokarin nema tun a kauyema bare yanzu ta na cikin gari kuma mijinta babban mutum ne kuma hamshaqin ɗan kasuwa.

Inna ta dan tabe baki sannan tace ”Hmmm!”



Tashi yayi ya wuce daki ya dage labulen tsayawa yayi cak yana kallona dama tunda naji ya shiga suna magana da Inna nayi lip abuna kamar ina bacci, sanye nake da dogon riga marar hannu irin roba dinnan yabi jikina sosai. Kamar kullum gashina ko parking babu haka na sake shi har ya É—an rufen fuska don ba gyarawa nakeyi ba Mama ne mai gyara min, nan kuma Sakina ce ko Zainab suke gyara min.

Dan ajiyar zuciya yayi ya fara neman tsarin Allah daga shaiÉ—an da yake kawata masa kyan surata.

Ya karasa dakin ganin bacci nake, Pillow da nake kwance ya ɗan bubbuga, da kyar na iya bude ido kamar mai bacci gaske. Na kalleshi da lumsassun idanuna fuskarsa ba fara'a yace ”ki tashi ki shirya ina jiranku keda Sakina a waje.”

Na tashi a hankali na zauna sannan na hau mika na iyayi sosai hade da salati na turo kirjina gaba, ina yamutsa fuska a dole na taso daga bacci

Kauda kai yayi da sauri don ya sake jin wani iri a jikinsa. Don haka yace min ”Kiyi sauri inada wurin zuwa da yawa karku ɓatan lokaci.”

Yana fadin haka ya saka kai ya fita, nima bayansa nabi, Inna na Palo bance mata komi ba na fita na É—ebi ruwa a bucket na shiga wanka a gurguje na shirya muka fita da Sakina muka samu yana jiranmu a motan Abba, baya na shiga Sakina a gaba. Mun Dade a kasuwa don ba abinda bamu tsiya ba na bukatar dan makarantan kwana. Mun kai kwana uku muna parking.

Sakina ta rigani tafiya don saida Ya Salman ya rakata, ya dawo daga Zarian kamin nan nima ya kaini na je na sallami Mama nasiha ta min sosai akai rayuwar jami'a.

Haka nan Abbansu Salman ma da Mmn Sakina, Inna kam cewa tayi ayi dai mu gani! Don ko kadan bata farin ciki da tafiyata makaranta.

Ya Salman ma yaja min kunne sosai a gameda kawayen banza da kuma samari. A ranar da ya kaini shima yana dawowa ya koma Lagos.

Wai sai ga Rumaisar ku a jami'a. Hmm masu karatu wani fata zaku min? Randa muka fara lectures na hadu da Salima itama ashe bangarenmu daya accounting itama takeyi.”

Ko kallo bamu ishi juna ba da ita.

A hostel dakinmu mu hudu ne da wata Maryam Ć´ar Gombe, sai Blessing Ć´ar Adamawa da Juliet Ć´ar Niger, dukansu babu Ć´ar Kano sai ni, kuma duk dinsu na lura idanunsu a bude yake, daga yanayin maganarsu zaku san shaidanu ne 'yan duniya, don haka ni na zama wawiya a tsakaninsu, kuma na lura Blessing kamar tana shaye shaye ma don har wani abu take dashi naji suna ce masa shisha, tace min baya bugarwa koni in ina so zan iya sha. Ni dei binsu nake da kallo kamar na sami film gashi basa son suturta jikinsu sai su tsaya su tube kayansu gabadaya haihuwar uwarsu amma ko a jikinsu haka suke fita har babban barandar hostel din

Ni kam fara shawaran canza daki na fara yi, don tsoron zama da gurbatattun mutane nakeyi gaskia..





 *❤️RUMAISA SALMAN BY MAMAN KAUTHAR❤️👍🏼*