Zaren Rayuwar Mu

BABI NA ARBA'IN DA UKU

by @zainabb

Zaren Rayuwar Mu 

LOKACIN SANYI ya shigo sosai har lokutan sallah sun yi ƙasa. Maghrib a Abuja ma ƙarfe 6.12 ake yi. Leaves masu faɗowa daga itace sun bushe sunyi kyau irin na lokacin sanyi. Dare ya zama yana da tsayi yanzu. Lokacin agogo kuma se ya jima be tafi ba. 

Ahmad ya fara amsar albashin shi daidai gwargwado. Allah yaso baya biyan kudin haya kuma ba a ciki yake cin abinci ba, gidan da yake zama har abinci ana bashi. Ita dai Farida ya saya mata takalmin da tace a cikin albashin shi na farko. A gida kuma duk aka mishi albashi yana turo reasonable amount yace su ƙara suyi abinda babu. Duk wata ya turo se mahaifan shi sun mishi godiya sosai. Mahaifin su har cewa yayi ya rage dubu talatin sun yi yawa yace a'a shi kam ba ze rage ba kuɗin da suke hannun shi isashshu ne baya buƙatar rage komai daga cikin nasu. 

Wata biyu yanzu be dawo gida ba wannan karon yace ze shirya yayi hutun sati a gida. A satin da za shi ya samu lokaci ya shiga boutique. 
Atamfa yake dubawa irin wacce zata fitting mahaifiyyar shi. Se ya ɗauko ya maida. Yayi haka aƙalla ya kai sau biyar. 
Wata yar matashiyar budurwa tana daga daura dashi tana lura da abinda yake. Ganin ya ɗauko na shida ya maida yasa ta tashi tsaye tazo wurin shi. 
Ahmad ji yayi an gaida shi da “Hello”
Juyowa yayi yasa fuskar shi a nata. “Hi” ya amsa tare da cire idanun shi akanta
   “Naga kana zaɓan atamfa kuma har yanzu baka samu wanda ya maka ba”
Nodding kai Ahamd yayi. 
  “Zan iya taya ka zaɓen? Looks like you're not good at choosing” 
Murmushi Ahmad yayi jin abinda tace. 
“Should I?” ta nema izini 
“Eh, nagode”
Fara duba mishi atamfa tayi. Ta ɗauko wata me kyau ta nuna mishi tace “Atamfar waye?”
     “Umma na” Ahmad yace 
Idanun ta suka yi haske tayi murmushi tace “Wannan ze mata kyau? Naga atamfar tana da kyau. Ka duba ka gani”
Kallon atamfar Ahmad yake se ta aza atamfar a jikinta tana nuna mishi zata yi. 
      “Zata yi kyau in Sha Allah. Nagode sosai”
Gyaɗa mishi kai tayi murmushi na kan fuskar ta. 
  “Ina da ƙanwa ko zaki zaɓa mata itama?”
Da sauri ta gyaɗa kanta ta fara dubawa Farida nata atamfar. Tana cikin dubawa ya matsa gefen shadda ya samowa Daddy me kyau. Koda ya dawo ta zaɓa wa Farida atamfa me kyau. Godiya yayi mata sosai yana jin sanyi a cikin ranshi. 
Gefen takalma Ahmad yaje ya ɗaukowa su Ummah takalma da Daddy da Farida. Buga mishi kuɗi akayi ya biya. Har ze tafi ya tsaya wurin yarinyar da ta mishi zaɓen kaya yace “Dan Allah sunan ki fa?”
Manyan idanun ta ta ɗago tace “Laila”
      “Laila” Ahmad ya maimaita 
“Kaifa?”
  “Sunana Ahmad”
“Nice to meet you, Ahmad” 
   “Same here, Laila”
Tsayawa Ahmad yayi yana kallon ta yana tunanin amsar number ta. 
“Can i have your number, please?” yayi ƙoƙarin faɗa. 
Da murmushi akan fuskar ta ta karanto mishi number ta. A nan wurin Ahmad yayi saving kuma ya kira ta. Itama saving number shi tayi tukuna suka yi sallama ya wuce. 

Ranar juma'a Ahmad ya ɗauki hanyar zuwa gida, Enugu. Farida ji tayi kamar ta canye shi akan murna. Tsalle kawai take tana rungumar shi. 
Abinci yaci yayi wanka tukuna ya fito musu da tsarabar da ya kawo musu. Farida ta gwada takalmin ta ya kai sau goma akan dad'i. Mahaifan shi se albarka suke sa mishi Maryam harda hawaye. Bata taɓa tunanin wannan abun ze risketa ba duk da ta yarda da ƴaƴan ta kuma ta yarda zasu samu. 
    “Umma kenan kar na sake kawowa ” Ahmad ya faɗi.
Murmushi tayi tace “Allah yayi muku albarka Ahmad. Amma Baffa ba ze samu ya taho ku ga juna ba?”
“Eh, gaskiya. Suna shirye-shiryen fara jarabawa kuma kinga jarabawar ƙarshe ce”
   “To ma sha Allah. Allah ya bashi sa'a yayi muku albarka”
     “Amin Amin Umma”

Washegari ranar Assabar yaso ya tafi University of Nigeria, Nsukka, wurin Baffa amma kuma ya fasa kar ya takura Baffa yana karatu. Fita yayi wurin shaƙatawa shi da Farida. Har zoo se da suka tafi. Zakin dake rufe a cikin gidan zoo Farida tace a buɗe mata tana so ta taɓa. 
   “Idan har dai buɗe miki za'a yi ki taɓa, ni zan tafiya na”
       “Yaya baka so ka gani ne?”
Wani kallo Ahmad yayi wa Farida ai kuwa ta fara dariya har duƙawa take. 
“Daga gani baki da lafiya. Idan muka koma gida se mun biya asibiti a barracks an duba ki”
     “Yaya, lafiya na lau. Daga cewa a buɗe mu ga. Ni nasan kaima fa you're curious about all these wild animals”
 “No, thank you. I'm not”
“Well, I'd love to touch and feel them”
    “You go feel your own death be that”
    “Yaya waya faɗa maka?”
   “My friend, shut up. Daga yau ba zamu kara zuwa gidan zoo ba naga baki da hankali har yanzu”
    “Hnm. Yaya dai”
Shiru Ahmad yayi be sake cewa komai ba. Wayar shi ce ta fara ringing ya ciro daga aljihun wando shi ya ɗauka. 
“Hello“ ta faɗi mishi da muryar ta me sanyi 
   “Hi Laila” Ahmad yace yana maintaining steeze nashi
  “Just called to know if they like their atamfa”
Murmushi Ahmad yayi yace “They like them. Very much. Thank you Laila”
Kallon shi Farida ke yi ta ɗaga girar ta. Kallon da ya mata ne yasa ta dena kallon shi tana kallon babbar giwar dake cikin gidan zoo. 
“You are welcome, Ahmad”
Daga haka suka yi shiru su biyu. Chan Ahmad yace “I'll talk to you later. Thank you”
“Okay, take care”
  “Take care too”
Wayar shi ya cire daga kunnen shi yana kallon number Laila. Murmushi yayi tukuna ya maida cikin aljihun wandon shi. 
   “Mu tafi gida, Farida. Maghrib na gabatowa”
Dawowa wurin shi Farida tayi suka fara tafiyar komawa gida. Suna cikin tafiya kafin su fito daga gidan zoo Ahmad ke tambayar Farida “Ke baki da saurayi?”
Rolling idanu Farida ta fara yi. “Saurayi Yaya? Me ya kawo wannan maganar?” tace, tana kuma so ta kara “Ko don kayi budurwa ne?” amma tayi shiru ba tace ba
   “Kina da ko baki da?”
Girgiza kai Farida tayi “A'a, bani dashi. Ba Yaya Baffa yace idan yaji ina da saurayi se ya tattaka ni ba? Bani dashi”
   “No any barrack boy has ever show interest in you?” Ahmad yace yana kallon ta
  “No” ta faɗi “Theres someone tho but he's a Christian so.... let's stop talking about this. I don't have any boyfriend yet”
   “Okay yet ne?” Ahmad yace 
Dariya Farida tayi “Of course Yaya. Ai ƙara girma zanyi kuma ku nan zaku ce na fitar da miji nayi aure”
   “To naji. Ya isa”
Shiru Farida tayi suna tafiyar su. Tana so ta ɗauko mishi zancen wacce taji yana waya da ita. 
“Yaya ka kusa aure ne?”
“Aure? Ina naga kuɗin aure?”
Rolling idanu Farida tayi “I heard you talking to a woman”
  “Okay duk macen da nake magana da ita auren ta zanyi?”
    “A'a, ban faɗa ba. Naga de kana yin murmushi bayan ka gama wayar”
  “So kike na shushshure ki nan ba?”
Shiru Farida tayi bata sake cewa wani abu ba har suka isa gida.