BABI NA ARBA'IN DA BIYAR
by @zainabb
Zaren Rayuwar Mu
CIKIN KITCHEN nake ina dafa abinci Zaid ya kusa dawowa daga wurin aiki. Yau ban ma fita aiki ba off nake se gobe. Yau ina so na mishi surprise with his favourite food. Bayan na gama na ɗaura komai a dining table, I made him my favourite mojito. Se yanzu nake yarda da koda baka so kayi abu, idan har dai kana ƙaunar mutum, ba girki ba komai zaka iya mishi wanda yake so wanda kuma ba ze cuta maka ba.
Bayan na gama komai ne nayi wanka. Fitted gown nasa na shafa janbaki a bakina na shafa kwalli saboda bana son naga idanuna da irin hasken da suke da. Ɗankwali na ban ɗaura ba na dunƙule sumar kaina ta baya nayi kalaba ɗaya a gaban kaina na hannun dama na sako shi. A gefen hagu ma haka nayi.
Bangon agogon ɗakina na kalla ƙarfe biyar har tayi ana ƙoƙarin zuwa ƙarfe shida. Shi Zaid idan ze yi late da dawowa daga wurin aiki ba ze kira ya sanar dani ba? Tashi nayi na leƙa window na ko zan ga shigowar shi amma babu alamar shi. Har na ɗauko waya zan kira shi se kuma na ajiye. Ina nan zaune ina danna waya ta har lokacin Maghrib yayi. Tashi nayi nayi Sallah. Bayan na gama Sallah na ƙara gyara fuska ta.
Fitowa nayi daga ciki daidai lokacin Zaid ya fito daga ɗakin shi yana gyara hannun rigar shi daga gani yayi alwala.
“A waje zaka yi Sallah?”
“Masallaci zan tafi” yace tare da kallona “A chan zanyi sallah”
“Okay se ka dawo. Idan ka gama fa ka dawo” na faɗi mishi
“Eh, zan dawo”
“Ba fa se anyi Isha ba fa. Da ka gama Maghrib ka dawo”
“Eh da nayi Maghrib zan dawo” ya faɗa tare da wucewa. Tsayawa nayi ina kallon shi har ya ɓace min daga gani.
A ɗakin shi na wuce na haɗa mishi ruwan wanka na fito na fidda mishi kayan da ze saka. Zaunawa nayi a gefen gado ina jiran Zaid. Saboda yanzu ana yin saurin Sallah Maghrib ne yasa ƙarfe shida da rabi da wasu yan mintuna akai ya dawo.
Banɗaki ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya muka fito zuwa dining table.
“Baka ce nayi kyau ba. Na ɗaya kenan” na faɗa muna zaunawa “Na biyu kuma na bar maka kaina a buɗe yau ban sa ɗankwali ba, nan ma baka ce komai ba. Ko ban maka kyau bane?”
Zaid be yi murmushi ba but he has this amusing look that I love on him yana kallo na.
“Nayi fushi da kai”
“Ki yi haƙuri”
“Ba zan yi ba” na faɗa tare da juya mishi baya
“Haba Dizan Zaid. Ki yi haƙuri mana”
“Ban maka kyau bane da ba zaka ce kinyi kyau ba har se na roƙa? Ba zan yi haƙuri ba”
Daga wurin shi ya tashi ya dawo wurina a gaba na ya tsugunna. “Ki yi haƙuri Diza na. Nasan kinyi kyau kuma a cikin raina na yaba”
“Ni ban san abinda yake cikin ranka ba so ba zan san ko ka yaba da gaske ba ko de banyi kyau bane”
“Kin yi kyau mana. Zan miki ƙarya ne?”
“Ka faɗa min abinda ya hana kace nayi kyau the first time da ka sa idanun ka a kaina. Se bayan da na gama aiki nayi wanka na shirya ina jiran ka dawo. Kuma ka dawo ka ganni all decked up baka ce nayi kyau ba. Kuma baka kira kace zaka dawo late ba tun ɗazu nake jiran ka”
Shiru Zaid yayi yana kallona har yanzu be cire amusing look da yake da ba a fuskar shi.
“Nayi fushi da kai kama sani”
“Nace kiyi haƙuri Hadiza na”
“Hadizan da baka iya cewa tayi kyau idan ta maka kwalliya”
“Me kike so? Duk me kike so zan miki idan zaki yi haƙuri”
“Babu abinda nake so. Ka de san nayi fushi da kai. Kuma ba yanzu zamu shirya ba amma ka tashi kaci abincin ka kafin kace ina barin ka da yunwa”
Tashi tsaye Zaid yayi ya riƙe hannuwana ban jenye ba yace “Haba Diza na. Dizan Zaid shi kaɗai, kiyi haƙuri ba zan sake ba. Yanzu idan kika yi fushi dani ina kike so hankalina ya tafi? Ki yi haƙuri nasan kinyi kyau ko ba kwalliya ke kyakkyawa ce”
"Zaka ƙara irin haka?” na faɗi ina kallon shi cikin idanu
Zaid kisses me and says “No, I won't. I won't. Ever”
“Na yafe maka amma zan baka punishment naka”
“Idan an yafe kuma me ya kawo maganar punishment, Diza na?”
“Zo kaci abinci tukuna”
“So nake a dena maganar”
“An dena, ranka ya dade”
Murmushi Zaid yayi ya zauna. Se bayan ya zauna ne naga gajiyar da yake ɗauke dashi. Duk haushin kaina naji da ban dube shi ba se duban abinda be min ba nayi. Ina cikin serving nashi ya ɗaura kanshi akan table.
“Hey, i cooked your favorite” I told him
Ɗago da kanshi yayi murmushin gajiya na ɗauke akan fuskar shi yace “Nagode Diza na. Allah yayi albarka. Nagode sosai”
Wani murmushi daban ne ya samu wuri akan fuska ta ina jin kaina kamar wanda ya ƙara girma. Zuciya ta tayi full ina ƙara jin ƙaunar Zaid a cikin raina.
“And i made you my favourite mojito”
Idanun shi suka yi sparkling na sa mishi mojito a cikin glass cup na aje a gaban shi. Ina kan zama yace “You can make mojito?”
“Yes and surprisingly, I made you my favourite one”
“What's your favourite?” yace tare da ɗaukar glass cup yana kallon mojito “It looks like virgin”
Nodding kaina nayi nace “Yes it is virgin mojito”
“When did you learn how to make it?” ya faɗa tare da sipping
“It tastes wonderful. I love it. Thank you Diza”
Murmushi ne akan fuska ta ya kasa barin fuska ta har cikin raina ina jin daɗi.
“You didn't tell me when you learned it”
“It was a long time ago. When I was in the university”
Gyaɗa kai Zaid yayi muka fara cin abinci.
“The food too....I love it. Thank you Diza” ya ƙara faɗa.
Bayan mun gama cin abinci ya taya ni muka kai kwanuka a kitchen. Ɗakin shi ya wuce yayi alwala ya fita zuwa sallah nima na wuce nayi nawa sallah.
Zaid be shigo gida ba se ƙarfe takwas da rabi. Jin shigowar shi se bayan ya tafi ɗakin shi na same shi a chan.
“Duk ka gaji ko?” nace tare da shafa fuskar shi
“Yes. I'm sleepy too”
“Yanzu bacci zaka yi?”
“Baki so nayi?”
“No, idan kana jin bacci kazo kayi mana. Bari na maka massage a kai. Zaka so?”
“I wouldn't mind”
“Ka jira ni bari na chanja kaya”
Zaid kallo ya bi ni dashi na wuce ɗaki na chanja kaya zuwa na bacci. Koda na dawo yana zaune a gefen gado yana jirana.
“Isnt it too early?”
“Early for?”
“Baccin da zanyi”
“No, idan ka gaji kayi. Ba wani Sallah yanzu se Fajr. Zo kayi bacci” Hannun shi na riƙe na fara kwantawa a gefe tukuna Zaid ya kwanta. Kanshi na ɗaura a gaban chest ɗina.
“Kayi bacci. Zan maka massage akai” na faɗi mishi.
Kanshi yasa yayi nudging nawa and I kiss his hair na fara mishi massage.
“I love you, Diza” ya faɗa min muryar shi ta fito irin na masu jin bacci sosai. So hoarse and tired
“Kayi bacci” nace mishi
“I love you”
“Idan ba zaka yi bacci ba zan cire kanka a chest ɗina”
“Kin isa?”
Murmushi nayi nace “Da gaske nake maka”
“I love you” ya ƙara faɗa.
Murmushi nayi wanda yake ji yace “You are in love, Diza”
“With Zaid, yes”
“Okay i love you”
“I love you too, Zaid”
“You are not supposed to say that”
“What should I say?”
“i love you with everything in me, Zaid”
Dariya nayi jin abinda Zaid ya faɗa.
“Stop laughing. Say it” ya faɗa tare da ƙara shigewa a jikina
“I won't say that”
“Zanyi fushi dake”
“Kayi mana”
“Ba zanyi ba. Ki faɗa naji”
“Kana so na buɗe maka zuciya ta?”
“Eh, ki buɗe”
“Na buɗe fa kace Zaid? I'm hurt. Mun yi faɗa da kai”
“Ban yi faɗa dake ba”
“Amma cewa kayi na buɗe zuciya ta”
“Eh, ina so naga soyayyar ki ne”
“Da gaske?”
“Eh” yace cikin gajiya sosai yana riƙe ni all to himself
“Baka yarda ba da gaske?”
Shiru Zaid yayi.
“Zaid?” nan ma shiru be amsa ba se na ɗauka yayi bacci ne saboda gajiyar shi. Hannu nasa a wurin hancin shi naji yana saukar da numfashi alamu na me bacci. Hannuna na ɗaura a sumar kanshi na dena massage ɗin nace “I love you, Zaid, to the moon and back. You're my home and you're my peace”
“Where did you learn those words from?”
Naji Zaid ya faɗa. Hannu nasa na kwaɗe kanshi ashe yaron nan idanun shi buɗe be yi bacci ba. Dariyar shi naji yasa hannuwan shi biyu ya riƙe kafaɗa ta.
“Zaid loves you too, Diza”