BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI
by @zainabb
Zaren Rayuwar Mu
FULLY FUNDED SCHOLARSHIP ɗin Baffa ya fito a United Kingdom a jami'ar Oxford domin karatun Master's ɗin shi a fannin Law. Ganin ya samu irin wannan damar a rayuwar shi yasa ya sunkuye kanshi tare da ɗaura hannun shi a goshin shi yana godiya ga Ubangijin shi. Zuciyar shi cike da farin ciki ya kira Umma ya faɗa mata.
“Ma sha Allah! Waya ga Baffa a ƙasar turawa? Ma sha Allah Baffa Allah ya bada Sa'a da nasara. Nayi farin ciki sosai Allah ya kare min ku”
Murmushi ne akan fuskar Baffa kamar yana ganin mahaifiyyar su ya amsa da Amin.
“Ka kira Daddy ka faɗa mishi”
“Zan faɗa mishi. Ahmad ma fa ya dace na fara kira amma ke na fara kira Umma. Bari na kira shi na faɗa mishi. Wannan duk yin shi ne”
Murmushi Umma tayi tace “To shikenan ka kira shi kuyi magana”
Waya suka kashe ya kira Ahmad. Ringing ɗaya biyu Ahmad ya ɗauka.
“Baffa” Ahmad ya kira shi “What's up?”
“All good o. Called to inform you that I got the scholarship”
Daga wurin da Ahmad yake zaune se da ya tashi akan murna “You don't mean it?!!!”
“Yes, Ahmad” ya faɗa yana murmushi. Katse kiran Ahmad yayi se ga ya kira video call. Baffa na dariya ya ɗauka kiran Ahmad.
“Yanzu se zuwa UK?”
“In Sha Allah Ahmad”
Alhamdulillah Baffa! Allah yasa albarka ya bada sa'a. Da yanzu ka tsaya baka cika ba ina zaka samu?! You have to take those steps bro”
“Yes, all thanks to you”
“Kaima kayi ƙoƙari. Idan ka tafi zaka dawo nan Nigeria?”
Shiru Baffa yayi yana nazari. Har yanzu be gama tunanin tsayawa chan ba ko dawowa ƙasar shi. “Se yanda Allah yayi. Amma idan na gama na samu aiki chan, why not stay?”
“Yes, hunt for a job and stay there. Don't come back oo. Abi you no see how Nigeria is going? You fit say there's hope? I doubt o. So stay for UK and work there. Don't come back to Nigeria. It'll be the same as you left it”
“Our country is in the hands of the wicked. No be lie. I go see if I can secure a job there after the Master's. You see, if I can't, I'll have to come back to my country no matter how rotten it is”
“Shut up man. Always call good for yourself. I know you'll secure the job. No worry”
“Okay Sha” Baffa yace yana kallon desktop dake gabanshi baya kallon fuskar Ahmad yace “You believe in me even if I don't believe in myself. I'll never forget this. And that's a lot of pressure oo. You're putting me to give out my best”
Dariya Ahmad yayi “Kai ne da saurin karaya ai. Ba'a yiwa rayuwa haka. Se idan kayi kaga baka samu ba. Idan ma baka samu ba ƙara trying kake ba de ka ƙyale ba”
“Yanzu na koya daga wurin ka. You keep on trying even if you fail”
“Yes, that's what humans do”
“Alright sha, thanks man. What's up with that your Laila girl? Are you guys still seeing each other? Umma said you should come have a family o”
Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke yace “Nima ina tunanin a tura gidansu. Se de halayen Laila wasu basu min ba. Saboda ya za'a yi kana son mace itama tana son ka amma idan kace ta dena wani abu da kake tunanin bayi da amfani gare ta se ta nuna ba zata dena ba? Bana so ace matsalar da muke samu yanzu su kasance irin su ne zamu fuskanta idan muka yi aure
“Laila?”
“Eh, ita fa”
“But she looks like a good girl”
“Of course, Laila is a good girl. Magana ce bata ji wani lokaci amma Laila na da kirki and I know she loves me”
“And you love her too”
“I do, Baffa”
“Kasan abinda zaka yi?” Baffa yace yana kallon Ahmad “Ka zauna kuyi magana tare da ita. Ka faɗa mata gaskiya akan so kake ka turo amma kana samun second thoughts akanta saboda wannan halin ta da baka so. Kowane reaction da maganar da ta baka, You take note of them anan zaka duba kaga idan kana son ka kasance tare da ita ko kuma akasin haka. You know women are fragile kuma ba zaka samu mace komai kace ta yarda dashi ba, ba zaka taɓa daidaitata ba. Kai ma daidai kake ne all the time? No, so sit down and have a talk with her. Ka duba kaga idan alkhairan ta yafi rashin alkhairan ta yawa. Don't lose a good woman because of one or two bad attitudes. We're all not perfect but we're trying”
Murmushi Ahmad yake tunda Baffa ya fara magana “Ashe Baffa haka ka girma kayi hankali? Wannan hankalin ya maka yawa. Aw, na manta, ƙanin nawa fa ya zama Lawyer yanzu haka yana shirye-shiryen Master's ne”
Dariya suka yi su biyu Baffa yace “Yes, a lawyer. Me sef no small”
“Kai ma auren ne zaka zo kayi nan bada jimawa ba. Ni fa bayan Temi ban taɓa jin ka kira sunan wata mace ba. Ko da ita za'a yi ko kuma dai se kaje chan zaka nemo mace?”
“Wherever God leads me, I'll go” Baffa yace “Temi was my university sweetheart and it ended there. No revisiting”
“Okay, no revisiting?”
“Yep”
“Okay that's nice”
“Okay so now what's next for you for going to the UK?”
“I'll secure my university admission and apply for a student visa. I think classes starts during a season they called autumn”
“Oh yeah, that's correct. I wish you good luck, Baffa and I'm proud of you”
“Thank you man. I owe you too. Without that link you sent me, I won't be here. Thank you”
“Thats why we're siblings and I'm the eldest” Ahmad yace
Murmushi Baffa yayi shima Ahmad yayi suka yiwa juna sallama.
Desktop ɗin Baffa yake kallo yana ganin inda rayuwa ke jefa shi. Yana da dreams nashi kuma a kodayaushe yana tunanin watarana zasu zama gaske idan ya jajirce a rayuwa. Kuma abubuwan da yake son cimma a rayuwa basu taɓa sa ya shiga tunani ba ya dai san ze tashi tsaye ga duk abinda yasa yake son cimma. Ya godewa mahaifan shi da suka yi tsaye akan karatun su koda su basu da irin wanda suka basu. Dama iyayenka kaɗai suke so kafi su a rayuwa kuma zasu ga inda suka kuskure baza so a sake maimaita wannan kuskuren a cikin ƴaƴansu ba. Shiyasa yake godiya ga Allah ga kuma iyayen shi; Daddy da Umma. Yasan ba zasu cimma waɗannan abubuwan da suka cimma ba tare dasu ba. A ran shi kuma ya kudirta ko kuma ze iya cewa ya zame mishi dole ya basu rayuwar da tafi wacce suke a cikinta kyau idan yafi haka.
Daddy yayi retire ga aikin soji har kuɗin shi sun fito saboda su sojoji kuɗin su basa jimawa suke fitowa idan suka yi retire ga aikin soji. Sun yanke shawarar zasu cigaba da zama a kudu saboda zaman Arewa ze musu wuya ganin mafi yawan rayuwar su sun yi ta ne a kudu. Wani ƙaramin gida Daddy ya samu ya siye anan Enugu cikin gari. Cikin kuɗin ya samu ya siya mota ƙarama me kyau wacce ze dinga hawa. A gaban gidansu kuma ya buɗe shago madaidaici na provision inda Daddy yasa wani ƙaramin yaron da ze dinga kula mishi da shagon. Last time da Baffa yaga Umma yaga tayi kama da wacce ke samun isasshen hutu yanzu tayi haske dama Umman su bata da duhu to ta ƙara haske abinta skin nata yayi kyau. Tana cikin wani irin farin ciki wanda yake so yana jin daɗin shi. Koda wannan aka bar shi a rayuwa, yasan ze iya cigaba da rayuwar shi sanin Umman su bata cikin damuwa yanzu.