Zaren Rayuwar Mu

BABI NA ARBA'IN DA TARA

by @zainabb

Zaren Rayuwar Mu  

ZAID BAYA NAN ya tafi Delta State wurin aikin shi. Ni kaɗai ce a cikin gida se gatekeeper. Gidan baya min daɗi kuma ga yadda nake yanzu akai akai nake jin jikina baya min daɗi. Ranar da ze tafi ma duk bana jin daɗin jikina amma ban nuna mishi ba bana son hankalin shi ya dawo kaina ni kaɗai. 

Rashin lafiyar nawa mostly morning sickness ne da safiya ta wuce shikenan bana jin rashin ƙarfi sosai a jikin. Amai ne nake yi akan mafi akasarin abincin da nake ci. Ga wata irin gajiya a jikina koda banyi wani abu ba. Ga cikina baya min daɗi bana son cin abinci kuma koda ban ci abincin ba so nake nayi amai. Duk juna biyun da na samu har biyu basu taɓa min irin haka ba a first trimester nawa se wannan. Har na fara gajiya da chanjin jikina. Duk na zama wata iri bana son kaya ko kaɗan saboda wani irin zafi nake ji. Idan ma nasa kaya bana son sa brassiere saboda takurar da nake ji ta min. Shiyasa yanzu bana sawa kuma dama bana sawa se idan aiki zan fita. Yanzu ko aikin zan tafi bana son sakawa. Sau ɗaya na tafi aiki babu brassiere Zaid yaga duk nayi wani ana ganin yadda jikina ya zama most especially bosoms nawa da suke full yanzu due to my pregnancy. He sat me down yace baya so dan Allah nayi haƙuri nake sawa saboda ana ganin jikina. Nan ne kawai ban ga ya min ba saboda ni kaɗai nasan yadda nake ji idan nasa ta. Haka de nayi haƙuri na bi maganar shi. Nasan with time, I'll be okay. 

Dawowa ta jiya daga wurin aiki ina kwance akan gado jikina bayi da ƙarfi. Morning sickness da nake ji sam yaƙi tafiya na kasa cin abinci ruwa kawai nake sha. Kwance nake idanuna na rufe ina jin yunwa amma abinci baya birgeni. Sallah kawai ke tada ni ko shi saboda ba yanda zanyi ne. Da na rufe idanuna bacci ze zo. Sama-sama nake jin ringing waya ta amma bani da halin ɗauka saboda baccin dake cikin idanuna ga wani irin haushi da takaici da nake ji. 

Ina kwance akan gado washegari ya riske ni. Nan ma kwance kawai nake, sumar kaina duk ta yamutse. Da na buɗe idanu da na rufe se bacci. Amai nake ji babu abinda naci a ina zan yi aman?!. Ina jin ringing na waya ta nasan dai Zaid ne kawai ze kira ni se Umma. Ban jawo wayar ba ina kallon ta from a little distance. Zaid ma haushi yake bani bana son naji muryar shi. 
Ina jin ringing a wayar har bacci ya ɗauke ni ban sake ji ba. Bayan na tashi daga baccin ma ringing din na fara ji. Ina nan kwance helpless na juyo da kaina ina kallon agogon bango har yamma tayi. Ina kallon agogon na rufe idanuna ahankali ina so na tashi daga kwancen da nake saboda har shi na gaji dashi. Kasa tashi nayi na ƙara komawa wani bacci. 

Bani na ƙara tashi ba se ƙarfe shida zuciya ta na min wani iri inaso naje asibiti saboda na gaji da wannan abubuwan da nake ji na gaji. Ringing waya ta ta fara yi nasa hannu na jawo. Ban duba wanda ya kira ba na ɗauka na ɗaura a kunnena cikin gajiya. Muryar Zaid naji ya fara magana “Hadiza, ina kika shiga? Lafiya kuwa? Tun jiya nake kira amma shiru baki ɗauka ba. Ko jikin ne?”
Ban san ina kukan da na fara yazo ba. Kawai de nasan na fara mishi kuka. 
    “Oh oh Hadiza! Yi haƙuri. Jikin ne baya miki daɗi. Yi haƙuri zan kira Yaya Hauwa tazo ta duba min ke. I'm sorry”
Kashe waya yayi. A gefen Zaid, Yaya Hauwa ya kira. Lokacin bata jima da dawowa daga aiki ba se ga kiran Zaid ta gani. Ɗauka tayi suka gaisa tana tambayar shi ya aikin shi a Delta yace Alhamdulillah. 
   “Yaya, Hadiza ce ba lafiya. Muna waya da ita ta fara kuka”
   “Kuka kuma? Matar nan taka she's a crybaby”
   “Tafi ganewa idan tana kuka”
Murmushi Yaya Hauwa tayi “Me yake damun ta?”
   “Bata yi min magana ba. Ina magana ta fara kuka nasan jikinta ne baya mata daɗi”
    “Okay bari na tashi naje na duba ta. Amma kaƙi faɗa min abinda yake damun ta ko?”
    “A'a Yaya” Zaid ya faɗa ya sake ce “Juna biyu ne fa yake wahalar da ita wannan first trimester”
  “Yawwa ka sani kenan”
Murmushi Zaid yayi yace “Idan kika je asibiti zaku tafi?”
Ɗaukar makullin motar ta tayi tana fitowa daga gida tace “Wani ciki da haka yake zuwa haƙuri zata yi har wannan lokaci ya tafi. Se dai idan akwai wani complication”
“Okay Yaya, mun gode, Allah ya saka miki da alkhairi”
   “So kake na shushshure ka ne?”
Murmushi Zaid ya ƙara yi yace “A'a, ki yi haƙuri”

Koda Hauwa ta isa gidan Zaid ta samu Hadiza kwance a gado bata yin komai ta zama wani pale idanun ta sunyi haske sosai a ciki. Bata ma son buɗe idanun ta. Wata ƙaramar riga ce a jikin ta se wandon da ya tsaya mata a laps. Akan gadon, akwai kayan ta na zuwa aiki da ta cire bata samu ɗauke wa ba. 
   “Hadiza” Yaya Hauwa ta faɗi tare da zama a gadon tana kallon Hadiza. 
Ƙoƙarin tashi Hadiza tayi se Hauwa tace tayi kwancin ta. 
   “Me kike ji haka ne?” Hauwa ta faɗi tare da taɓa wuyan Hadiza taji temperature ta. Jikin ta na da zafi kaɗan bada yawa ba. 
Shiru Hadiza tayi bata san inda zata fara ba. “I feel extremely tired. It's just....this is getting the best of me” Hadiza tace cikin frustration tare da ɗaura hannun ta a goshin ta ta cire kuma. 
Tsaye Hauwa tayi tana kallon ta for a few seconds kafin ta wuce banɗaki. Anan ta haɗa mata warm water domin tayi wanka. Fitowa tayi tace “Yanzu ki tashi kiyi wanka, zaki fi jin daɗin jikin ki”
Rufe idanu Hadiza tayi wankan ma gajiya ce a wurin ta. Haka dai tayi haƙuri ta tashi ta shiga banɗaki domin tayi wanka. Hauwa ta fara gyara mata ɗakin ta ta ɗauke kayan ta dake kan gado ta gyara zanen gado. 
Kitchen ta wuce ta ɗaura ruwan zafi ta haɗa mata tea ta zuba a flask. Ta kuma yi mata oats.
Koda ta dawo cikin ɗakin, Hadiza har ta fito ta shirya cikin abaya wadda yadin ta bayi da nauyi me tsaya mata daidai ankle ɗin ta. Kwanciya tazo yi a gado Hauwa ta hana. “Ki zauna a kujera ki ci abinci Hadiza”
Fuska Hadiza ta ɓata “Bana jin cin abinci”
  “Amma kina jin yunwa. Duba yanda kika zama. Zauna a kujera ki ci abinci. Idan kika gama se ki kwanta”
Bada son ran Hadiza ba ta zauna a kujera tayi relaxing jikinta a jikin kujerar. Idanun ta na rufe taji Yaya Hauwa na faɗin “Na haɗa miki oats. Ko dai nasa miki tea? Amma Oats ɗin se yafi, shi ze sa ba zaki ji yunwa da wuri ba” Yaya Hauwa tayi suggesting.
Gyaɗa kai Hadiza tayi. 
A cikin bowl Hauwa ta mika wa Hadiza oats harda strawberry tasa a sama. Amsa tayi ta aje bata da niyyar sha. 
  “You have to take this oats, Hadiza” Yaya Hauwa ta faɗa tana kallon Hadiza 
   “Bana jin cin abinci” Hadiza ta ƙara faɗa 
“To zaki sha Yoghurt ko hollandia?”
Girgiza kai Hadiza tayi. “To dole se kin ci oats ɗin nan. Ko zaki amaye nafi so ki sha. Kin ma ci abinci yau gabaɗaya?! Please ki ci oats kika sani ko jikin ki yayi ƙarfi”
Jin abinda Hauwa ke faɗa yasa Hadiza ta ɗauka bowl ta fara cin oats. Wani amai taji yazo mata ahankali ta aje ta tashi ta shiga bathroom. A chan sink ta fara amai Yaya Hauwa tabi bayan ta. Bayan ta gama tayi rinsing bakin ta suka fito. Cikin gajiya Hadiza ta zauna a kujera Hauwa tace “Ba zaki ƙara ci ba ko ze tsaya? Please try”
Hadiza bata ce komai ba ta ƙara ɗaukar bowl na oats ta fara ci. Har ta sha dayawa Allah yasa batayi wani amai ba. 

Yaya Hauwa na gidan Zaid ya ƙara kira dama jira yake koda akwai wani abu da zata yiwa Hadiza kar ya takura da kira. 
    “Barka da wuni Yaya”
        “Zaid”
“Ya jikin Hadiza?”
Yaya Hauwa na kallon Hadiza dake kwance a gado ba bacci take ba tace “Da sauƙi alhamdulillah. Ta ci oats and she didn't throw up”
Gyaɗa kai Zaid yayi kamar yana ganin ta. “Thank you Yaya”
    “Ban sani ba ko tana so tayi waya da kai”
   “A'a. Zamu yi magana anjima da ita”
     “Alright. Yaushe zaka dawo?”
     “A cikin satin nan in sha Allah”
     “Okay Allah ya dawo daku lafiya”
   “Amin Yaya, mun gode. Allah ya bada lada”

Sallama suka yiwa juna Hauwa na nan tare da Hadiza har ƙarfe tara na dare.
 
Bayan wucewar Yaya Hauwa, ina kwance akan gado hawaye suka fara fitowa a idanuna. Zuciyata ce ta cika da godiya da wani irin duba da nake yiwa Zaid da Yayar shi, most especially ma yanzu Yayar shi da ta taho inda nake cikin wannan hali nawa tasa nayi wanka, ta haɗa min abinda zan ci kuma tasa naci ta zauna tare dani. Hawayen haka kawai suke fitowa saboda yadda zuciyata ta kasa containing.... happiness ne zan faɗa ko kuma dai wani abu daban na adoration da admiration da nake ji game da Yaya Hauwa.