MENE RIBATA

1

by @pendingamarya223

Zaune ta ke a takure waje ɗaya ta na backing ƙofar shigowa cikin ɗakin, waƙar Tantiana manaois na tashi a hankali wanda a kowani lokaci ta kan ji  shi dan ta ƙara tuno da pain ɗin da ta ke ciki.

Waƙar ta ke bi da iya ƙarfinta wanda ke tattare da shashsheƙar kuka ta na kuka ta na ƙara buga kanta akan gwiwarta, she's just imagining few years back in her life. Tana danasanin ina ma ba ta ba shi second chance ya yi ruining life ɗinta ba.


Ya yi mata alƙawarin cewa zai aure ta bayan ya keta mata haddinta buh unfortunately ga pictures ɗinsa na yawo a social media last week aka yi bikinsa.

Dai-dai wurin da Tantiana ke faɗin _ See this could be us in a few years, but just tell me you like to play, it's like every day , am kicking rocks I could fly away buh you got me at a complete stop, how do you manage to keep me going buh somehow you keep me from going, see you distract me boy I'm distracted with out you...._.

Kuka ne ya ci ƙarfinta ta kasa ƙarasa wurin ta na sake janyo wayarta da screen ɗin sa ya farfashe ta na kallon pictures ɗin bikin nasa da aka yi posting a Facebook.




Dafatan da aka yi ne shi ya yi sanadiyar juyowanta  sannan ta yi saurin kashe screen ɗin wayar tare da kallon wadda ta dafata ɗin. "Maami"  shi ne abin da Tawalkaltu ta iya furtawa, muryarta ta yi tsananin dashewa a wannan lokacin she is totally confused. 
Tarasa yadda za ta faɗawa mahaifiyyarta she's no longer a virgin ta tabbatar mahaifiyyarta duk ƙaunar da ta ke mata za ta kaita ne ayi sercrifice da ita a wajen ATA, barimma in ta ji hausa guy ta ɗamƙawa budurcinta, ai tata ta sameta ne kawai.



"Tawa! Saboda Exam ɗin da kika faɗi shine kike wannan kukan? Allahn da ya ba ni kuɗin da na biya miki neco shi zai ba ni wani kuɗin na biya miki next year Ebó(kinji).”
Gyaɗa kai kawai ta yi sannan cikin sanyin muryarta ta ce " Maami gobe zamu fita kasuwar kwarin??". 

"Mai zai hana mu zuwa in har ba mutuwa na yi ba, ai nan ne kaɗai hanyar samun mu in rufawa kanmu asiri, kina gani dai mahaifinki daga gidan giyan sabon gari sai kwanciyya a ɗaki kamar kasa, ɗauki kuɗi na ajiye a saman sif, ki ɗauko ki siya min kayan miya, na ajiye shi acan ne dan nasan halinsa da karyamin jari." 

"Toh Maami na biya ta gidansu Nafisat mu je tare, ɗazu ma Farida ta ce za ta je Babban layi siyan kayan miyya, Maami dan Allah karki ce A'a.'' ta faɗa tare da mariraice fuska.

''Iyemi  (Mamana) kinsan dai ba alaƙarki na ke so da yaran gidan uncles ɗinki ba stay away from them, ke ma kin sani no need na tsaya gaya miki kin zama budurwa yanzu ba ko ina zan ɗin ga barinki ki na zuwa ba, ko yawon siyar da abinci da ki ke bina ba ason raina bane ba, ajiye hijab ɗin nan Lemme tell you something da baki sani ba my daughter.''


Hijab ɗin hannunta ta ajiye a sanyaye sannan ta zauna kusa da bencin da mahaifiyyarta ke zaune a ɗakin.

"Oma mi(ƴa ta) yau zan gaya miki abin da ba ki sani ba akan ƴaƴa maza, musamman na zamanin yanzu.” ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi sannan ta ce ''Ojonugwa''( sunanta ne na yare yana nufin Godiya ga Allah).

'' Dan muna zama a ƙasar Hausa wannan kar ya ba ki daman friending yaran hausawa anyhow, they can cheat, su kan yaudari yarinya ta fatar baki da sunan zasu aureta daga ƙarshe kuma suna mallakar abin da kika daɗe kina ajiyar shi, to ki sa mark daga ranar ba zai ƙara neman ki ba.”

“Budurcin ƴa mace madara ne, budurcin ƴa mace ƙimarta ce darajarta ce, shin kin san darajar da zan samu a ranar lahira idan kika kai mutumcin ki har ɗakin mijinki??   (Igala mothers for you 😂🌚),  Iyemi ki kula da kanki sosai  namiji kan iya yin komai domin ya mallaki jikin ki ba wai zuciyar ki ba. Sau da yawan maza yaudara ke kawo su wurin ƴaƴa mata Tawa kuma ba za ki yarda da hakan ba sai in har hakan ta faru da ke wanda ba na miki fatan hakan.''

Wani kalan kuka ne ya ƙwacewa Tawa ta shiga rairaiwa tare da jinginar da kanta akan gwiwar mahaifiyyarta, shin Mami tasan mai ta aikata ne ko kuma nasiha ce da ta saba yi mata, shin ta gaya mata ne ko kuma ta barwa kanta kaɗai sani tun da ciki ba zai fito ba.

Ina ma zata so mafarki ta ke yi da ta fi kowacce ƴa mace sa'a a rayuwar nan.


'' Saurin kukan ki ke haɗa ni da ke maza tashi ki je Babban layin kuma ki yi sauri ki dawo kinga yamma ta fara ko kayan miya ban ɗaura ba balle a fara kiciniyar gyaran ta."


Fitowa ta yi sanye da hijab ɗin ta har ƙasa hannunta riƙe da dubu biyar ɗin da zata yi wa Maami cefane.

Bayan layinsu ta zaga sannan ta shiga wani ɗan madaidaicin gidan da ke na farko a unguwar wanda ƙarar engine markaɗe ke ta shi cikin gidan.

Matar da ke tsaye ta na niƙan wake wanda alamu sun nuna waken na ƙosai ne na yamma, ta ɗago ta kalli Tawa da ke tsaye sanye da maroon ɗin hijab.


Murmusa ma ta matar ta yi wanda hakan yasa ita ma Tawar ta murmusa mata tare da faɗin Maa Óla né( Mama ina wuni) ''Áné há''( ya yamman) '' Lafiya lau wallahi Maama Faridat na ciki?."  da eh ta amsa mata sannan ta ci gaba da niƙan wakenta.

Flat shoes ɗinta ta cire sannan ta shiga ɗakin su Faridat, tana kwance a saman katifa ta na sauraran littafin Khairat na Fadnas, gaba ɗaya hankalinta na kan novel ɗin.
Duka ta ɗaka ma ta sannan ta ce ''kin fasa zuwa babban layin ne??..........