MENE RIBATA

2

by @pendingamarya223

Not edited 


Flat shoes ɗinta ta cire sannan ta shiga ɗakin su Faridat, tana kwance a saman katifa tana sauraran littafin Khairat na Fadnas, gaba ɗaya hankalinta na kan novel ɗin.
Duka ta ɗaka ma ta sannan ta ce ''kin fasa zuwa babban layin ne??.....''

" Harara Farida ta watsa mata sannan ta ɗauki hijab ɗinta baƙi har dai dai gwiwa ta sanya sannan suka yi hanyar fita daga gidan tare da yiwa Maa sallama sannan suka ƙarasa gidansu Nafisat da mamansu ke ta jera bread a stainless tray ƙato.''


A hanyarsu na tafiya hira kawai suke daga can nesa su ka hango wata ƴar matashiyyar budurwa da ta ci matsatsen kaya waƴanda su ka amshi jikinta.


''Saddiƙa!!.'' su ka ƙwala mata kira wanda hakan yayi sanadiyar juyowanta kanta ɗauke da ear plugs mai baby hannun ta riƙe da iphone 12promax, isowar saddiƙa kam musabaha su kai sannan su kai mata ya haƙurin rashin mahaifiyyarta suka yi mata taaziyya.

Faridat ta ce ''Ya akai nanganki da iphone 12promax ga wani shegen fresh da kikai daga dawowa daga ogun state are we all safe??.''  Nafisat kuma ta ce ''You sure say no be runs.'' daman sun saba kalar wannan wasan a tsakanin su tunda su gabaɗayan ƙawayen juna ne tun na yarinta sannan kuma cousins, amma yau saddiƙa abin ya ɓata ma ta rai ko dan yanzu ba ta da zuciya kalar na mutane? ( Nima pending amarya ban sani ba).


Still dai suka ƙyalƙyale da dariya gaba ɗayansu.


Banda Tawa da ta ƙafe Saddiƙa  da kallo wanda hakan ya sa Saddiƙa jin wani iri, because ita ba kamar su bace ba, bata da wani burin da ya wuce ta inganta rayuwar mahaifiyyarta da ma al'umma gaba ɗaya.



Murmushi ta sakarwa Saddiƙa wanda itama ta mayar mata sannan ta ke tambayar su ina zasu je da wannan yammacin ranar?, ataƙaice suka amsa da Babban layi.

''Okay.'' ta ce sannan ta ƙara da '' Lemme drop you guys off ''

'' Soo you don buy car abi?? '' Farida ta faɗa ta na ƙara kallon Saddiƙa, ''Ni bana son iskanci in za ki  hau ki hau kar ki mana yanga.'' Tawa na faɗan hakan ta ja hannun Saddiƙa suka wuce can gaban unguwar su suka shige mota.

Duk abin da suka siya Saddiƙa ce ta siya musu, da Tawa ta ga ba haza kawai ta hau siyayyan komai na abincinsu amaimakon kayan miyyan da Mami ta aiketa.


Ko da suka dawo gidan wake ta ɗaura ta yi shirye-shiryen su na zuwa kasuwar siyar da abincin na su which is Kwari market.


Da Asussuba ta ɗaura shinkafa kafin ƙarfe ba kwai har ta shirya ta ta shi Maami da ta koma bacci itama tayi wanka, tasaka kayanta Palazzo trousers with T_ shirts yayi mata kyau sai ƙaramin hijab baƙi, abinka da farar fata yayi mata kyau ɗass da ita.


Napep ta fita ta kira arround 10 O'clock sannan suka nufi hanyar kasuwa zuciyarta na dukan Uku Uku. 

Because tasan dole yau Ahmad zai zo kasuwa kuma ita ba ta son ta ganshi balle ya ƙara kallon ta da idon zina kamar yadda ya ce mata bazai taɓa auran mazinaciyya ba.

Hawaye ta ga yana neman taruwa a fuskarta wanda batai aune ba taji ya zubo saman ƙuncinta.
Tai sauri ta goge saboda gudun kar Maami ta gani.

Hira Maami tai ta mata a napep wanda duk rabin hankalinta ba ya nan sai dai tai ta murmushi da umm,umm umm.



Bayan sun ƙarasa suka sauke table ɗinsu na jera komai kafin 11 aka cika anata siyan abinci.
Bayan kasuwa ta ɗan lafa ƙaramar wayar nokiar Maami ta ɗau ringing. Cikin sauri ta ɗauka tare da kallon Tawa ta na faɗin ''Ahmad ba shi da contact ɗinki ne ya ke kirana.''

Yi ta yi kamar ba ta ji Maami ba ta cigaba da Attending customers ɗin da ke zuwa ɗaɗɗaya.

Bayan ta ɗaga sun gaisa ya ke cewa Maami ta bawa Tawa plate ɗaya ta kawo masa, bayan ta katse wayar ta je har wurin table ɗin ta zuba mai shinkafa da pourage beans da ya ji mai sannan ta saka mai ɓomo biyu a maimakon ɗaya ( Ganda) .


Cikin sanyinta ta amshi plate ɗin a hannun Maami sannan ta kalli fuskar ta ba tare da tace komai ba ta nufi hanyar da zai sadata da shagon shi.


Idonsa ya ƙafeta da shi sannan ya ke faɗa mata ''ba dariya ko dai kishi kike??.''

Fashewa ta yi da kuka sannan ta gayamai same message da ta gani bayan aurensa da ya turamata.

''Am not the one, wallahi Tawa bazan taɓa tura miki kalar wannan message ɗin ba and aurena is an incident that I can't escape it,  as I told you wallahi she's my cousin sister.''

''Daman ku arewa guys is always that one cousin da ta ke addabar rayuwarku, na yanke alaƙar da ke tsakanin mu, ban kuɗin abincina na wuce.''
'' Tawa.''' ''Ahmad.'' daman ni ƴar talla ce kuma na amince give me my money make I dey go abeg you dey waste my time.''

''Tawa I dey Sorry abeg, no punish me like that nahh.'' Malam ban kuɗi na ko zaka kai har gobe kaima kasan wacece Tawalkaltu.''
20k ya zaro a aljihun sa sannan ya miƙa mata 1 k ɗinta ta zara sannan ta ajiye mai sauran akan table ɗinsa ta ƙara gaba.
Almajirai har sun gama gyara komai nasu ta taro napep su ka shiga har sai da ya ajiyesu a Bachirawa.

In brief 🤔

Tawalkaltu Ibrahim Sa'idu ta kasance yarinya ƴar shekara 19 wadda ke zaune da iyayenta a garin kano, mahaifiyyarta ta kasance ƴar garin Kogi state mahaifinta shi ma ɗan jihar Kogi yankin dekina   a rayuwar ta tana burin ta ga ta gina rayuwa mai kyau domin hutu ga iyayenta musamman mahaifiyyarta. Tayi secondary da primary ɗinta a Annur college da ke bachirawa sannan ta zana waec da neco har sau biyu ba ta ciba a makarantar Khadijah memorial academy, ta haɗu da Ahmad a kasuwar kwari inda suke siyar da abinci, amma sai dai mahaifiyyarta ta ce ba za ta auri bahaushe ba wanda har hakan ya yi sanadiyar shaidan ya hura musu kunne sukai abinda ya zamo ba dai-dai ba a tsakanin su, Tawalkaltu nada ƙawaye uku rakk a duniya Saddiƙa,Faridat, Nafisat.

*******

Mahaifiyarta kamar yadda na faɗa ƴar garin kogi ce a yankin Ankpa, a unguwar angwa ogebe. Unguwar da asalin su tun kakanni sun ka kasance hausawan bebeji wanda sanadin zama cikin ƙabilar igaloli yasa hausar ta su ɓacewa sunan mahaifiyyarta Salamatu Muhammad shaliya ( Shari'a).
Wannan kenan wanda ya gane bazan kashe kaina ba.........''

Back to story 🌸🥀

 Sai da ya ajiye su a ƙofar gidansu sannan ta ciro one thousand ɗin Ahmad ta bawa mai napep ya bata canjin 500 , sannan har Maami ta shiga cikin gidan da ya ke kaca wanda ya bada alamun baban Tawalkaltu ne ya dawo.



Buhun gawayin da ya yi scatter a ƙasa Maami ta fara kwashewa, kafin Tawa ta iso a minti ƙalilan ta gama gyara komai tsaf sannan tayi wanka ta shirya cikin kaya marasa nauyi sannan ta ɗauki wayarta da number Ahmad ke ta nuna missed calls, tsaki ta ja ta re da kunna data buh unfortunately ba ta data, tsaki ta ƙara ja akaro na biyu sannan ta ɗaga kiran wayan Ahmad da ya ƙara shigowa........