Baban Mijina

Chapter 1

by @herrr

Masallacin Sultan Bello da ke cigin babban garin Kaduna, ya kama a cike da mutane daga wurare daban daban. Kowa na farin ciki da sanya alkhairi a zuwa daurin auren ikram da usman. ranar da aka dade ana jira ya qaraso. 

A cikin masallacin, yayyan ikram neh suke zauna da farin cikin aurar da yar autar su, kuma mace kadai a cikin su. Ta dayan bangaren kuma dangin usman neh a zaune, kowa na jiran karasowan ango da cikan lokacin da aka yarda a kai. 

"Your excellency kenan. Ai dole mu taya ka murna. Auran babban yaro ya taho."

"Aikuwa dai, maman ango na can gida ta kasa zama wuri daya." 

Mubarak Danjiddah, da aka fi sani da baba baba koh kuma his excellency ma wasu, yana zaune yana ansa gaisuwan mutane a cikin murmushi da natsuna. Usman ya kasance babban yaro a wurinsa, kuma duk da cewa ba shi ne mahaifinsa na jini ba, babu wani abu da ya rage tsakaninsu na uba da da.

A duk lokacin da aka ambaci Usman, Mubarak yakan yi murmushi. Ya sha fada cewa tarbiyyar yaro ba wai sai ka haife shi ba. Mutane da dama sun san irin gudunmawar da ya bayar wajen ganin Usman ya zama mutumin da yake a yau. Haqiqan mutane ma basu san cewa bashi neh ya haifi usman bah, sabida tun usman na shekarun da basu wuce goma bah, ya koma gidan Mubarak, a lokacin da mubarak ya aura babban yar usman. Duk wani ciyarwa, kayan sawa, karatu, tarbiyya, da jin dadi, babu wanda usman beh samu a wurin Mubarak bah. Sabida haka neh yasa ya tabbata uba a wurin usman. 

Babban yayan ikram, wato yaya ismail, shine ya qarasa wurin baba babba domin yi mishi magana. Tare su biyu suka fita wajen masallacin domin gaisawa da wasu dattijai. Sukayi gaisuwa a cikin natsuwa da kamala, kafin sauran mutane suka shiga ciki bayan yin addua ga sabon maauratan. 

Baba babba da yaya ismail neh suka juya shirin komawa cikin masallacin, amma abokin usman da ya taho aguje neh ya tsayar dasu. Ganin halin da yake ciki neh yasa suka fara tambayan koh dai lafiya. da sauri ya girgiza musu kai alamun a'a. "baba babba ka taimaka ka kira mana usman, we've been trying him not reachable, yanzu kuma he just texted wai ya fasa." 

zuciyoyin dasu girjinsu neh gabadaya ya fado zuwa kafafuwansu. wani dogon salati neh ya fito daga bakin yaya ismail. shi kuwa baba babba beyi wani jinkiri bah, da sauri ya dakko waya da danna ma usman kira. suna tsaye yayi ringing na farko, na biyu, har ya tsinke. ba aje wayen ba ya kara dialing dinsa dan ko wani hali ake ciki usman beh taba ganin kiran baba babba ba yaqi dauka. 

tabba kuwa wayan na qara shiga, usman ya dauka. a matsayin sallama, baba babba ya dauke shi da ashar. "you're very stupid. kaci kutumar burauban ka. wani irin wasan banza neh da rashin hankali kake qoqarin yi. banason wasan jahilci." 

muryar usman ce da saqi wata qaramar dariya kafin yayi magana. "babana. baba kayi haquri but ni na fasa, a bata haquri da samu wani." 

gashin giran baba babba neh suka hade saboda tsabar bacin rai da takaici, saboda daga jin muryan usman yasan cewa baa hayyacinsa yake bah. "kanada hankali kuwa? na gaya maka banasan wasan banza, kuma na baka minti goma ka same ni a cikin masallacin nan idan ba haka ba zan mugun saba maka."

"aa baba ni gaskiya banaso. I've tasted what i wanted and i realized she's not my type. tayi min girma kuma there are things she cant do for me. kaima namiji neh baba, ka gane i have needs as a man." 

Wayan da keh hannunsa neh ya fadi qasa, yana ambatun hasbunallahu waniimal wakeel, innalillahi wainnailaihi rajiun. Duk wata lissafi da kwanciyar hakali suka zauce daga gareshi, yana tunanin irin rashin mutuncin da usman ya shirya mishi, da ta yanda zaayi ya kamo kan matsalan. 

yaya ismail neh a cikin mutuwan jiki da surrender, ya juya a shirin komawa ya gaya ma yanuwansa da abunda keh faruwa, amma baba babba yayi saurin kamo hannunsa. "dan tsaya ismail kafin ka shiga, mu dan tsaya muyi lissafin ya zaayi."

"ya koh zamuyi your excellency, abu neh dai gashinan Allah ya rubuta ya faru, zamuyi addua da fatan Allah yasa shine mafi alkhairi." baba babba neh ya girgiza kanshi yana matuqar jin nauyi da ganin mutuncin ismail da yan uwanshi saboda sun tabbata mutane masu mutunci da hankali, saboda haka yana bawin cikin kunyar da ake shirin basu. 

"a'a ismail we'll find a way. ka bani mintina kadan kawai, yanzu zansa ya taho seh mu koma, kuma...." ismail neh ya tsayar dashi. "haba your excellency, yanzu koh da ace bamu zo nan bah naji abun da usman ya gaya, koh kuma koh da yana wurin na na shaida abunda ya gaya ai bazan mashi qanwata guda daya ita kadai a matsayin matarsa bah. ya nuna min yanada hankali a da, amma a yanzu ai bazan taba yarda ma aurannan bah. kaima kayi haquri ka gaya ma mutanenka seh ku wuce." 

"nasani, nasani wallahi, kuma kanada gaskiya, amma bazan so ku wuce hakanan bah, ai mutunci ya wuce nan..." baba babba ya dan dakata a maganan shi, yana lissafi daban daban da yanda zaayi ya bullo da wata hanya. beh tsaya yin lissafi bah ya fada abu na farko daya fado mishi rai. "ismail, abunda zeh faru yanzu, ka ansa min eh da izinin ni zan aura ikram."

Daga ismail har abokin usman dake tsaya a wurin neh suka tsaya cak saboda mamaki. A duk abubuwan da sukayi tsammani, basuyi zatan cewa abunda zeh fito daga bakin shi ba kenan. shi kanshi yana mamaki da yanda akayi ya fada abu haka. beh taba lissafin qara aure a rayuwanshi ba saboda ya zaman lafiya da matarsa ita kadai, amma saboda halin da qaninta ya sashi a ciki, beyi nadaman fadin abunda yace bah. he was ready to go with it. 

"a'a baba baza muyi haka bah. nasan kaji ciwon abunda ya faru kuma nasan ba laifin ka bane, amma ai baze yiwu bah. shekaru nawa ka ba ikram? kuma da tana a matsayin sirikar ka ya zaayi ka yarda da haka." 

girgiza mishi kai baba babba yayi. "wannan ba matsala bane, we'll figure it out daga baya, yanzu dai don Allah, don son mazon Allah ka yarda seh mu shiga ciki, lokaci nata tafiya." Ganin cewa baba babba na shirin tsugunna mishi, kuma da mutuncin shi da yake gani yasa ismail saurin riqo hannunshi. 

Ismail ya kasa sakin hannun Baba Babba din nan take. Ya kalli fuskarsa, yana kokarin fahimtar yadda komai ya kasance cikin dan kankanin lokaci. Har yanzu bai gama yarda da abin da kunnuwansa suka ji ba. A cikin 'yan mintuna kadan, an sauya wanda ake shirin aura wa Ikram, kuma ba wani daban ba sai mutumin da har yanzu yake kira da Baba Babba.

"Ismail, na fahimci abin da kake ji. Kuma idan ni ne kai, watakila tambayoyin da zan yi ma sun fi haka. Amma ka taimaka ka fahimce ni. A yau ne ake shirin aurar da yarinyar nan. An shirya komai, iyaye sun hallara, malamai sun zauna, mutane sun zo daga wurare daban-daban. Yanzu idan muka bar komai ya watse haka, wa zai tsaya ya kare mutuncinta? Ina rokon ka ne ka taimaka min mu bi wannan al'amari cikin mutunci. Mu shiga ciki, mu kammala abin da ya dace a kammala. Sauran kuma, Allah Ya sa mu dace."

Ismail ya yi dogon numfashi. A fili yake cewa har yanzu zuciyarsa ba ta gama karbar lamarin ba, amma kuma ya san Baba Babba ba mutumin da zai yi irin wannan magana saboda wasa ba ne. Ya saki hannunsa, sannan ya gyara hularsa. "Allah Ya sa haka neh mafi alheri. Amma Baba, ina rokonka, ka tuna cewa Ikram amanar Allah ce. Kada ka bari wannan al'amari ya zama wani abu da za ta yi nadama a kansa."

A cikin hanzari neh suka nufin hanyar shiga masallacin da sauri, ismail ya nufi wurin yanuwansa domin ya gaya masu sauyin da aka samu, shi kuwa baba babba ya nufi limamin domin ya gaya masa. 

A haka kuwa, limamin ya gyara zama tare da sauran malamai. Ya bude da addu'a, sannan ya nemi a gayyato waliyyi da wakili domin a fara daurin aure. Ismail ne ya fito gaba a matsayin wakilin waliyyin amarya, shi kuma Baba Babba ya zabi babban abokinsa domin ya wakilce shi. Bayan an tabbatar da dukkan bayanai, sai wakilin ango ya fara magana. "Ina neman auren Ikram Salihu, ga Alhaji Mubarak Danjidda, bisa Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam."

Wasu maganganu na mamaki suka fara yawo a cikin masallacin. Da dama daga cikin mutanen da ke wurin sun kasa boye mamakinsu. Ba karamin abin mamaki ba ne a gare su, ganin yadda auren da aka shirya yi wa Usman ya koma neman aure ga wanda ya kasance kamar mahaifinsa. Wasu sun kalli juna, wasu kuma suka sunkuyar da kansu suna rada. Amma Mubarak bai nuna alamun damuwa da abin da ake fada ba.
Sai Ismail ya mike, ya amsa,  "Na aurar da Ikram Salihu, 'yata, ga Alhaji Mubarak Danjidda, bisa Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam."

Daga nan limamin ya nemi a kawo sadaki. Wani abokin Usman ne ya kasance yana rike da sadakin tun da farko. Ya matso gaba da niyyar mika kudin ga wakilin waliyyi, amma kafin ya karasa, Baba Babba ya daga hannu. "Ka riqe kudin. Zanyi transfee." Mutumin ya tsaya, ya kalli Mubarak, sannan ya koma da kudin.
Nan take aka nemi account number din da za a tura sadakin. Da aka mika masa, Mubarak ya dauko wayarsa. Bai yi wani dogon nazari ko tambayar wani abu ba. Ya shiga bank application dinsa, ya saka adadin kudin sannan ya tabbatar da transfer din miliyan biyu. 

A cikin qanqanin lokaci aka qarasa abunda ya kamata, aka shafa fatiha, kuma aka nada taro da Ikram a matsyin amaryar Alhaji Mubarak, mutumin da ya kamata ya zamo baban mijinta