3
by @zainabamzah
✨𝐍𝐨𝐮𝐫 𝐀𝐲𝐧✨
𝐁𝐲 𝐙𝐚𝐢𝐧𝐚𝐛 𝐀𝐦𝐳𝐚𝐡
***
***
*PAGE 3*
Sai da ya biya ta pharmacy, ya sayi magani da drip ɗin da zai saka wa Mimi a gida, sannan suka bar Asibitin. Suna isa gida, kai tsaye part ɗin Ammi suka wuce gabaɗaya, ya saka mata drip ɗin a ɗakinsu, bayan ya gama komai ya duba lokaci a wayarsa. Ya san dare ya yi, amma bai san lokacin ya tafi haka ba sai yanzu da ya duba wayarsa, part ɗinsu ya wuce shi ma, duk da cewa a gajiye yake, amma sai da ya yi wanka ya canza kayan jikinsa zuwa na barci, ya shafa turarukansa masu ƙamshi da tsada, sannan ya haye gadonsa, nan take Bacci ya yi gaba da shi. Ba shi ya farka daga Bacci ba sai wajen ƙarfe 10:30 na dare, Ƙarar wayarsa ce ta tashe shi daga barcin da bai gama yin isasshe ba. A hankali ya lalubo wayar dake gefen gadonsa, ya duba screen ɗin. Fahad ne ke kira, sai a lokacin ya tuna da missed calls ɗinsa da ya gani dazun a hospital, ya tilasta wa kansa ɗaga kiran duk da nauyin baccin dake idanunsa. “Hey, what’s up, bruh?” Ya faɗa cikin muryar barci. Daga ɗayan ɓangaren, Fahad ya ce, “Likita, bakan Turai! Ina ka shiga haka Ina ta kira, ba kai picking ba?”
Faruk ya ɗan gyara kwanciyarsa, sannan ya amsa,
“Sorry, bruh, yau na daɗe a Hospital, tun safe muna theatre sai after Maghrib muka gama. Kuma da na fito, na ga missed calls ɗin Ammi sun kawo wannan…” Ya ɗan yi shiru, zuwa can ya ƙara da cewa, “Brat ɗin nan wai ba ta da lafiya.” Fahad ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce, “Oh! Wai, ne ma ashe? Wannan sunan har yanzu ba zai fita a bakinka ba? Allah ya shirya mana kai, big bruh. Dama dalilin kiran ka a lokacin shi ne Nadiya ta kira ni da zun, ta ce min suna hospital an yi admitting Mimi. Ta ce sun kira ka, ba su same ka ba, kuma da suka zo hospital ba su gan ka ba, shi ya sa na kira ka. Ashe ka yi busy da patients, kuna can kuna heɗe mutane. Amma ta ce min kun dawo gida tare gabaɗaya.” Duk Fahad ne ke wannan maganar.
Murmushi Faruk ya yi. A ransa ya ce, ‘Wai heɗe mutane kamar wasu ba mutane ba!’ Sanin cewa ba zai ce komai ba, Fahad ya ci gaba da maganarsa cikin rashin damuwa.
“Ina son in yi magana da Mimi ma, but it seems like ba ta iya magana..” Sai a lokacin Faruk ya taɓe baki ya ce, “Dama yaushe za ta iya yin magana? A very lazy girl who cannot endure period pain.” Fahad ya yi murmushi saboda ya saba da halin Faruk, musamman a kan alaƙarsa da Mimi, komai zai iya faɗi a kanta. Bai kaunar alaƙar ko kaɗan, kawai dai ba shi da yadda zai yi ne, ba tare da damuwa ba, Fahad ya ce,
“Nadiya ta ce ko abinci ba ta iya ci, shi ya sa na sake kiran ka. Please, bruh, ka yi ƙoƙari ka sa ta ci abinci, ka lallaɓa ta don Allah. Na san duk gidan nan kai kaɗai ne za ka iya saka ta ta ci abinci cikin daɗin rai. Idan ka yi hakan, zan ji daɗi. She’s also your sister, ba wani abu ba ne idan ka yi hakan, ka sani, ko da can Mimi ba ta son cin abinci, bare yanzu da ba ta da lafiya.”
Faruk ya yi murmushi, domin ya san halin Mimi sosai. Ya san yadda take wahalar da mutane idan ana son ta ci abinci, Musamman yanzu da ba ta lafiya, shiru ya yi, After a few seconds, ya ce “I will try.”
Cikin farin ciki Fahad ya ce,
“That’s my bruh! To, yanzu mene ne mafita? Me za mu yi game da wannan ciwon? I’m worried, wallahi.”
Faruk ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba. Shi yana mamakin yadda Fahad ba ya gajiya da yin magana mai tsawo a kan ƙaramar yarinya, yarinyar da kila ma ya kusa haihuwarta. Jin ya yi shiru, Fahad ya ce, “I’m talking to you, bruh.”
“Me kake so in ce?” Faruk ya faɗa cikin sanyin murya.
“As in? Ban gane me nake so ka ce ba?” Fahad ya faɗa cikin ɓacin rai. “A matsayinka na babban likitan mata, ina tambayar ka mafita a kan yadda za a magance matsalar nan, shi ne za ka ce me nake so ka faɗa? Field ɗin ka ne, bruh. Idan ban tambaye ka ba, wa kake so in tambaya?” Faruk ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba, sai wani ƙaramin tsaki da ya yi wanda har Fahad ɗin ya ji, duk da cewa ba da ƙarfi ya yi ba.
“Hold on, Faruk! What’s your problem with Mimi, please? Me ta yi maka? Me yarinyar nan ta tsare maka?” Fahad ya faɗa cikin jin haushi. Faruk ya yi shiru kamar ba zai ce komai ba.Bayan wasu daƙiƙu kaɗan ya ce “Ohon maka! Haka za ka ce?” Fahad ya faɗa sounding so pissed off. Cikin natsuwa Faruk ya ce, “Me zan ce maka bayan wannan, Fahad? Bayan ka zubar mana da mutunci a gaban yara. A ce duk ’yan matan dake garin Abuja, ka rasa wacce za ka ce kana so sai wannan brat ɗin? Imagine, mate ɗin Nadiya! Yarinyar da ta tashi a gabanmu, kawai ka zubar mana da mutunci a wurin yara.” Ya ƙarasa maganar cikin yanayin ɓacin rai. Duk da cewa Fahad ya san Faruk bai taɓa son wannan alaƙa ba, amma bai yi tunanin har yanzu yana ɗauke da irin wannan ɓacin ran ba. Tun da Faruk yaji Fahad ya yi shiru bai sake cewa komai ba ya san yaji haushi ne, don haka shima ya sake yin shiru. Sun daɗe a haka babu wanda ya sake cewa komai, zuwa can Faruk da ya gaji ya yi breaking silence din ya ce, “Solution kuma na riga na faɗa maka. Apart from pain reliever, aure ko haihuwa shine zasu iya taimakawa wajen magance matsalar ta.” Duk da ran fahad a b’a ce yake, amma ya daure ya ce “Me ya sa sai aure ko haihuwa ne mafita?”
“Because in some women, menstrual cramps may change after childbirth. But it’s not a guaranteed cure. Akwai matan da suke samun sauƙi bayan sun haihu, yayin da wasu kuma ciwon yake ci gaba da damunsu. It depends on the individual and the underlying cause.” Ya ɗan dakata sannan ya ƙara da cewa, “Research has shown that menstrual pain can change with age and after childbirth in some women, but that doesn’t mean pregnancy or childbirth is a treatment for period cramps. Idan ciwon ya yi tsanani haka, dole a duba ko akwai wani underlying condition dake haddasa shi, wanda duk a riga anyi mata.”
Ajiyar zuciya Fahad ya sauke cikin damuwa sannan ya ce, “To yanzu menene shawara? Me kake ganin ya kamata mu yi? Shiru Faruk ya yi bai ce komai ba, domin har ya gaji da surutun da Fahad ya saka shi yi. Cike da gajiya ya ce masa “That’s all I can say for now.” Kafin Fahad ya ce komai, Faruk ya katse kiran. Ya ajiye wayar a gefensa, sannan ya sauke numfashi.
After a while ya duba lokaci sai ya ga drip ɗin yana gab da ƙarewa. Nan take ya tashi ya nufi part ɗin Ammi. A lokacin tana zaune a ɗakinta tana waya da Daddy, sai da ya jira ta gama wayar sannan ya gaishe ta. Bayan sun gaisa ta ce, “Faruk ba ka zo ka yi dinner ba.”
“Ammi barci nayi, kuma na gaji sosai shiyasa.” Cike da kulawa ta ce “To a kawo maka yanzu?”Da kaina na na dafa bayan mundawo?” Ta faɗa masa hakan ne saboda ta san halinsa. Ta san ba lallai ya ci abincin ba tun da ba ya cin abincin da masu aiki suka dafa, musamman da yake ya san ba su gida gabaɗaya, shi yasa ta ce ita ta yi. Girgiza kai ya yi ya sannan ya ce “Zan sha tea later, ya jikin ta?” “Da sauƙi. Amai ya tsaya gabaɗaya, but still jikinta babu wani ƙarfi, tun da ta ƙi cin abinci har yanzu. Ka san ba ta son cin abinci ko da can, bare yanzu da ba ta da lafiya kuma, ko magani sai an yi fama da ita kafin ta sha. Na yi na yi wallahi, ta ƙi cin komai sai tea kawai. Amma duk da haka Alhamdulillah, ta ɗan samu sauƙi ba kamar ɗa zun ba.” Miƙewa ya yi, sannan ya ɗan dubi Ammi ya ce, “Let me go check on her.” Ammi ta gyada kai. “To, ka duba ta. Amma don Allah ka yi ƙoƙari ka sa ta ci wani abu. Ni dai na gaji da lallaɓarta.” Faruk ya yi murmushi.
“Don’t worry, Ammi. I’ll handle her.” Ya faɗa sannan ya juya ya fita…
*SANARWA 📢*
*Ina mai farin cikin sanar daku muna siyar da Kaya Kala Kala masu kyau da quality direct from Egypt Abaya, jalbabs, boubou, scarfs, jersey hijabs, jersey veils, comfy gowns,tie back caps,crinkle turban caps,nightwear’s,and lots more. Muna yin adashe na kome kake so ga wanda bashida halin siya lokaci daya..Masu son fara business su ma muna maraba dasu.* For more info +201508856397
WhatsApp only.
+201508856397
My WhatsApp number
Tiktok @amzaah
Instagram @zainabuh_Amzah
Snapchat @Zainabuh Amzah
Wattpad @zainabuh Amzah
Arewapen @zainab Amzah
Wattpad @zainab Amzah