Nour AynFree

ArewaPen original

Short StoryFreeCompleted

Nour Ayn

  • 1views
  • 4chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

About the author

I am Zainab Amzah, a passionate Hausa novelist and storyteller. Writing is my passion, and storytelling is my way of expressing creativity, emotions, and imagination. I write Hausa novels that explore love, family, relationships, suspense, and real-life experiences. My goal is t...

More from @zainabamzah

Sample · Chapter 1

✨*𝐍𝐨𝐮𝐫 𝐀𝐲𝐧*✨𝐁𝐲 𝐙𝐚𝐢𝐧𝐚𝐛 𝐀𝐦𝐳𝐚𝐡*** *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️*(J.W.A)*_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.*As you read this book, I kindly ask you to pray for my late mother. May Allah forgive her shortcomings, illuminate her grave, and grant her eternal peace in Jannatul Firdaus. Ameen. 🤲🏻🙏🏻*_Wannan labari kirkirarre ne, kuma ba a rubuta shi da niyyar ɓata wa wani ko wata ba ko cin zarafin kowa ba. Duk wani kamanceceniya da sunan mutum, halayyarsa ko wani abu da ya faru a rayuwarsa, idan ka/ki ga wani abu da ya yi kama da labarinka/labarinki a yi haƙuri please._🙏🏻*PAGE 1*Kyakkyawar matashiyar budurwa ce, wacce ba za ta wuce shekara sha takwas ba. Fara ce, amma ba fara tas ba. Tana da matsakaicin tsayi, ba za mu ce doguwa ba ce, kuma ba gajera ba ce. Allah Ya yi mata kyau da wani irin sura mai jan hankali. Sai dai a saman ta, ba ta da cikar ƙirji sosai. Duk da a kwance take, Amma za ka iya ganin yadda jikinta yake da kyau, kwance take a kan wani katafaren gado na alfarma dake cikin ɗakin, wanda aka k’awata shi tamkar ɗakin amarya. Komai na ɗakin ya nuna tsantsar tsada da haɗuwa, tun daga kayan ɗakin har zuwa labulen da aka saka a tagogin ɗakin. Tana sanye da kyawawan kayan barci silk pyjamas, masu launin pink, waɗanda suka kwanta luf-luf a jikinta. Lulluɓe take da duvet mai shegen kyau da laushi, sai juyi take yi a kan gadon, tana sauke wani irin nishi saboda tsananin ciwon mara da take fama da shi.(Period cramps.)Ta yi amai har ta gaji. Ba ƙaramin wahala take sha ba ko wane lokaci, domin kuwa duk zagayowar wata, sai ta shiga wani irin hali na rashin lafiya da yake hana ta gudanar da abubuwan da ta saba yi a rayuwarta. Wani lokacin ciwon kan yi tsanani har ta kasa tashi daga kan gado. Wani lokacin kuma Amai ne yake damunta, tare da ciwon baya da kuma kasala da take ji a dukkan jikinta, ba ita ce mace ta farko da take fama da ciwon al’ada ba, amma irin azabar da take sha a duk wata ya bambanta da yadda mutane da yawa suke sha, wannan ne ya sa take jin tsoron zagayowar wata fiye da yadda za a iya zato.A duk lokacin da wata ya kusa zagayowa, takan shiga damuwa, zuciyarta takan yi nauyi saboda tunanin irin azabar da za ta sake fuskanta. Wani lokaci ma tun kafin lokacin ya yi, sai ta fara jin fargaba, tana tunanin ko wannan karon ma za ta sake shiga irin halin da ta saba shiga.Ba ita kaɗai ce take shiga wannan fargabar ba, gabaɗayan su sukan kasance cikin zullumi da damuwa a duk lokacin da wannan lokaci ya zo, musamman ƙawarta kuma ‘yar’uwarta, wacce ta fi kowa sanin halin da take shiga ciki sabod...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters4
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play