Chapter 12: The Insult she wouldn’t forget
Ta nufi wajen tana tafiya cikin nutsuwa, hannunta riƙe da wayarta. Da ta isa, ta kwankwasa ƙofar kafin ta shiga
Daddy yana zaune a falo yana karanta wasu takardu, gilashinsa a kan hancinsa. Da ya ɗago ya gan ta, sai ya ajiye takardun gefe
“Good morning, Daddy”
“Good morning my daughter, kin tashi lafiya?”
“Lafiya lau Daddy?”
“Ma shaa Allah, ya kika kwana? Ina ba wani takura ko?”
Rahama ta zauna a gefen kujerar da ke kusa da shi, tana gyara gefen hijabinta “Alhamdulillah, Hajiya ma ta kula da ni sosai”
Daddy ya yi murmushi “To, Allah ya saka mata, na ji daɗin yadda kika nuna ƙwazo a wannan tafiyar, Ahmad ya faɗa min kaɗan daga abin da kuka yi a workshop ɗin”
“Thank you Daddy, na ji daɗin yadda aka gudanar da shi, na kuma koyi abubuwa da yawa”
“Good! Wannan shi ne abin da nake so, ki riƙa amfani da duk wata dama da ta zo miki wajen ƙara ilimi”
“In shaa Allah Daddy”
Sun ɗan yi hira na wasu mintuna kafin Rahama ta miƙe “To bari na tafi, sai anjima Daddy”
“Alright Rahama”
Ta yi masa murmushi sannan ta juya ta nufi ƙofa, ta buɗe ta fita bayan ta fita ta kama handle din ta fara ja a hankali don ta rufe
A daidai lokacin ne Rameez da Rayyan suka iso, suna shirin shiga sashen Daddyn suma
“Good morning, Ya Rameez” ta faɗa cikin ladabi, ta tsaya dan ta gaishe shi
Rameez ya amsa da murmushi “Good morning Rahama, kin tashi lafiya?”
“Lafiya lau, ya gida?”
“Alhamdulillah, lafiya”
While da suke gaisawa, Rayyan dake kusa da su, hannunsa ɗaya a aljihun wando Rahama ta ɗan karkata kanta zuwa gare shi “Good morning”
Ba tare da ya amsa gaisuwar ba, Rayyan ya ciro wata tissue daga aljihunsa, ya lanƙwashe jikinsa ya goge handle ɗin ƙofar da Rahama ta fito ta riƙe da hannunta
Ya gogewa sosai sannan sai ya jefar da tissue ɗin a cikin ƙaramin kwandon shara da ke kusa da ƙofar, ya tura ƙofar ya shiga
Rahama ta tsaya cak, murmushin da ke fuskarta ya ɓace a hankali
Abin da ya yi ya fi rashin amsa gaisuwarta zafi, ya goge ƙofar ne saboda ta taɓa ta? Kamar ta shafa masa wani abu marar kyau ne? Or ko tana da wata cuta?
Rameez ya kalle ta sannan ya kalli ƙanin nasa da ya riga ya shiga, fuskarsa ta nuna rashin jin daɗi, amma bai ce komai ba sbd a gabanta ba zai masa mgn ba
Rahama ta yi ƙwafa a hankali “Nayi na farko kuma nayi ta karshe, ko kallon side dinka na daina har abada, kuma ban yafe ba” ta furta sannan ta juya ta wuce su ba tare da ta sake kallon cikin sashen ba
“Rahama…” Rameez ya kira ta, ta tsaya na ɗan secs kawai ta ce “Na’am, Ya Rameez?”
Ya buɗe baki kamar zai ce wani abu, amma da ya tuna abin da ƙanin nasa ya yi, sai ya kasa samun kalmomin da za su dace “Babu komai, sai anjima”
Ta ɗan gyada kai “To”
Ta wuce tana tafiya da sauri, tana ƙoƙarin kada ta nuna yadda abin ya taɓa ta. Amma duk da ƙoƙarinta, jikinta ya yi sanyi sosai, ba wai don tana buƙatar amsa gaisuwarsa ba, ko don tana son ya kula ta ba, sai dai akwai wani irin wulaƙanci a cikin abin da ya yi, wanda ko maƙiyinka bai kamata ya nuna maka haka ba
Da ta isa kitchen, ta tarar da masu aikin gidan suna shirya abincin breakfast “Good morning y’all” ta gaishe su
Suka amsa mata, wasu daga cikinsu suna ci gaba da aikinsu
Rahama ta ajiye wayarta a kan tebur, ta ɗaure hannun rigarta sama kaɗan “Ku bar min komai, ni ce zan yi breakfast yau”
Wata daga cikin matan ta juya tana kallonta “Hajiya ai mun riga mun fara, ki bari kawai, za mu yi”
“No, no…. Ku bar shi, I want to do it myself”
“Amma Hajiya….”
“Please ku bari nace, ba wani abu mai wahala zan yi ba” Ta faɗa cikin murmushi, amma sautinta ya nuna cewa ta riga ta yanke shawara, ma’aikatan suka kalli juna kafin su ajiye abin da suke yi, suka ba ta wuri
Rahama ta fara duba kayan da ke kitchen, tana tattara abin da take buƙata, ta ɗauki ƙwai, ta fito da kayan tea, sannan ta fara shirya abin da za ta haɗa
Tana cikin fasa ƙwai a cikin kwano ne Mommy ta shigo “Rahama, ke kuma me kike yi?”
Rahama ta ɗago kai ta yi murmushi “Breakfast nake yi, Mommy”
“Kin kori masu aikin kenan?”
“Na ce su bar ni ne kawai, I want to make it myself”
Mommy ta ƙaraso kusa da ita, tana kallon kayan da ta jera kan cabinet din “Amma ai suna nan sbd wannan aikin ne, ko har kin huta daga ganjiyan jiya ne”
Rahama ta yi dariya “Kai Mommy ai gajiya kam ya tafi fah”
Mommy ta girgiza kai tana murmushi “Ke kam! Ni dai ina so ki huta ne, haba jiya da daddare fah kika dawo daga tafiya, ya kamata ki bar su su yi aikin”
“Wlh Mommy ba gajiya nake ji ba ynx, sai ma karfi, don Allah ki bar ni”
Mommy ta tsaya tana kallonta, kafin ta yi ajiyar zuciya “To shikenan, amma idan kin gama, ki kira ni kar ki yi ta aikin nan ke kaɗai har ki gaji”
“Okay Mommy. Thank you”
Mommy ta fita, Rahama kuma ta ci gaba da aikinta
Kitchen din ya cika da ƙamshin breakfast ɗin da take shiryawa, ta yi ƙoƙari ta haɗa komai cikin tsari, tana wanke abubuwan da take amfani da su kafin ta koma ga na next, although duk da time to time sai an samu ɗaya daga cikin masu aikin gidan su zo suna cewa zasu taimaka mata, amma sai ta ce musu ta kusa gamawa
Bayan ta kammala, sai ta fara jera abincin a kan dining table, ta shirya komai cikin tsari , ta gyara plates da spoons, ta ajiye tea a gefe, sannan ta kalli table din ta gamsu, ta goge hannunta da tawul, ta fito daga dining area ta nufi ciki inda Hajiya take zaune
“Hajiya breakfast ya kammalu”
Hajiya ta ɗago kai daga abin da take karantawa “To madallah Allah ya yi miki da albarka dear”
“Amin Hajiya taaa”
Rahama ta wuce zuwa ɗakin Mommy, ta sanar da ita
Ba da daɗewa ba, kowa ya fara fitowa zuwa dining area. Daddy ya zo tare da Mommy, Hajiya ta zauna a kujerarta, Rameez ma ya iso. Rayyan ne ya zo daga baya, sanye da wata riga mai sauƙi, fuskarsa babu alamar cewa akwai wani abu da zai dame shi a safiyar
Ya ja kujera ya zauna, bai ko kalli Rahama ba
Rahama ma ba ta damu da hakan ba. Ta zauna a inda Hajiya ta nuna mata, tana kallon yadda kowa ya fara ɗaukar abinci
Suka fara breakfast cikin nutsuwa. Mommy ta ɗanɗana abincin, ta gyada kai cikin gamsuwa. Daddy ma ya ci gaba da cin nasa ba tare da ya ce komai ba
Rahama ta ɗago kai ta kalli Mommy a ranta tace nasan maganinka Rayyan “Mommy, breakfast ɗin ya yi daɗi?”
Mommy ta ɗan yi murmushi “Sosai ma”
Hajiya ta dakata da abin da take yi, ta kalli Rahama “Au, ke kika yi?”
Rahama ta gyada kai “Eh, Hajiya” Sai ta ɗauki tissue daga gefenta, ta ɗaga ta zuwa hancinta, ta yi kamar tana fama da mura, ta share hancinta a hankali
While Rayyan yana shirin saka cokali na uku a bakinsa cak ya dakata, musamman jin ita tayi girkin kuma yaga tana share hanci
Cokalin ya tsaya, ya kasa karasa da shi bakinsa, idanunsa suka sauka kan Rahama, ya kalleta na ɗan lokaci, yana kallon tissue ɗin da take riƙe da shi, sannan ya ɗago kai ya kalli abincin da ke gabansa
Rahama ta ji idanunsa a kanta, ta kuma san abin da yake tunani, amma ta ci gaba da cin nata breakfast ba tare da ta ɗago ta kalle shi ba
Rayyan ya sauke cokalin a hankali “Me ya sa masu aikin gidan ba su yi breakfast ba sai ita? “
Muryarsa ta fito cike da amo
Mommy ta ɗago kai ta watsa masa wani kallo mai tsauri “Rayyan!”
Amma kamar bai kalli kallon da take masa ba, ya ci gaba da kallon abincin da ke gabansa “Gidan nan cike take da masu aiki, me ya sa za a bar baƙuwa ta yi abinci wa kowa?”
Rahama ta ɗan matsar da plate ɗinta gaba, amma ba ta ce komai ba
Rayyan ya juya ya kalli Mommy “Please taya za’a na barin kowa anyhow yana mana girki bayan ba kowa ne yake da tsafta ba, imagine?”
Mommy ta sauke cokalin da ke hannunta “Enough, Rayyan”
Ya kalli Mommy na ɗan lokaci, sannan ya ture plate ɗinsa daga gabansa, kujerar da yake zaune ta yi ƙara yayin da ya miƙe da sauri
“Ba zan iya ba”
Ya rufe bakinsa da tafin hannunsa, ya yi kamar zai yi amai, sannan ya yi kakarin iska sau biyu
“Rayyan!” Mommy ta kira shi, wannan karon cikin fushi
Sai dai ya riga ya fara tafiya. Ya fita daga dining area ba tare da ya sake kallon kowa ba, yana ci gaba da yin kamar zaiyi amai
Rahama ta tsaya da cokalin da ke hannunta, ba ta ce komai ba, ta ɗauki gilashin ruwanta ta sha kaɗan, sannan ta ajiye shi a hankali
Hajiya kuwa ta bi Rayyan da kallo har ya ɓace daga dining area. Ta ɗaga hannunta ta rufe bakinta, ta girgiza kai cikin ɓacin rai da rashin yarda “Ohhh! Lalle ma yaron nan!”
Ta juya ta kalli hanyar da Rayyan ya bi, sannan ta mayar da idanunta kan sauran mutanen table dinner “Amma zan yi maganinka dole kuwa. Dole ne a dawo da maganar nan gadan-gadan, ayi kowa ma ya huta. Har kana da bakin nuna kyamarta haka? To ai sai mu ga yadda za ka yi!”
Rameez ya sauke cokalin da ke hannunsa, bai ji daɗin abin da ƙanin nasa ya yi ba sam, musamman ganin yadda Rahama ta yi shiru tana ƙoƙarin kada ta nuna komai a fuskarta
Ya yi saurin y katse shirun kafin maganar ta ƙara tsananta “Mommy, Hajiya, ku bar shi pls kun san Rayyan ba ya son cin abinci idan ba Mommy ce ta yi ba, Maybe shi ya sa ya yi haka”
Mommy ta juya ta kalle shi “Rameez, don Allah kada ka fara kare shi, ka ga abin da ya yi fa”
Rameez ya sauke idanunsa kan plate ɗinsa
“I know Mommy ba na ce abin da ya yi daidai ba ne, Ina dai cewa kun san halinsa ne”
Ya ɗan kalli Rahama a hankali, yana son ya ga cewa bata ji wani iri ba, amma Rahama ta sunkuyar da kanta tana cin abincinta, kamar ba ta ji abin da suka faɗa ba
Daddy kuwa ya zauna shiru mamaki ne ma yasa ya kasa cewa uffan
Ya kalli plate ɗin da Rayyan ya bari, sannan ya kalli Rahama, da alama yana da abin faɗa, amma ya kasa furta komai, ya ɗauki cup ya sha ruwa, sannan ya cigaba da breakfast ɗinsa
Hajiya ta sauke ajiyar zuciya “Allah ya kyauta mana”
Haka suka cigaba babu wanda ya sake cewa komai, jikinsu dai duk yayi sanyin
Da aka gama, ta miƙe ta tattara kayanta “Na gode da breakfast Mommy, Hajiya na gode”
Mommy ta kalleta, fuskarta cike da tausayi “Rahama zauna mana”
Rahama ta ƙaraso kusa da ita “Na’am, Mommy?”
Mommy ta riƙe hannunta “Ki yi haƙuri da abin da ya faru. Kin ji?”
Rahama ta yi murmushi, duk da cewa ba shi ne murmushin da ta saba yi ba “Ba komai Mommy, I’m fine”
“Kin tabbata?”
“Eh, Mommy” Ta sumbaci hannunta cikin ladabi, sannan ta juya ta nufi ɗakinta dan ta ɗauki kayanta
Bayan ta shirya, Daddy ya sa aka kira direba dan ya kai ta gida. Rameez ya raka ta har ƙofar mota, yana son ya yi mata magana game da halin Rayyan, amma bai san ta inda zai fara ba
“Rahama”
Ta juya ta kalle shi “Na’am, Ya Rameez?”
“Game da abin da ya faru da safe… I’m sorry”
Rahama ta ɗan yi murmushi “Ba kai ka yi ba, Ya Rameez. Don haka babu abin da za ka ba ni haƙuri a kai”
“Na sani, amma bai kamata ya yi haka ba”
Ta gyara hijabinta “To Allah ya kyauta, ni zan wuce yanzu”
“Okay, Ki gaida Mammy”
“In shaa Allah” Ta shiga motar, direba yaja motar. Rameez ya tsaya yana kallon motar har ta fice daga gidan, kafin ya juya ya koma ciki
Da ta isa gida, Rahama ta tarar da Mammy a falo, da Mammy ta gan ta, sai ta yi murmushi ta miƙe “Ah, ga dear ta dawo!”
Rahama ta ƙarasa ta rungume ta “Missed you, Mammy”
“Ni ma na yi kewarki, ya gajjiyanku, ya su Hajiya”
“Alhamdulillah Mammy, sun kula da ni sosai”
Mammy ta janye ta kaɗan don ta kalleta
“To zauna ki ba ni labari, ya workshop ɗin? Na san kin samu abubuwa masu amfani”
Rahama ta zauna kusa da ita, ta cire hijabinta ta ajiye a gefe
“Mammy wlh workshop ɗin ya yi kyau, an tattauna abubuwa da yawa, musamman yadda ake gudanar da wasu ayyuka da yadda ake warware matsaloli a tsakanin ma’aikata. Sun kuma nuna mana yadda ake duba bayanai kafin a yanke hukunci, saboda wani lokaci abin da mutum ya fara gani ba shi ne ainihin matsalar ba”
Mammy ta gyada kai “Haka ne, ya kamata a riƙa bincike sosai kafin a yanke hukunci”
“Exactly! An ba mu wasu bayanai da muka yi aiki a kansu, muka tattauna hanyoyin da za a bi wajen inganta aiki. Na ji daɗin yadda aka ba mu damar bayar da ra’ayi. Da farko dai na yi tunanin zan zauna ne kawai ina sauraro, amma daga baya sai na tsinci kaina ina shiga discussion ɗin sosai”
Mammy ta yi dariya “See you wai ke din? Ai tun kina ƙarama ba kya iya zama shiru idan an ba ki damar magana”
Rahama ta buɗe baki cikin mamaki “Mammy! Ashe ni mai yawan magana ce?”
“Kin fi kowa sani”
Suka yi dariya tare. Rahama ta ci gaba da ba ta lbrn workshop ɗin, yadda aka raba su zuwa ƙananan group, yadda suka yi nazarin matsalolin da aka gabatar musu, da kuma yadda aka gabatar da sakamakon aikinsu a gaban sauran mahalarta
Mammy ta saurare ta cikin kulawa, tana yi mata tambayoyi a inda ta ga ya da ce
“Allah ya ƙara miki ilimi my love, Ina so ki riƙa cin moriyar duk wata dama da ta zo miki”
“Amin Mammy”
Mammy ta ɗan yi shiru tana kallonta, sannan ta tambaya “To ya Rayyan? Kun yi tafiyar lafiya?”
Rahama ta ɗauki wayarta daga kan kujera, ta fara dannawa kamar tambayar ba ta da wani muhimmanci “Lafiya lau, mun je, mun dawo”
Mammy ta ɗan karkatar da kai “Shi kenan? Babu wani abu da ya faru?”
Rahama ta ɗago ta kalleta “Mammy ai ba wani abu, mun je workshop ne, ba yawon shakatawa ba”
Mammy ta yi murmushi “Na sani, na sani ai, Ina dai tambayarki ne”
Rahama ta sake mayar da hankalinta kan wayarta “Everything was fine, Mammy”
Ta faɗi hakan cikin sauri, ta miƙe tana cewa za ta je ta canza kaya. Ba ta son ta sake tuna yadda Rayyan ya goge handle ɗin ƙofar, balle yadda ya ture abincin da ta yi ya tashi yana kakarin amai a gaban kowa, though da gangan tayi kamar tana mura ne
Ba ta da niyyar ɓata ran Mammy da irin wannan labarin. Kuma ba ta ga dalilin da zai sa ta zauna tana bayyana halin mutumin da ya riga ya nuna mata cewa ba ya son ko kasancewarta kusa da shi
Meanwhile Rayyan yana zaune a cikin ɗakinsa, ya canza kaya, ya zauna a gefen gado yana duba wasu message a wayarsa
Wayar ta fara ringing
Da ya ga sunan Safiyya a screen, fuskarsa ta sauya, ya ɗauki wayar da sauri, ya amsa kiran “Hello my love”
“Habibi!” muryar Safiyya ta fito cikin fara’a “Finally! Ka tuna cewa kana da girlfriend ne?”
Rayyan ya ɗan yi murmushi “Safiyya please…. Don’t start”
“Me zai hana na fara? Tun jiya nake jira ka kira ni, ka tafi Lagos ni na Kira, ka dawo har yanzu sai ni zan kira ka?”
Ya jingina bayansa da headboard na gadon, yana gyara yadda yake riƙe da wayar “I’m sorry baby, jiya na gaji sosai. Komai ya yi min yawa, kuma na dawo gida Ada daddare”
“Ka gaji har ka kasa turo min ko message?”
“I know! I should have called I’m sorry Habibti”
Safiyya ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin ta tambaya cikin sanyi “Ka yi missing dina kuwa?”
Rayyan ya sauke numfashi, murmushinsa ya ƙara faɗaɗa “Of course I did. Do you even have to ask?”
“Hmm! Ban yarda ba”
“Why?”
“Saboda idan da gaske ka yi missing dina, da ka kira ni tun da ka dawo”
Rayyan ya yi dariya a hankali, ba irin dariyar da yake yi wa sauran mutane ba, muryarsa ta yi laushi “Okay fine, I missed you so much, Happy now?”
Safiyya ta yi dariya “Very happy, Habibi”
“Good! Yanzu ki daina fushi da ni”
“Ban yi fushi ba ai, na dai yi kewarka ne”
Rayyan ya sauke kansa kan headboard, idanunsa a rufe “Ni ma na yi kewarki Safiyya, I wish you were here”
“Really?”
“Yes baby! Really”
“Then when are you coming to see me?”
“Soon in shaa Allah. Zan shirya yadda za mu haɗu”
“Promise?”
“I promise”
Safiyya ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta fara ba shi labarin abubuwan da suka faru, Rayyan ya saurare ta, yana amsa mata da kalmomi masu sanyaya zuciya, lokaci-lokaci yana tambayar ta ƙarin bayani, bai nuna gajiyar da take damunsa a da ba, kuma bai katse ta ba lokacin da take magana
“Habibi, I love you” Safiyya ta faɗa a hankali
Rayyan ya buɗe idanunsa, ya kalli silin ɗakin “I love you too, baby”
“More than I love you?”
“Much more”
“Liar!”
Ya yi murmushi “Believe whatever you want Safiyya”
“Okay, I’ll believe you this time, amma ka yi min alƙawarin ba za ka sake ɓacewa haka ba”
“I promise I’ll do better”
Suka ci gaba da hira cikin raha da kalaman soyayya
A wajensa, Safiyya ita ce mutumin da yake son ya ji muryarta, ya saurari korafinta, ya kwantar mata da hankali idan ta yi fushi. Ita ce wadda yake iya yi wa magana cikin sanyi ba tare da ya ji kamar yana tilasta wa kansa hakan ba
Da suka gama wayar, Rayyan ya ajiye wayar a gefensa, ya miƙa hannunsa ya ɗauki remote ɗin da ke kan table
Amma kafin ya kunna tvn, hoton safiyar da ta wuce ya faɗo masa a rai… Rahama tana zaune a table breakfast, tana share hancinta da tissue, yayin da shi kuma ya ture plate ɗinsa ya tashi
Fuskarsa ta ɗa sake tsuke wa, ya ajiye remote ɗin, ya miƙe ya nufi window
Ba ya son Rahama, kuma a tunaninsa, babu wani dalili da zai sa ya yi ƙoƙarin ɓoye hakan
Idan kuna jin dadin labarin kuyi following dina, kuyi liking na book din, sannan kuyi comment plssss Habibtis