MEERAH

28

by @oumfatima33

*MEERAH*

     *028*


      "In sha Allah zan cika alƙawari." Nawaz ya faɗa yana ƙoƙarin juyawa aka yi horn a bakin ƙofa mai gadi ya tashi ya buɗe. Tsala-tsalan motocin Dady ne suka shigo suka yi parking a parking space.

   Duk motocin muka bi da kallo dai-dai lokacin da aka buɗe motar dake gaba da wacce ke baya, securities ɗinsa suka shiga fito wa cikin sauri suka ƙara sa motar dake tsakiya wacce Dady ke a cikinta.

   Buɗe masa aka yi ya fito cike da ƙasaita yana kai kallonsa inda ya hango ƴar sa abar ƙaunar sa da ya gani tsaye da wani yaro, mamaki sosai ya kama shi ganinta tsaye da wani don bai taɓa sanin cewa tana tsayu wa da samari ba.

 *****  A ɓangare na kuwa sai da ya fito na gansa da idona sannan na tabbatar da cewa shi ɗin ne, don bamu tsanmaci ganinsa a yau ba kasancewar ba Friday bace ranar da ya saba zuwa ya mana weekend.

   Cike da murna da farin cikin ganinsa na tafi da sauri zuwa inda yake na rungume sa ina cewa.

   "Oyoyo Dadyna, I miss you so much." Na faɗa cikin tsananin farin cikin ganinsa da na yi.

   Faɗaɗa murmushinsa Dady ya yi ya ɗago ni daga jikinsa yana kallon fuskata yace.

   "I miss you more My princess." Ƙaramar dariya na yi ina ƙara rungume sa cike da jin daɗin sunan da ya kira ni da shi.

   "Barka da yanma ranka ya daɗe." Nawaz da ya ƙaraso wurin ya tsuguna har ƙasa ya faɗa cike da girmamawa. Kallonsa Dady ya yi na ƴan daƙiƙu sannan ya amsa masa da.

   "Barka dai." A takaice, daga haka ya riƙe hannun ƴarsa suka shiga ciki ɗaya daga cikin securities ɗinsa na bin bayansu riƙe da breaf case ɗinsa.

   Nawaz kuwa sai da suka ɓace wa ganinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe ya nufi bakin gate aka buɗe masa ya fice.

   Wata babbar ajiyar zuciyar ya ƙara sauke wa lokacin da ya kammala fita daga gidan baki ɗaya, Wani irin kwarjini Dady yake masa tun ranar farko da ya fara ganinsa. Shida Ajmal idan suna wuri baya taɓa iya haɗa ido da su domin cika masa wajen suke yi.

   Cikin sanyin jiki ya fara takawa har ya fita daga street ɗin sannan ya samu abin hawa ya faɗa masa inda zai kai shi suka wuce.

***** A ɓangaren mu nida Dady kuwa har muka shiga ciki yana riƙe da hannuna, Momy dake saukowa daga sama ce taci birki tana kallonsa cike da mamaki.

  Saukowa ta ƙarasa yi faɗin.

    "Sannu da zuwa Alhaji."

       "Yauwa Hajiya na same ku lafiya."

   "Lafiya lau Alhamdulillah, tafiyar yamma ka yi ne haka?." Momy ta faɗa lokacin da take ƙarasa saukowa ta amshi jakar hannunsa.

   "Meeting ne na gaggawa ya kama ni shi yasa na taho ban sanar dake ba." Dady ya bawa Momy amsa lokacin da suke haurawa sama ɓangarensa.

   Bedroom ɗina na wuce nima na kira Nawaz don jin ko yaje gida lafiya.


******* A ɓangaren Dady kuwa lokacin da suka shige ruwa Momy ta haɗa masa ya yi wanka, yana fitowa ya samu ta ajiye masa jallabiya mai laushi don haka ya shirya cikin natsuwa.

   Zama ya yi bakin gado yana amsa waya dai-dai lokacin Momy ta shigo ɗauke da abincin da ta shirya masa, ruwa kawai ya sha ya miƙe ya fita Masallaci saboda sallar magrib da aka kira.

  Bayan an idar da sallah ya dawo gida sannan ta gabatar masa da abinci, yana cikin cin abincin ne ya jefo mata tambayar da ta tsaya masa a rai.

   "Yaushe Mamana ta fara tsayawa da samari a gidan nan?." Ya yi maganar yana zuba mata ido sosai don jin amsar da zata bashi. Ajiyar zuciya Momy ta sauke tace.

   "Bata tsayawa da samari gaskiya."

   "Shi kuma yaron da na same su tare fa?." Ya kuma jefo mata tambayar yana tsare ta da ido. Murmushi Momy ta yi tace.

   "Wannan ai Nawaz ne yaron nan da ya taimake ta, shine ya kawo mana ziyara tayi masa rakiya." Shiru yayi yana nazari na ɗan lokaci kafin yace.

   "Bana son wata alaƙa ta shiga tsakaninsu, taimako ne ya yi mata nun kuma saka masa da abinda ya kamata. Bana son in ƙara ganinsa tare da ita, saboda haka sai a kiyaye." 

   "In sha Allah." Momy ta faɗa daga haka suka bar maganar suka shiga wata.

★★★ 

  Washe gari nida Dady muka je Gwangwazo muka yini a can, daga nan kuma gidan Baba Alhaji muka je wato Mahaifin Dady. Inna (Hafsat Mahaifiyar Dady, wacce naci sunanta) tayi farin cikin ganinsa sosai don haka tayi ta min hidima.

   Inna Maimuna (Matar Baba Alhaji ta biyu) ita ma ta kula dani sosai ta bani kayan gargajiya tace na kai wa Momy.

   ★ Washe gari gaba ɗayan mu muka wuce Abuja don taya Ya Ajmal bikin buɗe sabon Company ɗin sa, a gidan Dady na Abuja muka sauka inda aka buɗe mana part ɗin Momy dake can.

 Mun samu tarba daga Aunty amarya daidai gwargwado don basa faɗa ita da Momy kowa sabgar gabansa yake yi, idan an haɗu a gaisa a mutunce shine kawai.

  Ƙarfe 4 na yamma za'a fara taron don haka kowa ya nemi wuri ya kwanta domin ya huta kasancewar tun ƙarfe 10 muka isa Abuja. 

  Ni kam bacci ne ya ɗauke ni bayan na kammala waya da Nawaz da ya kira don jin ko mun sauka lafiya.

  Sai da aka kira sallar la'asar sannan muka tashi muka yi sallah muka hau shiri, tsaf na shirya cikin wani haɗaɗɗen leshi da Momy ta zaɓa min tace na saka. Ɗinkin riga da siket ne half bubu da ya zauna min sosai a jikina. 

  Kayan sun matuƙar yi min kyau musamman da na kashe ɗauri ya zauna ɗas a kaina, na ɗauki mayafin da ya dace da kayan na saka, sannan na ɗauki jaka da takalmin da suka dace na baza ƙamshi na fita.

  "Masha Allah Auta, to ko kefa. Baki ga yanda kayan suka yi maki kyau ba amma ko kaɗan ba kya son saka su." Momy ta faɗa lokacin da na kammala saukowa daga sama.

   Murmushi na yi ina rungumeta sannan muka wuce. Tun daga bakin gate ɗin farko na Company ya ɗauki hankalina, domin kuwa ƙaton gini ne mai hawa uku da aka ƙawata shi sosai da gini irin na zamani.

  Tun daga nesa muke hango manyan motoci suna parking a inda aka tanada domin hakan, kai da ganin irin motocin dake tsayawa ka san cewa babban biki ne ake yi da manyan mutane suke halarta. Domin irin tsaron dake wurin ma kawai ya isa ya shaida hakan.

   Lokacin da muka isa tuni su Ya Ajmal suna wurin, shi na fara hangowa ya yi kyau sosai cikin TOM FORD _ O, Connor Midnight Tuxedo. Suit ɗin ya zauna sosai a buɗaɗen jikinsa irin na Mazan da suka san darajar motsa jiki.

   Shagalar da na yi a kallonsa har ban san lokacin da Momy ta fita ta bar ni a motar ba, sai sautin muryarta da naji tana cewa.

   "Hala a motar zaki zauna ba zaki fito bane?." Ajiyar zuciyar dawowa hayyaci na sauke, sai kuma na ɓata rai ina jin haushin kaina a kan shagalar da na yi a kallonsa.

   Fitowa na yi a hankali na tsaya a kusa da Momy ina gyara riƙon hand bag ɗina, a hankali na ɗaga idanuna da niyyar yiwa Ya Sultan magana, wanda na hango tsaye a kusa da ya Ajmal ɗin.

  Sai dai ina ɗaga kai idanuna suka faɗa cikin na Ya Ajmal ɗin da ya tsare ni da wani irin kallo da nake kasa fassara shi. Sai da nayi da ƙyar na iya janye idanuna daga cikin nasa ina sauke ajiyar zuciya.

   A zuciyata nake ƙun-ƙunin cewa. 'sai ka tsare mutum da waɗan nan idanun naka masu kama dana Zaki, to ni dai ba zaka bani tsoro ba.'

  Ajmal kuwa sarai yaga ƙun-ƙunin da tayi masa don idanunsa a kan ɗan ƙaramin bakinta mai surutu suke, tsaf kuma ya karanci motsin lips ɗinta. Hakan yasa ƙaramin murmushi ya ƙwace masa wand ya yi shi a kan idon Mamy da Jauhar da hankalinsu kacokan yake a kansu shida Meerah, wacce tunda ta fito a motar suka zuba mata idanu suna kallonta.

   Momy dake lure da irin kallon da suke bin Meerah da shi ne ta kama hannunta suka shiga takawa zuwa inda suke. Ita ta fara gaishe da Mamy ta amsa mata da ƙyar tana ɗauke fuska.

   Sai ma ta bar wurin ta tafi tarbar wasu baƙinta da suka ƙaraso, murmushi kawai Momy ta yi cikin rashin damuwa, domin kuwa halin Mamy ba baƙon abu bane a wurinta.

  Ajmal kuwa cikin sauri ya ƙaraso inda muke ya tsuguna ya gushe da Momy cike da girmamawa, amsa masa tayi haɗi da sanya masa albarka da yi masa fatan alkairi.

  Cike da jin daɗi ya amsa mata haɗi da yi mata godiya, ido muka sake haɗa wa ya  kalle ni  ƙasa-ƙasa ya ɗauke kai. 

   "Good evening Yaya." Na faɗa a hankali ina kallonsa, idanu ya lumshe ya buɗe su lokaci ɗaya sannan ya jin-jina min kai. Ɗauke kai na yi ina mitar rashin amsa min da baki da ya yi.

***** Duk wasu manyan baƙi da aka gayyata don buɗe Company sun halarta, don haka gaban ginin aka matsa domin aiwatar da abinda ya tara mutane. Gaba ɗaya ginin zagaye yake da irin ribbon ɗin nan da ake yanka wa idan za'a buɗe sabon wuri.

   Mamy ce ta matso kusa da Ajmal fuskarta ɗauke murmushi ta bashi almakashi domin ya yanka. Sai dai maimakon ya yanka da kansa kamar yanda ta buƙata sai ya kamo hannuna ya saka min almakashin.

kasancewar muna tsaye ta gefen hagunsa nida Momy, yayinda su Mamy suke tsaye ta gefen damar sa. Kallonsa na yi cike da mamaki da neman ƙarin bayani kan abinda yake nufi.

   Idanunsa ya lumshe sannan ya buɗe min ya yi min alamar na yanka, kasa yin hakan na yi sai ma idanu da na zuba masa kawai ina kallonsa. Ban ankara ba sai hasken Camera da na riƙa ji yana haske mu.

  Ajmal kuwa ganin ta kasa yanka wa ya saka shi ƙara yin taku ɗaya ya haɗe tazarar dake tsakanin mu, hannunsa ya ɗora a saman nawa mai riƙe da almakashin. Hakan ya saka na kalli hannayen namu dake sarƙe da juna sannan na ɗago na kalli fuskarsa.

   Ido ya ƙara lumshe min sannan ya gyara riƙon hannuna a cikin nasa muka yanka ribbon ɗin tare, tafi wurin ya kaure da shi yayinda masu ɗaukar hotuna da videos suke ɗaukar duk abinda ke faruwa.

    Ɗagowa muka yi a tare idanun mu suka ƙara sarƙe wa cikin na jina. Ban san lokacin da murmushi ya suɓuce min ba saboda abin ya matuƙar birge ni. Girarsa ta dama ya ɗan ɗage min kaɗan alamar ya dai ɗin nan.

  Murmushi mai sauti na ƙara sakar masa a hankali nace.

  "Congratulations Ya Jam, Allah ya sanya alkairi ya kawo kasuwa mai albarka da nasarori masu yawa."

   Idanunsa ya lumshe a hankali yana jin yanda addu'ar take ratsa masa zuciya. Hannu ya bani muka yi musabiha alamar amsa min. A hankali ya furta.

   "Than you MM." Murmushi na ƙara sakar masa duk da cewa ban san me MM ɗin da ya kira ni da ita yake nufi ba.

**** A ɓangaren Mamy kuwa tunda Ajmal ya bawa Meerah almakashi ta haɗe rai sosai tana jin ɓacin rai na taso mata, wato ita zata bashi almakashi ya buɗe abinda yake mallakinsa amma shine zai bawa wannan yarinyar ta buɗe.

  Lallai abin nasa ya wuce duk inda take tunani, Jauhar kuwa lokacin da taga ya riƙe hannun Meerah suna yi wa juna wani irin kallo mai ɗauke da sirrika ji tayi ƙafafunta na ƙoƙarin kasa ɗaukar ta. Yayin da take jin wani azababben kishi yana taso wa tun daga ƙasan zuciyarta yana toshe mata mashaƙar isa.

  Lokacin da suka yanka ribbon ɗin kuwa suka ɗago a tare fuskar aljanar Yarinyar ɗauke da wani tattausan murmushi ta furta masa maganar da babu wanda yaji me ta faɗa sai shi. Kasa riƙe kanta tayi sai da hawaye suka zubo mata.

  Ji take yi da zata samu dama babu abinda zai hana ta shaƙe wuyan yarinyar can ta kashe ta har lahira, domin kuwa ta tsani ta ga wata mace ta raɓi Ajmal komai kusancinsa da ita kuwa.

   Kai ita fa ko Fatima bata son taga tana shige masa sosai bare kuma wacce mai kama da yaran aljanun da take Cousin ɗinsa.

     Duk abin nan dake faruwa a gaban Momy, Dady, Abby da sauran Iyayenmu da suka samu halarta ya faru. Don haka babu abinda suke yi sai murmushi, musanman ma Dady da ya fi kowa farin cikin samun kusanci tsakanin yaran nasa guda biyu.....

 
   (Assalamualaikum barkanmu da wannan lokacin, ina mai bayar da haƙurin jina shiru kwana biyu sakamakon rashin lafiyar da nayi fama da shi. Alhamdulillah na samu sauƙi zamu ci gaba in sha Allah, na gode.)

  *Oum Fatima*