29
by @oumfatima33
*MEERAH*
*029*
Bayan yanka ribbon ne aka buɗe farin ƙyallen da aka rufe rubutun sunan Companyn da aka yi da golden color, sai a lokacin ne suna da tambarin Company ya bayyana. Inda aka rubuta da manyan baƙi.
*AJMERA GLOBAL LUXURY FURNITURE & ELECTRONICS LTD.*
Tafi aka saka sosai sannan kowa ya shiga ciki, sosai sunan ya ɗauki hankalina salon yanda aka yi tsarin rubutun kaɗai abin kallo ne. Wayata na ciro na ɗauki hoto na mayar cikin jaka.
Ajmal dake kallon duk abinda take yi murmushi kawai ya saki ya ɗauke kai.
Taro yaci gaba da gudana inda aka nuna mana ko ina dake cikin Company tun daga kan ƙananan ofisoshi har zuwa manya, an tsara komai a ɓangaren da ya dace dashi.
Ofishin C. E. O yana a hawa na ƙarshe ne, wanda tsayawa bayyana irin yanda aka tsara shi ma ɓata lokaci ne. Kawai ku hango yanda office ɗin mamallakin wannan katafaren Company zai kasance.
An buƙaci Ya Ajmal ya gabatar da bayani, inda ya fito cikin natsuwar sa da kame wa. Ya fara da miƙa godiya ga Allah sannan ya yi godiya ga Iyayensa da jajircewarsu ce ta kawo shi har wannan matakin da yake kai, sannan ya ɗaora da taƙaitaccen bayani a game tsare-tsaren Company.
An ci an sha an ƙulla alaƙar Kasuwanci, sannan aka raba kyautuka inda duk wanda ya halarci taron ya samu rabonsa daga cikin kayan da Company yake samar wa.
Taro ya tashi lafiya cikin farin ciki da wal-wala, yayinda Ajmal ke shan addu'o'i da fatan alkairi daga bakunan jama'a.
Cikin ƙan-ƙanen lokaci shagalin buɗe Company ya zagaye ko ina a cikin Abuja da kewayenta, domin duk abinda ke faruwa ana yaɗawa kai tsaye ne.
****** A gajiye muka koma gida muna zuwa na shige bedroom ɗina na gabatar da sallar magriba, ina zaune ina karatun Alkur'ani a cikin tab ɗina kiran Nawaz ya shigo min.
Sai da na kammala ayar da na fara sannan na ɗaga kiran nasa da ya shigo a karo na biyu, gaishe sa na yi ya amsa min da kulawa haɗi da tambaya ta yanda taron ya kasance.
Ai kuwa cikin farin ciki na shiga bashi labarin yanda taron ya kasance da duk abinda ya faru a wurin, addu'a ya yi da fatan alkairi sannan muka yi sallama bayan na bashi saƙon gaisuwa ga su Umma.
Sai da na yi sallar isha sannan na fita muka ci abinci tare da su Dady gaba ɗaya, muna kammalawa kuma na shige bedroom ɗina na yi wanka na kwanta bacci saboda na gaji sosai.
€€€€€€€€€€€
A ɓangaren Ajmal kuwa sai dare sosai ya samu kansa bayan ya gama sallamar baƙinsa da sababbin abokan kasuwanci da suka ƙulla alaƙa a yau ɗin.
Yana cikin matuƙar farin ciki a yau ɗin irin wanda ba zai misaltu ba, babu abinda zai ce sai godiya ga Ubangiji da roƙon yaci gaba da yi masa jagora.
Lokacin daya isa gida kai tsaye ɓangarensa ya nufa ya yi wanka ya ɗauro alwala ya fito, tattausar jallabiya ya saka ya fesa turare ya tayar da sallah. Nafiloli ya shiga jera wa na godiya ga Allah da irin ni'imomin da ya yi masa.
Ya rufe da shafa'i da wutiri sannan ya gabatar da doguwar addu'a na neman tsari da taimakon Ubangiji a kan dukkanin abinda ya saka a gaba. Sai ƙarfe 2 na dare sannan ya tashi daga saman abin sallar yaje ya kwanta nutsatstsen bacci ya ɗauke shi.
******
A ɓangaren Mamy kuwa abinda Ajmal ɗin ya aikata a wurin taron ya matuƙar ɓata mata rai, daurewa kawai ta yi ta danne komai ta riƙa yaƙen dole ko don idon mutanen da ta gayyata. Amma a ranta jira kawai take yi ta samu keɓewa da shi ya mata bayanin dalilinsa na yin hakan.
Da ƙyar suka taushi Jauhar ita da Mimi aka samu aka tashi taron lafiya ba tare da tayi abinda zai janyo hankali gare ta ba, koda aka tashi basu samu damar tafiya gida tare da shi ba. Saboda ya tsaya sallamar baƙinsa.
Dole suka wuce a ranta tana ayyana cewar duk dare dai ai a gida zai kwana, dole zai zo ya same ta. Da wannan suka wuce kowa da abinda ke tsiƙarin zuciyarsa a tsakanin ita da su Mimi.
Sai dai ko da suka koma ta fara yi wa Abby ƙorafin abinda ya aikata ɗin, dakatar da ita Abby ya yi ta hanyar ce mata.
"Kin ga Mamyn yara, a gajiye nake bana buƙatar ƙorafinki a yanzu, ki ajiye shi idan yaron naki ya dawo sai ki yi masa." Daga haka ya shige ciki ya barta da takaicin sa.
Tun tana zaman jiran dawowar Ajmal ɗin har ta gaji ta tashi ta shige ita ma don kuwa bai shigo gidan ba sai dare sosai, wannan ne ya cece sa daga abinda ta tanadar masa.
★ washe gari Ajmal tun da safe ya shirya fita saboda a ranar duka ma'aikatan da suka ɗauka zasu fara aiki, hakan yasa Mamy bata samu damar yin magana da shi ba.
Saboda ko breakfast bai tsaya yi ba, iya gaisuwa kawai suka yi yace yana sauri zai wuce. Koda ta buƙaci ya tsaya ya yi breakfast ce mata ya yi zai yi a office, haka ya wuce ya barta tana mita, shi dai Abby bai tanka mata ba ya kammala breakfast ɗin sa ya wuce.
Sai ma tashi da yayi ya tafi nasa wurin aikin, ita ma harkokin gabanta ta shiga yi a waya tana duba wasu sababbin kaya da suke son yin order ɗin su daga Dubai na bikin ƴar aminiyarta da za'a yi.
*Meerah....*
Yau bacci na sha sosai kasancewar na gaji sosai da zirga-zirgar da muka yi jiya, hakan yasa tun da na yi sallar asuba na koma na kwanta.
Bacci na sha sosai wanda ban tashi ba sai ƙarfe 10 shima sai da Momy ta gaji ta tashe ni da ƙyar.
Wanka na yi na shirya na fito na yi breakfast, Dady na tambaya Momy tace.
"Ya shigo kina bacci, ki tashi kije ɓangaren Auntynku ki gaishe ta."
"Okay Momy." Na faɗa ina miƙe wa. Ɓangaren Aunty dake ta gefen dama na nufa kamar yanda Momy ta umarce ni. Babban gini ne da ya yi matuƙar tsaru wa, sai dai bai kai namu girma ba wanda muke sauka idan mun zo hutu ko wani abin da ban.
Tun farko sai da Dady ya buƙaci Momy ita ma ta koma Abujan da zama saboda ƙatoton Mansion ne mai ɗauke da part huɗu, kuma ko wanne upstairs ne. Momy ita ce bata buƙatar zuwa can ɗin ta zaɓi zama a gida kusa da Iyayensu.
Knocking na yi a bakin ƙofa na tsaya jiran azo a buɗe min, ban jima a tsaye ba mai aikinta tazo ta buɗe min.
"Bari na kira wo Hajiyar tana sama." Matashiyar budurwa da zata yi shekaru na ta faɗa cikin girmamawa.
"Okay." Kawai na bata amsa na samu wuri saman kujera na zauna ina danna wayata ina amsa chat ɗin da Zeezee ta yi min.
Kusan mintuna biyar da zama na naji sautin takun saukowar ta, kaina na ɗaga na kalle ta tana saukowa cike da ƙasaita. Taci gayu cikin wani hamshaƙin leshinta irin na matan manya tana ta baza ƙamshi.
Hajiya Asiya wato amaryar Dady da muke kira da Aunty irin matan nan ne ƴan gayu waɗan da suka san darajar kwalliya da ɗaukar wanka, duk wani abinda ya shafi harkokin siyasar Dady wanda Matarsa zata wakilce sa ita ce ke yi.
Kasancewar ta gogaggiyar Mace wacce tayi karatun boko mai zurfi, saɓanin Momy da iya secondary school tayi. Sannan ita sam harkokin siyasar basu dame ta ba, hakan yasa ko kaɗan abin baya damunta, tafi gane ta tsaya a gida ta kula da tarbiyyar yaranta.
Wuri ta samu ta zauna a saman kujerar dake facing ɗina tana kallona sannan tace.
"A'a Meerah kece a gidan namu?." Ta faɗa tana ɗan sakin fuskarta kaɗan. Ɗan zamo wa na yi ƙasa kaɗan nace.
"Eh Aunty, good morning." Na faɗa ina ɗan duƙa wa alamar girmamawa, amsa min tayi da sakin fuska haɗi da tambayar Momy.
"Tana lafiya." Na bata amsa, mai aikin ta ta kira tace tazo ta shirya min breakfast.
"No Aunty yanzu nayi breakfast." Na faɗa ina miƙe wa nayi mata sallama na koma ɓangarenmu. Sai dare Dady ya dawo daga wurin harkokinsa, tare damu yaci abinci muka yi hira sannan na haye sama na kwanta.
★ washe gari muka shirya muka koma Kano inda Momy don su Ya Sultan sun riga mu tafiya, Ya Ajmal da kansa ya kai mu airport inda yake sanar wa Momy cewar da zarar ya gama dai-daita abubuwan zai dawo Kanon.
Bayan kwana biyu na huta sosai na roƙi Momy ta bar ni naje gidan su Nawaz na duba Abbansu, da farko hana ni tayi saboda gargaɗin Dady amma da na dage da roƙonta sai ta amince ta saka driver ya kai ni bayan ta min gargaɗin kar na zauna.
Cike da farin ciki na shirya muka tafi, na samu tarba sosai an karrama ni kamar yanda aka saba yi min idan na je. Ban daɗe ba na yi musu sallama saboda gargaɗin Momy na tafi bayan na ajiye tsarabar da na je musu da ita.
***** Rayuwa taci gaba da gara wa inda Zeezee ta wuce India domin fara karatunta, domin Dad ɗinta bai amince da maganar fasawar da taje masa da ita ba.
Yayin da ni kuma Dady yace na zaɓi duk makarantar da nake so a Abuja ko nan Kano a nema min na fara nawa karatun.
A zahiri bana son barin Kano shi yasa nayi tunanin duba ɗaya daga cikin makarantun dake a nan Kano ɗin, inda zaɓina ya tsaya a BUK.
A wanan lokacin ne kuma aka sake yin magana da iyayen Aunty Amani a kan maganar aurensu ita da Yaya Sultan aka tsayar musu da rana dai-dai lokacin da zata kammala mata karatun da ta kusa ƙare wa.
A ɓangaren Ya Ajmal kuwa, aikin da ya sakosa a gaba yasa yanzu bashi da wadataccen lokaci kamar da. Domin kuwa aiki yake tuƙuru wurin gina sunan Companynsa, kuma Alhamdulillah yana samun abinda yake nema.
Wannan dalilin ne yasa baya samun lokacin zuwa Kano yanzu, ko yazo a ranar yake koma wa saboda ƙoƙarin buɗe wani sabon reshen Companyn AJMERA GLOBAL LUXURY FURNITURE'S AND ELECTRONICS LTD da zai yi a Lagos.
A ɓangaren Nawaz ma Alhamdulillah rayuwa tana zo masa da buɗi dai-dai gwargwado, sai dai tarin nauyin da yake kansa da rashin mataimaki da bashi da akwai yasa har yanzu rayuwarsu bata sauya daga yanda suke ba.
Sai dai kuma Alhamdulillah sunfi ƙarfin ci da sha da sutura, karatun ƙannensa har ma da kuɗin maganin Iyayensa guda biyu. Sannan a gefe guda yana ci gaba da ƙoƙarin ganin ya gina sunansa a duniyar waƙa, inda yake ƙara samun karɓuwa a hankali.
A ɓangaren soyayyar mu kuwa kullum ƙara gaba take yi a cikin zukatanmu, yana matuƙar kulawa da ni yana damuwa da duk wani abinda ya shafe ni.
Sannan yana iya ɗaukar duk wani shirmen da zan zo masa da shi, wanda hakan yake ƙara jefa ni a cikin kogin ƙaunar sa wacce nake jin duk duniya nafi kowace Mace sa'ar samun masoyi.
Yayin da a gefe ɗaya Momy ke jin tsoron abinda zai faru duk ranar da Dady ya gane irin alaƙar da ta yi ƙarfi a tsakaninmu, duk da irin ƙoƙarin da take yi wurin hana faruwar hakan.
Domin koda ta ƙara yi min magana a kan hakan na nuna mata cewar ina sonsa tsakani da Allah, kuma ba zan iya rabuwa da shi ba.
***** A ɓangaren Nawaz ma Ummansa ta fara tsorata da irin soyayyar da yake yi min, saboda ganin ban-bancin dake tsakanin mu wanda yake saka wa take jin tsoron a hana sa yazo ya shiga wani hali.
Wanda ko kaɗan bata fatan hakan, saboda Nawaz ɗin shine komai nasu.
***** Yau na matsa masa a kan yazo na gansa ko kuma ni naje na same sa idan yaƙi zuwa, don nayi matuƙar kewarsa. Tunda muka dawo daga Abuja bai zo gidanmu ba, sai dai kullum muyi waya.
Jin hakan da na faɗa yasa ya amince a kan zai zo da yamma, nayi farin ciki sosai naci kwalliya nayi zaman jiransa. Ita dai Momy kallona kawai take yi domin ta fahimci cewa abun nawa ba na wasa bane.
Kamar yanda ya yi min alƙawari ƙarfe 5 na yanma ya iso, bayan na masa iso ya gaishe da Momy na sauke sa a ƙarƙashin rumfar da muke huta wa. Ya Aryan ne ya dawo ya ganni da shi don haka koda ya shiga ya samu Momy da maganar ganin namu tare.
Don suma tun suna ɗaukar abin wasa har hankalinsu ya fara dawo wa kai na, domin kuwa yanayin alaƙar tamu ta fara zarce yanda suke ɗauka da farko. Zaunar da shi Momy ta yi tayi masa bayanin halin da ake ciki.
Sosai ransa ya ɓaci da jin abinda nake shirin aikatawa, hakan yasa cikin ɓacin ran da ya kasa riƙe wa yace.
"Amma lallai yarinyar nan bata da hankali Momy, ta rasa wanda zata faɗa soyayya da shi sai mawaƙi. Mawaƙin ma matsiyacin wanda ko duniya bata san da shi ba. Ai kuwa hakan ba zai yiwu ba don ba zamu ɗauki ƙanwarmu ƙwara ɗaya ƙwal mu kaita inda rayuwarta zata lalace ba. Tsiyar ka saki jiki da matsiyaci kenan, don ya san duk yanda zai yi ya shiga jikinka ya cutar da kai ta hanyar da baka yi tsammani ba. Amma in banda tsaurin ido ina gayen nan ina Meerah!." Ya ƙare maganar yana miƙe wa zai fice a fusace.
"Koma ka zauna." Momy ta dakatar da shi cikin bada umarni. Zaman ya yi kamar yanda ta buƙata, sai dai kana kallon sa zaka san cewa ransa a ɓace yake sosai.
Cikin natsuwa Momy ta kalle sa tace.
"Me kake shirin yi da ka tashi a fusacen?." Tayi masa tambayar tana tsare sa da ido. Duƙar da kai Aryan ya yi ya bata amsa da cewa.
"Zan je ne na tuna masa da matsayinsa sannan in yi masa iyaka da ƙanwata tun kafin abin ya yi nisa." Kallon tsanaki ta yi masa sannan ta sassauta da murya cikin rarrashi tace.
"Ba haka ya kamata ka yi ba, ka natsu ka jira ta shigo da kanta. In yaso sai ka zauna da ita cikin natsuwa ka fahimtar da ita." Ajiyar zuciya Aryan ya sauke ya gyaɗa mata kai don basa iya yin musu da ita.
Momy kuwa mamakin zafin zuciyar ɗan nata take yi, domin kuwa in yana wani abin yana mata yanayi da Ajmal ne, don shima haka yake da zafin zuciya sosai. Aryan da Ajmal ɗin duk Dady suka ɗauko ta ɓangaren zafin zuciyar.
A ɓangare mu ni da Nawaz kuwa hira muke yi cikin farin ciki da kwanciyar hankali yana bani labarin cewar wani kamfanin shirya fina-finan Hausa sun tuntuɓe shi a kan da yiwuwar cewar zasu iya yin aiki da shi.
Ina cikin wannan farin cikin ne aka buɗe gate da nake hangowa daga inda nake zaune saman kujera ina fuskantar Nawaz. Motocin Dady ne suka shigo suka gama parking a parking space.
Murmushi na saki a hankali na furta cewar.
"Dadyna ya dawo." Na ƙare maganar ina miƙewa tsaye, sai dai ganin wanda ya fito tare da Dadyn ya saka ni tsayawa cak daga ƙoƙarin zuwa wurin Dady da nake yi.......
Oum Fatima