Page 28
by @oumamani
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 28
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
A hankali na shiga bude idona jin kiran sallah, hannu nasa don shafa kan mimi naji wayam da sauri na bude idona.
Bin dakin da kallo nai da inda nake kwace kwalla ce ta tarar min a ido don tsaf na tuna komai.
Mike wa nai na shiga toilet sai anan na shiga bin toilet din da kallo ya hadu iya haduwa, da sauri na yi alwala jin za'a tayar da sallah, kan sallayar dana kwana na hau nau nayi sallah ban tashi ba sai da na gama azkar dina sannan na mike.
Har lokacin da ragowar bacci a idona sai na koma Kan makeken royal bed din dakin na kwanta.
Bani na tashi ba sai karfe 10 da sauri na mike ganin lokaci yaja sosai ga yunwa dake kwakwular hanji na, gadon dakin na gyara tsaf na dame sa sanna na fita don gyara part din.
Tsayawa nai cak ina bin palourn da kallo, set din kujeru ne golden colour mai hade da dining da console table sai katon show glass komai golden har curtains din palourn, juyawa nai na kalli gadon dakin naga shima set din kujerun ne kato mai dauke da babbar wardrobe da bed side drower sai tafkeken Mirrow da standing mirror shima komai golden yayi kyau har ya gaji, daga ganin set din ba sai an fada ma masu tsada ne.
A hankali na shiga tunanin Abba ne ya siya min wannan ko kuskure akai bani za'a kawo waba, kofofi 6 ne a Palourn dakin dana kwana yana daga lungu a hankali na dinga bin kofofin ina budewa ashe 4 bedrooms ne amm guda 3 ne aka sa gadaje daya katifa ce kawai a dakin, sai kofar kitchen dake gurin dinning area shiga nai naga kayan kitchen din dasu Umma suka min, murmushi nai hawaye yana sakko min don su Umma sunyi kokari sosai, store na shiga naga an cika sa da kayan abinci da drinks kuma nidai nasan ba'a mana gara na, fridge din shima a cike yake da kayan miya.
Dayar kofar kitchen din na bude Ashe bayan gidan ne gurin kamar garden yake, murmushi nai na rufe kofar na dauki tsintsiya a store na shiga share gidan, duk kuwa da ba wani datti ina gama sharewa na debo ruwa a mop bucket daki na shiga na dauko turaren Mopping da Maman Hidaya ta mana nida Aisha.
Turaren Mopping din na zuba a ruwan na shiga Mopping din ai kuwa naji kamshin sbd wani sassanyan kamshi da part dn ya dauka, ina gama mopping din na dauko freshner na fesa lumshe idona nai jin wani lafiyayan kamshin yana ratsa kofofin hanci na, turaren wuta na kunna nan danan gidan ya hade ya bada wani irin kamshi.
Daki na shiga nai wanka ina fitowa na shafa body cream dina, a gaggauce na shirya cikin lace Riga da skirt sun min kyau sosai sun dame ni, kwalli kawai nasa sai humra dana shafa na fesa turare, flat shoe na zira a kafata na fita zuwa kitchen don yunwa nake ji sosai, tea na dafa kawai a kitchen din nasha na wanke duk abinda na bata.
Palour na koma na zauna akan kujera ina kallon makekiyar TV mai curve dake zaune a kan TV stand din palourn, janyo waya ta nai na Kira Umma, sai da ta kusa katsewa sannan ta daga.
A shagwabe nace "Umma ina wuni"
Tsaki Umma tai tace "ni kike yiwa shagwaba Batul"
Kwal nai da idona cikin rawar murya nace "Umma bakiyi missing dina ba"
Haba Umma ta kama tace "yau naji shakiyanci meye haka wai ko Aisha dai baxa ta min haka na"
Turo baki nai nace "Umma ina Mimi, yaushe zata dawo nan?"
Katseni Umma tai tace "sai kin dade inji Abbanku"
Kamar zan kuka nace “Umma kiyi hakuri don Allah, a kawo ta yau"
Gyada kai Umma tai tace "eh na yadda baki da hankali Batul to ba ynxu ba"
Shiru nai sai kuma nace "Umma kayan palourn nan kamar ba nawa ba?"
Dariya Umma tai tace "Baffa ne ya Miki, Abban ku yaso ya hana amma baffa yace ai ya dauke ki matsayin jikar sa sunyi kyau koh haka su Bilkisu sukai ta Santi"
Murmushi nai zuciya ta cike da kaunar Baffa nace "Angode sosai, Umma a bawa Mimin mu gaisa."
Karba Mimi tai wacce dama tunda Umma ta fara waya taji an Kira sunan Maa dinta tayi tagumi tana kallon Umma, a shagwabe tace "Maaa"
Dariya nai nace "uhm Babyn Maa ya kk, kinyi bacci jiya?"
Daga kai tai tace "uhm Maa Umma tace kin koma gidan Daddy na da Zama wai Nima zan dawo gurin ku in banyi kuka ba, baxan yi kukan ba ai Maa"
Cike da tausayin ta nace "kar ki damu kinji Mimi na kin kusa dawowa gurina muyi ta wasan mu tare"
A darare tace "hadda daddy zamu dinga wasan?"
Hadiyar yawu nai nace "uhm hadda Shi"
Dariya tai, mun dade muna hira ina biyewa shirmen ta kafin na katse wayar, Abba na Kira shima na gaishe sa ya Kara min nasiha sosai sannan na dannawa Aisha kira.
Tana dagawa ta fashe da kuka, haba na rike nace "mun shiga uku lafia ke daga kira sai kuka"
Kara sautin kukan ta tai tace "Ya batul Ya Yusuf mugune wallahi"
Dariya na fashe da shi ina fadin "subhanallah, Aisha lafia meye na muguntar ina ke kike murna za'a miki aure kiji abinda ake ji toh meye na kuka"
Gyada kai tai tana share hawayen ta tace "bkm wallahi ya batul don na fada Miki abinda yake damuna shine zaki dinga min", ta karashe tana kara fashewa da kuka
Dariyar dake son kwace min nayi kokarin controling nace "kiyi hakuri toh Aisha kin shiga cikin ruwan zafi"
Daga kai tai tace "ya sakani amma ban Kara shiga ba ya fita ya siyo min magani"
Murmushi nai nace "kiyi hakuri kinji ki Zama mai dauriya banda ragwanta ynxu kafin ya dawo ki kara shiga ruwan xafin, ko zaki ji zafi ki daure"
Daga mun kai tai sai kuma tace "Ya Batul kece fa uwar gida kar ki barwa amarya kwanan ki wallahi don yadda naji muryar ki kamar ba'a gunki Daddyn Mimi ya kwana ba"
Hade rai nai a raina ina fadin yazo yamin ne amma sai nace mata “je kiyi abinda na fada Miki kin tsaya surutu"
Dariya ta kwalkwale dashi tace "Allah ya kaimu lokacin ki kema ya Batul muga ya zakiyi," da sauri ta kashe wayar tana dariya don tasan tsaf Zan iya zaginta..
Bin wayar nai da kallo nayi kwafa ina fadin "kin shiga gonar manya dole ki raina ni"
***********
Zeey dake zaune a Palourn ta tana sanye da kayan baccin ta ko wanka batai ba ga yawun bacci nan a fuskar ta kiran Mummy take amma bata daga ba.
Tana ajiye wayar Mummy na biyo bayan Kiran, da sauri ta dauka ta fashe da kuka, dafe kai Mummy tai tace "lafia Mene kuma"
Cikin kuka tace “Mummy bai shigo bafa jiya har 3 ina zaune a Palour ina jiran shigowar sa amma ko knocking door banji anyi na, nasan yana can gurin waccen mamar shegiar yar tasa”
Tsaki Mummy tai tace "ke kam kamar mai brain dn kifi ya kamata ace ynxu kinsan waye Azlan, in har Azlan din dana sani ne bazai shiga part din wannan shegiar ba, ni ba wannan bama wai ashe Baffa tare ya muku set din kujerun nan?"
Cikin Mamaki Zeey dake share hawayen ta tace "wani set din Mummy kar kice min na palour na"
Tsaki Mummy tai tace "komai har gadon, na dauka ke da Azlan din kawai yayi ma Ashe wai hadda ita banbancin colour ne da naki kawai nata golden, naki silver mama tace min nata ma yafi kyau kuma nata colour daya ne dana Azlan"
Kuka Zeey ta kara fashe wa dashi tace "Mummy mai yasa baffa yake min haka kamar baya sona wallahi Mummy, ni ji nake ma kamar yafi son wannan shegiar"
Ajiyar zuciya mummy ta sauke tace "ki kwantar da hankalin ki zan aiko Miki da wani turare, duk lokacin da kika san zaki hadu da Azlan ki dinga shafawa xaki mallake zuciyar sa sosai zai ma manta da waccan yar iskar"
Murmushi tai tace"yauwa Mummy na, ina sonki"
**********
Ina zaune na kunna kayan kallo naji ana bude wata kofa da dazu na gwada budewa naji a rufe, da sauri na maida hankalina kan kofar ina mamakin taya za'a bude kofar ko wani ya kwana a gidan ne.
A hankali ya shigo yana lumshe idonsa Jin wani sassanyan kamshi dake tashi a Palourn, da sauri na mike tsaye tun daga kasa nake kallon sa yana sanye da kananun kaya as usual sai bada wani fitinannan kamshi yake.
Idonsa daya sha kwalli yake kankance wa yana kallon ta ba abinda yafi daukar hankalin sa sai kirjin dinta da suka fito sosai da kuma kirjin ta Wanda yai kamar balloon aka hura, tabe bakinsa yai yana lasar lips dinsa.
Ni kuwa da sauri na shiga rufe kirjina da hannuna, kallon abinda take yai ya saki wani murmushi cike da shakiyanci yake takowa har ya iso inda take a tsakiyar palourn, tunda ga Sama har kasa yake sake kallon ta dan yatsina fuska yai yace "me kike yi anan"
Da sauri na dago na kalle sa sai dai kwallin dake idon sa yasa ni dauke kaina, bana son ganin sa da wannan kwallin, hade rai nai cikin rainin hankali kamar yadda yamin magana nace "kai Zan tambaya mai kake min a gida"
Zaro manyan idonsa yai ya zura hannayen sa a aljihun wandon sa yace "A'a lallai mai gida"
Juyar da kaina gefe nai duk a takure nake jina sbd rashin mayafi a gabansa, tabe baki yai yace "sai kawai ga Mr Wicked ya zama mijin ki"
Da sauri na kallesa, dage min gira yai yace "Uhmm ko dayake dole akai miki kamar yadda aka min koh"
Harara na watsa masa nace"Ashe madai kasan dole akai min.. " kasa karasa wa nai ganin ya matso kusa dani har muna Jin numfashin juna, baya nai ina kallon sa.
Tabe baki yai yana hade rai yace "ki kiyaye ni bana daukar raini, in kika ce zaki raina ni karya ki Zan" ya karashe yana zare min idon sa kamar Yana ma yaro warning
Nima zaro idona nai nace “kai ma kar ka raina ni don Ka ganni karama Allah"
Yunkurawa yai da karfi kamar zai kamo ni, da sauri na kwashi gudu zuwa bedroom dina ina fadin "wayyooo Allah Ummana"
Murmushi yai yana shafa gemun sa, juya wa yai ya koma ta kofar daya shigo, kofofin a Palourn sa suke daya zata Kaisa cikin palourn Batul ba tare daya fita kofar compound ba dayar kuma palourn Zeey zata Kaisa.
Ta palour Zeey din ya shiga a hankali yake bin palourn da kallo tana kwance akan kujera tana chatting ga robar lemo nan ta yar akan carpet tayi nisa da chatting din ko shigowar sa bata ji ba.
Gyaran murya yai da sauri ta mike tsaye, Dan kallon sa tai wani kaunar shi yana sake ratsa ta, hade rai yai yace "meye haka baki wanka ba?"
A dan darare tace "ynxu nake son naje nayi Yaya yunwa nake ji shine nasha lemo"
Tabe baki yai yace "baxa ki iya girki ba ko ba kayan abinci ne?"
Cikin rawar murya tace "da akwai yaya"
Gyada kai yai ya kalli agogon hannun sa yace "ba abinda kike bukata Zan fita"
Kamar zata yi kuka tace "Yaya jiya baka shigo ba kuma ko kazar amare baka siyo min ba"
Zare ido yai yace "Zainabu yaushe kika koma mayya, kaza ce baki taba Ciba da dole sai na siyo miki"
Fashewa tai da kukan bakin ciki wai zainabu, haba Azlan ya rike yace "Zainabu mai ya faru zaki sa kuka duk sbd kazar ce"
Girgiza kai tai tace "Yaya don Allah Ka daina cemin Zainabu ynxu in kishiya ta taji ai sai ta raina ni"
Dan hade rai yace "toh in ba Zainabu ba Abu kike son na dinga cewa"
Girgiza kai tai tace "Yaya toh Ka dinga cemin Zeey don Allah"
Daga kai yai yace "Shi zeey din haka dama aka rada miki ban sani ba Zainabu"
Girgiza kai kawai tai tana share hawayen ta wallahi ta manta ma Zainabu Azlan yake ce Mata sbd ta dade bata ji ya ambaci sunan taba
Ganin tayi Shiru yace "na fita sai anjima"
Bin sa da kallo tai har ya fita, fashewa da kuka tai ta dauki wayar ta ta dannawa aminiyar ta Malika waya don fada mata halin data ke ciki daga kaita gidan miji..
*******
Kallon Azlan Baffa yai yace "ango mijin Mata biyu, ya Ka baro min jikokin nawa"
Shiru ya masa yana shan kankanar sa, ganin yayi shiru yasa Baffa cewa “wai
Zaki baxa Ka daina sa wannan shegen kwallin ba naga ynxu kayi aure wane farin jini kuma kake bukata.
Kallon Baffa yai kamar baxai magana ba sai kuma yace “Baffa ai duk matan da kuka aura min ba zabi na bane, ynxu Nima zan nemo zabina nayi ta uku da ita.....”
Baki bude Baffa yake kallon sa yace...
***