Page 29
by @oumamani
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 29
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Baki bude Baffa yake kallon sa yace "ynxu mata biyu gare kafa Zaki sai Ka Kara ta uku"
Cikin tabbatar wa yace "sosai ma kuwa Baffa, ai tunda kuka fara min da biyu naji dadin haka nace toh cikashe biyun kawai zanyi nayi hudu, kaga in na tashi sai na samo guda biyu a Kara aura min su rana daya"
Kama baki Baffa yai yace "zaki Ka kuwa san mai kake fada, rike mata hudu ba abu bane na rago bane bafa"
Kankance idonsa yai yace "tsoho da kuka aura min Mata biyu baku tambaye ni ko zan iya Kula dasu ko baxan iya ba, sannan ai kaga ba laifi bane in na karo hudu ko baxan iya daukar nauyin su ba bani da fargaba tunda ina dakai"
A mamakance Baffa yace "ban gane tunda kana dani ba mai zan ma?"
Wani killer smile ya saki yace "sai Ka hado min magungunan gargajiya Wanda zai Kara min kuzari da karfi irin Wanda kuke sha a zamanin ku kaga ne ai".
Dakuwa Baffa yai masa yace "ungo nan zaki"
Dariya sosai Azlan ya saki yana lumshe idonsa, da sauri ya bude idona sbd hoton Batul dake masa yawo a kansa.
Cikin nutsuwa baffa yace "zaki Ka Kula da amanar yaran nn don Allah, ynxu nauyin su ya dawo kanka cinsu shansu suturar su lafiyar su Ka Kula don Allah sannan kayi kokarin yin adalci a tsakanin su, nasan baka da mugunta kuma kana da fahimta don Allah ka Kula"
Dan murmushi yai yace "in shaa Allah Baffa"
Ganin da Baffa yai ya nutsu yasa shi cigaba da masa nasiha....
***********
Fitowa nai daga daki ina sanye da hijab din danai sallah, karar door bell ce kawai ke tashi a Palourn tun dazu ake dannawa kuma ina sallah.
Bude kofar nai ina dan matsawa baya yadda zan bawa wanda suka zo damar shigowa, yan mata ne su biyu suka shigo za muyi sa'anni da su.
Zama sukai a kujera nima duk da ban san su amma sai na saki fuska don nasan baxai wuce yan uwan sa bane, kitchen na shiga na kawo musu ruwa da lemo, Zama nai nace "sannun ku da zuwa"
Cikin fara'a suka gaishe ni, ajiyar zuciya na sauke a raina nace suna da kirki ashe, amsa musu nai nima fuskata a sake.
Mufeeda ce tace "sunana Mufeeda, nice autar su Ya Azlan kuma nice kadai mace" ta kada tana murmushi.
Dan ware idona nai nace "ke kadai ce mace baki da sister?"
Dariya tai tace "babu sai Aunty Samira matar Ya Junaid ynxu ma gaki nn kin zama sister na"
Dariya nai nace "in shaa Allah"
Nuna ta gefen ta tai tace "wannan Zahra ce yar Uncle M kanin Abie"
Murmushi nai nace "Ashe namesake ce"
Dariya zahra tai tace "eh amma ni zahra ake cemin"
Murmushi nai nace "ni kuma Batul"
Mufeeda ce tace "amma Aunty Batul kamar na taba ganin ki a BUK"
Dan Murmushi nai nace "ina karatu can ai"
Zahra ce tace "Aunty Batul kema acan kike muma nida Mufeeda acan muke, muna karanta micro biology level 1 muke"
Cikin Jin dadin hirar da muke nace"nima level 1 nake ina karanta Architecture"
Zaro ido sukai suka kalli juna sai suka sa dariya, cikin dariya Mufeeda tace "Aunty Batul Ya Azlan yana lecturing dinku knn?"
Tuno Shi da nai sai nadan hade rai nace "uhm yana mana"
Mufeeda ce tace "tab kuma wai kuna ganewa?"
Da mamaki nace "mai meyasa baza mu gane ba, sosai ma in Ka mayar da hankali zaka gane in kuma Ka tsaya Wasa ba abinda zaka fahimta, Amma Mai yasa kika tambaye ni"
Gyada kai tai tace "ai kowa yasan Ya Azlan baya son yana koyawa mutum karatu, haushi yake ji sosai shiyasa nake taso na samu daya daga cikin students dinsa na tambaye su wai suna ganewa"
Dariya nai nace"ai kuwa sai na fada masa"
Xaro ido tai tace "don Allah kiyi hakuri wasa nake yi"
Dariya kawai na Mata nace "Nima wasa nake miki"
Basket din dake gefenta ta kalla tace "Mun manta mun tsaya hira, Aunty Batul ga abinci inji Mami tace a kawo muku"
Mikewa nai na karbi Basket din nace "angode sosai kuwa, mu biyu ne?
Girgiza min kai Mufeeda tai tace "A'a Banda Ya Zeey itama mun kai mata"
Murmushi nai nace "angode," kitchen na nufa ina maimaita sunan Zeey knn Zainab sunan kishiyar tawa, tabe baki kawai nai.
Bayan na dawo daga kitchen din na karbi numbern Mami da Mama da Abie da Baffa, sai Aunty Sarah maman Zahra, a gurin na kira Mami cikin mutuntawa muka gaisa sai sunkuyar da kai nake don haka kurn naji wani irin kunyar ta ta rufe ni, a nan take fada min za'a kawo min Mai aiki wacce zata dinga taya ni aiki.
Godia nai Mata sannan mukai sallama, mun sha hira sosai tare muka ci abincin da Mami ta kawo, sai wajen 6 suka tashi tafiya.
Kitchen na shiga na wanke flask din Mami, kai wa palour nai na ajiye daki na shiga na dauki pose dita 5k na dauka a ciki sannan na sa musu turare a ciki.
Fitowa nai na mika musu, godia suka min sosai.
Zahra ce ta kalli Mufeeda tace "zamu shiga gurin Ya Zeey ne muyi mata sallama"
Tabe baki Mufeeda tai tace "wallahi ba inda zani, kyaleta taji da wulakancin ta"
Nidai ban tanka musu ba har na rakasu, daga kofar palour na rakasu ban fita ba.
Bayan tafiyar su duk sai naji ni wani iri, Zama nai na kunna zee world don an saita komai, ina son kallon india amma a gida kuma bana kalla don Umma bata bari kasancewa in har zamuyi kallo tare muke kalla gaba daya har dasu Kamal.
Bayan Isha'i ragowar abincin da mami ta kawo naci na wanke kayan dana bata, wanka nai nasa doguwar rigar bacci iya gwiwa, humra na shafa na fesa turare Mai sassanyan kamshi, hula na dora akaina na fito Palour hannuna rike da wayata..
Turus naja na tsaya ganin sa tsaye sanye da jallabiya mai gajeran hannu yayi kyau sosai kuma fuskar sa tayi fresh alamun daga wanka ya fito
Diricewa nai sai janyo rigata nake ina rufe kafata duk da ba abinda take rufewar, ga kuma gaban rigar Kai v.
Murmushi Azlan yai yana shafa gemun sa sai kallon ta yake.
Turo baki nai cikin tsiwa nace "ni Ka daina kallona"
Shafa kirjin sa yai yace "ki same ni ynxu a part dina, ta kofar nn zaki shigo"
Zaro ido nai nace "Mai zan yima?"
Kankance idonsa yai yace "mai mata take yiwa miji a irin wannan lokacin?"
Gaba nane ya buga da karfi amma na kasa magana.
Juyawa yai yace "kizo ynxun nan bana son maimaita magana"
Bin bayansa da ido nai har ya fita, kamar kar na je sai dai kuma ina tunanin illar hakan.
Cikin sanyin jiki na koma daki hijab dina nasa sai na samu kaina da sake fesa turare, a hankali na nufi kofar dayake shigowa na murda na shiga palourn..
***