TASWIRAR KADDARA

Page 30

by @oumamani

*TASWIRAR KADDARA*



 DijahAM(Oum Amani)





Page 30


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM





   Kamshin freshner ne ya doki hanci na, lumshe ido nai na shiga bin palourn da kallo yaji furnitures masu kyau da tsada, ajiyar zuciya na sauke na samu guri na zauna aka kujera a darare.



       Zainab na zaune sanye da rigar bacci iya gwiwa mai kamar net ko bra babu a jikinta, rigar ta fallasa surar ta ko ina a, gabanta plate din abinci ne da ta gama ci tun dazu amma ta kasa dauke plate din sbd son jiki.



Da sallama Azlan ya shigo, da sauri ta dago ta kalle sa mikewa tai tana wani turo shafaffen kirjin ta kamar na wacce ta fara kirgan dangi, sai wani kwarkwasa take yi.



Dan gajeran murmushin Azlan yai yace "kizo part dina ynxu"



Daga haka ya juya y fita, tsalle ta buga tana wani turo kirji sai da ta shafa turaren da Mummy ta aiko mata dashi sannan ta nufi kofar daya fita.



Cikin yanga ta shiga bakinta dauke da sallama, dagowa nai muka hada ido da ita a tare gabanmu ya buga amma sai nai saurin dauke kaina ba tare da ko murmushi nayi Mata ba don na ga kalar kallon da take min da kuma shigar ta.



A bangaren Zeey ma wani irin bacin rai ne ya bayyana a fuskar ta har ta kasa boyewe, Zama tai a kujerar dake nesa dani tana wani harare Harare.

Ko kallon ta ban ba don tsaf na bawa banxa ajiyar ta Wanda hakan ba karamin kona Mata rai yai ba.



Mun kusa 10 minutes a zaune sannan Azlan ya fito hannun sa rike da robar ruwa, Zama yai a kujerar dake kallon tamu gaba daya, sai da ya dan jingina bayansa da kujerar sannan yai sallama.



Amsa mishi mukai dukkan mu, nidai kaina yana kasa ina wasa da hannu na.



Addu'a ya farayi tukun sannan yace "na taraku ne anan sbd rashin damar hakan da ban samu yiba jiya, fatan zaku hade kanku don bana son hayaniya kamar yadda kuma kuka sani dukkan ku nan zabin Baffa ne don haka in na samu zabina zan iya auro ta koda gobe ne".



Dagowa nai da sauri na kalle sa ganin ya kalle ni ne yasa na juyar da kaina ina turo baki, murmushi yai sannan yace "kamar yadda yake a addini ana yiwa budurwa sati a dakin ta haka Nima zanyi ke Batul kece uwar gida daga kanki zan fara yau insha Allah, in kin gama satin ki sai kema zainabu nai miki sati daga nan kuma sai a koma kwana biyu biyu haka nake da ra'ayi ko da akwai Wanda hakan bai masa ba"



Shiru nai ina maimaita maganar sa knn raba mana kwana yai.



Ganin nayi shiru yasa Zeey da ta cika tai fam sbd takaici cikin Iyayi tace "hakan yayi Yaya"



Gyada kai yai yace "sannan duk mai girki ita zata dinga gyara min bangare na da Kula da abinci na, bana wasa da cikina shiyasa nake fada muku tun ynxu, kowaccen ku tana da kofar da zata sada ta da part dina a cikin palourn ta don haka basai ta fita ba, in kuma bake ce da girki ba Zan kulle Miki kofar ta yadda baxa ki iya shigowa ba sai dai ni nazo na same ki, fatan hakan duk ya muku"



Wannan karan ma Zeey ce ta amsa shi, kallon zainab yai yace “sai da safe zaki iya tafiya"



Kamar zata fashe da kuka ta mike tana jin zuciyar ta na tafarfasa, part dinta ta wuce hawaye na zubo Mata.



Kallona yai yace "zaki iya tafiya kema in kuma a dakina kike son kwana baki da damuwa"



Da sauri na kalle sa nace "yaushe nace zan kwana a dakin Ka?"



Kafada ya daga yace "alamu na gani, tunda gashi kinki tashi kina zaune"



Kamar zanyi kuka nace "kaine fa baka cemin na tashi ba"



Idonsa nakan TV yace "ynxu na baki dama in kina so ki koma part dinki ki kwana ni dama ban Saba kwana da mace ba a daki daya".



Harara na maka masa nace "Nima ai ban saba kwana da namiji ba"



Kallona yai da idonsa da suka shanye sai lumshe su yake, wani Abu naji yana yawo a gaba daya sassan jikina hakan yasa na mike da sauri ina turo baki nace "sai da safe"



Gyada kai kawai yai ya juya yana kallo.



Ina zuwa daki hijab dina na cire na shiga toilet nai alwala, kwanciya nai akan gado bayan nayi addu'a tunani na fada akan zeey wacce take kishiya ta yadda take harara ta da yadda take wani iyayi yasa ni Jan tsaki, haka kawai naji tana bani haushi.



Ganin tunanin zai Jani zuwa wani wajen yasa na rufe idona ina karanta suratul mulk har bacci ya dauke ni.





Washe gari da safe bayan na idar da sallah dan gyara part din nawa nai sama sama don baiyi datti ba, ina gamawa na dauki tsintsiya da mop da rag na nufi part din oga.



Shiru yake ko ina fitilu a kashe da kyar na samu makunnar na kunna, share palourn nai na goge sosai kitchen din na shiga ba kayan tarkace daga gas sai kettle da microwave ko ina tsaf, gyara shi nai na fito kofofi biyu ne Wanda nake tunanin dakuna ne kuma yana cikin daya knn, kofar da ta kusa da dining na bude ba kowa aciki hakan yasa ni saurin gyarawa na fito.



Ban yi gigin shiga dayan ba na bar sa kawai anjima in na tabbatar ya fita sai na gyara.



Komawa part dina nai a gaggauce na shiga kitchen tea na dafa na soya dankali sai kwai dana soya masa, dibar masa nai a flask nawa kuma nasa plate, ajiye basket din dana sa miki nai akan dining na shiga wanka.



Ban dade ba na fito sai kamshi sabulun wanka nake mai dadi, Zama nai na shafa body cream din shima sannan nabi jikina da humrar mai sanyi da dadin kamshi.



Ganin 9 yasa na zira doguwar riga ta atampa, light make up nai na fesa turare sannan na janyo hijab nasa, daukar basket din nai bayan na dauki turaren wuta da fresher na tafi dasu part din.



A dinning na jera masa flask din, show glass din palourn na bude dake dauke da set din plates da cups da jugs, plate da cup na dauko masa na ajiye a akan dining din.



Turare na kunna a burner sannan na koma part dina, abinci naci na koshi na koma bacci daki.



*******
Haka har akai sati daya kuma yau Zan fita girki knn, ji na nake cikin farin ciki don dama duk a takure nake gashi gobe zamu koma makarant ma.



Cikin satin ba abinda yake hada mu dashi sai gaisuwa, kullum zan masa breakfast da dinner kuma Zan shiga part dinsa na gyara masa na bade masa shi da turaren wuta, ynxu ma haka ina kitchen sanye da Riga da skirt da suka kamani sun min kyau sosai, jallof din taliya nake dafawa yar daidai tunda baxan yi abincin dare da shi ba na fita  duty na, kuma a iya sani na baya dawowa da wuri.



Na gama ina wanke tukunyar data baci kamar a mafarki naji muryar Mimi tana cewa "Maa kina ina gani nan"



Da sauri na fito hannuna da ruwa sbd son tabbatar wa, ai kuwa ina zuwa tsakiyar palourn na ganta tana sanye da doguwar riga ware ido nai nace "Mimi ta"



A guje ta taho ta rungume ni tana ihu, Nima rungume ta nai ina lumshe idona nayi kewar ta sosai.



Dago ta nai nace "yaushe kika zo waye ya kawo ki"



Dariya tai tace "Daddy nane ya dauko ni, yace ynxu na dawo nan da Zama shiknn kullum zan dinga ganin ku"



Daga kai nai na kalle sa Yana tsaye ya rungume hannu yana kallon mu, fuska ta dauke da murmushi nace "Umma ta yadda ka kawo min ita"



Lumshe idonsa yai yace "gashi kuwa kin gani, mai kika dafa ne nake Jin kamshi"



Turo baki nai nace "nawa ne ni kadai fa ai na fita daga girki yau"



Kallon agogon sa yai yace "baki fita ba tukun don Magriba batai ba"



Sauke Mimi nai na shiga kitchen daura plate din nai akan tray na sa masa fork sai ruwa da glass cup dana sa mishi, a zaune na same sa a kan dinning ya daura Mimi akan dinning din tana game a wayar sa.



Ajiye masa tray din nai, bai ki kalle ni ba ya janyo ya fara ci bakinsa dauke da bismillah, yarinyar ta bata sa da taste din abincin ta da kallon wacce bata iya komai yake mata ba amma tuni ya daina mata wannn kallon, kullum bangaren sa kamshi yake gashi ko ina tsaf ga kuma abinci lafiyayye tana basa, shidai a jikinsa yana jin har kiba ya Kara.



Ina zaune daga kan kujera ina Kallonsa shida Mimi sai surutu take masa yana biye mata Yana bata abincin a baki, kallon katuwar akwatin Mimi nai janta nai zuwa dayan dakin dake kusa da nawa.



Sbd kar na koma palourn yasa na shiga gyara mata kayan a wardrobe, kasancewar kayan a ninke suke nan da nan na gama.



Murmushi nai ina jina cikin nutsuwa sbd zuwan Mimi, fito wa nai har lokacin suna zaune akan dining sai dai sun gama cin abincin, plate din na dauka nakai kitchen na wanke.



Ina fitowa na gansa a tsaye yana yiwa Mimi magana, kallona yai yace "Zan wuce amma ku shirya gab da magrib kamar 6 zamu je gida ku gaida su Mami"



Daga kai nai nace "Allah ya kaimu, sai Ka dawo Allah ya kiyaye".



Daga kai yai yana amsawa a ransa, sai da ya shafa kan Mimi  sannan ya fita.





***