BABI NA HAMSIN DA UKU
by @zainabb
Zaren Rayuwar Mu
AN: Ban fa fara rubutun nan domin sa Hadiza ta mutu ba, lol. Ba ma kuga Hadiza ce ke bada labarin su ba, kaɗan ne keda point of view na Zaid, slightly small. Se kuma inda take cikin ciwo ko wani abu me girma se nasa ayi magana a point of view na third person. Idan ma mutuwa za'a yi, ai se de Zaid 😂. I'm kidding by the way.
ZAID NE YASA obstetric team rikicewa suka yi kan Hadiza amma ga monitor nan na nuna numfashin ta. Doctor na kai hannun shi a pulse ɗin ta ya ɗaura idanun shi a monitor. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke ganin har yanzu monitor na nan be ɗauke ba.
“Tana numfashi ba suma tayi ba” Doctor yace se anan ne obstetric team suka tsaya daga masu yin sigh of relief se masu zama tiredly “She's still breathing” Doctor yace hannun shi na kan pulse na Hadiza “She's asleep because of exhaustion and labour stress”
Zaid be san abinda yake ji cikin ranshi ba amma saura kaɗan ya fara kuka amma ya danne.
“We'll move her out of this room” Doctor yace tare da dafa kafaɗar Zaid ya ƙara ce “Congratulations. Your wife and your baby are alive and healthy”
Fita aka yi aka amso kayan baby daga wurin su Yaya Hauwa, nan ake musu albishir da an ciro baby girl.
“Ma Sha Allah Barakallah” Mummy tace da farin ciki a fuskar ta
“Alhamdulillah. Mahaifiyar fa?”
“Itama lafiya tana bacci ta gaji”
“Bacci kuma?” Mummy ta faɗa
“Ta gaji ne. Kin san ta jima tana labour Mummy”
Gyaɗa kai Mummy tayi. Yaya Hauwa tayi dialling number Umman Hadiza. Bata jima da fara ringing ba aka ɗauka. Gaisawa suka fara yi tukunna Hauwa tace “Hadiza ta samu baby girl Umma. Amma tana ciki ba'a fito da ita ba tukun, cs aka mata”
“Allah sarki Hadiza! Ma sha Allah, Allah ya raya baby. Wannan ƙawa na samu kenan. Allah ya raya ta. Gobe zamu shigo in sha Allah. Allah ya raya”
“Amin Amin Umma”
Zaid ne ya fito tare da baby an gyara ta an sa mata kaya. Idanun ta rufe hannuwan ta haɗe ana ganin sumar kanta a gefe biyu. Hancin ta tsaye koda da jarirantakar ta. Zaid yana tafiya yana kallon ta, zuciyar shi ta cika. Wani gefe farin ciki ne na samun baby girl albarkar da Allah ya basu a cikin auren su, wani gefe kuma tsoro yake ji yafi so yaga idanun Hadiza buɗe koda surutun banza ne tayi.
Shahida ta fara amsar baby tana ta kallon ta da murmushi akan fuskar ta. “A beautiful baby girl indeed”
Khalil ya amsa baby daga hannun Shahida shima kallon ta yake ya kalla Zaid ya kalla baby ya dawo ya kalla Yayan su Muhammad ya kalla baby ya kalla Hauwa ya kuma kalla Shahida. “Na kasa gane da wa take kama. Se naga Yaya Hadiza tukunna”
“Kaga hanci ya fito tun tana baby kasan hancin ƴan gidanmu ne”
Murmushi Mummy da Yaya Hauwa suka yi. Ana ta bada baby kowa na gani.
Mazan aka kira su a chanjawa Hadiza gado se an ɗauke ta. Zuwa suka yi su uku aka cira Hadiza daga gadon da take aka maida ta wani na cikin ɗaki. Jikin ta an rufe shi fuskar ta kaɗai ake gani har yanzu idanun ta a rufe tana bacci. Har jin numfashin ta ake idan aka shiga ɗakin da take kwance. Zaid na tsaye cikin ɗakin yayi folding hannuwan shi a kirjin shi yana kallon Hadiza. Ganin yanda take numfashi ne yasa ya dawo kusa da ita sosai ya taɓa goshinta ya kuma riƙe hannun ta yana jin yanda temperaturen jikinta ya canja zuwa ga zafi kaɗan. Nurse dake cikin ɗakin ya kalla yace “Ba haka take numfashi ba. Ba zaki kira Doctor ya duba ta ba?”
“No, don't worry about that. She's okay”
“I insist you call a doctor please”
Tsayawa Nurse tayi tana kallon Zaid kafin ta wuce ta kira Doctor. Tare suka dawo yana gaba tana bayan shi.
“She is breathing heavily and it's not how she used to breath. I'm just worried”
Duk da doctor yasan lafiyan Hadiza ƙalau gajiya ce kawai da labour stress amma be cewa Zaid haka ba. Duba ta yayi da duka vitals nata, bayan ya gama ya dafa kafaɗar Zaid yace “Lafiyar ta ƙalau Zaid. Kar ka damu. Gajiya ce ta mata yawa da labour stress kaga ta jima tana labour kafin aka mata cs, kar ka damu. Zata tashi in sha Allah”
Nodding Kai Zaid yayi yayi wa Doctor godiya ya tafi.
Hadiza bata tashi daga bacci ba se ƙarfe huɗu ana batun fara kiraye-kirayen Sallah Fajr. Idanunta ta buɗe ahankali tana kallon surrounding ɗin ta. A private room take daga ita se Yaya Hauwa da Shahida ne a ciki. Daidai lokacin da ta buɗe idanun ta tashin Yaya Hauwa kenan. Tasowa Yaya Hauwa tayi daga inda take ta dawo gefen Hadiza.
“Hadiza” Yaya Hauwa tace
“Yaya” shine abinda Hadiza tace muryar ta bata fitowa, nan take hawaye suka fara fitowa a idanun ta
“To kuma kukan menene Hadiza? Ba an haihu an gama ba? Ko ciwo kike ji? A ina ne?” Yaya Hauwa ta jerowa Hadiza tambayoyi.
Sau ɗaya Hadiza ta girgiza kai hawayen da take basu dena zubowa ba.
Hannu Yaya Hauwa tasa tana sharewa Hadiza hawaye tace “Your baby is sleeping.”
“Har yanzu ina jin gajiya baccin be ishe ni ba”
“Saboda kin gaji ne. Baccin zaki koma kodai na kira Nurse?”
“A kira Nurse”
Anan call button Yaya Hauwa tayi notifying nursing station. Bada jimawa ba se ga nurses sun zo.
“Hadiza is awake” ɗayan Nurse tace tare da yin murmushi. Murmushi sauran suka yi suka fara taimakawa Hadiza wurin sponge bath anan. Tayi changing daga hospital gown zuwa kayan ta. Da taimakon su Hadiza tayi tafiya from one end to the other to avoid blood clot se kuma ta dawo ta zauna.
“Har yanzu ba'a yi breastfeeding baby ba ko?” Shahida da itama ta tashi tace eh. Amsar baby nurse tayi tana kallon ta idanun ta rufe amma bakin ta motsi yake alaman yunwa dai.
“The baby is hungry. Let's help you breastfeed her”
Wata ajiyar zuciya Hadiza ta sauke. Yaya Hauwa na tsaye tana kallon su suna aikin su. Duk abinda suke yiwa Hadiza zata iya mata amma de ta bar su suyi aikinsu.
Pillows suka ɗaura wa Hadiza kar wurin aikin ta ya samu matsala aka bata baby. Da taimakon su suka nuna mata yadda zata riƙe baby ta fara shayar da ita. Tunda ta fara shayar da babyn ta tasan breastfeeding is not for her bari dai ta samu sauƙi ta koma gida zata san yadda zata yi. Hadiza kallon baby take yi idanunta a rufe but she's sucking. Tana sanye da hula amma ana ganin suma a gefen kanta. Motsa ƙafafuwan ta tayi da hannuwa Hadiza na cigaba da kallon ta. Yaya Hauwa tace “Wannan kallon Hadiza! Ko dai zaki maida ta ciki ne?”
Kunya Hadiza taji tayi murmushi tasan ko me za'a bata a duniya ba zata so ta maida babyn ta ciki ba. Tana dai kallon ta ne tana admiring ɗin ta ta biyo mahaifin ta da dangin shi. Har ƙafafuwan ta ma irin na Zaid.
Bayan ta gama shayar da ita ne Yaya Hauwa ta amsa baby Hadiza ta kwanta. Dad'i take ji har yanzu bata ji baby ta fara kuka ba.
“Har yanzu gajiyar nan bata cire a jiki na ba”
“Wani baccin zaki koma? Bari ki ci abinci tukunna”
“Idan baccin yazo zanyi idan aka kawo abincin se a tada ni”
“Okay. Yanzu bari na tafi da baby inda Mummy ayi mata wanka. Kafin a gama wankan zan dawo miki da abinci” Hauwa ta faɗa ta kalla Shahida tace “Shahida, ki bari na dawo se ki tafi gida ki huta”
“Okay Yaya se kin dawo. Allah ya tsare”
“Yawwa Amin”
Nurse Yaya Hauwa ta faɗa wa zata je da baby gida ayi wanka tukuna ta fita.
Yaya Hauwa na isa gida dama gari ya waye ta haɗu da Abba. Shi dai Abba yaga ta fito a mota daga ita se baby yana mamakin wanda ya riƙe mata baby har tayi driving.
“Hauwa tare da waye kike?”
Kallon motar ta tayi ta dawo da kallon ta ga Abba tace “Abba Barka da safiya”
“Yawwa Barka. Kun tashi lafiya? Ya jikin Hadizar?”
“Alhamdulillah da sauƙi Abba. Ga baby, Abba” Hauwa tace tare da miƙa wa Abba baby ya amsa yana kallon ta “Ma sha Allah. Ma sha Allah. Wannan ƴar Zaid ce?! Ma sha Allah”
Murmushi Hadiza tayi jin abinda Abba yace.
“Allah ya raya Ya ba Maman ta lafiya”
“Amin Abba”
“Wanka za'a yi ne?”
“Eh Abba”
“Ina tambayar ki ko ke kike riƙe da baby kuma kina tuƙi?”
“Eh, Abba” Hauwa ta faɗa tasan tayi kuskure amma babu wanda ze dawo da ita gida ne shiyasa ba za'a bar Hadiza ita kaɗai ba.
“Za'a yi haka kuwa Hauwa? Ya zaki ɗauko baby kuma kina driving? Da duk wane hannu kika yi waɗannan aikin? Kar na sake ji ko gani. Kina ji ko?”
Gyaɗa kai Hauwa tayi.
“Ki shiga ciki kar a sake dai”
“In sha Allah Abba, nagode” Hauwa tace ta amsa baby hannun Abba ta wuce ciki.
A ciki dama Mummy tasan da zuwan ta already an haɗa ruwan wankan yarinya har breakfast na asibiti duk an haɗa. Amsar baby Mummy tayi ana mata wanka ita kuma Hauwa ta koma asibitin da abincin Hadiza. Shahida se da taci abinci tukunna ta wuce gida.
Hadiza na shan tea Zaid yayi sallama. Ganin ta a yadda ya ganta yasa yaji wani sanyi a zuciyar shi.
“Matar subsea engineer in all of her glory”
Wani kallo Hadiza tayi wa Zaid na wasa tace “Wane glory kuma? Glory a haka?”
Murmushi yayi ya zauna a gefen ta. Yaya Hauwa ce ta dawo cikin ɗakin riƙe da flask “Yaya. Barka da safiya. Mun tashi lafiya?”
“Alhamdulillah Zaid. Kaga Hadiza ko?”
“Shine nake cewa she's in all of her glory but she's not taking it”
Murmushi Yaya Hauwa tayi ya maida duban shi ga Hadiza. “How are you?”
“Not good”
“Not good?” yace yana kallon ta “Na ga yankan” yace tare da ɗaga rigar ta yana kallon inda aka yi yanka aka fidda baby anyi incising wurin . Zaid rasa abin faɗa yayi kuma be rufe wurin ba ya dai kalla fuskar Hadiza. Shi dai yasan tunda aka ce jinin ta ya hau da duk wahalar da tayi a labour room da cs da yaga ana mata, yasan wannan lokacin ne yasa yake ƙara jin ta a cikin ranshi. Tausayin ta da yake ji ya ƙara ƙaruwa , ƙaunar da yake mata ya ƙaru yana jin kamar ana rurawa a cikin zuciyar shi.
“We're sorry” Zaid yace yana kallon Hadiza cikin idanu.
Murmushi tayi ta kauda idanun ta ba tace mishi komai ba.
“Yaron nan ba zaka ma tambaya baby ba ganin Hadiza ta tashi ko?”
“Inaso na tambaya yanzu Yaya. Nasan tana kusa” yace yana kallon ɗakin amma be gan ta ba
“Se bayan har se da na roƙa kake tambaya”
“Yaya dan Allah kiyi haƙuri. Tana cikin raina”
“Aa yanzu dai idan an kawo baby da ita zan je gida na samu new baby”
Murmushi Zaid yayi itama Hadiza har yanzu murmushi be ɗauke akan fuskar ta ba.
Tashi Zaid yayi yana kallon Hadiza. “Me kike so na dawo miki dashi?” ya faɗa tare da kallon agogon hannun shi takwas da rabi tayi.
“Komai ka dawo dashi”
“Harda kan ɗan mutum?” Zaid yace.
Wani irin kallo Hadiza ta yiwa Zaid inda lafiya take da ta watsa mishi pillow. Hadiza tace “Harda kanka ka biyo dashi”
Murmushi Zaid yayi sosai tukuna yayi wa Yaya Hauwa sallama ya fita.
A chan ShopRite ya haɗu da Khalifa dama sunyi magana. Shiga suka yi suka yi siyayya dama abinda yasa be tafi dasu lokacin da yaje basu fito bane ɗazu. Kama daga ruwan gora ne, Yoghurt, hollandia, toiletries, kayan tea da duk wasu abubuwa da zasu buƙata a asibiti. Tare da Khalifa suka koma asibitin, Khalifa na shigowa da kayan. Hadiza lokacin na bacci. Yaya Hauwa har yanzu tana nan, Mummy itama ta taho, itace riƙe da baby.
“Zaid da ka faɗa min kaya zaka siyo. Babu baby wipes se ka siyo kuma ka ƙaro da pampers”
“Okay bari mu tafi mu kawo”
Tare da Khalifa suka ƙara fita. Sun siyo kayan da Yaya Hauwa tace suka dawo. Anan ne Mummy ke ce mata taje gida ta huta. Yaya Hauwa ta ƙara spending wasu ƴan mintuna a asibitin kafin ta wuce.
Khalifa ya wuce shi kuma Zaid be tafi ba yana nan. Hadiza ce ta farka daga baccin ta. Ganin yayi tana neman support tashin ta daga baccin. A wurin ta ya matso ya riƙe hannun ta “Ya akayi, Hadiza?”
“Juwa nake gani. Kaina ke min ciwo ina ganin ka bibbiyu”
“Juwa da ciwon kai? Hawan jinin nan ne a kira Doctor Zaid” Mummy tace tare da tashi tsaye ta dawo wurin Hadiza.
Nursing station yayi notifying se ga Nurse ɗaya ta shigo. Anan ne yake faɗa mata abinda Hadiza ke ji. Fitowa Nurse tayi taje ta faɗawa Doctor.
Shigowa ɗakin Hadiza Doctor yayi da kanshi ya auna bpn ta shine har yanzu be yi saukar da ake so ba.
“Hadiza!” doctor yace “Ba gashi an haihu ba? Me kike sawa a cikin ranki? Dan Allah ki kwantar da hankalin ki kinji?”
Zaid na riƙe da ɗayan hannunta yana kallon ta cikin damuwa.
Tambayoyi doctor yayi wa Hadiza tana bashi amsa. Ya duba abdominal tenderness nata da vaginal bleeding da incision site nata. Bayan ya gama dubawa aka mata allura through IV. Bayan sun gama Hadiza ta kwanta a gado ta rufe idanun ta. Mummy dama ta fita lokacin da Doctorn ya shigo. Zaid ya zauna gefen Hadiza “Wani bacci zaki yi?”
Girgiza mishi kai tayi “Akwai abinda nake yi wanda baki so? Zan dena”
Murmushi tayi ta girgiza mishi kai ya cigaba da kallon ta. “Me kike so yanzu?”
“Ba komai”
“Idan na fita, na dawo haka nan ba da komai ba?”
Juyawa Hadiza tayi ta ba Zaid baya tace “Ka dawo min da kanka”
Kallon bayan ta yake ya ɗan jima yana kallon ta kafin ya fita.