BA NI DA MADOGARA

Chapter 27

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*











*Ba ni da Madogara*
  (Sai Allah...)




 




   

027


Sosai Hujayrah ta koɗa Mami sai faman ɗadɗaga kai take ita ala dole ta yi kyau kamar yadda Hujayrah ta ce, nan da nan Mami ta washe guraguran haƙoranta wanda basu fi a ƙirga ba ta ce

"Yawwa Hujuryata, dukansu makiyana ne, ke kaɗai ce mai sona"

Murmushi Hujayrah ta yi mata tare da riƙe hannunta har cikin falon ta zaunar da ita a kujera, Allah ya gani Hujayrah na jin ƴar tsohuwar nan a ranta, kallon Kakullenta take kamar ita ce ta zo gareta, kamar yadda Kakullenta keda daru haka Mami take dashi sai dai sun ɗan bambanta, ita Kakullenta bata da budurwar zuciya irin ta Mami, wanka ma a sati sau ɗaya take yi, balle a kai da ƙunshi da kitso wannan ta daɗe da sallamawa,sabon ɗinki idan a yi mata irin na zamani ta yi ta faɗa tana cewa ba za ta saka, sai an lallaɓata kafin ta saka kayan, idan ma ta saka kayan ba a tsira ba don ta dinga mita tana cewa an yi mata ɗinkin yara, ita kuwa Mami komanta na yara ne musamman ƴan mata, abubuwan zamani yana matuƙar birgeta. Bayan sun zauna sai Hujayrah ta sake dubanta da murmushi ta ce

"Kakulleta me za ki ci yanzu"

"A'a jikalleta har yanzu akwai sauran ɓirɓishin abincin da na ci ɗazu, Kinsan ban je masai ba balle na zazzage" Mami ta ce tana bin sauran ƴan ɗakin da mugun kallo irin za ku sani. 

"To ai shikenan, idan kin zazzage sauran in kina buƙatar wani abincin sai kimin magana na dafa miki" cewar Hujayrah. 

"Mami amma kin dawo nan da zama ne ko" cewar Nazima don ta ji amsarta, tasan ba ƙaunar zama Nijeriya take ba. 

Ɗan waro ido Mami ta yi tana faɗin

"Ni Asiyatu, Ina ni ina zaman Nijeriya wannan sai ku da Allah ya jarabceku da zamanta, da zarar Mubinatu ta samu sauƙi zan tattara ƴan komatsaina na koma ƙasata, ko bikin yayanku bazan tsaya a yi dani ba. " 

"Haba dai Mami, ai dole ki tsaya a yi miki dannar ƙirji, da alama kishi kike da budurwar Ya Arqam" cewar Nazima tana ƙunshe dariyarta. 

Yatsina fuska Mami ta yi tare da taɓe baki irin ko a jikinta ɗin nan, bata so  amsa mata ba sai kuma can mai ta gani ta ce

"Kishi tab! , ai sai dai ku yi wa yarinyar dannar ƙirji bani ba, mijina kafin ya rasu ni kaɗai ce ƙwallin-ƙwal, har ya mutu yana tsananin so da ƙaunata, nasan koda nike tsohuwa nafi yarinyar kyau" 

"Wannan haka yayi Kakulleta kifinta kyau koda kika tsufa" 

Shiru ɗakin ya yi kamar mutuwa ta  gitta, Arqam na can side ɗin falon yana aiki a system ɗinsa ga files nan ya warware, yanason zuwa Germany amma rashin lafiyar Ammiensa ta hanashi lafiya. Akwai wasu muhimman abubuwan da yake so ya yi a can Germany wanda suka fi ƙarfin Bilal, dole ta system yake aikin dare da rana. A cikin falon Mami ta katse shurin da cewa

"Wai ni kuwa wani kalan magani aka yi wa Mubinatu ne? Na asibiti ne ko kuwa na gargajiya" 

Razina ta caɓe da cewa

"Maganin aljanu ake yi mata" 

Waro ido Mami ta yi tare da sakin baki tana kallon Razina, sosai ta shiga tashin hankali, a can Niger da Alhaji ya kira yaronta, ya ce Hajiya momma na cikin matsanancin ciwo amma bai faɗi kalan ciwon da ya sameta ba. Sauke sassanyar ajiyar zuciya Mami ta yi sannan ta ce

"Ni Asiyatu aljanu ne a jikin Mubinatu! Muhammadu ɗan Abdullahi, ya aka yi ta samu aljanu" 

Razina mai bakin surutu, ai kamar jira take Mami ta tambaueta, nan da nan da sanar mata da abin da ke damun Ammiensa, har da ƙurajen da suka feso mata. Mamaki da tashin hankali lokaci guda suka ziyarce Mami, salati haɗi da salallami ta hau yi tana tafi. Can ta ce

"Yanzu wani malami ke bata maganin" 

"Ƙawarki ne Hujayrah malamar" cewar Nazima 

Juyowa ta yi gun Hujayrah ta ce

"Au Hujurya ke ce malamar, Ashe kina bada maganin aljanu, nima wani lokacin nakan ji gurnanin zaki a a cikin kunnuwa ƙila su ne" 

Murmushi Hujayrah ta yi ba tare da ta ce komai ba.Nazima da Halima a  gidan za su kwana da yake Hajiya Nafisa ta ce sai zuwa gobe za ta fito, idan ta zo za su wuce baki ɗaya. Kiran Halima aka yi a waya tana kallon screen ɗin wayar ta saki murmushi ta miƙe ta fita. Mahmoud ne ya kirata, tun lokacin da ta zo garin basu haɗu ba saboda an turashi aiki sannan ba yanzu zai dawo ba, shi yasa idan ya ɗan samu lokaci sai ya kira su yi waya cikin nishaɗi da kwanciyar hankali, wani lokacin har video call suke yi da yake Prof ya canja mata Waya zuwa Samsung mai tsada. Ta jima tana waya daga bisani ta koma cikin falon lokacin su Hujayrah na cikin bedroom ɗin Hajiya momma sun je dubata, sosai sauƙi ke samuwa sai dai har yanzu bata fara  magana ba sai kallo.Sun jima a ɗakin daga bisani suka fito, Alhaji sai cikin dare ya dawo lokacin har Mami ta koma masaukinta ta yi bacci, Hujayrah da Razina ne a falon suna kallo bayan sun kunna wa Hajiya momma suratul Baqara, shiga bedroom ɗinta ya yi ya dubata sannan ya fito zuwa part ɗinsa, ya so gaisawa da Mami amma ta yi bacci, sai zuwa gobe ya zo su gaisa, Arqam  ya sake shigowa ya duba Ammiensa sannan ya koma part ɗinsa ya kwanta. 


*Washe gari da safe*
*Ƙarfe 10:30amma safe*

A daidai wannan lokacin Hajiyan Sama da su Fauziyya suka a shigo part ɗin Hajiya momma dubata, da sallama a bisa labɓansu suka shigo ciki lokacin su Hujayrah na falon bayan sun karya kumallo. Amsa musu sallama su Nazima suka yi, Hujayrah ko kallon inda suke bata yi ba, cike da girmamawa Hajiyan Sama ta gaida Mami tare da tambayar ya mai jiki, su Fauziyya ma haka, fuskar Mami ɗauke da murmushi ta amsa musu. Basu daɗe da zama ba Alhaji ya shigo falon da sallama, wuri ya samu ya zauna tare da gaisawa da Mami. Shiru ɗaki ya yi sai can Alhaji ya dubi Hujayrah ta ce

"Hujayrah Ammienki za ta iya fitowa koda falon ne ta zauna, zaman uwar ɗakan babu daɗi ita kaɗai" 

"Eh Abbu babu damuwa, Nima yau nake tunanin ya dace ta fara fitowa falo ta zauna" cewar Hujayrah tana miƙewa. 

"Nazima ku je su taimaka wa Hujayrah ku fito da Ammienku" 

Babu musu Halima da Nazima suka miƙe tare da bin bayan Hujayrah. Wani mugun kallo irin na tsananin ƙiyayya Hajiyan Sama ke jifan Hujayrah, a cikin ɗakin babu wanda ya lura da hakan sai Mami, sosai mamaki ya cikata har ta so tambayar Hajiyan sama wani kalan kallo ne haka, mai ta gani sai kuma da fasa amma ta ayya a ranta sai ta tambayi Hujayrah ko ta yi wa Hajiyan Sama laifi ne yasa take mata irin wannan kallon tsana. 

A hankali suka taimakawa Hajiya momma ta fito daga bedroom ɗinta kai tsaye suka zaunar da ita a saman three sitter saboda ta ji daɗin zaman. Da ido take bin kowa a falon ba tare da ta ce dasu komai ba. Bakinta kamar an manna masa Selotape. Ba a yi mintuna ashirin da fitowan Hajiya momma  falo, Hajiya Ramla ta shigo Tahseen na biye da ita  hannunta riƙe da leather fara babba, ɗauke da kayan marmari na marasa lafiya. Mami da Hujayrah na zaune a kujera ɗaya, Nazima da Halima suna saman carpet, Razina kuwa ta daɗe a school da ya ke sun kusa fara exams. Hajiyan Sama na zaune a one sitter, su Fauziyya sun yi manage a one sitter. Bakinsu Hajiya Ramlat ɗauke da sallama sua shigo ciki, Mami na haɗa ido da Tahseen,ta tsira mata idanu tare da sakin baki ta ce

"Ni Asiyatu me za gani haka, har da ahlul kitab a cikin masu zuwa gaida Mubina, Allah ɗaya gari bamban" 

Tana maganar tana kallon Tahseen, shiga ce wacce ta bayyana surar jikinta, gashi ta ƙwama tabarau baƙi sai taunar chewing gum take yana bada sauti Ƙas! Ƙas!. Abun nema ya samu da sauri Hujayrah ta matso kusa da Mami tana mata raɗa a kunne. 

"Tohhhhh babbar maganar!" cewar Mami tana jinjina kai. 

"Hmmmm ai Nima Kakulle na yi ta jinjina maganar, don akwai ruɗu" cewar Hujayrah tana taɓe baki. Da ciwo a ce. Don auran Arqam da Tahseen yana matuƙar bata mamaki, kamar makafi basu ganin gaskiya. Koda bata zauna da Arqam ba tasan baya ɗaya daga cikin watsattsun mutane marasa kamun kai. Tahseen daga ganinta ko ba a faɗa maka ba kasan watsattsiya ce ta ajin ƙarshe, ga rashin kamun kai da natsuwa. Yafuto Hujayrah Mami ta yi tare da yi mata nuni ta matso da kunnanta, kamar jira Hujayrah take Mami ta umurceta, da sauri ta matso da kunnanta cikin ƙasa da murya Mami ta ce

"Sha kuruminki Hujurya bazan bari Qamqam ya auri wannan ahlul kitabin ba,da Mubinatu ta samu sauƙi zan wargaza auran, a da na ce zan koma Niger idan Mubinatu ta samu sauƙi, amma yanzu na fasa ina nan daram dam kujerar tsakar gida, sai an fasa auran sannan zan bar Nijeriya, inaaa! "

Da ƙarfi ta ƙarshe zancen hakan yasa ƴan ɗakin juyowa suna kallonta. Yatsina fuska ta yi sannan ta ce

" Nifa abin da na tsana a rayuwata shi ne kallo, to namana da ɗaci "

Murmushi Alhaji ya yi yasan kaɗan daga cikin aikin Mami ne faɗi haka. Hujayrah da Nazima har da Halima kuwa murmushi suka yi. Kusa da Hajiya momma Tahseen ta je tere da gaidata a tsaye ba tare da ta duƙa ba. Tsawa Mami ta daka mata mai ƙarfi duk da tsufanta amma tsabar jarabar da ke cinta sai da ta ɗaga murya wanda kowa a falon ya ji. Tahseen sai da ta waiwayo ta ga shegen da ya daka mata tsawa. 

"A gidan ubanki haka ake gaida mara lafiya! Nace a gidan ubanki haka kike gaida iyayenki!!! mara tarbiyya!!! ce niƙe ɗanta za ki aura!!! a haka ake girmama suruka!!! amma idan haka surukan zamani suke Allah ya wadaranku!!!" cewar Mami tana miƙewa tsaye tare da riƙe ƙugunta kamar mai shirin faɗa. Sai kumfam baki take tana ware manyan idanunta farare tar! Duk da ta tsufa amma idanun nan nata suna nan da haskensu. 

Daɗi kasheni inji Hajiyan sama a ranta, sosai Mami ta birgeta, ta ji daɗi da Mami ta yi wa Tahseen wankin babban bargo, da alama Mami za ta kasance makaminta, tasan idan Mami tasan Tahseen ce Arqam zai aura bazata taɓa yarda da auran ba. Bata jin Hajiya momma da Alhaji duk maganar Mami za su bi don kowa shakkar masifarta yake, idan ta fara faɗa bata gajiya sai ta kwana ta hantse tana mitar abu ɗaya. Gyara zama Hajiyan Sama ta yi don ta ji daɗin ƙara gishiri da suga ta ce

"Ai Mami yaran zamanin yanzu sai a hankali, haka suke da banzar ɗabi'a musamman waɗanda aka sangarta. Duk da haka akwai ƴaƴan ƙwarai irin albarkha masu daraja iyayansu da waɗanda suke sama da..." 

"Ya isheki annaminiya kanwa uwar gami! To ahir ɗinki wallahi! Idan kika ce za ki shiga abin da bai shafeki ba to wahala za ki sha! Ta ci darajar tsufanta shiyasa bazan ɗauki mummunan mataki akanta ba, amma da wani ne ya yi wa ɗiyata cin mutunci irin haka da kuliya manta sabo zan kaisa " cewar Hajiya Ramla tana miƙewa. 

" Ramla ya isa haka, bai dace kuna tare da mara lafiya kuna hatsaniya ba kamar yara! Haba don Allah " faɗin Alhaji a ɗan zafafe. 

Tahseen ta ƙulu iya ƙuluwa, idanunta sun cicciko da ƙwalla amma hawayen sun ƙi zuba, juyawa kawai ta yi ta bar ɗakin, Hajiya Ramla ta bita da sauri. Suna fita Hajiyan Sama ta saki lallausan murmushi mai ƙayatarwa, dole ta shiga jikin Mami don ta samu haƙarta ta cimma ruwa. Alamu sun nuna nasara na gefensu duba da yadda Mami ta amsa wa su Fauziyya gaisuwa cike da fara'ah. 

"Hmmmm ai ina da magana da ku Imrana, jira nake Mubinatu da samu sauƙi na zauna da ku" cewar Mami tana karkaɗa ƙaga. 

"To Mami Allah ya Bata lafiya ya nuna mana lokacin" 

"Ameen dai amma akwai ƙura" cewar Mami. 

Miƙewa Hajiyan Sama ta yi ita da yaranta suka bar ɗakin,  Fauziyya  durƙusawa ta yi har ƙasa tana yi wa Mami sun tafi. (A'ahhh su Fauziyya ana so a samu shiga wurin Mami 😂😂😂 to ki yi haƙuri Hujayrah ce ontop🤭🤭🤭🤭)  

Bayan Tahseen ta fito kai tsaye ta wuce garden ɗin gidan, kujerar garden ɗin ta samu ta zauna sai a sannan wasu zafafan hawaye suka fara gangarowa daga gurbin idanunta. Tunda uwarta ta haifeta babu wanda ya taɓa mata faɗa ko tozarci irin wanda Mami ta yi mata. Ko mintuna uku bata yi da zama ba Hajiya Ramla ta iso wurinta, kusa da ita ta zauna tare da rungumota tana shafa mata baya. Rushewa da kuka Tahseen ta yi tana faɗin 

"Mom I hate her! ta yarfani a gaban mutane" 

Cike da tausayi Hajiya Ramla ta ce

"Yi shiru daddy's princess da sauƙi tunda Arqam baya nan, Kin ga ai bai san da hakan ba" 

Cikin kuka Tahseen ta ce

"Mom za ta hana Arqam  ya aureni! Baki ga Fauziyya sai dariya take min ba, bazan kwana a gidan nan ba" 

Still hannunta na bayan Tahseen tana shafawa ta ce

"Tahseen" 

Tashi Tahseen ta yi daga ƙirjin Hajiya Ramla tana share hawayanta ta ɗago kanta ba tare da ta ce komai ba. Gyara zama Hajiya Ramla ta yi tare da gyaran murya sannan ta ce 

"Tahseen abin da nake so da ke yanzu shi ne, duk wani ragontaka ba naki ba ne, duk wani fushi da zuciya ba naki ba ne. Ki dage ki siye zuciyan Mami, ki yi haƙuri da faɗanta don tun ba yau ba nasan halin Mami, tana da faɗa amma tana da saurin sauka. My Angel I want you to become your own hero, duk faɗan da Mami za ta yi miki kamar yadda na faɗa miki jiya, ki toshe kunnanki sannan ki bata haƙuri, domin Yaya da Hajiya momma suna jin maganar Mami sosai. Yaya ya ɗauki Mami a matsayin uwarsa, duk abin da ta faɗa shi yake bi.All I want you to do now is to ignore her harshness and be friendly to her"

Shiru Tahseen ta yi tana sauraron mahaifiyarta, sosai ta gamsu da zantukanta don Tahseen akwai raunin zuciya, cikin ƙanƙanin lokaci zaka shawo kanta da daɗaɗan kalamai. Cike da raunin murya Tahseen ta ce

"Mom I will try to be nice to her, but but Mom a gaban kowa ta yi embracing ɗina fa, and also tana da faɗa, gashi a yadda nake gani Hujayrah is her friend" 

Juya idanunta Hajiya Ramla ta yi tare da ƙanƙancesu tana nazarin maganar Tahseen, tabbas a yadda taga Hujayrah da Mami a zaune a kujera ɗaya hakan yana nuni da suna ɗasawa. Dole tasa yadda ta yi Tahseen ta shiga jikin Mami domin ita ce makaminsu, idan Tahseen ta fara shiri da Mami to komai yanzu zai zo musu cikin sauƙi. Ɗan nisa wa Hajiya Ramla ta yi sannan ta ce

"I know Tahseen but you have to try, Kin ga Hajiyan Sama tana so Fauziyya ta auri Arqam, shiyasa ɗazu take sakin maganganu don Mami ta ce baki da kunya, amma ni nasan ƴata mai tarbiyya ce, yanzu mu koma ciki sannan ki bawa Mami haƙuri, kamar yadda ta ce ki duƙa wurin gaida Hajiya momma just do it kawai sannan ki canja dressing code ɗinki a gidan nan kin ji"

" OK Mom, zan yi iya ƙoƙarina naga Mami tana sona, kome ta ce na yi zan yi "

Cike da jin daɗi Hajiya Ramla ta rungume ƴarta  ta ce

" Yawwa my little Angel, shiyasa nake sonki kina da saurin fahimta, yanzu tashi mu koma ciki ki ba Mami haƙuri sannan ki gaida Hajiya momma"

Babu musu ta miƙe tare da gyara zaman jakanta ta ce

"Mom duk saboda Arqam ne zan yi wannan abubuwan" 

"I know my gurl shima idan yaga haka sai ji daɗi ya koma yana sonki, who knows kiga ya zo zance gunki" Hajiya Ramla ta faɗa taan miƙewa itama. 

Ƙayattacan murmushi Tahseen ta saki har fararan haƙoran na bayyana ta ce

"Mom da har party saina shirya saboda farin ciki, I really really love Yaa Arqam with all my heart, Ina sonsa sosai Mom" 

Ɗan murmushi Hajiya Ramla ta yi tana tausayawa ɗiyarta soyayyar data faɗa, bata ce da ita komai ba suka koma part ɗin Hajiya momma. 

Bayan fitarsu Arqam ya shigo falon tare da wani bodyguard ɗinsa, sanye yake cikin baƙar suit, ya yi kyau sosai ya riƙe Tab da wayarsa. Bodyguard ɗin ya riƙe briefcase da laptop ɗin Arqam ya tsaya a bayansa. Bayan ya gaida kowa sai ya samu wuri ya zauna yana kallon Alhaji ya ce

"Abba zan yi tafiya zuwa Kano, daga can zan shiga jahohin da business ɗina suke zan kwana uku a can, saboda rashin lafiyar Ammie ne yasa bazan tafi Germany, although Bilal da sauran manyan ma'aikata na suna can, I prefer going myself" 

Ɗan nisa wa Alhaji ya yi sannan ya ce

"That's good is better ka je kaga How your business is moving, Sannan ya batun ginin company da ka ce ana kan yi, ka je ka duba kuwa?" 

"Aa Abba ana min video ɗin ginin, idan na dawo daga tafiya zan samu time na je ba duba ginin" Arqam ya faɗa yana miƙewa 

"Allah ya taimaka ya bada nasara ya kuma tsare hanya" cewar Alhaji. Mami ma da sauran ƴan ɗakin sun yi masa addu'a. 

"Allah ya kaika lafiya Yaa Raqam qam, ya dawo mana dakai lafiya ya kuma bada sa a" 

Har ya zo tafiya Hujayrah ta yi masa addu'ar, cak! Ya tsaya tare da waiwayowa suka haɗa ido, ɗan lumshesu ya yi tare da buɗesu akanta, sassayan murmushi ya sakar mata, a can ƙasa maƙoshi ya furta

"Ameen ya Rahman" yana faɗin haka ya juya ya fita, bodyguard yabi bayansa. 

Babu wanda bai yi mamakin Arqam ba har da Alhaji, don a idon kowa Arqam ya yi reacting sannan babu wanda ya amsa masa sai Hujayrah, sannan yadda ya amsa mata ya saka zuciyar kowa kokwanto a cikin ɗakin musamman Mami, a ranta tana faɗin ' kodai Hujuryata Qamqam ke so ba wannan yarinyar ba, don yadda yake murmushi hakan ya nuna akwai abu a ƙasa, kai Qam qam na son Hujuryata, don ƙwayar idanunsa sun nuna tsantsan so da ƙaunar Hujuryata' lallausan murmushi ta saki tana addu'a Allah yasa hakan ne, idan hakan ta tabbata tafi kowa farin ciki don tana son Hujayrah sosai jinya take kamar jikarta. Mantuwa Arqam ya yi a part ɗinsa, kai tsaye ya nufi part ɗinsa. Hajiya Ramla ta Tahseen sun shanyo kwana Arqam na shiga part ɗinsa, sai basu ga  gilmawan Arqam da bodyguard ɗinsa ba har suka shiga falon Hajiya momma. Ko mintuna uku Arqam bai yi a part ɗinsa ba ya fito shida bodyguard ɗinsa suka wuce. Kai tsaye ya shiga tsadaddiyar motarsa mai lumfashi suka bar gidan. Motoci uku ne suka jeru, ta tsakiyar ce Arqam ke ciki. 

A cikin gida da sallama Tahseen da Hajiya Ramla suka shiga cikin falon, Tahseen ce a gaba Hajiya Ramla na biye da ita, kai tsaye Tahseen ta je har inda Mami take ta durƙusa kanta a ƙasa ta ce

"Mami I'm so sorry for what I did..." 

"Dakata ƴar ahlul kitabi, Ni bana jin yaranku, Kimin magana ta harshen da zan fahimta ba yaran Yahudawa ba" 

Shiruuuu! Tahseen ta yi har Mami ta ƙaraci maganarta ta yi shiru, sosai ran Tahseen ya ɓaci amma ta dake taƙi nunawa tuno da nasihar da mominta ta yi mata. Cikin sanyin murya Tahseen ta ce

"Ki yi haƙuri Mami bazan sake ba" 

Kallon ƙasa da zama Mami ta yi ma Tahseen sannan ta ce

"Ya wuce" daga haka bata ce da ita komai ba, wani killing smile Hujayrah ta saki lokacin da suka haɗa ido da Tahseen tare da ɗaga mata gira irin How fa ɗin nan. Tsammm! Tahseen ta miƙe zuwa wurin Hajiya momma da ke zaune kamar mutum mutumi ba um ba um-um, durƙusawa ta yi har ƙasa sannan ta ce

"Ammie ya jiki, Allah ya baki lafiya, ya tashi kafaɗunki" 

Alhaji da su Nazima suka amsa mata sai ta Miƙe. Hajiya Ramla na kallon yadda Mami ta taɓe baki, a ranta tana faɗin 'Za ki gane kuranki tsohuwar kilaki,bari dai ki zo hannun ubanki zanci, hegiya'  

"Yaya ya mai jiki" cewar Hajiya Ramla ta duban Alhaji. 

"Jiki Alhamdulillah Ramla, sauƙi na ta samuwa baki ga babu ƙuraje ko ɗaya a jikinta ba" 

"Haka ake so ai, Ni bari na tashi, gidan Yaya Ayyub zani" Tana maganar ta miƙe zuwa waje, Tahseen ta biyota a baya, daga can Tahseen ta wuce masauki ta ta yi kwanciyarta. Bayan fitarsu Tahseen Alhaji ya fito zuwa sashensa don yau yana hutu. Nazima da Halima suka wuce gida da yake tun safe Hajiya Nafisa ta kirasu akan su dawo gida bata jin daɗin jikinta. Mami, Hujayrah da Hajiya momma suka rage a falon, tun safe Razina ta wuce school. Hira ta ɓarke tsakanin Mami da Hujayrah kamar su daɗe da sanin junansu... ✍️

                🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangaren Hajiyan sama suna isa falon sama kowanne a cikinsu ya kwashe da dariya kamar wasu taɓabɓu,Fauziyya har da duƙawa tsabar dariya tana riƙe ciki. Wuri Hajiyan sama ta zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana jin ta a sama. Saman carpet su Fauziyya suka yada zango Still suna dariyar ƙata, sun jima a haka daga bisani Hajiyan sama ta yi gyaran murya ta ce

"Alhamdulillahi yau ina cikin farin ciki mara misaltuwa, ji nike kamar har an ɗaura miki aure keda Arqam, Nazima da Khalil, don da alamu muke da nasara" 

"Allah yasa Mom, Allah ya amsa addu'arki, da kuwa na yi murna sosai har ina taka rawa da tsalle." cewar Fauziyya tana murmushi. 

"Allah yasa Aunty Fauziyya" Zahriyya ta faɗa taan murna. 

Suna tsaka da farin ciki Khalil ya shigo falon bakinta ɗauke da sallama. Kallon kowannansu ya yi da  mamaki lulluɓe a fuskarsa, kujerar da ke kusa da Hajiyan sama ya zauna yana bin kowannansu da kallo. 

"Khalil lafiya kake bin mu da kallo kamar wani tsohon maye" 

Ɗan Murmushi ya yi sannan ya ce

"Mom ban saba ganinku in this kind of situation ba ne, kowa is happy , Kamar an yi muku wani  albishir babba " 

"Ai Khalil wannan yafi albishir a wurina, yanzu dai ba wannan ba tunda ka zo to sai a yi maganar da kai, daman ina so na samu lokaci muzanta" 

Gyara zama ya yi tare da maida hankalinsa kacokar a kanta. Sai data ɗan nisa sannan ta fara magana

"Khalil maganar auranka ne da Nazima sai kuma Arqam da Fauziyya,nasan kai tun farko baka wani ra'ayin Nazima, ko kana yi yanzu?" 

Shiru ya yi ba tare da yace komai, shi dai tsakakinsa da Allah ba wani son Nazima yake ba don yana da budurwarsa ƴar Japan, yasan ba zai ma fara tuntuɓar  Hajiya sama da zancen Mu doek , ƴar japan ce a can suka haɗu, tana masifar son shi don har cewa take za ta zo Nijeriya saboda shi, sannan ya yi mata alƙawarin zai aureta idan mahaifiyarshi ta yarda. Hajiyan Sama ita ce komanta don tun yana ɗan shekara biyar mahaifansa suka rasu a sanadin hatsarin mota wanda shi da driver ne kawai suka rayu. Tun lokacin yake hannun Hajiyan sama, ya yi makaranta mai tsada tun daga primary har secondary sannan ya tafi Spain Karatun architecture Wato ɓangaren zane-zane, bayan ya dawo Nijeriya ya yi bautar ƙasa sai ya tafi Japan yin degree ɗinsa na biyu wanda a can ya haɗu da sahibarsa Mudoek. Cikin ransa yake faɗin 'Mom ita ce komai na dole na faranta mata kamar yadda a kullum take faranta min rai, dole n haƙura da Mudoek na so wacce Mom ɗina take so' 

"Khalil ya dai! ka yi shiru kabarni da tagumi zaman jiran amsarka, har yanzu baka ra'ayin Nazima" 

Firgigit! Ya dawo cikin hankalinsa, ɗan sosa kai ya yi sannan ya ce

"Mom idan har auran Nazima shi ne farin cikinki, to ina sonta kuma zan aura" 

(A'aah my Esteem fans ana shagali a gidan nan, wato dai idan na fahimta Hajiyan sama ta gama yarda ita za ta yi nasara, tunda ta samu Mami a matsayin makamin shikenan baya da sauran matsala 😂😂😂🤭🤭🤭karku manta Hajiya Ramla da uwar gayya Tahseen suma hakan yake a wurinsu, Mami ce makaminsu, ƙaƙaƙara-ƙaƙa wai ƙura a ƙasa, Ni da Esteem fans ɗin ƴan kallo ne🔥🔥🔥🔥😂😂😂😂💃💃💃💃🤭🤭🤭🤭) 

Daɗi sosai Hajiyan Sama ta ji a ranta, duk da tasan ba wani son Nazima yake ba amma saboda ta yi farin ciki ya amince da auran. Cike da farin ciki ta ce


"To ai shikenan, yanzu dai ka yi amfani da salonka ka sace zuciyar Nazima, sannan akwai wata tsohuwa a part ɗin Hajiya momma, Ina so kullum ka dinga shiga gaidata tare da gabatar da kanka, sannan Hajiya momma ba ka dinga dubata, nasan da wuya kaje dubata Khalil"

"Hakane gaskiya ban je ba, Kin san ba shiri nake da Arqam ba so ni bana son raini, I don't tolerate rubbish" Khalil ya ce yana ɓata fuska. 

"Ina ruwanka dashi kai da za ka gaida tsohuwa da mara lafiya, ka yi harkar gabanka shima ya yi harkar gabansa, yanzu dai zuwa can anjima ko gobe ka je ka gaidasu sannan ka fallasa kanka a gun Nazima, Don Bana don a ɗauki tsawan lokaci" 

Jinjina mata kai ya yi sannan ya miƙe yabar falon rai ɓace. Yana barin falon Hajiyan Sama ta juyo kan Fauziyya, magana ta fara mata akan yadda zata ja hankalin Arqam ta hanyar rangwaɗa da kisisina da kuma yadda zata yi Mami ta sota. Sai faman ɗaga kai Fauziyya take kamar wata ƙadangaruwa. Duka kalaman Hajiyan sama tana ajiyesu daki-daki a ƙwaƙwalwarta. Sun daɗe suna hira daga bisani su Fauziyya suka komai ɗakinsu don Hajiya Zinatu ta kira Hajiyan Sama ta hanya. 


            🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*ƙarfe 12:13pm na rana*

A daidai wannan lokacin motar Hajiya Zinatu ta yi parking a parking space, da sauri ta fito daga motar buguzum-buguzum da ita kama wata motsattsa sai faman sauri take, da alama ko wanka bata yi ba, kai tsaye ta wuce sama inda Hajiyan sa'a take. Babu sallama ta shiga, Hajiyan Sama na zaune taan kallon Tv hankalin kwance ta ji muryar Hajiya Zinatu cikin kuka tana faɗin

"Aminiya Nadiya ta kasheni! Nadiya ta kasheni I! Na mutu na lalace ni Zinatu!" 

Cikin hanzari Hajiyan Sama ta miƙe zuwa wuri Hajiya Zinatu wacce take duƙe ta dafe ƙirjinta, hawaye na mata zirya a bisa kuncinta. Cike da tashin hankali Hajiyan sama ta ɗagota tare da taimaka mata ta zauna saman kujera sannan ta ce

" Aminiya don girman Allah kibar kukan! Haba don Allah kamar wacce aka aikowa mutuwa" 

"Ai da mutuwar aka aikomin da ban damu haka ba! Aminiya da  bazan shiga tashin hankali kamar wanda nake ciki a yanzu ba! Aminiya ciki da Nadiya keda shi a jikinta!" Hajiya Zinatu ta ce tana sake rushewa da sabon kuka mai tsuma rai. 

"Duk ba wannan ba Aminiya, Kin tambayeta wa ya yi mata cikin?" Hajiyan Sama ta faɗa tana gyara zamanta. 

Murmushin takaici Hajiya Zinatu tana kallon sama hawaye na zuba a idanunta, duk ta faɗa kamar wacce ta yi masassarar sati ɗaga, idanunta sun kumbura sun ja. Majina ta share da hanki ɗinta sannan ta ce.... ✍️




*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***