Chapter 47
by @barista
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover)
Page 47 end of book 1
Sayyada barrister
YOTA 13
The five ink legends
A hankali ta lumshe idanunta kunya ta rufe ta, jin abin da ya yi mata, ta sanya tafin hannayenta ta rufe fuskar ta, murmushi sosai ya yi yana kallonta, ya kurawa yatsun hannunta idanu tsira da su sanye da zoben da ya sanya mata a lokacin da zai koma Nigeria. Zane ɗankwalin kanta ya yi, bakin gashin ta ya bayyana, sai sheƙi yake yi, ya yi luf saboda gyara, ya sanya hannu yana shafa wa a hankali, ya sauke numfashi tana ji ya zame ribon da aka tufke gashin da shi, jin haka yasa Angel sauke numfashi ta cire hannayenta daga fuskar ta, ta kurawa wuyan Dr Waahab kallo, ganin yawan gashin kanta ya sa ya yi mamaki ya ce
"Wannan gashin ki ne ko ciko?"
Ta ɗago suna kallon junansu ta ce
"Ba ciko bane"
Yana kallon cikin ƙwayar idanunta, yana hango son da take yi masa kwance cikin su, yana kare mata kallo tabbas ya yi dacen irin matar da yake so, Angel kyakkyawa ce kuma ajin farko, yana son mace me kunya, dabi'unta sake burge shi take yi ya shafa gashin a hankali ya furta
"Fatabarakallahu ahsanulkhaliqeen"
Ta fahimci ma'anar ayar, ta sudda kai ƙasa jin yana yi mata wasu abubuwan yasa jikinta rawa ya ɗago da fuskarta ganin idanunta sun ciko da ƙwalla yasa ya maida mata ɗankwali tare da cewa
"Da ɗan'uwana na taho"
Ta ɗaura ribon ɗin tare da ɗaura ɗankwalin ta ce
"Yana ina?"
"Dandalin da muke zama mu yi hira"
Ta yi murmushi a hankali ta ce
"Me yasa bai shigo ba?"
"Yana waya ne a lokacin"
"To"
Ta faɗa ya sake janyota kusa da shi baya so ta tafi, wayarsa ta yi ringing ya duba Dr Faisal ne kamar ba zai ɗauka ba, ya ɗauka zai yi magana Dr Faisal ya ce
"Sir cike da girmamawa na ce baka kyauta ba"
"Da na yi me?"
"Na ji labarin kana Ghana, da ka sanar da ni tare za mu taho"
"Eh ba shiri na taho MD kawai na sanarwa, ayi min afuwa"
"Ba komai ko na taho ne, na yi kewar abincin ALAJA SPECIAL RESTAURANT"
Murmushi Angel ta yi, shi ma ya yi murmushi tare da cewa
"Na yi aure"
"Don't tell me Sir! Da wannan yarinyar?"
"Eh yanzu haka muna tare"
"Shege sir wallahi ka burge ni"
"Shege kuma Faisal"
"Yi hakuri duk a cikin farin ciki ne, wannan kuna dawowa zan kai Beb su gaisa"
"To ba damuwa, sai ka kashe wayar don yau ango nake"
Dariya Dr Faisal ya yi ya ce
"Shi kenan ka shigo wasu, wato ka maida min magana"
Su ka yi dariya, Dr Faisal ya kashe wayar, Dr Waahab ya mik'e tare da riƙe hannunta ya ce
"Mu je ku gaisa"
Ta ce
"To zan faɗawa ALAJA"
"Ok ba damuwa ina ba kin ƙofar fita"
Ya fito ita kuma ta shigo wajen ALAJA, tare da cewa
"Maa"
ALAJA ta ɗago daga lissafin da ta ke yi ta ce
"Har ya tafi?"
"A'a ya ce na yi masa rakiya sai mu gaisa da ɗan'uwansa"
"A ina"
"Yana waje"
"Ungo naki Angel, na ce ba kin zama matarsa ba, nan da wajen ne sai kin taho ki sanar dani"
"Wai kada ki neme ni ne?"
"Na yi miki uwar me? Kina tare da mijinki"
"To"
Ta faɗa ALAJA cike da ɓacin rai ta ce
"Ke bari na faɗa miki ki buɗe idanunki ki san yadda za ki kula da mijin ki ko so kike yi ni zan din ga faɗa miki abubuwan da za ki yi?"
"A'a Maa"
"To ku je ku gaisa sai ki dawo"
"To Maa"
Ta fito jiki a sanyaye, ALAJA ba a iya mata, ta tadda Yallaɓai likita yana tsaye ganinta yasa ya miƙa mata hannu alamar ki sanya nata hannun, ta matso a hankali ta sanya hannunta ta rike sosai suka fito, suna taku ɗaiɗai yana yi mata hira, sai abin ya baiwa su Zee Dollers da Sadeebaby da sauran matan da suke zaune sha'awa, Zee Dollers ta ce
"Na rantse mijin aure zan nemo na gaji da ƴan iska mara kan gado"
Sadeebaby ta sheƙa da dariya ta ce
"Kin ga wani kallon love abin ba a cewa komai, ni har mamaki nake yi Angel ta yi aure"
"Ke ina faɗa miki kina gani kamar wasa, ni ma za ki ji Malliman ya ɗaura min aure"
Sadeebaby ta ce
"To da waye?"
"Da koma waye"
"Allah ya sa ba da me bakin sigari ba"
"God forbid! Me zan yi da shi"
Da yake yana zaune sai busa sigari yake yi yana jin hirar su jin abin da Zee Dollers ta ce ya sa ya tanka mata
"Ni ma me zan yi dake"
Ta juyo jin amsar da ya bata ta ce
"Wallahi ƙarya kake, ba za ka taɓa samun kamata ba"
Dariya ya yi sosai ya zuƙi sigari ya busar da hayaƙi ya ce
"Ragowar garada kawai, irin ki ma dubu ake samu, ni fa handsome man dani"
"Sunan wata dabba kunkuru, kin ji in wai handsome man, ba ki ya yi baki saboda shan sigari"
"Ai ni sigari kawai na ke sha, bana...
"To mayu za ku fara shegen faɗan ku da bai ƙarewa"
Cewar wani mutumin da yake zaune, sai jefawa juna magana suke yi....
*****
Dr Waahab suka iso suka tadda Sa'eed yana waya, ya zaunar da Angel kan dakali, tare da cewa
"Ki zauna kada ƙafafunki su gaji"
Murmushi ta yi, ya zauna kusa da ita, ya riƙe hannunta suna hira, Sa'eed ya kurawa Dr Waahab idanu murmushi ya yi tun da suke bai taɓa ganin ɗan'uwansa yana cikin farin ciki ba irin na yau, ya kashe wayar ya kalli Angel tare da cewa
"Amarya da ango masu kama da juna"
Cike da kunya ta ce
"Ina wuni"
"Lafiya kalau matar Yaya"
Murmushi Dr Waahab ya yi, Sa'eed ya ce
"Na yi tunanin ka manta da ni"
"Kamar ko ka sani gaba ɗaya na manta da kai"
Su ka yi dariya, Sa'eed yana ta yabon ɗan'uwansa wajen Angel, tana sake ganin Yallaɓai likita da kima, ganin yadda yan'uwansa ke sonsa, ba ƙaramin ɗan gata bane da har iyayensa suka taso daga nesa su ka zo neman aurenta. Ba za ta taɓa manta wannan mutunta ta da Yallaɓai likita ya yi mata ba
"Mon Ange mu ɗan fita sai na dawo dake"
Ya mik'e ita ma ta tashi tsaye, Sa'eed ya ce
"Ina kuma za a tafi a bar ni?"
"Ta shi mu tafi siyayya"
Ya mik'e suka iso bakin titi, Dr Waahab ya tare mashin guda biyu, a tunanin Sa'eed za su hau ɗaya su biyu amarya ma ta hau ɗaya sai yaga akasin haka, shi ya gau tare da riƙe hannunta ya yi mata nuni da ta hau ta zauna a bayansa, shi yana sakiya don bai so jikin Angel ya taɓa na me mashin, Sa'eed ya ce
"Amma tare muka taho a mashin"
"Kishi kake yi?"
Cewar Dr Waahab, Sa'eed ya ce
"Eh mana an kwace min aboki"
Su ka yi dariya, Dr Waahab ya zagaye cikin sa da hannayen Ange ya ce ta riƙe shi sosai kada ta faɗi, haka ko aka yi har suka tafi shopping, siyayya su ka yi kamar babu gobe, texi suka hau ya kawo su Tumbin Giwa, har side na su Bilqees Dr Waahab da Sa'eed suka shigo da kayan ciye-ciyen, a verender su Bilqees suka ajiye, Mamata ta ji motsi ta ce
"Waye ne?"
"Mama mu ne"
Ta ji muryar Bilqees, Mamanta ta yafa mayafi ta fito, kasancewar dare ina take tsaye babu haske, sai sai in da Yallaɓai likita ke tsaye ne hasken ya haske fuskar su, cike da girmamawa suka sunkuya har ƙasa suna gaishe ta, ta amsa tana kare musu kallo ganin su biyun ne yasa ta jinjina kai, suka mik'e suka fito, kai tsaye suka wuce hotel.
****
Angel ta yi farin ciki Mamanta sun gaisa da Yallaɓai likita, da man haka take so...
"Menene wannan?"
"Siyayyya ne Yallaɓai likita ya yi mana, na ce ya bari amma ya ki"
"Ki je ki kirawo ALAJA ta gani kada ta rufe mu da bala'i"
"To"
Ta faɗa ta wuce ta kirawota, aiko ALAJA kamar ta tashi sama don murna ta ɗebi rabonta ta bar musu sauran, Bilqees ta shigar musu ciki.
**********************
WASHE GARI
Tun safe ake ta faman shirye-shiryen DINNER PARTY, Alaja ta sa a shirya mata babban hall dake cikin Tumbin Giwa, ta tura Angel gyaran jiki, ta haɗa ta da Majada ta zame mata ƴar rakiya, sai da aka yi mata gyaran jiki sannan suka wuce aka yi mata lalle da suffa, ta yi matukar kyau sai kusan la'asar suka dawo, a lokacin har an gama shirya komai Laraba da Jummai Sadeebaby da zee Dollers suka shirya snacks ɗin da za a ci da drinks.
Kasancewar babu lokacin yin ɗinki hakan ya sa kowacce ta yi renting baƙar riga doguwar, Bilqees kuma za ta saka doguwar riga ta net, nevey blue, aka hau shirya ta, ana idar da sallah ishai aka fara hallara cikin hall ɗin.
DR Waahab da Sa'eed kawai suka iso, sanye da set na binjima gare kenan nevey blue kamar ya sani, aka yi musu isowa cikin hall ɗin da ya cika da ƴan Tumbin Giwa maza da mata, suka zauna babu jimawa aka shigo da Angel ta sha kyau kamar babu gobe, yana ganinta ya mik'e har ta iso suna zauna tare.
Babu jimawa aka soma shagali Dr Waahab bai shiga filin rawa ba, haka ma Angel daga zaune Sa'eed ya yi musu liki haka ma sauran mutane Alaja kama uwar amarya ta sha kyau ta yi ɗaure kama cokali, ya yi sama kamar ariyan mota sai dancewa take yi ko a kwalarta, haka ma su Majada da Laraba da Jummai, Sadeebaby da zee Dollers kam ba a magana sai cashewa suke yi.
Dr Waahab ya kurawa Angel idanu ganin yadda tayi kyau kamar ya ɗauke ta su tafi yake ji, ita kam sai sudda kai ƙasa ta ke yi don kunya, ta ɗago tana kallon uwar ta ALAJA wacce ke taka rawa ba abin da dameta don ita kunya gaba ta bata ba baya ba, sai liki take yi wa duk wanda ya ke rawa.
Kusan awa guda ana abu ɗaya, me bakin sigari ya shigo sakiyar fili, sai rawa yake yi, alamu sun nuna ya afka ƙwayoyi kamin ya shigo, sai gumi yake yi yana rawa kamar dole, Alaja tana yi masa liki, cen negah ma ya shigo yana ta ya shi kamar wani abin kirki, Sa'eed ne ya dubi Dr Waahab ya ce
"Bari na je na yi musu liki su bar wajen nan, don na kula mahaukata ne"
Ya mik'e ya yi musu liki tare da cewa su bar cikin hall ɗin, suka fito suna ƙananan maganganu, haka kurum suna cikin nishaɗi a kora su...
Sai kusan 11:00 pm sannan aka tashi a PARTY bayan an ci an sha, a raba gift na abubuwa daban-daban me ɗauke da stickers na dinner party da sunan Bilkisu Ja'afar da Abdulwahab Waseem KIRAWA.
Dr Waahab ya ce yana son yin magana da ALAJA, ta ce a yi masa isowa palourn baya, suna zaune da Sa'eed suna hira ta shigo, ta zauna tare da cewa
"Ango ya gajiya"
Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, ya ce
"Ai ku ne da gajiya, Alhaji babba ne ya ce, gobe jirgin safe za mu bi a shirya da wuri"
"Ok ba matsala to waye za su kai ta, ita kaɗai dai ka san ba zai yu ba"
"Eh shi ne na zo mu yi magana, da son samu ne dake za mu tafi Nigeria a ƙalla a samu mutane biyar"
"To ai an yi yawa jirgi fa za a hau ba mota ba"
"Ba matsala daga yanzu zuwa safe sai ku yi shawara"
"To Allah ya kai mu"
"Amin"
Ya faɗa ta mik'e tare da cewa
"To bari na turo Angel ku yi sallama"
Yana murmushi kamar tasan abin da ke cikin ransa, ta fice Sa'eed ya ce
"Gobe warhaka muna Nigeria"
"In sha Allahu"
Suna zaune Angel ta shigo da sallama, ta zauna a 1 seater da yake kusa da bakin ƙofar shigowa ganin Yallaɓai likita yana tare da ɗan'uwansa yasa ta sudda kai ƙasa, Dr Waahab ya taso ya iso kusa da ita ya rage tsawonsa ya ɗago da haɓarta suna kallon junansu ya sakar mata murmushi, Sa'eed ya ce
"Matar ɗan'uwa ya hidimar biki?"
A kunya ce ta ce
"Alhamdulillah, ya naka gajiyan"
"Sai godiya"
Sa'eed ganin Dr Waahab ya daina jin kunyarsa ya sa ya mik'e tare da cewa
"Ina cen dakalin da na jira ka jiya"
"Ok ɗan'uwan in ban fito ba kawai ka wuce hotel"
Dariya su ka yi har da Angel, Sa'eed ya ce
"Ai naga alama, amma dai ka fiton ya fi"
Ya fice yana dariya, Dr Waahab mik'e tare da Angel ya zauna kan kujerar ita kuma ya zaunar da ita kan cinyarsa ta sudda kai ƙasa tana jin nauyin sa, shi kuma yana so ta saki jiki da shi, sai dai kuma ya ga alama sai ya dage, duk da shi ma wani abin zuwar masa yake ba gwani bane wajen iya soyayya, ya juyo da fuskarta gare shi yana kallon cikin ƙwayar idanunta suna yi masa kyau, yana karewa jikinta kallo ya riƙe hannunta yana kallon lalle da aka yi mata, a hankali yake juya hannun, ya kai hannun bakinsa ya sumbaci shi yana kallon fuskarta, ta kasa nutsuwa, zuciyar ta na bugawa, ya kai ba kinsa cikin kunnenta ya ce
"I do love you my wife"
Hannunta yana rawa tana shirin janye jikinta ya riƙe sosai, yana kallon fuskarta, idanunta suka ciko da ƙwalla, yana shafa gefen fuskarta ya ce
"Mene ne?"
Ta ce
"Babu"
"Ba ki sona kusa da ke?"
Ta girgiza masa kanta alamun a'a, ya sauke numfashi tare da cewa
"To me ya sa kin daina yi min hira? A waya kina iya bani labarai masu daɗi amma kuma da na zo ba a yi min magana"
"A'a"
Kawai ta iya cewa, ya yana kallon lips nata ya ce
"Can I...
Sai ya yi shiru, ya kwantar da ita bisa ƙirjinsa, yana shafa bayanta, yana jin yadda zuciyarta ke bugawa, sam baya so ya takure ta, don haka ya ɗago da ita yana kallon fuskarta ya ce
"Gobe warhaka muna gidan mu"
Ya kasa yin magana, ta koma kamar kurma, murmushi ya yi ya mik'e ya riƙe hannunta suka fito, ya shafa fuskarta tare da cewa
"Sai da safe, muna jiran isowarku"
Ya juya da sauri ya bar Tumbin Giwa, don nema take ta kunce masa brain.
*******************
Washegari
Angel kuka take yi sosai, zata bar Mamanta, a side na ALAJA suka kwana, don tun dare ALAJA ta yi selecting waɗan da za su yi wa Bilqees rakiya Nigeria, ita da Laraba da Jummai sai kuma Abeedah da Majada.
Kowannen su a shirye suke saf, saura tafiya, Bilqees ta shirya cikin doguwar riga ta lace tayi kyau sosai ta yafa mayafi idanunta sun yi ja saboda kuka sun ɗan ciko, a hankali ta shigo ɗakin Mamanta ta taddata zaune ta yi tagumi, tana isowa kusa da ita ta kwantar da kanta a ƙafaɗarta ta fashe da kuka, Mamanta ta ɗan daure ta ɗago da fuskarta ta ƙwakulo murmushi ta ce
"Sai ki ce mun yi rabuwa ta har abada, ai ina nan kuma zan je har Nigeria naga ɗakin Angel"
Bilqees ta yi murmushi Mamanta ta kira ta da Angel, ta ce
"Mama zan yi kewar abincin ki me daɗi"
Murmushi Mamanta ta yi ta ce
"Ni ma zan yi kewar surutun ki"
Su ka yi dariya, Mamanta ta tashi ta ɗauko hoto ta kawo ta miƙa mata, ta karɓa tana kallon Mamanta, a hankali ta ce
"Mama me zan yi da hoton?"
"Hoton ki ne tun kina yarinya"
"To ki ajiye a wajen ki kada na ɓatat"
"Ki tafi da shi, zai yi miki amfani, ki adana shi a cikin kayanki za ki buƙa ce shi"
"To"
Ta faɗa don ita bata san amfanin hoton ba, ta mik'e a lokacin da Alaja ta leƙo tana cewa
"Sai ki fito mu tafi kada su jira mu"
"To"
Ta faɗa, tana hawaye riƙe da hoton da Mamanta ta bata, ta iso bakin kofa, sai kuma ta ruga da gudu ta iso ta faɗa jikin Mamanta, sai dai kuka ya tsaya chak a lokacin da ta tsinci kanta a jikin Mamanta, wasu al'amura ta ji da brain nata ya kasa fassara su, ta yi sauri ta yi baya, tana kallon fuskar Mamanta, sai dai Maman Bilqees ta kasa ɗagowa ballantana su haɗa ido, a hankali Bilqees ke komawa da baya baya har ta iso ƙofar fita, ta tsaya tana kallon ta, Maman Bilqees ta shiga tashin hankalin da bata taɓa shiga irinsa ba, a duniya bata so Bilqees ta yi mata wani fassara ko kallo sam bata so taga aibunta ko kasarwata, a hankali ta ɗago suka haɗa idanu, tabbas ta hango tashin hankali da kaɗuwa a idanun Bilqees, tsoro da fargaba suka mamaye zuciyarsa Bilqees ta lumshe idanunta mamanta na ƙoƙarin isowa gare ta, tayi sauri ta buɗe idanunta ta fice tana hawaye, maman Bilqees ta sauke ajiyar zuciya tare da furtawa
"I lost her! Na rasa ta, shikenan ta fahimci komai....
ALAJA uwar jagora, har airport suka iso Bilqees tana sharar ƙwalla, sai da ta yi mata faɗa tukuna ta yi shiru, ta saka hoton da Mamanta ta bata cikin hand bag nata.
Suka tadda su Yallaɓai likita a zaune suna jiran fitowar su, Dr Waahab yana ganin Angel ya mik'e ya iso wajenta ganin duk ta shiga cikin tashin hankali yasa jikinsa sanyi, yasan ta yi kukan rabuwa da Mamanta ne. Babu jimawa jirgi ya ɗaukosu zuwa Abuja Nigeria, suka bi jirgin yamma zuwa Maiduguri.....
______________________
Alhamdulillah book 1 ya kammala, abin da na rubuta daidai a cikin sa ubangiji ya bani lada kuskuren da na yi Allah ya yafe min.
Gamu kuma a gida Nigeria, Maiduguri KIRAWA'S FAMILY da Ango da amarya ko wacce irin BADAQALA za a sake yi? ku dai ku biyo ni cikin littafi na BIYU.
Ayi hakuri da typing errors
Comments and share fisabilillah