011
by @swrites22
_ NI DA YAYA NABEEL _
_YOUNG WRITER✍️
* 011 *
"Oga sawun giwa fa ya take na raqumi, dan da alama mafarautan biyu ne, tunda gashi wani ya mana shigar sauri".
Wata mahaukaciyar dariya ogan yayi kafin yace, "Hmmmm kuna wasa da Nabeel Kenan, ni na sanshi na san waye shi, na san duk abinda zai iya da wanda ba zai iya ba. Dan haka kar ku tsaya ku bisu whl, koma wani dan iskan ne karamar kwakwalwar sa ta bashi shawarar yin farauta a yankina sai na shafe tarihin sa a doron kasa, sannan kar ku manta da deal din aikin nan, a cikin daya ne in baku kawo min ita ba, Ku kashe ta, in baku kasheta ba Ku ci abincin karshe". Yana gama fadar haka ya kashe wayar.
A wani daji suka tsaya tare da bata umarnin fitowa, haka ta fito suka sa ta a gaba. Tafiya sukayi me dan tazara kafin su bulla bakin wani teku, jirgin ruwan dake wurin suka hau. Ita dai Asum in banda addu'a ba abinda take Allah ya kawo mata dauki, dan ta gama saddaqarwa kasa ce ta kawo ta garin nan, shikenan ita tata ta qare, mutuwa zatayi.
A bakin wani tsuburi suka sauka tare da nuna mata wani daki da aka zagaye da katakwaye alamar ta shige ciki, girgiza masu kai ta shiga yi tana kuka ta fara tafiya da baya² tana kallon wurin a tsorace, cire mask ɗin da ke fuskokin su sukayi, take ta shaida fuskar mutum biyu a ciki, dan suna daga cikin sojojin da suka taho dasu daga Russia. Sai a lokacin ta samu kwarin guiwar faɗin, "Meysa zaku kawoni nan? Ina mijina? Dama ku maciya amana ne? zagon qasa kuke masa?".
Kallon juna sukayi kafin ɗaya daga cikin biyun yace, "Kiyi haƙuri ma'am, umarni ne daga sir, kuma duk abinda mukayi cikin shirin sa ne dan ta hakan ne kawai zamu iya cetan ki lpy".
"Ku ceceni Ku kaini uwar ina? ni whl ban yadda daku ba, kuma bazan yadda da duk wani surutan banzan Ku ba". Miqa Mata waya dayan yayi inda ta jiyo muryar Nabeel na faɗin, "Kibi umarnin su Asum baza su cutar dake ba, nima ina nan zuwa".
Cikin muryar kuka tace, "Ni ba inda zani, kawai kazo ka maidani gaban iyaye na, dama shiyasa ka kawoni makasa saboda baka damu dani ba, ka bar matar so din taka a can cikin koshin lpy". Ta faɗa a rikice.
"Babu lokaci Asum, ki bi umarnin su, Sannan ki kulamin da kanki, in sha allah zan isko ku nan ba da jimawa ba". Yana gama fadin haka ya datse Kiran .
"Ma'am muje ko". Ko kallon sa batayi ba. Ɗayan ya bude baki zaiyi magana kamar daga sama sukaji an buɗe musu wuta ta ko ina, zagayeta sojojin sukayi suka mata zobe, take aka harbe biyu. Ai kuwa cikin tsoro ta fada dakin da suka nuna mata ba shiri, da sauri sauran sukabi bayanta. Manhole cover suka haɗu suka ɗage da karfi, wata sirritacciyar hanya ta bayyana a wurin. Ba bata lokaci ta shige suka bi bayan ta, tafiya suka shigayi cikin underground din, sosai mamaki ya kasheta ganin tsubirin tsakiyar ruwa yake amma gashi suna tafiya ta qasan ruwan kuma ba alamar ruwa a ciki, lalle akace da dan gari a kan ci gari.
A cikin wata kasuwa suka bulla, mutum ɗaya ne ya fara fita sai gashi ya dawo da wani scarf a hannun sa, ya miqa mata yana fadin ta rufe fuskar ta dashi. Da sauri kuwa ta karba tayi yadda yace sai idanunta kawai ake gani. Dayan ya sake cewa, "Fita zakiyi kiyi tafiya, in kika kure kasuwar zaki ga wani gida ash daga left side, nan zaki shiga karki ji tsoro muna zagaye dake amma bazai yiwu mu tafi tare ba". Tana jin haka ta taka steps din ta fice, duk a tsorace take tun da taga an harbe mutum biyu a gabanta.
Tafiya ta shiga yi tana waige² duk ta rikice ta kasa gane ma in da suka ce tabi, kamar daga sama ta hango fauza, da sauri ta karasa tana fadin, "Sister ni ce". Kallon sama da ƙasa fauza ta mata kafin tace, "Kece wa?".
Dan bude fuskar ta tayi tare da faɗin, "Ni ce wadda muka hadu a hotel ranar, kina tare da brother ɗin ki". Kamar bata gane ta ba tace, "Wai matar field Marshal Nabeel, to me kikeyi a nan kuma?".
Asum bata kai ga magana ba taji harbi, wani Ƙara Fauza ta fasa, da sauri ta ja baya tana kallon hannu Fauzan, Wani ɗan abu ta gani kamar water gun ta yara, tana yunqurin harba mata a ciki, ɗaya daga cikin sojojin su dake zagaye da ita ya ganta shi ne ya harbi Fauza ɗin. Bata gama dawowa hayyacinta ba taji harbe harbe tako ina, kasuwar ta hargitse gabaɗaya an shiga musayar wuta. Ba shiri ta ƙara a guje.
Dakyar ta gano gidan da suka kwatanta mata, tana ƙoƙarin shiga ta jiyo magana daga bayan ta, "Ma'am kwanta kasaaaa". Kafin tayi yadda yace aka bude mata wuta ta ko ina, wani irin juyi tayi tana kokarin gudu ƙafarta ta goce ta tafi gabaɗaya ta faɗa kan wani slab, wata irin kara ta fasa tare da dafe cikin ta, daga nan kuma bata sake sanin in da kanta yake ba.
****************
Bude idanun ta tayi a hankali ta shiga bin ɗakin da kallo, ba kowa a ciki amma daga yanayin dakin ta fahimci cewa a asibiti take. Da mamaki take kallon ruwan da ake kara mata kafin ta maida kallonta kan Nabeel da ya buɗe ƙofar ya shigo sanye da ash jeans da polo t-shirt black, kayan sun masa sosai saboda sun dace da tsarin jikinsa, saidai ya rame gsky, ga hannun sa ɗaya nannade da bandage. Da sassarfa ya karaso gaban ta ganin ta farka, alhamdulillah alhamdulillah kawai yake nanatawa, yayin da ya kai fuskar sa jikin tata.
Ya dade a haka sai ajiyar zuciya yake saukewa kafin can ya dago yana kallon ta, ya kamo hannunta yayi kissing kafin cikin kulawa ya ce, "Me ke miki ciwo ne yanzun? Ya kikejin jikin naki?". Ƙoƙarin tashi ta fara ya taimaka mata ta zauna, ai sai kawai ta fashe da kuka, nan da nan hankalin sa ya tashi, ya fita da sauri sai gashi sun dawo shi da wasu doctors biyu, gwaje² suka fara mata saida suka tabbatar da ba wata matsala sannan suka basu wuri.
Wani zazzafan numfashi ya furzar kana yace, "Dan Allah ki daina kukan nan haka Love, kar kanki yayi ciwo kinga baki da lpy sosai". Cikin kuka tace, "Ka rabu dani Nabil, Ka kyaleni, ba abinda zaka faɗa min a yanzu da ya wuce Ka maidani gida, whl ko maqiyi na bazan masa fatan shiga irin tashin hankalin da na shiga ba, ni kadai nasan abinda na gani, allah ne kawai yasa da sauran shan ruwa na a duniya da yanzu ba dani kake magana ba. Dama shine dalilin da yasa kace sai dani zakayi tafiyar wato ni ko oho, ko na mutu baka damu ba". Ta karashe tana sake rushewa da wani sabon kukan.
Ajiyar zuciya Nabil ya sauke, kafin a sanyaye yace, "Kiyi hakuri ki yafe min matata, whl ban kawoki nan bane dan a cutar dake, kuma Jumayma kanta da kike magana akai, to ita kanta bata tsiraba, maganar da nake miki tana ɗakin dake jikin naki tana jinya, ban taɓajin na tsani aiki na ba sai dalilin abun da ya faru, kuma a yanzu whl a shirye nake dana ajjeshi. Ki bar faɗin irin wadannan maganganun, ya kamata ace zuwa yanzu kin fahimci ke din ta daban ce a wurina, kina da muhimmanci sosai a rayuwata, ina sonki son da ban taba tunanin zan wa wata mace irin sa ba, ina jin zan iya sadaukar da komai nawa saboda ke ciki kuwa harda aikina dana fi kauna wanda nake shirin ajje shi a yanzun. Na cutu Assum, na cutu da yawa". Ya ƙarashe da muryar dake fallasa ciwon da yake ji a zuciyarsa.
Girgiza masa kai ta shiga yi tana hawaye a lokacin da ya ƙare Maganar. Sai kawai ta fada jikinsa ta rungume shi tana faɗin, "Baza ka ajje aikin ka saboda ni ba, aikin ka shine farin cikin ka ni kuma farin cikin ka shi ne nawa, ni addu'a kawai zan tayaka da ita Moodi'am, duk abinda ya faru damu ba laifin ka bane, haka Allah ya qaddara". Rungume ta ya sakeyi tsam a jikin sa yana maida kwallar data taru nasa a ido. Ina ma, ina ma, ina ma ina da ikon dawo da hannun agogo baya. Ya faɗa a zuciyarsa.
Ita ta fara breaking hug ɗin tare da riqo fuskarsa wanda yayi sanadiyyar dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula, "Ya akayi yah Nabil yake ƙoƙarin zama rago ne?". Ta fada tana kallon cikin idon sa da yake sheqi sakamakon kwallar dake kwance a ciki. Murmushi yayi kawai yaja hancin ta amma baice komai ba.
"Ina fatan kayi nasarar aikin nan da kake yi?". Gyada mata kai yayi alamar eh. Dube² ta shiga yi kafin tace, "Kasan na ebo ma wasu takardu daka bari lokacin daka fita, ban sani ba ko masu amfani ne, bana so ka samu matsala a aikin ka. Gashi yanzu bansan inda suke ba ma ko na yasar oho".
Kamo hannun ta yayi yana murzawa da hannunsa me lpy kafin a hankali yace, "Masu amfani ne kwarai Assum, dan aikin da nake ma da babu su da ya tashi a banza dukda mafi yawan bayanan suna system din amma alhamdulillah akwai dayawa a wa'annan papers din, kuma suna hannuna".
Da sauri tace, "Ka gansu Ya Nabil?". Gyada mata kai yayi alamar eh. Sai lokacin ta lura da hannun nasa tace, "Hamma nah me ya same ka?". Shafa kumatun ta yayi tare da faɗin, "Bakomai fa, ya warke ma". Ganin ta fara hawaye ya sashi girgiza mata kai tare da faɗin, "Umm umm dan Allah, a daina zubar min da hawayen nan masu tsada".
"To ka tashi muje a duba ma, nasan maybe ma harbin ka akayi". Rungumota ya sake yi tare da kwantar da kanta a kafardar sa yace, "Karki damu, ba ciwon yanzu bane ai yama warke kawai basu cire bandage ɗin bane dama yanzu ma nake cewa zanje su cire".
"Ya Nabeel, kace Jumayma na nan, yaushe tazo Germany itama?".
"Dukkanmu nan muna Russia ne ai". Da sauri ta dago tana kallon sa. Gyada mata kai yayi alamar tabbatar wa kafin ya cigaba da faɗin, "Dogon suma kikayi shiyasa baki sani ba amma kusan kwanan mu goma anan". Waro Ido tayi da mamaki tace, "Har munyi kwana goma ma? Kenan na dade a kwance? Wayyo Mummyy, dan Allah ka kiramin Umma ko mommy inji muryar su".
"Zan Kira miki su amma bana so ki fada musu abinda ya faru saboda hankalin su ne zai tashi Kinji?". Gyada masa kai tayi alamar to, shi kuma ya zaro wayar sa ya shiga kiran umma. Bayan ta ɗaga suka gaisa sannan ya miqawa Assum. Da sauri ta karba bayan sun gaisa Umma tace, "Ina kika shiga haka Assum, wayarki kwata² bata shiga amma Abban ki yace kina lpy yana waya da mijin ki ".
"Eh umma ina lpy, wayata ce ta samu matsala ga kuma sha'anin makaranta sai yau na samu dama sai nace ya kiramun ke".
"To alhamdulillah tunda kuna lpy". Hira suka dan taɓa kafin suyi sallama. Karbar wayar yayi, ta kwabe fuska tare da faɗin, "Saura Mommy ".
"Kinyi surutu da yawa ya isa haka, sai Anjima". Rikici tasa masa dan dole ya Kira Mommy, tana dagawa ya miqa mata ba tare da yace komai ba. Masifa Mommy ta fara, "Kai Nabeel ina fatan ba wani gallazawar kake wa yar mutane ba ko? Ya anata neman number ta ba'a samu, whl karka sake Baffahn ka yaji wani abu marar dadi kasan halin sa dai kuma kasan abinda ya fada ma kafin Ku tafi....". Katseta Assum tayi ta hanyar yin sallama. Cikin farin ciki ta amsa tana faɗin, "Yata ta kaina kuna lpy? ya makarantar?".
"Alhamdulillah Mommy na, ku ma ya kuke ya duk mutanan gidan".
"Kowa lpy kalau, meke faruwa ne ana ta neman wayarki ba'a samu?.
" Eyyerh Mommy lalacewa tayi ne".
" Ohk shine shi kuma Nabeel ɗin yaqi siyo wata kenan? Kinga faɗamin gsky Assum ya zaman naku yake?".
"Ba wata matsala Mommy lpy lau muke zaune".
"Karkiji kunyata Assum ki fadamin Inda wani abu, ni ba matsayin surukar ki nake ba matsayin uwa nake a wurinki".
"Allah Mommy da gaske bakomai, lpy kalau muke".
"To Alhamdulillahi, bani shi inji dalilin daya sa yaqi siyo Miki wata sabuwar wayar ko duk san ya nuna shi isasshe ne". Kallon sa tayi taga shima ita yake kallo sai kawai tace, "Mommy baya kusa dani, kuma ma ba laifin sa bane ni ce ban fada masa ba saboda karatu ma wayar na distracting dina Shiyasa".
Sosai Mommy ta sake jin son Asum ɗin a zuciyarta dan haka tace, "To shikenan assumi ta, amma ki faɗa masa ya siyo miki wata ko da baza ki dinga amfani da ita ko da yaushe ba. Ai zaki dinga gaisawa da gida ana jin lpyr ki. Allah ya muku Albarka ya baku zurriya dayyaba shi kuma Allah ya bashi ikon kwatanta adalci a tsakanin ku, ya dafa masa a lamuran sa bakidaya".
Cikin jin dadin addu'ar tace, "Allahumma ameen mommy na, Allah ya bar mana ke".
"Ameen yata ta kaina, ki gaida Nabeel din da abokiyar zaman taki duk da ita tafi karfin ta kira ta gaisheni".
"In sha zasuji Mommy". Daga haka sukayi sallama ta miqa masa wayar. A sanyaye yace, "Allah ya miki Albarka Love".
Murmushi tayi cikin ɗan jin kunya tace, " Ameen ya rabbi. Ni kam me ya sameni na dau tsawon wannan lokacin a kwance ba tare da nasan inda kai na yake ba ?". Shuru yayi yana kallon ta kamar me tunani. Shagwabe fuska tayi kamar zata sa kuka ta sake cewa, "Ehhh?".
"Ba komai fa, kawai likitoci sunce tsoratar da kikayi ce lokacin da kika fadi, da kuma gudun da kika yi kafin faruwar hakan ya haifarwa da zuciyarki attack wanda yasa kika shiga dogon suma, kuma....". Ganin yadda ta tsareshi da Ido ya sashi janye ansa idon, yana ɗan ciza baki yace, "Kin..yi miscarria..ge". Ya fada a rarrabe, zuciyarsa na masa zafi.
Cikin rashin gasgata abinda kunnuwan ta suka ji tace, "Me kace ne Hamma?". Shuru ya mata, bai kuma motsa ba. "Kamar ciki kake nufin ina dashi, kuma ya zube? Ciki dai na haihuwa? Ni fa? Anya likitocin nan sun ga daidai kuwa?". Jinjina mata kai yayi, kafin ya kalleta yace, "Karami ne, domin ko sati uku bai cika ba, nayi kukan baƙin ciki Assum, abunda na dade ina nema Allah ya bani amma ta sanadin aikin nan na rasa shi, shiyasa har yanzu in na tuna sai inji gabaɗaya aikin ya fice min a rai. Duk qannaina daga mai ya'ya biyu sai uku kullum addu'a ta Allah ya bani nima, dan nasan haihuwa ba abu bane da kudi ko mulki ke saya, duk dukiyar ka baka isa ka siya ba, shi din wata kyauta ce daga allah am......". Kasa qarasawa yayi saboda nauyin da zuciyarsa ta masa, ya riqe kansa da hannuwansa, yayi shuru.
Tsawon lokaci suna a haka kowa da tunanin da yake kafin Assum tayi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin, "Yah Nabeel ka daina damuwa dan Allah, ba sanadin aikin ka bane dama Allah ya qaddara wanna din ba rayayye bane ba kuma mu isa mu gujewa qaddara ba, addu'a kawai zamuyi Allah ya kawo mana wasu masu albarka, in sha ALLAH sai na cika ma gida da yara". Murmushin da yafi kuka ciwo yayi tare da gyada mata Kai alamar to.
"To ita kuma Jumayman me ya sameta?". Sai da ya dau wani lokaci bai amsa mata ba har ta fidda ran zai amsa ɗin taji yace, "Kwata² ba wanda ya san abinda ke tsakanina dake amma zaman da kikayi da Smasher a hotel kika shaida musu ke matata ce, a lokacin ne abun harin su ya zama biyu, domin jumayma dama sun gama mata tanadi kuma nima sun shirya hara ta a wannan tafiyar shiyasa suka tura mutanen su can tun kafin mu muje, sunyi mamakin ganina tare dake a airport saboda sun san Jumayma na Russia kuma basu san ina da wata matar ba bayan ita.
Duk da ban yadda mun jera tafiyar ba daga airport ɗin na hadaki da wani sojan mu aka wuce dake hotel saidai na makara domin masu iya magana na faɗin in taqamarka sammako wani acan ya kwana. Ashe sun bibiyi hotel din da muka sauka, ba wai zuwa sukayi dan brother ta ya ganki yana son ki bane, ah ah sunzo ne su tabbatar in ke ba matata bace kawai na dauko ki ne mu huta zasu hada baki dake su cutar dani in kuma matata ce ke zasu kasheki dan su kuntata min. Matar data zo wurinki ranar da abun zai faru bani na aikota ba amma sun san ba zan dawo da wuri ba, ta shigo ne ta sanya miki Toxic gas bomb, but abinda bata sani ba kuwa shi ne tun ranar da muka sauka a hotel ɗin na shirya falon saboda ban yarda da kowa ba, ina cikin aiki wayata ta fara alerting ɗi na, ina dubawa naga abinda ke faruwa, nayi kokarin yin wani abu amma ta riga ta saita shi da karancin lokaci har ma ya fara counting, ba kuma iya falon mu aka saita ba, an riga an gama shirya gabadaya hotel ɗin ta yadda baki isa ki tsira lpy ba.
Dan a lokacin nan da nace ki bar hotel din da kin fita ta kofa da yanzu ba wanna zancen ake ba. Sannan a daidai wannan lokacin kuma wasu suka je gidana a zuwan qawayen Jumayma saboda ba kowa ke shiga gidan kai tsaye ba, amma karawar da sukayi a zuwan qawayen ta ne, kasancewar ta uwar kwashe² da nagari da na banza kowa nata ne, kowa abokin ta ne ita dai a kira ta mai mutane. Shi ne da securities suka Kira suka tambayeta sai tace musu Eh kawayen ta ne, ta san da zuwansu, a barsu su shiga. Su kuwa suna shiga suka sakar mata bullet din qawance.
A rikice Asum da gabaɗaya maganganun sa suka sa kwakwalwar ta ɗaukan zafi tace, " Ya Nabeel na kasa ganewa, ka sani a duhu, yaushe fauza ta zama smasher ? Dama Ka san fauza? Ya akayi kasan sunzo wurina a hotel ? Su waye kuma suke son kuntata ma? Meysa kuma ake neman rayukan mu ?