KADDARAR ZUCIYA

GIRLS OUTING

by @jiddaahbarkum

KADDARAR ZUCIYA

CHAPTER FORTY-NINE: 49

GIRLS OUTINGS

JIDDAAH BARKUM

———

Bayan sun fito daga office din likitar, har yanzu Nana tana tafiya ne kamar wacce take cikin mafarki ba zahiri ba. A hannunta yana rike da result din, farar takarda ce kawai, amma a gare ta, ita ce takardar da ta sauya rayuwarta gaba daya. Takardar da ta kawo karshen shekaru bakwai na jira, shekaru bakwai na addu'a, shekaru bakwai na fatan alheri, da shekaru bakwai na cewa: "Ya Allah ko sau daya ne…" Tana tafiya a hankali tana kallon takardar, sai ta sake kallonta ta sake karantawa, kamar wacce take tsoron idan ta dauke idonta daga gare ta, kalmomin za su bace. Umar kuwa yana tafiya a gefenta. Tun bayan da suka ji labarin, shi ma bai dawo daidai ba; sai dai nashi shock din ya gaurayu da farin ciki, da godiya, da kuma wani irin sanyi da ya mamaye zuciyarsa. Ya bude mata kofar mota ta shiga a hankali, ya jira har ta zauna kafin ya rufe, sai ya zagaya ya shiga mazaunin driver yayin da Farida da Inteesar suka shiga baya. Sun dauki lokaci ba wanda ya yi magana, sai sautin AC kadai da kuma bugun zuciyoyin mutane hudu masu farin ciki. Nana ta sake kallon result din, nan take hawayen da ta goge mintuna kalilan da suka gabata suka sake taruwa a idanunta. Ta lumshe ido ta bude, ta sake karanta kalmar "Positive." Nan take ta dafe bakinta, sabbin hawaye suka zubo. Umar ya waigo ya kalle ta, sai zuciyarsa ta narke; a hankali ya kai hannunsa ya kamo nata, ya matse cikin nasa, ya daga hannun ya sumbaci bayan hannunta yayin da idanunsa suka dan yi ja "Sweetheart…" muryarsa ta yi laushi. Nana ta dago idanunta tana kallonsa. "After seven years…" ya hade wani abu mai nauyi, "…Allah ya amsa mana." Nan take Nana ta fashe da kuka, ba kukan bakin ciki ba, kukan da ya dade yana jiran fitowa ne, kukan da ya tara shekaru. Ta girgiza kai, "Babe… muryarta na rawa, na daina kirga shekarun tun tuni." Umar ya runtse ido domin ya san gaskiyar maganar; ya san dararen da ta kwana tana kuka a boye, ya san lokutan da take murmushi alhali zuciyarta na ciwo, kuma ya san yadda ta dinga cewa "Alhamdulillah" ko da zuciyarta tana zubar da hawaye. Nana ta sauke idonta, "Kasan wani lokaci har na daina addu'ar Allah ya bani yaro." Umar ya kalle ta, ta yi murmushi cikin hawaye, "Sai kawai nake addu'ar Allah ya bani hakuri." Wani abu ya tsaya masa a makoshi, ya matse hannunta cikin sanyin murya yace, "Sweetheart… Allah bai taba mantawa da mu ba." Nana ta sake fashewa da kuka, Farida ta juya gefe tana goge idanunta, ita kuwa Inteesar ta yi shiru tana kallon su, zuciyarta cike da farin ciki. Lokacin da suka isa gida, Nana ta fito daga motar a hankali ta tsaya a harabar gidan, sai ta daga kai tana kallon ginin. Gidan da ya shafe shekaru tana zaune a cikinsa, gidan da ya sha ganin murmushinta, hawayenta, da addu'o'inta. Ta yi murmushi, sai ta ce cikin kasa da murya, "Babe… Wannan gidan zai samu karuwar yaro ko Yarinya Arzikin da da bamu dashi yau Allah ya bamu zamu samu masu guje guje a cikinsa." Umar ya kalle ta, sai ya yi dariya, "Masu guje guje? Wannan gidan zai zama stadium." Duk suka yi dariya, har Nana, dariyar da ta gaurayu da hawaye, farin ciki, godiya, da wata irin nutsuwa da ta dade ba ta ji ba.

A can sama kuwa, Inteesar da Farida suna zaune a dakinsu. Ba dariya suke yi ba yanzu, ba tsokana ba, sai maganar Nana da mu'ujizar da Allah ya yi. Farida ta jingina da headboard ta sauke numfashi, "Wallahi Allah yana amsa addu'a." Inteesar ta gyada kai a hankali, idanunta suka dan yi nisa tana tuna shekaru da yadda Nana ta kasance; ba ta taba jin ta tana korafi ba, ko cewa me yasa ita bata haihu ba, sai dai addu'a, hakuri, da murmushi ko da zuciyarta tana ciwo. Inteesar ta yi murmushi, "Allah ya bata lafiya ya sa yanzu ne zata fara Allah ya bata yara masu albarka Wanda zasu kasance sanyin idaniya a gareta." Farida ta amsa da "Aamiin", sai shiru ya biyo baya, kowacce tana tuna yadda Allah ke sauya rayuwa cikin lokaci daya. Da dare, Inteesar tana zaune a kan gadonta, wayarta a hannu tana chat da Khalil ne sai wayar ta yi vibrating: Mi Amor. Nan take murmushi ya bayyana a fuskarta ta daga, "Assalamu alaikum." Wa alaikumus salam Babygirl. Muryarsa kadai ta isa ta sa ta yi murmushi. "How are you?" Alhamdulillah. Bayan sun gaisa kamar yanda suka saba, sai ta kasa jurewa, "Mi Amor! Guess what happened today?" What happened? Cikin farin ciki ta ba shi labarin komai. Aliyu yana sauraro cikin nutsuwa, da ta gama, sai ya yi murmushi, "Alhamdulillah. Na tayata murna sosai Allah ya bata lafiya." A hankali ta amsa da "Amin". Sai ya ce a hankali, "The house is becoming complete." Inteesar ta yi murmushi, "True." Sai ya yi dariya, "Kinga kowa yana samun baby news." Nan take Inteesar ta dafe goshinta, "Mi Amor… kar ka fara." Aliyu ya fashe da dariya, ita ma ta kasa hana kanta dariya amma maimakon dariyar sai kawai tayi murmushi. A wannan daren, bacci ya ki zuwa wa Nana, kuma ba ita kadai ba, har Umar. Suna kwance a daki inda dim light kadai ke haskawa, Nana tana kwance da kanta a kirjin Umar yayin da yatsunsa suna yawo cikin gashinta. Duk sun yi shiru, zuciyarsu ta yi nisa an imagination mai dadi cike da salama. Sai can kuma Nana ta kira Umar, "Babe." Na'am sweetheart. Ta yi shiru na dan lokaci, sai ta ce, "Thank you." Ya dan murmusa, "For what?" Ta hade wani abu, "Thank you for never giving up on me." Nan take Umar ya dago kanta daga kirjinsa, ya kafe idanunshi cikin nata fuskarsa ta canza, "Never say that again." Nana ta lumshe ido, "Why?" Ya kama hannunta ya matse, ya yi kasa da murya sosai yace, "Because from the beginning… It was never you against the problem." Hawayen Nana suka sake fitowa, ya saka babban yatsanshi ya goge su a hankali, sai ya ce muryarsa ta yi kasa, "It was always us. Always." Nana ta fashe da kukan farin ciki da godiya da ya fito dga can kasan zuciya. Umar ya rungume ta sosai, ya manna goshinsa da nata; suka zauna haka ba tare da magana ba, domin wasu lokutan farin ciki yana da girma fiye da kalmomi. Kuma a wannan daren, a karon farko bayan shekaru bakwai, sun kwanta suna mafarkin abin da suka dade suna jira, dansu ko diyarsu, kyautar da Allah Ya ajiye musu tsawon lokaci kuma Ya ba su ita a lokacin da Ya ga ya dace.

Washegarin ranar da suka dawo daga asibiti, Nana ta bude idanunta a hankali, na wasu dakiku ta kasa gane inda take. Ta kwanta tana kallon silin din dakin cikin shiru da sanyi mai dadi na safiya dake ratsawa ta cikin labule. Sai kuma a hankali abubuwan da suka faru jiya suka fara dawowa cikin kanta: Asibiti, Likita, Result, "Congratulations. You are pregnant." Nan take ta tashi zaune da sauri kamar wacce ta tuna wani abu mai muhimmanci, gabanta yana bugawa. Idanunta suka kai kan drawer da ke gefen gadon, takardar tana nan. A hankali ta mika hannu ta dauka, ta buɗe ta sake karantawa, sai hawaye na farin ciki da jin cewa Allah yana iya yin komai a lokacin da Ya ga dama suka cika idanunta. Ta kai hannu ta dafe cikinta a hankali, wani irin murmushi ya bayyana a fuskarta, "Alhamdulillah…" ta furta cikin sanyin murya. Daga bayanta ta ji wata murya mai cike da bacci, "Har yanzu kina kallon result din?" Ta waigo; Umar ne, yana kwance yana kallon ta, murmushi dauke a fuskarsa. Nana ta yi dariya kadan, "Babe…" Ya mika mata hannu, ta matsa kusa da shi, nan take ya jawota jikinsa ya rungume ta kamar ba zai sake sakinta ba. "Good morning, sweetheart." Morning. Ya sumbaci goshinta, "Wallahi har yanzu ban yarda ba" ta fada Tana murmushi. Sa yace "Yesterday felt like a dream." Ta gyada kai, "Exactly." Ya kai hannu ya dafe kumatunta, "Allah ya yi mana babban alkhair ya bamu kyautar da dan Adam baya bawa wani Saidai Allah shi da Kansa ya bawa Wanda yaso." Nan take idanunta suka sake cikowa da hawaye, ya girgiza kai, "No, karki yi kuka," ya goge mata hawaye da babban yatsansa sannan ya manna goshinsa da nata, "Alhamdulillah." Alhamdulillah. Bayan kusan rabin awa, Nana ta shirya zata fito daga dakin, tana sanye da wata atamfa mai launin sky blue da light gold ta daura dan karamin gyale. Tana kokarin saukowa daga kan gado, sai Umar ya mike da sauri, "Wait." Ta tsaya tana kallonsa, "Babe?" Ya karasa kusa da ita, "Me kike nema?" Ta yi dariya, "Zan sauka ne." Bari na taimaka miki ki sauko. Sai ya kamo hannunta kamar wata yarinya karama. Nana ta zaro ido, "Babe." Yes? Ba na jin ciwon komai fa. Na sani. Toh? Still. Ta girgiza kai tana dariya, "Ka fara kenan?" Na fara. Haka ya kamota har zuwa downstairs. A downstairs kuwa, Inteesar da Farida sun riga sun tashi, dukansu suna dining area; Farida tana cin pancake, Inteesar kuma tana hada tea. Sai suka ji muryoyi daga stairs, duk suka waigo, kuma abin da suka gani ya sa suka fashe da dariya. Umar yana rike da hannun Nana kamar wacce aka yi wa operation, a hankali suke saukowa step daya, sannan wani, sannan wani. Farida ta dafe baki, "Ya Allah." Inteesar kuwa kawai murmushi take tana kallonsu cike da burgewa. "Uncle," Farida ta kira, "Yes?" What happened to her? Sai ya kalle ta, "Me kika gani?" Farida ta nuna Nana, "Ba patient ba ce ba fa," ta fada tana kunshe dariyar ta. Umar ya girgiza kai, "Ku ba zaku gane ba." Farida ta kara dariya, "Yaya Nana kina ganin abin da nake gani?" Nana ta dafe goshinta, "Wallahi tun safe haka yake." Farida ta fashe da dariya. Umar ya ja kujera ya zaunar da Nana, sannan ya juya ya dauko mata ruwa da kansa. Inteesar da Farida suka kalli juna. "Tun yanzu?" Farida ta sake tambaya. "Eh mana," Umar ya amsa ba tare da wata-wata ba, "Ba zan yi risk ba." Farida ta dafe kirji, "Yaya Nana… enjoy this treatment." Duk suka yi dariya.

Bayan dariyar ta dan lafa, Farida ta dan matsa gaba a kujerarta, ta dora haba a tafin hannunta sannan ta kalli Nana sosai, wani irin murmushi na farin ciki na gaskiya a fuskarta. "Yaya Nana." Nana ta dago kai, "Uhmm?" Farida ta girgiza kai a hankali, "Wallahi har yanzu ban yarda ba." Nana ta yi murmushi, "Ni ma." Inteesar ta kawo tea ta ajiye a gabanta, "Kowa dai haka yake." Umar kuwa ya ja tea din daga gaban Nana, nan take duk suka tsaya suna kallonsa. Nana ta daga gira, "Babe?" Ya kalli cup din, "Sai ya huce." Farida ta dafe baki, Inteesar kuma ta jingina da kujera tana murmushi. "Uncle." Yes? Tea din ma? Eh mana. Nana ta girgiza kai, "Ka san dai ba ni ce farko mai ciki ba a duniya?" Na sani. Toh? Still. Duk suka sake fashewa da dariya. Bayan sun gama breakfast, suka koma falo; wurin ya cika da annuri da walwala da kuma wani irin farin ciki da ya mamaye gidan tun jiya. Farida tana zaune a kasa kan carpet, Inteesar kuma tana gefe tana yanka apple, Nana na zaune a sofa, Umar kuwa yana gefenta a kujera daban kamar bodyguard. Farida ta girgiza kai, "Wallahi." Inteesar ta kalle ta, "Me kuma?" Yaya Nana. Na'am. Kina ganin yadda ake kallonki kuwa? Nana ta yi dariya, Umar ya daga gira, "Farida ki kiyayeni kin maida ni kamar kakanki koh." Farida ta rufe bakinta da hannu tana dariya, "I'm sorry uncle." Better, ya fada yana relaxing bayanshi a jikin kujera. Duk suka yi dariya. Sai Inteesar ta ce, "Yaya Nana, kin fara tunanin baby names?" Nan take Nana ta yi murmushi ta kai hannu ta dafe cikinta a hankali; har yanzu ba ta saba da tunanin ba, Baby, danta, ko diyarta, kalmar kanta tana sa zuciyarta bugawa. Farida ta matsa gaba da sauri, "Eh mana, mu fara." Umar yana jinsu bai ce komai ba sai wayarshi da yake dannawa. Inteesar ta gyara zamanta, "Ni dai na fara tunanin wani abu." Nana ta kalle ta, "Kan me?" Inteesar ta yi murmushi, "Twins ne." Nan take Farida ta bude baki, "A'a." Me a'a? Guda daya ne tukuna. Inteesar ta girgiza kai, "Twins." Farida ta nuna cikinta, "Wa ya gaya miki?" Ni na sani. Farida ta kanne ido tana kallon ta sai tayi kasa da murya, "Saboda Aliyu yace zaki haifi twins sau biyu shine har kin mikawa yaya nana ta fara koh." Inteesar ta zaro ido tana kallon ta, a hankali tace "Farida stopppp!" Farida ta fashe da dariya har da hawaye. Nana kawai murmushi take tana kallonsu kafin Farida ta maida dubanta kan Nana, ta kirata a nutse, "Yaya Nana… Wane lokaci kika fi jin ba dadi akan rashin haihuwa?" Shiru ya dan ratsa wurin, Inteesar ma ta yi shiru. Nana ta sauke numfashi a hankali, idanunta suka dan lumshe kamar tana kallon shekaru bakwai da suka shude. "Kullum," ta amsa a hankali, "Kullum akwai wahala." Sai tayi shiru, "Amma abin da ya fi ciwo… shi ne idan mutum ya tambaye ki tambayar da ba shi da niyyar cutar da ke…" Inteesar ta lumshe ido domin ta san irin tambayoyin: "Yaushe za ki haihu?", "Kuna jira ne?", "Ko ba ku fara planning ba?" Nana ta yi murmushi, "Wani lokacin mutum zai yi murmushi ya amsa, amma idan ya shiga daki…" ta dafe kirji, "sai ya yi kuka shi kadai." Shiru ya mamaye falon. Inteesar ta kama hannunta, Farida ma ta matsa kusa da ita. Nana ta yi murmushi, sai ta goge karamin hawayen farin ciki da ya zubo, "Amma komai na Allah yana da lokacin sa." Umar yana gefe yana kallonsu bai ce komai ba. Inteesar ta matse hannun nana a hankali, Nana ta kalle sai inteesar tace cikin tausasawa, "Da na ce miki Allah bai manta da ke ba kin tuna?" Ta gyada kai, "Eh." Ga amsar nan yanzu. Nan take hawaye suka sake cikowa idanunta, amma wannan karon ba hawaye na ciwo ba ne, na cikakkiyar godiya ne da addu'ar da aka amsa, na shekaru bakwai da suka zama tarihi. Falon ya sake yin shiru, kowanne cikinsu yana jin nauyin lokacin da girman ni'imar da Allah Ya saukar a gidan, kuma a karon farko cikin lokaci mai tsawo, Nana ta ji cikakkiyar nutsuwa a zuciyarta kamar wani babban nauyi da ta dauka tsawon shekaru ya sauka.

Sun yi kusan awa guda suna hira da dariya. Farida ta gyara zamanta a kan kujera, ta kalli Umar tana murmushi, sannan ta ce, "Uncle Umar, dama muna son mu dan fita da yammacin nan mu je gidansu Amira, kawar Inteesar. Daga nan kuma idan mun fito muna son mu dan zaga gari mu sha iska." Umar ya juyo a hankali, ya kalli Farida sannan ya kalli Inteesar da ke zaune tana wasa da yatsun hannunta. Ya gyara zamansa, fuskarsa dauke da kulawa. "Okay," ya fada muryarsa a natse, "Amma don Allah kar ku dade a can, kuma ku kula da kanku sosai." In Shaa Allah Uncle, Farida ta amsa fuskarta cike da murna da gamsuwa da izinin da ya ba su. Da misalin karfe hudu na yamma, Inteesar da Farida suka fara shirye-shiryen fita. A dakin Inteesar kuwa, tana tsaye a gaban babban wardrobe dinta ta bude kofofin duka; cikin mintuna kalilan, ta dinga janyo kaya tana watsawa a saman gadon. Ta kwaso abayoyi da dogayen riguna na alfarma gaba daya saman gadon ya cika taf da launuka daban-daban tamkar kantin sayar da kaya. Tana tsaka da hargitsa ragowar, Farida ta turo kofar toilet ta fito tana daure da wani farin towel mai laushi tun daga kirjinta zuwa gwiwarta, gashinta danye dake digar da ruwa tana tsane shi da wani karamin towel. Ta tsaya cak a tsakiyar dakin, ta saki baki tana kallon yadda gadon ya bace gaba daya, ta zaro idanunta cikin tsananin mamaki ta dafe kugunta da hannu daya. "Yanzu Intee," Farida ta fada muryarta cike da tsokana, "Duk wannan kayan da kika baje a nan saman gadon saboda kina neman kayan sawa ne kawai na fita yau? Lallai kam, lallai Aliyu ya hadu da aiki!" Inteesar ta juyo da sauri fuskarta dauke da shagwaba, ta turo baki gaba tana dan tura wasu kayan gefe, "Farida ba zaki gane ba ne, kawai ina neman abin da zai yi min daidai ne da yanayin garin yau." Ta juya ta sake duba cikin tarin kayan har idanunta suka sauka a kan wata kyakkyawar gown launinta dusty rose mai laushi, ba pink sosai ba, ba peach sosai ba, tsakaninsu, an yi mata dan karamin stone work a gefen hannaye da wuya. Ta shirya tsaf a cikin rigar, kayan ya zauna a jikinta tamkar an yi shi ne domin ita; ta bar gashinta a rufe cikin matching veil mai laushi wanda ya sauko har kirjinta. Da ta tsaya gaban mirror, Farida ta yi shiru na wasu dakiku. Inteesar ta kalle ta, "Me?" Farida ta girgiza kai, "Wallahi Aliyu yayi dacen mace." Nan take Inteesar ta dauki pillow ta jefa mata, "Farida!" Farida ta kuce tana dariya. Ita ma ta shirya cikin nata kayan, wata doguwar flowing gown mai launin lavender. Kalar ta yi mata matukar kyau; kayan ba su matse jiki ba, sun kasance masu sauki da nutsuwa tare da dan silver embroidery a hannaye da gefen kasa, ta daura gyale mai laushi wanda ya dace da kayan. Fuskarta kuwa ta yi wani irin haske na musamman, ba makeup mai yawa ba, amma kuma tayi kyau sosai. Kafin suka sauko kasa inda suka tarar da Nana a kwance a kujera hannunta da remote tana neman channel, ta bi su da kallo tana murmushi, "Uhmm yammata an sha kyau Haka da yamma nan." Duk sukayi dariya, sai ga yaya Umar nan ya fito daga kitchen da tea a hannunshi ya karasa ya ajiye a stool din gefen Nana kafin ya zauna a gefenta. "Uncle!" Farida ta kira, "Yes?" Take good care of her kafin mu dawo, ta fada tana murmushi. "Sure I will" ya amsa ta. Bayan wasu mintuna, Inteesar da Farida suka yi sallama da Nana. "Drive safely," Umar ya fada yana kallon Inteesar, sai ta sauke idonta a hankali sannan ta gyada kai, "Yes sir," cewar Farida tana murmushi. Bayan sun shiga mota, Inteesar ta kunna engine, a hankali suka fice daga harabar gidan. Farida ta jingina da kujerar baya tana kallon wajen; iskar yammaci tana ratsawa ta taga, kuma Abuja ta yi kyau sosai a lokacin. Sama tana dauke da launin golden orange na faduwar rana, manyan tituna masu fadi, tsabtatatun layuka, da bishiyoyi a gefen tituna, komai yana da nutsuwa. Farida ta yi shiru tana kallo, Inteesar ta kalle ta, "Me kike kallo?" Farida ta sauke numfashi, "Wallahi Abuja tana da kyau." Inteesar ta yi murmushi, "Sosai." Farida ta girgiza kai, "A Lagos yanzu… da mun yi mintuna talatin a wuri daya saboda traffic." Inteesar ta fashe da dariya, "Gaskiya ne.", Farida ta sake kallon hanya, "Nan kuwa kamar mutane suna rayuwa cikin peace." "Ki dawo nan da zama mana" cewar inteesar Farida ta zaro ido, "Ni?" "Eh" "Na bar Lagos? Inteesar ta yi dariya. Bayan kusan mintuna ashirin, suka isa Wuse 2. Unguwar tana da kyau, gidajen akwai tsari, shuke-shuke masu kyau, da tsabtatatun hanyoyi. Inteesar ta juya cikin wani layi, Farida ta fara gyara zamanta, "Muna kusa kenan." Eh. Da suka tsaya a gaban gate din gidan, Farida ta saki karamar kara, "Finally!" Inteesar ta yi dariya ta yi horn kadan. Bayan yan dakiku gate din ya bude suka shiga. Tun kafin motar ta tsaya, wata yarinya mai tsayi da fara'a ta fito daga entrance din gidan da gudu, "Inteeeeee!" Inteesar ta bude kofar mota, "Amiraaaaa!" Kafin Farida ta fito, tuni su biyun sun rungume juna suna ihu kamar wadanda ba su hadu ba tsawon shekaru. Amira ta ja baya tana kallon Inteesar, "Wallahi a kwana biyun nan har kin qara kyau." Inteesar ta zaro ido, "Ni?" Ehh. Farida ta tsaya tana kallonsu tana dariya, "Allah ya shirye ku." Nan suka waigo, "Farida!" Amira ta rungume Farida ma, "It's nice meeting you Farida." Farida ta yi murmushi, "How are you?" Very fine. Amira ta ja su, "Ku shigo mana." Da suka shiga falon, kamshin tsaddadan turaren wuta da kuma air freshener mai dadi ya cika falon. Farida ta zauna tana kallon wajen, "Hmmm. Allah shaida Ina son kamshi," ta fada tana lumshe ido tare da relaxing a jikin sofa da kyau. Amira ta yi murmushi, Inteesar ta girgiza kai, "Wannan yarinyar." Farida ta murguda mata baki kafin tace "Barni na fadi ra'ayi na." Duk suka fashe da dariya. Sai suka zauna suna hira, daga makaranta, zuwa Lagos, zuwa rayuwa, har zuwa labarin Nana. Da Amira ta ji labarin cikin, fuskarta ta cika da murmushi, "Maa Shaa Allah this is a good news." Farida ta gyada kai, "Wallahi." Amira ta yi murmushi, "Allah mai iko ne." Inteesar ta gyada kai, "Sosai." Sai falon ya cika da tattaunawa, dariya, walwala, da irin farin ciki da ake samu idan kawaye sun kebe a tare. Kuma wannan dai shi ne farkon yammacin da zai zama daya daga cikin mafi dadin kwanakin hutun Farida a Abuja.

Bayan kusan awa daya suna hira, Farida ta mike daga kan kujera, "Wallahi idan muka ci gaba da zama a gidan nan haka, yau ba za muje inda muke so ba." Amira ta daga gira, "Toh me kike proposing?" Farida ta yi murmushi, "Let's go out." Nan take Farida ta tafa hannu, "Yesss!" Inteesar ta girgiza kai tana dariya, "Kinga Amira inde rawar kaine? Uhmm sai kuma kika hadu da Farida itama." Amira ta dauki pillow ta jefa mata, "Ke ma ai kina cikinmu." Duk suka yi dariya. Bayan mintuna kalilan, suka sake gyara veils dinsu, suka dauki bags dinsu, sannan suka fita. Yammacin Abuja ya yi kyau sosai, iskar da ke kadawa tana da sanyi mai dade. Suka shiga motar da suka zo da ita, Amira ta zauna a baya Farida kuma tana front seat. Tun daga parking lot, dariyar su ta fara. "Inteesar kin tuna secondary school?" Farida ta tambaya. Inteesar ta fashe da dariya, "Which part of it?" Lokacin da kika fada wa principal cewa… Tun kafin ta karasa, Inteesar ta katseta, "Kar ki fara." Amira tana kallonsu tana dariya, "Wani abu ne?" Farida ta dafe ciki, "Wannan yarinyar ce ta taba gaya wa principal cewa…" FARIDA! Duk motar ta kaure da dariya, Inteesar har ta kasa maida hankali saboda dariya. Motar ta faka daram a cikin parking lot na Millennium Park. Sanyin AC mai dadi dake hurgawa a cikin motar ya hadu da dadadan kamshin turarensu, wanda ya mamaye ko'ina. Farida ta gyara zaman gilashin idon ta, ta juyo tana kallon Inteesar dake murmushi, "Wato Intee, har yanzu dariyar secondary school din ce a rai? Kalli yadda kika yi parking da sauri." Inteesar ta kashe injin motar, ta juyo tana gyara zaman mayafinta wanda ya zauna daram a kanta, "Farida ke dai bari, ke kika jawo mana wannan dariyar ai. Amira, mu fito ko?" Amira dake zaune a bayan motar ta bude jaka ta ciro Lip gloss ta dan shafa a lebenta, sannan ta gyara zaman abayarta ta emerald green mai adon duwatsun swarovski dake ta walkiya, "Gaskiya mu fito, iskar wajen ma daga nan ana jiyowa da dadi." Suka bude kofofin motar gaba daya suka fito, wani sanyayyan sanyin iska mai ratsa jiki ya bugi fuskarsu. Suka fara takawa a kan tattausan koriyar ciyawa dake shimfide a cikin park din, takunsu cike da natsuwa da kamala irin ta 'yan matan da suka san daular birni. Suka sami wuri mai kyau a karkashin inuwar wata bishiya, kowace ta gyara zamanta. Kafin suka kira waiter sukayi order Ice Vanilla Latte masu sanyi da Croissants masu laushi. Bayan sun gama cinye-iyensu, Amira ta mike tana gyara zaman abayarta, "Wai bari mu dauki hotuna mana, kalli yadda hasken ranar yamma (golden hour) ya sauka a kan bishiyoyin nan." Suka fito da wayoyinsu, suka shiga fito da mabanbantan poses na kasaita da nuna kyansu. Farida ce ke ta kokarin saita musu angles masu kyau inda hasken yake dukan fuskarsu fes. Suna tsaka da hotunan, suka hango masu dawakai dake tafe a hankali a kan koriyar ciyawar. "Wow! Gaskiya sai mun hau doki yau," Amira ta fada cikin zumudi, ta kalli Farida suka tafa hannu. Ba tare da bata lokaci ba, Amira da Farida suka nufi dawakai guda biyu masu kyau da aka kawata su da kayan ado. Kowace ta hau saman dokinta cikin karsashi da dariya mai sauti, suna zagayawa a hankali suna waving hannu. Inteesar kuwa ta ja baya da sauri, ta matse mayafinta a kirjinta, fuskarta ta bayyana tsananin tsoro; ta rika kallon dawakai dake takawa, idanunta sun fito waje. Farida dake saman doki ta fashe da dariya tana nuna ta, "Intee! Dubi yadda kika koma daidai kusa da bishiya saboda tsoro. Gaskiya baki da jarumta sam!" Amira ma ta biye mata suna ta mata dariya duka, yayin da Inteesar ta turo baki tana cewa, "Ku dai ji da shi, ni dai ba zan hau ba." Wannan yanayin ya kara kawo musu wani farin ciki da nishadi mai dadi suka dade suna wasa da dawakan a wajen. Bayan sun sauko daga kan dawakan suna takawa a hankali don komawa inuwar bishiyarsu, wani matashi mai gayu da asalin tsafta sanye da tsadaddan dinkin yadi mai kalar sky blue ya fito daga cikin rukunin mutanen wajen. Ya dade yana kallon Inteesar tun lokacin da take tsoron doki, kuma kyan da ta yi cikin gown dinta ya tafi da hankalinsa gaba daya. Ya matso kusa da nufin yayi magana da ita, fuskarsa dauke da murmushin matasan samari, "Sannunku 'yan mata, don Allah alfarma nake nema a wajen amarya…" Ya fada yana pointing Inteesar. Inteesar ta hade fuska, ta janye idanunta daga kansa ta kalli gefe guda, ta yi kamar ba ta ma san da zaman mutum a wajen ba. Ganin yadda ta nuna masa halin ko-in-kula da nuna rashin sauraronsa, ya sa matashin ya san ba ta da lokacinsa, ya dan gyara tsayuwarsa sannan ya janye jiki ya wuce cikin sanyin gwiwa. Farida ta saki wata daddadan dariya ta taba kafadar Inteesar, "MashaAllah, kalli yadda kika koro mutumin nan. Aliyu dai ya riga ya kame zuciyarki." Lokaci ya tafi cikin dadin hira har sai da yamma ta yi lis, garin Abuja ya canza kala zuwa launi na musamman bayan gabatowar magariba. Suka gudanar da sallar Magrib a wani fili mai tsabta dake cikin park din. Bayan sun kammala, suka fara shirin barin wajen. Wayar Amira ta yi vibrating; ta duba screen, nan take wani dan murmushi ya bayyana a fuskarta. Farida uwar yan tsegumi tace, "Aha." Amira ta zaro ido, "Mene ne?" Mr right is calling. Inteesar ta yi dariya. Amira ta girgiza kai, "Kuyi shiru." Farida ta matsa kusa da ita, "Shine ai answer the call kar ya gaji." Amira ta bude baki, duk suka fashe da dariya. Bayan mintuna kalilan, ta amsa kiran ta yi magana a hankali, sai ta kashe ta juya tana kallonsu, "He's coming." Farida ta dan daga gira, "Oho." Inteesar kuwa tayi murmushi. Kusan mintuna ashirin bayan haka, wata mota ta tsaya kusa da su. Amira ta mike, "That's him." Farida ta yi murmushi, "Okayyy." Inteesar ta yi dariya tana girgiza kai. Bayan sun yi sallama, Amira ta rungume Inteesar, "Sai gobe ko?" In Sha Allah. Ta rungume Farida, "Drive safely." Don't worry. Suka yi sallama, Amira ta shiga motar saurayinta, motar ta tafi. Suka shiga motarsu, Inteesar ta kunna engine, suka kama hanyan zuwa gida.

A wannan lokacin dare ya fara sauka a Abuja. Farida tayi resting bayanta da bayan kujera ta lumshe ido tana jin sanyin AC, "Wallahi na ji dadin yau." Inteesar ta kalle ta na dan lokaci, "Ni ma." Sai suka ci gaba da tafiya cikin nutsuwa. Wayar Inteesar da ke kan dashboard ta yi vibrating, Farida ta waigo sai ta ga sunan da ya bayyana: Mi Amor. Nan take ta fara dariya, "Aha." Inteesar ta harare ta, "Me?" Ga shi nan. Inteesar ta kasa hana kanta murmushi, ta dan rage volume na rediyon motar sannan ta daga kiran. "Assalamu alaikum." A daya bangaren, muryar Aliyu ta fito cikin natsuwa, "Wa alaikumus salam Babygirl." Wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta. "Kina lafiya?" Alhamdulillah. Kai fa? Very well. Sai ya dan yi shiru, "Kina ina?" Ina hanya. Daga ina? Inteesar ta yi murmushi, "Daga outing." With Farida and Amira? Ta zaro ido, "How did you know?" Aliyu ya yi dariya, "Saboda na san Farida ba za ta zo Abuja ta zauna a gida ba." Farida ta ji an ambaci sunanta, ta daga murya, "Na ji fa." Aliyu ya yi dariya, "Good evening Farida." Good evening Angonmu. Nan take Inteesar ta dafe goshinta, "Farida." Farida ta fashe da dariya. Aliyu ya sake mayar da hankalinsa gare ta, "So…" Uhmm? How was your day? Inteesar ta jingina da seat dinta, wani murmushi yana zaune a fuskarta, "It was beautiful." Tell me. Sai ta fara ba shi labarin komai, yadda suka je gidansu Amira, yadda suka yi hira, yadda suka fita yawo, yadda suka yi dariya, da yadda Farida ta kasa daina magana. Aliyu yana sauraro cikin nutsuwa; lokaci-lokaci yana dariya, lokaci-lokaci kuma yana yi mata tambayoyi, kamar wanda yake son sanin ko da karamin abin da ya faru da ita ne. Da ta gama, sai ya yi shiru na wasu dakiku, "Kina farin ciki?" Tambayar ta zo a hankali, mai sauki amma mai nauyi. Inteesar ta yi murmushi, "Eh." Aliyu ya sauke numfashi, "Good." Why? Because your happiness matters to me. Nan take zuciyarta ta yi wani irin bugawa. Motar ta tsaya a traffic light. Inteesar ta dan kalli sararin sama, sai ta ce a hankali, "Mi Amor." Na'am. Na yi kewarka. A daya bangaren, Aliyu ya lumshe idanunsa, murya mai laushi ta fito, "Me yasa kike son ki sa na hau mota Yanzu na kamo hanyar Abuja?" Inteesar ta yi dariya, "Ban ce haka ba." But I miss you too. Murmushinta ya kara fadada. Sai ya yi shiru na dan lokaci kafin ya tambaya cikin wani irin salon nasa, "Toh… Hope babu wanda ya kalle min mata yau." Farida ta juya da sauri, ta rufe bakinta da hannu tana dariya. Inteesar kuwa ta yi murmushi, "Mi Amor." Na'am. Ko an kalleni… Ya yi shiru yana sauraro, sai ta ci gaba cikin murmushi, "Ni ban kallon kowa." Aliyu ya dan gyara zamansa, "Oh really?" "Yes" "But Why?" ya tambaya Inteesar ta yi dariya sannan ta ce a hankali, "Saboda ni makaunia ce idan maganar kallon wasu maza ne. Kai kadai nake kallo namiji." Na wasu dakiku, Aliyu bai ce komai ba, sai numfashinsa kawai take ji. Daga karshe ya yi murmushi, murmushin da ya fito har cikin muryarsa, "Babygirl…" Uhmm. I love you so much. Ta lumshe ido, "I love you way more." A wannan lokacin, motar ta shiga layin gidansu, fitilun gidan suna haskakawa daga nesa. Aliyu ya lura daga sautin motar, "Kin kusa isa gida ko?" Eh. Good. Sai ya yi shiru kafin ya ce a hankali, "Ki shiga lafiya." Okay. Text me when you enter. In Sha Allah. Sai ya dan yi murmushi, "Good girl." Wani irin kunya mai dadi ya sake mamaye ta, Inteesar ta lumshe ido tana murmushi. Kiran ya katse, amma murmushin da ya bari a fuskarta bai katse ba. Kuma Farida, tun kafin motar ta tsaya, ta riga ta fara dariya, "Intee…" Inteesar ta waigo, Farida ta girgiza kai, "Kin shiga uku. Gabadaya fa kin manta Ina existing a wajen nan."