Chapter 8
by @hauwa3030
*đź’«MATAR SALMAN đź’«*
➡️ *PART ONE*
*Page 8*
Yana tsaye idanunsa a kaina ya rasa ma me zai ce min. Ganin ba daina kukan zanyi ba, sai ya daure yace ”Shikenan taso muje ciki ya isa kukan.”
Ba musu na tashi na dauki abincin su ya wuce gaba na bishi a baya. Bayan mun zauna ya dan sauke ajiyar zuciya yace ”Bansan me yasa kike kuka ba amma dai nasan kinji maganata Salima ne ko? Rumaisa ko dai kina son Ahmad din ne?”
Girgiza kai nayi nace" Yaya ni bansan shi ba fa sai yau ne haduwarmu ta farko.”
Yayi ajiyar zuciya sannan yace ”To meyasa kike kuka?”
Na share hawayen da ya ke zubowa nace ”Bana son ace nice silar rabuwarka da Salima bayan kun dade kuna tare kowa ya sani.”
Shiru yayi shima tsawon lokaci, na dauka ma ko maganar tawa ta bata masa rai ne har ya kasa magana.
Don haka nayi kasa da murya nace ”Kayi hakuri idan maganar da nayi ta.....
Ya girgiza kai yace ”Baki bata min rai ba, kawai abinda nake son ince miki shine ki dinga sanin irin mutanen da zaki na mu'amala dasu domin duniya ta zama abin tsoro, mutane irin su Ahmad ba alkairi bane a rayuwarki.”
Na gyada kai nace ”To Yaya.” Yaci gaba da faɗin ”bansani ba kila kina da ra'ayin yin aure yanzu idan kika sami wanda kike so, bazan hanaki ba kar ki ga abinda ya faru dazu kiji tsoro, sai dai faa ki sani bazan taba yarda ki auri mutumin da bai cancanta ba, domin nayiwa Goggo Amina alkawarin zan kula da dukkan lamuranki don haka bazan taba yarda kiyi mu'amala da gurbatattun mutane ba Rumaisa.”
Nace ”Zan kula Yaya.”
Yace ”Shikenan ki tashi ki tafi.”
Na dan sosa kai nace ”Yaya dama maganar......
Nayi shiru na rasa ta inda zan fara maganar.
Shiru yayi yana saurarena jin nayi shiru yasa shi fadin ”Shikenan ki tafi sai kin tuno maganar taki.”
Na daure nace ”Yaya dama shawarace nake son in baka in ranka bazai baci ba.”
Yace ”Go ahead ina jinki.”
Na Sosa kai nace ”Huhm dama dama....nace ....me ..zai zai hana idan iyayen Salima sunki ka aureta.....ka ...auri ...uhm uhmm.... Fa'iza kawai.”
Ina gama fada naji zuciyata na bugawa ina jiran saukan mari don tuni na dafe kumatuna da hannuna duka biyu.
Duk abinda nake yana kallona sannan yace ”In iyayen Salima sunki bani ita, sai dai ki nemo min wata matar, amma banda Fa'iza kam don ban taɓa mata kallon wacce ba ciki daya muka fito ba, kuma akwai wanda yake sonta ai.”
Na girgiza kai nace ”Bata da kowa Yaya kai kawai take so.”
Yace ”Bana sonta idan aikoki tayi kuma kika mata kunne daga yau makamancin wannan maganar kar na kara ji.....Ke kuma tunda kin iya campaign to na baki aiki nima ki nemo min wata matar kawai tunda kema kin fahimci iyayen Salima baza su bani ita ba, yanzu ina nan ina jira sai naji daga gareki, tashi kije dare nayi sai da safe.”
Na mike jikina ba kwari bakina ya jan yo min masifa ni ina nasan inda zan samowa Ya Salman Mata, gaskia Fa'iza da Ya Salman sun sakani a matsala babba. Da wannan tunanin na bar dakin shikam bina yayi da ido har na fita. A waje na hadu da Ya Salim da Ra'is sun dawo a mota muka gaisa Ya Salim yacewa Ra'is ”Ba kaga ni ba saboda ita Salman yaki yarda muje meeting din friends, wai ya gaji wato so yake mu tafi ya samu yayi hira da Rumaisa.”
Murmushi nayi nace ”Kai Yaya ba fa haka bane, abinci na kawo muku yanzu.”
Ra'is yayi murmushi yace ”Ba wani nan mun ganoku tuni, kar ku raina mana hankali.”
Dariya nayi nace ”Wallahi fa ba komi abincinku na kawo.”
Ya Salim yace ”Ai shikenan idan tayi tsami ma ji.” Ni dai na musu sai da safe na wuce gida, ina Allah Allah kar in sami Inna a daki, aikuwa banci sa'a ba ina zuwa tace min ”Ke kuma daga kai abinci kika je kika zauna, wai ina kika je ne? Don nasan tun dazu ba gidan kike ba tunda su Salim yanzu dawowarsu Salman kuwa nasan ba dariya ma yake miki ba bare ince gunsa kika zauna ina kika je?”
Na danyi shiru sannan nace ”Inna Yaya ne ya sakani aikin shirya masa kayansa na kara gyara dakin.” Ina fadar haka na wuce ciki bina tayi da kallon tuhuma amma tayi saurin watsarwa taci gaba da harkokinta.
A kwanakin kowa sai da ya fahimci Salman ya sami sabani da Salima don kuka ta dinga yi tazo ta gayawa Inna ta fadawa Ya Salim harma da Sadiya nace kashhh!
Inna kam bata ji dadi ba ta tambayi Ya Salman yace shi dama ba wani son ta yake ba fa, kawai tausayi take bashi ganin tana da hankali amma ake son hadata aure da wani shashasha mara tarbiyya.
Inna tana kallon shi da mamaki tace ”Hmm Salman kenan, Salima ta gayan komi fa wato saboda ɗan'uwanta yace zai auri Rumaisa.........
Ya katseta da faɗin ”Inna Ahmad fa ba mutumin arziki bane, karya kuma takeyi, ɗan iskane zai batawa Rumaisa rayuwartane ba kuma auren
ta zaiyi din ba.”
Tace ”To sai me kai ina ruwanka me ya shafeka? Waya fada maka Rumaisa zatayi abin kirki? Bari kaji in kara jaddada maka indai Amina ce ta haifi Rumaisa to Rumaisa bazata taba zama ƴa ta gari ba, don ma kaji da kyau don haka ka fita harkanta taje tayi duk abinda take so ba ruwanka. Salima kuwa ita tafi dacewa da kai don haka ga dama ta samu karkayi wasa da shi.”
Shiru yayi can kuma yace ”Inna Ahmad fa ba auren.....
Ta katseshi da fadin ”Na shiga uku ina maka maganar Salima kana min maganar Rumaisa, to kai meye naka ko aurenta zaiyi ko ba aurenta zaiyi ba, ai sa'a ma taci da Ahmad yace yana sonta ɗan babban gida irin wannan sannan uwa uba mahaifinsa gwamna fa? Ai ba wanda ya kaita sa'a in dai zai aure ta da wannan bakin fentin da ke tare da ita na rashin takamaiman asali Hmmm......
Ya katseta da fadin ”Kawai Inna ki bar maganar nan, ni zan tafi in kina bukatar wani abu ki turo Zainab.” Ya fita da sauri ransa a bace.
Faiza kuwa koda mukayi waya na fada mata duk yadda nayi da Ya Salman. Shiru ta danyi sannan tace ”Hmmm Rumaisa kinsan meya ke faruwa?”
Nace ”A'a me ya faru ne sis?”
Tace ”Kinji wai ashe tuntuni wannan Yaya
Ra'is wai sona yake, babu wanda ya fadan a cikinsu wai suna jiran sai na fara University na mallaki hankalina kiji wani abu kuma don Allah?”
Cikeda mamaki nace ”To ke waya gaya miki?”
Tace ”Shekaranjiya suka shigo Zaria dukansu ai shine fa yake fadamin, Rumaisa in fada miki su Yaya suka min tittsiye, kinga yanda shima Yaya Ra'is din ya rikice daga ganina ko kunyan su Yaya baiji ba ya dinga min surutai kamar zai cinyeni?”
Dariya nayi nace ”Wayyo Allah sisi na aikuwa guy din ya hadu wlh ki amince kawai musha biki. Don dama abinda kike buri kenan ai, aure kike so ido rufe nasani.”
Ta ɗanyi dariya tace ”Ai aure abin so ne kedai, sai dai fa nafi son jarumi inga namiji a tsaye kamar Yaya ba wai irin wadan da basuda banbanci da mata ba, Ra'is ɗin naga kamar yayi slow da yawa nidai gaskiya bana son irin shi.”
Dariya nayi nace ”Ai ba daga nan bane Hajjaju, kuma wallahi mutumin nan daga gani zaki sha love wurinsa da tarairaya ya zauna cikin turawa fa, Nidai gaskiya naga kun dace indai zan baki shawara ki ɗauka to kawai ki amince musha biki.
Tace Hmm to shikenan Allah dai yasa yadda kike hasashen nasa ya zama gaskiya, amma wallahi nidai Fa'iza har abada bazan daina son Ya Salman ba, amma anfi karfina ban isa na bijire ba yanda su Yaya suka dage akan maganar Ra'is shi kuma uban gayyan cewa yayi ma auren a karshen wannan shekaran za'ayi yanzu muna watan hudu fa.”
Nace ”Kai kai kice sharp sharp, masha Allah, Allah muma ya samu a danshinki nida Sakina, Allah na tayaki murna sis Allah sanya alkhairi.”
Tace ”To ameen da, kuma zamu tayaki da addua sis inshaa Allah amma Sakina kam ta sami wani Prof Hafiz babban lecturer ne anan, har sun daidaita fa kinga yadda yake rawan jiki akanta hmm amma fa kiyi shiru kinsanta da zurfin ciki wai bata son kowa ya sani sai maganar tayi karfi.”
Nace ”To masha Allah na tayata murna ta shiga ABU da kafar dama ni dai har yanzu shiru ne.”
Tace ”Kar ki damu sisi Allah zai kawo na gari Insha Allah, wani jinkirin fa alkhairi ne.”
Nace ”Hakane kam Allah yasa to.”
Tace ”ameen.” Anan mukayi sallama. Na zauna shiru ina tunanin rayuwata yadda zata kasance ni kuma.........
Yau mun gama lectures da wuri don haka na shirya zan tafi gidan Mama sai ga Salima tazo dakinmu abin ya bani mamaki sosai, nasan dai tana shigowa hostel gun kawayenta don nikam bamu ishi juna kallo ba.
Maryam ce tayi mata magana inaji suna gaisawa nikam naci gaba da harkokina kamar ban ganta ba.
Maryam tuni ta fita ta barmu don tace zatayi wanki ne.
Tana zaune shiru har na gama shiryawata na dauki jakata zan fita a sanyaye tace ”Rumaisa gurinki nazo faa.”
Na kalleta cike da mamaki sannan nace ”Ni kuma? To Allah yasa lafiya?”
Tace ”Lafiya qalau in ba damuwa ki zauna.”
Nace ”A'ah kinga sauri nake, zan tafi cikin gari, ke dai ki fadi maganarki ina jinki daga nan.”
Ta numfasa cikeda damuwa tace ”Nasan kinsan komai gameda abinda ke faruwa tsakanina da Ya Salman.”
Kallonta nayi sama da kasa na yatsuna fuska nace ”Uhumm.”
Tuni hawaye ya cika idanunta ta sunkuyar da kanta tace ”Rumaisa nazo in rokeki ne don Allah ki amince da Yaya Ahmad, wlh duk abinda ake fada a kansa zai daina domin da bakinsa yace min in dai har kika amince masa zai iya barin komi saboda bai taba jin son wata 'ya mace kamar yadda yake jin sonki ba wlh Rumaisa ya Ahmad na sonki kamar yadda Ya Salman ke sona don Allah kiyi hakuri da abinda ya faru a baya ki karbi soyayyar Ya Ahmad ko nima zan samu su Dad su amince da aurena da Salman.”
Murmushin nayi sannan nace ”hmmm wannan magana taki kamar tatsuniya ne ko labarin novel ko film. Salima ni bana son Ahmad ko da kuwa baida wata mugun hali. Sannan tsakaninki da Ya Salman kuma shawara daya zan baki shine ki tashi tsaye wurin addua kwanciya baccin dare ba naki bane ki tashi kiyi nafila ki dinga istikhara ki kai ma Allah kukanki ya miki zabi mafi alheri ba wai ki dinga kuka kije nan kije can kina a taimakeki Ya Salman ya juya miki baya ba, abin kunyama yake bani nikam.”
Share hawaye tayi sannan tace ”Hmm bazaki gane ba don har yanzu baki san meye so ba, shiyasa baki fahimtata, amma babu komai nagode.”
Ta mike ta fita na bita da kallo hade da tabe baki nace ”Ke da kika san shi meya amfanar miki banda bakin ciki da takaici, ai namiji sai a slow, ku duba yanda ya ke riritata dinnan amma lokaci daya ya juya wai shi dama ba wani sonta ma yake ba tausayi take bashi kawai hmm!”
Ban sake biyowa ta kanta ba gidan Mama na tafi, tunda na shiga ɓangaren nata ban sameta ba don haka na wuce bedroom na ajiye jakata kitchen na nufa na shiga dube duben me zanci don yunwa nakeji sosai. Daga karshe noodles kawai na tafasa da kwai da sardine na dauko lemo mai sanyi na zauna a dining hankali kwance kaman gidan Ubana.
Na soma ci kenan saiga kiran Ya Salman. Murmushi nayi nace " su Yaya sai yau aka tuno dani.”
Na daga hade da yi mashi sallama. Ya amsa kamar kullum nace ”Yaya ina wuni?”
Yace ”Lafiya lau fatan kina lafiya kema?”
Murmushi nayi nace ”Lafiya lou Yaya, naga sakon kudi na gode Allah ya kara budi, na ta kiranka baka dauka ba.”
Kai tsaye yace ”aiki nakeyi.”
Muka danyi shiru yace ”Kina ina ne haka?”
Nace ”Gidan Mama nazo bai jima ba.”
Yace ”Ok. To ya maganarmu na jiki shiru?”
Rass naji zuciyata ya tsinke da kyar na tattaro nitsuwata nace ”Yaya dama tuntuni na ke so in kiraka in gaya maka ni ban samu ba......
Da sauri yace ”What! Kina haukane, shine kika saka na saki jiki ina jiranki bayan kinga mun fara shirinmu, nan da watanni kadan zamu kammala komi, Salim fa tuni ya sami mata a Abuja sun daidai ta.”
Shiru nayi hankalina tashe.
Yace ”Kinga ni fa ke nake jira ki samo min, zan kara miki lokaci, kuma nafison fara doguwa kyakkyawa mai gashi, mai ilimin Arabic da boko wayaiyiya mai tarbiyya nitsassiya kin gane ai? Na baki satar amsa yanzu sai naji daga gareki.”
Ba shiri na runtse idona, Wayyo Allah na na fada a raina na daure nace ”Yaya kawai ka auri Saliman kaga ɗazu ma muka hadu tayi min maganarka, tana cikin damuwa sosai ......
Ya katseni da fadin ”Kar ki kuma kawo min zancen Salima daga yau bana so, ki kyaleta taje ta auri ɗan'uwanta tunda shi iyayenta sukeso bani ba.”
Nace ”Inshaa Allah Yaya bazan kara ba kayi hakuri.”
Yace ”Shikenan ki gaida min Goggo Amina.”
Ya kashe wayar daga ji nasan ransa a bacene.
”Ohh Allah mutum kamar mai aljanni hmm.” Nayi shiru ina tunanin irin matar da ya lissafo min yake so wai dama Yaya yana lura da Mata ne haka?”
Hmmm kawai na tsinci kaina da yin murmushi na mike na tafi dakin Mama gaban madubi na tsaya ina karewa kaina kallo a madubi. Ni dai farace kuma doguwace haka nan ina da gashi, to ko ince mishi gani kawai a wuce wurin?”
Kunya ce ta kamani da sauri na juya na bar gaban madubin na fita zuwa dining anan na iske Mama zaune a palon taci kwalliya da wata lace mai shegen tsada sai kamshi take tashi.
Tana ganina tace ”Ke kuma yaushe kika zo?”
Nace ”Bai jima na shigo ba kya nan.” Batayi magana ba na wuce na dauko abinci na a dining duk ya huce ma na dawo Palo na zauna nace ”Mama ina wad'ancan dogayen riguna da kika ce kin ajiye mun zan tafi dasu in zan koma?”
Tace ”Ai da na baki ba cewa kikayi kaya sun miki yawa ba? Tuni na bawa masu bukata.”
Na bata fuska nace ”Mama fa cewa nayi ki ajiye mun sai na sake zuwa.”
Tace ”Tsohon zance kenan. Sai kiyi hakuri in na sake zuwa Dubai a kawo miki wasu.”
Shiru nayi ina cin Noodles din. Ta kalleni tace ”Ba kije gidan naku bane?”
Nace ”Ni na kai wata banje ba sai dai in kira Kawu a waya mu gaisa kawai, wani abu ya farune?”
Tace ”Kedai baki kyauta ba, nima shekaranjiya da naje ne, na sami Raihana a gida tana wanki shine Yayan yake ce min wai sakinta akayi nace to yaushe akayi auren ma tukunna?”
Na zaro ido nace ”Raihana kuma ba Sadiya ba? Tab aiki ya sami Inna, don Sadiya ma tana hanya ba fata nake musu ba kam. hmmm bari ya Salman yaji labari, Sadiya fa har duka tasha.”
Mama tace ”To Allah dai ya kyauta, amma ni banga laifinsu ba wallahi, laifin uwarsu ce duk ta bi ta bata yara da rashin tarbiya ga rashin kunya, a zamanin yanzu namiji ka bishi sau da kafa ma ya kuke karewa bare kuma kana mishi rashin arziki, Allah ya shiryesu kawai.”
Nace ”Ameen.”
Kwana daya kawai nayi a gidan Mama na yi shirin komawa school saboda shirin exams. Ina isa makaranta sai ga Ahmad cikin wata mota kuma na daban ba na ranar ba, yazo yayi parking a gefena ya sauko da glass ya leko da kai yana murmushi yace ”Queen Allah yayi haduwarmu yau kuma, na jima a nan ina nemanki ashe kina cikin gari.”
Kamar bada ni yake ba tuni nayi wucewata fuska É—aure.
Sai kawai naga mutum ya tari gabana ya marairace fuska yace ”Haba Queen wulakanta mutum ba dabi'arki bane ba, na sani kowa nakine banzo gunki ba sai da mutane suka tabbatar min da haka me yasa kika zabe ni a cikin mutane kike wulakantani? Don Allah ki gaya min laifina pls my Queen.”
Kauda kai nayi nace ”Ni fa ba wulakantaka nake ba sauri nake I have more important things to do so pls let me......”
Yayi saurin fadin ”Noo my Queen bazan iya barinki ki tafi ba, yau dai kawai so nake ayita ta kare gaskia, haba mana.”
Kallonshi nayi cikin mamakin yadda ya wani marairace fuska, na tabe baki na raba gefe zan wuce kawai ya sake shan gabana sai gashi ya durkushe a gabana har kasa.
Na É—an zaro ido ina mamaki na shiga waige waige ai tuni gayun BUK sun fara cika wurin kasancewar daddaya ne wayanda basusan Ahmad ba yasha zuwa yana musu karyan kudi a hada casu kowa ya rabarbashe son rai don naji labarin har clubs ne dashi,duk wata harkar nishadi na matasa shine mai jagoranta, shiyasa da ya shigo gayu su fara zagayeshi.
Da sauri na kalleshi nace ”Mene ne haka don Allah ka rufa min asiri ka tashi, kaga tuni ka fara sa attention din mutane yana dawowa kanmu.”
Ya girgiza kai yana buda hannayensa yace ”Ban damu ba kowa ma ya ganni a haka me ne ne a ciki don na durkusa a gabanki wlh kin cancanci in miki kuka ma, kawai dai babban burina shine ki amince min ko da kuwa bada soyayya ba burina inga muna tare muna gaisawa muna mutunta juna shikenan faa kawai.”
Shiru nayi na rasa mafita ga idon jama'a kanmu na kalleshi nace ”Shikenan naji na amince zamu dinga gaisawa hade da mutunta juna amma babu maganar soyayya ka amince?”
Murmushi yayi haɗe da salute dina yace ”Yes my Queen.”
Ya mike yana kakkabe kayansa sannan ya juya ya kalli mutanen da ke kewaye damu yana murmushi yace ”My guys daga karshe dai nayi winning heart dinta ku tayani murna, kuna yau zan shirya mana party na musamman kowa ya cashe.”
Tuni gayu suka shiga ihu suna tafi ni dai anan na barsu sai ruwan kudi yake musu suka sake kiÉ—a suna rawa, harda ordern snacks ya musu da soft drinks.
Ina zuwa hostel na cire kayana na nemi wando da vest na saka na jawo takarduna na hau karatu don ko da wasa banson in fadi jarabawata.
Anan wayata ta shiga ringing na duba naga Sadiq ne mijin Raihana dan tsaki nayi nace ”Anyita kira baka dauka ba tuntuni sai yau ka gani.”
Kamar bazan daga amma dana tuno da Raihana kawai na dauka. Bayan mun gaisa nace ”Malam na nemeka tun shekaranjiya sai yanga ake mana ko dai an sami wata ce aka share mu?”
Yace ”Uhumm ke dai Rumaisa bari ku din ne sai a slow.”
Nace ”Ba wani nan Malam yanzu dai gaya mana laifinmu sai mu baka hakuri, ai matar na tuba bata rasa mijin aure ko?”
Ya danyi shiru yace ”Hakane kam, amma Rumaisa ba'a son raina hakan ta faru ba kin dai san ina son Raihana amma abubuwa da yawa yasha faruwa daga aurenmu zuwa yanzu ina ta hakuri amma babu canji, yanzu abin ya wuce kaina ya koma iyayena da 'yan uwana ni kuma gaskia wannan kam I can't tolerate it shi yasa na sawwaka mata amma ba don bana son ta ba kin gane?”
Na ce ”Eh na gane kuma a gaskia Raihana bata kyauta ba kayi hakuri dama shiyasa na kira don in baka hkr Malam ka daure ka dawo da ita ba don halinta ba ni kuma inshaa Allah zan yi kokari in gayawa Ya Salman domin a mata fada a ja mata kunne, tasan cewa aure ba abin wasa bane sannan iyaye ko ba su suka haifeka ba basu cancanci ka wulakanta su ba, inshaa Allah zata daina kayi hakuri.”
Yayi shiru da farko sai daga bisani yace ”Babu komai Rumaisa idan har Raihana ta gyaru me zai hana in dawo da ita ai mugun halinta yaja na sallameta.”
Nace ”Ta gyaru ma inshaa Allah, kuma Malam mun gode sosai Allah ya bar kauna.
Yace ”Na gode Rumaisa Allah ya saka da alkhairi..... ke bana ganinki ma a school ko office baza kina zuwa mu gaisa ba, ko don ba'a department dinku nake lecturing ba?”
Nayi dan murmushi nace ”Wallahi Malam bana samun lokacine, zanzo watarana inshaa Allah.”
Yace ”To babu matsala Rumaisa sai dai na ganki Nagode sosai
Daga nan mukayi sallama, shiru nayi ina mamakin hali irin na Sadiya da Raihana, ya kamata yanzu kam su nitsu ai ko....
RUMAISA SALMAN BY MAMAN KAUTHAR