HAƊUWAR ƘADDARA

Chapter 23&24

by @aishatuoumbhanat42

      💦HAƊUWAR ƘADDARA💦
               (Hatsari da Rai)

Story and writing by ✍️
AISHA (Oumbhanat)✍️❤️‍🔥

Follow my WhatsApp channel 
***

Follow this link to join my WhatsApp group 
***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W\.A)*
*Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi*.✏️

Wannan shine Littafina Na farko dan haka sabuwar marubuciya ce, idan Anga kuskure Aciki to Ayimin Uzuri. 

FREE BOOK 

                 ~●~●~●~●~●~●~
       BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PAGE 23

              ♧♧♧♧♣︎♧♧♧♧

JAZY

Saida ya tabbatar da an tafi kai kayan inda ya dace kafin ya baro gurin ya nufo gidansu da tun da ya fito da safe bai koma ba.

A falo ya tadda Mamma a zaune ta zabga tagumi har ba ta san lokacin da ya shigo ba, zama ya yi a kusa da ita yana kamo hannayenta, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kalleshi a hankali ta ce.

“Ka dawo Babana?, bari a kawo maka abinci.” Ta faɗa tana ƙoƙarin ta shi tsaye.

“A'a Mamma bana jin yunwa yi zamanki, meke damunki ne Mamma?.” 

“Ba ko mai Babana kawai bana jin daɗi ne.” 

Ya kaɗa kai ba dan ya yarda ba, a hankali ya ji ta fara magana.

“Babana dan Allah ka daina waɗan nan abubuwan, kadaina shaye-shaye yana zubar da ƙima da daraja, ga zunubin da kake kwasa a wajan Allah, kana jawa kanka zagi a wajan mutane.”

Ta ɗan kalle shi ta ga ko yana jinta sannan ta ci gaba.

“Ga wannan harkar dabar da kuke yi duk sanda rigima ta haɗo ku sai kun zubda jini, bakasan cewa da zubar da jinin mumini babban bala'i ne da yake hana al'umma zaman lafiya ba?.”

‘Wai wannan ce ake faɗa masa ba ta ƙaunarsa, shi kuma ya hau kai ya zauna a lokacin da sheɗan yake kaɗa masa gangi, ga wanda suke nuna sune masoyansa a da yanzu ba shi da maƙiya kamar su’ Ya faɗi hakan cikin ransa, a zahiri kuma sai ya ce.

“Ki ci gaba da yi mun addu'a Mamma in sha Allah wata rana ko mai zai zamo labari.” 

Mamma ta jinjina kai tana murmushi ‘tabbas kam tana ganin tasirin addu'a, wai yau ita ce ta ke zaune tare da ɗanta wanda aka rabata da shi shekarun baya ya daina ganin ƙima da darajarta ita kam ba ta da abun godiya sai Allah’.

Shigowar su khalid ne ya katse shirun da suka yi ƴan biyu ne a bayansa sanye da uniform light blue da farin hijabi suna ajin ƙarshe na babbar secondary, da sauri suka zo wajansa suka tsaya suna gaishesa, ya saki hannun Mamma ya kamo nasu yana ɗan murmushi ya ce. “ ya ne twins ya school i hope kuna karatu dai?.”

Baki suka washe suna dariya cike da farinciki, yanzu kan suna matuƙar son Yayansu ba kamar da ba,in banda faɗa babu abun da yake musu, yanzu kuwa sun san yana sonsu.

Tashi tsaye ya yi ya fara tafiya zuwa ɗakinsa har ya kama handle zai buɗe sai ya juyo ya yafito Khalid da hannu sannan ya buɗe ya shiga ɗakin,bin bayansa ya yi shima ya shiga ɗakin.

A zaune ya tadda shi a bakin gado, sai ya nufi kan sofar da ke ɗakin ya zaune yana gaishe shi, ya amsa sannan ya fara tambayarsa me ya faru bayan ya fita.

Khalid ya sunkuyar da kai kafin ya ɗago ya fara basa labarin abun da ya faru.

Abba ne ya shigo part ɗin da safe suna breakfast ya kalli Mamma ya ce.

“Ke Juwairiyya ki saurare ni ki ji me zan faɗa miki, ba ruwana da harkar bikin ƴarki iya kayan ɗaki zan yi sauran abubuwa kuma ki san yanda za ki yi da su dan haka zan tura miki 2.5M gaba ɗaya kada a ƙara neman komai daga gare ni.” yana kaiwa nan a maganarsa ya juya ya fita ya barsu cikin tsananin mamaki, ita kuwa amarya Nuriyya har ta fara kuka.

“Ki yi shiru Nuri babu abun da baza a yi miki ba irin na ƴaƴan gata, ki kwantar da hankalinki in sha Allah baza muji kunya ba.” Mamma ta faɗa tana murmushi. 

Wallahi Allah Yaya gabaɗaya Abba ya sauya sai abun da Maman su Sajida ta ce yake yi.

Jinjina kai kawai ya yi sannan ya ce.
“Saura kwana nawa bikin?.”

“Saura sati kwana 25 yanzu.” Khalid ya ba shi amsa.

“Ok, zan tura maka 3M kuje da su ta zaɓi duk abun da take so a siya mata.”

Cikin mamaki Khalid yake kallonsa ina ya samu kuɗi haka, shi dai yasan Yayan nasa baya sana'a, amma ganin babu fuskar tambaya yasa kawai ya yi godiya sannan ya fita daga ɗakin.

Kwantawa ya yi ya yana ta tunani kafin can bacci ya kwashe sa.

             ♡♡♡♡♥︎♥︎♡♡♡♡

NANAH

“Dan Allah Nanah ki yi sauri ki gama wannan kwalliyar ki zo mu tafi.” faɗin Habiba da take yafa mayafi.

“To na gama ai sarkin ƙorafi.” Ta faɗa tana gyara yafen mayafinta, sannan ta ɗauki handbag ɗin ta suka yiwa Mutanen gidan sallama suka fita.

Abun hawa suka tare suna faɗa masa inda zasu, suga suka yi ya ja suka yi gaba, hira suke ɗan taɓawa har suka kai gidan Aunty binta da ke tarauni suka sallama shi suka fara tafiya cikin layin.

Gidan Aunty Binta babban gida ne dan kuwa har da sirikarta a gidan da kishiyoyinta biyu, mijinta babban ɗan kasuwa ne yana da rufin asiri ba laifi, ita ce mace ta biyu a gidan Hanifa ƙawarsu Nanah ƴar uwargidanta ce.

Da sallama suka shiga sashenta, tana zaune ita da yaranta biyu Mubin da Na'im ƴan biyu ne.

“A'a yau kace ina da manyan baƙi, sannun ku da zuwa.” Aunty Binta ta faɗa fuskarta cike da fara'a.

Zubewa sukai akan kujera suna gaisheta,kafin su miƙe su shiga sauran sassan gidan suka gaida su sannan suka dawo tare da Hanifa aka shiga fira Har zuwa ƙarfe 6 na yamma, sannan suka yi shirin tafiya gida bayan sun amshi style ɗin Aunty Binta ta basu saƙo su kaiwa Inno saboda baza ta samu damar zuwa gida nan gaba ba, suka yi mata sallama Hanifa ta rakasu bakin titi suka tare napep suka shiga.

      ~~~~~~~~~●~~~~~~~~~
JAZY

Sai ƙarfe huɗu da rabi ya farka daga barcin da ya ɗaukesa, tashi ya yi ya faɗa bathroom ya yi wanka da alwala sannan ya fito shiryawa ya yi ya rama sallar la'asar, kafin ya ɗauki wayarsa ya fito falon, dining table ya nufa ya zuba abinci ya ci sannan ya yiwa Mamma sallama ya fita daga gidan.

Yamma ta yi sosai ana wahalar abun hawa yana nan tsaye sai ga mai napep ya zo wucewa da mutane a ciki, Tsaki ya yi amma ba yanda ze yi dole ya tare shi, ganin mata ne a ciki sai ya zauna a gaba, kamar an ce masa ya kalli madubi karab idonsa ya faɗa cikin nata.

Ƙuuuu cikin Nanah ya bada sauti, saurin sunkuyar da kanta ta yi ta daina kallon ko ina Habiba na ta magana ta ji shiru babu amsa hakan yasa ta juyo tana kallonta.

“Ke kuma lafiya kike ta haɗa gumi kamar kin haɗiyi kunama.” Ta tambayi Nanah.

“Ba ko mai.” ta iya cewa.

“A'a wannan kuma ƙarya ne ya muna hira lafiya lau na ji kin yi ɗif kuma ki ce ba ko mai, Malama meke damunki ne?.” Ta faɗa tana leƙa fuskarta.

Ganin dai ba kulata za ta yi ba sai kawai ta ƙyaleta, har suka kai kan layinsu, suka sauka bata tsaya Habiba ba wadda take bawa mai napep kuɗinsa, ta kama zuba sauri har tana harɗe ƙafafu.

Daga ɓangaren Jazy kuwa kallo ɗaya ya yi mata ya ganeta, ko me yasa suke haɗuwa shi fa wannan yarinyar haushi take bashi ta fiya tsoro, ya siririn tsaki, Har suka sauka bai ɗago kansa ba dan shi a layin dake gaban nasu zai sauka.

            ■■■■■■■■■■■■

Ajiyar zuciya ta sauke ganinta zaune a ɗakinsu lafiya ƙalau, yanzu kam ta yarda da maganar Umma da ta ce babu abun da za su yi mata.

To wai tsaya ma, kalamansa na rannan ne suke dawo mata in da ya ce mata ‘ki faɗa masa kada ya sake ya shiga gonata idan har hakan ta kasance lallai zai biya farashi’ kenan Hamza yake nufi?, yasan shi ɗansanda ne’ ta ayyana hakan a cikin ranta.

“Lallai akwai aiki to banda abun Sangami ni sai jiya ma nasan waye Hamza.” Ta faɗa tana taɓe baki, sannan ta fito dan yin alwala…✍️

OUMBHANAT ✍️❤️‍🔥



   💦HAƊUWAR ƘADDARA💦
            (Hatsari da Rai)

Story and writing by ✍️
AISHA (Oumbhanat)✍️❤️‍🔥

Follow my WhatsApp channel 
***

Follow this link to join my WhatsApp group 
***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W\.A)*

THE STRONGER'S WRITER'S TEAM 🌟 

FREE BOOK 
              
                  ~●~●~●~●~●~●~
       BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PAGE 24

                  ♡♡♡♡♥︎♡♡♡♡

“Wanne irin wulaƙanci ne haka Nanah kamar wadda wani ya koro ina miki magana ko amsa ni ba za ki yi ba.” faɗin Habiba.

“Yi haƙuri dan Allah wallahi mutumin nan da ya shigo napep ɗan daba ne, na taɓa faɗawa komarsu shiyasa duk in da na gansa alla-alla nake na bar wajan.”

“Ahh to ai sai ki faɗa mun na yi ta kaina.” Habiba ta faɗa tana zama a kusa da Nanah.

“Ba ki da hankali kawai sai na ce miki ki yi hankali da wannan ɗan daba ne ga shi a gabanmu.” Nanah ta faɗa tana hararta.

Dariya ta yi haɗe da tsokanarta wai ta fiye tsoro.
      ~~~○○○○~~~~○○○○~~~
HAMZA

Barka da safiya Inna fatan kun tashi lafiya.”Hamza ya faɗa yana durƙusawa a gaban Inna.

Da murmushi take amsawa “Lafiya lau Hamza ya su Samira.” ya amsa mata sannan ya fara magana.

“Inna dama wata magana mai muhimmanci nake so mu tattauna, akwai yarinyar da nake son aura shi ne nake so a faɗawa Baffa a je a tambayo mun aurenta idan da hali ma a saka rana.” ya faɗa kansa a ƙasa.

Inna ta girgiza kai kafin ta ce “ To aure kuma ka ƙara nemowa bayan duk abun da ya faru a baya.”

Girgiza kai ya yi yana tuno can baya ya sha neman aure amma sai maganar ta lalace ya rasa dalilin faruwar hakan.

“Inna a yi mana addu'a in sha Allah wannan karon babu abun da zai faru sai alkairi.”

Gyaɗa kai ta yi bayan ya gama magana ta ce “To shi ke nan zan faɗa masa Allah ya tabbatar da alkairi.”

Sannan suka ci gaba da fira, yana wajanta har ƙarfe tara da rabi na safe amma ba'a kawo breakfast ba, kallon Raihana ya yi wadda ke kwance a kan gado ya ce.

“Tashi ki je kitchen idan an kammala breakfast ki ɗakko muku.”

Tashi ta yi ta fita daga ɗakin, ko da ta je kitchen ɗin ba abun da ta ga an yi, juyowa ta yi ta dawo ɗakin ta faɗa masa ba a dafa komai ba.

Da mamaki yake kallonta, bai ce komai ba ya mike ya fice daga ɗakin ya nufi ɗakin Samira, a kwance ya gan ta tana danna waya, tsaye ya yi riƙe da murfin ƙofar yana kallonta kafin ya ce.

“Me ya hana ki ɗora abinci bayan kin san Inna tana nan kuma su da wuri suke karin kumallo.”

“To ai gani na yi ga Raihana nan me ya sa sai na wahalar da kaina ai ita ya kamata ta dafa mana ko?.” Ta faɗa tana yatsuna fuska.

Ohh dama ita ce take yi miki girkin kenan, kar ki ɓata mun rai ki tashi ki je ki ɗora abinci.

Haka ba dab ranta ya so ba ta mike fuska a kunbure ta fita daga ɗakin ta shiga kitchen ta fara aikin.
       
             ~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~

JAZY

“Jafar a ina ka samu kuɗi haka ni a sanin da na yi maka baka aikin komai amma ban sani ba ko ka samu aiki ne ba labari.” Mamma ta faɗa tana kallon Jazy wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa.

“Mamma Ina aiki da wani ƙaramin company na haɗa magunguna kuma ina samun kuɗi sosai kawai ki yi amfani da kuɗin kar ki damu.”

Yana gama faɗar hakan ya miƙe ya nufi ɗakinsa dan ba ya son ta ƙara yi masa tambaya be san me zai ce mata ba, yana shiga kayan jikinsa ya fara cirewa ya faɗa bathroom ya yi wanka bayan ya fito ya sa guntun wando ya nufi ma’ajiyar kayan mayensa ya kwaso wasu ƙwayoyi guda huɗu ya ƙura musu idanu yana wani tunani kafin ya buɗe baki ya watsa su ya haɗiye ba tare da ya sha ruwa ba.

Ko minti goma ba a yi ba kansa ya fara juyawa ya nemi bakin gado ya zaune yana dafe goshinsa, lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta fara zano wa idanuwansa wasu hotuna da ba ya son ganinsu, kamar wani mahaukaci haka ya fara kaiwa iska duka yana magana da ƙarfi.

“Ki bar nan, bana son ganinki i will kill you, ke.. ke ce kika kassara min rayuwata sai na kashe ki.”

 Kafin a hankali ya sulale ya kwanta a kan gadon yana zantuka marasa ma'ana.

Bubbuga ƙofar ɗakin ake da ɗan ƙarfi, a hankali ya motsa yana buɗe idanunsa wanda suka ɗan yi ja ogogon da ke maƙale jikin bango ya kalla 06:07am zumbur ya miƙe zaune yana furta. “Astagfiruullah.”

Bathroom ya faɗa ya dauro alwala sannan ya saka jallabiya ya je ya buɗe ƙofar, Khalid ne tsaye.

“Yaya lafiya kake?, tun asuba nake buga ƙofarka baka buɗe ba.”

Bai ce komai ba ya juya cikin ɗakin ya nufi in da yake sallah, shi ma Khalid ɗin ciki ya shigo ya zauna akan gadon yana jiran ya idar da sallar su yi magana.

“Ina kwana Yaya.”

Be yi magana ba sai gyaɗa masa kai ya yi haɗe da lumshe idanu kafin ya buɗe ya zuba su a kansa.

“Yaya dan Allah ka nemo mata ka yi aure lokaci yana tafiya fa yanzu yaushe ka yi auren bare ni ma na yi kar fa mu mutu ba mu yi aure ba.” ya ƙarasa maganar yana karkata kai.

Murmushin gefen baki ya yi kamar ba zai magana ba sai can ya ce “Ka ce kawai aure ka ke so, ba damuwa ka nemo matar zan maka aure ni ba yanzu zan yi ba.”

“A a wallahi Yaya ba haka nake nufi ba kawai dai.” Khalid ya faɗa yana sunne kai ƙasa.

“Kawo mun coffee.”

Ok, Yaya.” Ya faɗa yana miƙewa ya nufi kitchen.
       ~~~~~~●●●●●●~~~~~~

Gidan Alhaji Umar Sabo 

Yau ne ake saka ran zuwan magabatan saurayin Habiba dan a tsayar da maganar aure.

To sun zo dai da kuɗinsu Naira 100k da madaidaiciyar akwati sai sweet da goro, aka karɓa cikin mutunci aka ba su tukwici, amma Baba ya roƙi alfarma a bar saka rana sai an kawo na ƴan uwanta tukunna.

Mama sai buɗe hanci take ƴar ta ta yi goshi ana ta sakarwa Umma magana.

Washegari sai ga na Amira ma sun kawo nasu Ita ma dai 100k ne da ƙatuwar akwati da sweet da goro, sai kuma bakin Mama ya rufe, ana kuma jiran na Nanah aga da me za su zo.
        ~~~~~~~○●●●●~~~~~

HAMZA 

Yau dai Inna ta yi shirin tafiya bayan zaman gwagwarmaya da aka sha da Samira dan kuwa daina aikin komai ta yi a gidan sai Raihana ce ke yi girkin safe kawai take yi saboda Hamza yana gida, don idan ta ga dama ma ficewa ta ke yi sai dare kafin ya dawo take dawowa gidan, amma Inna ba ta taɓa faɗa masa ba haka kuma ta gargaɗi yaran kar su faɗa su ma a gidan take barinsu, a kullum addu'ar Inna Allah ya sa wannan auren da ze yi ya zame musu alkhairi shi ma ya samu nutsuwa a gidansa.

Kasancewar yana cikin hutun aiki sai ya ɗauke su da kansa ya tafi kai su, suka bar Samira cikin murnar ta rabu da ƙaya.

Tunda suka iso ake zuwa yi musu maraba, bai samu nutsuwa ba sai bayan sallar la'asar sanna suka kaɗaice da Baffa, sun tattauna maganar auren da kuma tsayar da ranar da za a je ayi magana da iyayen Nanah, kafin su yi sallama ya kamo hanyar kano.

Da daddare ya fito ƙofar gidan ya kira Nana ba ta amsa ba sai a kira na uku sannan ta ɗaga tana ba sa haƙurin rashin ɗauka da wuri.

“Ba komai habibty albishirinki.”

Daga can ɓangaren Nana da ke kwance akan gadon Umma ta amsa da “Goro fari ƙall habiby.”

“In sha Allah ranar Monday za a zo a tambayar mun aurenki ki zama mallakina ni kaɗai.” Ya faɗa muryarsa cike da farinciki Allah na gani yana son Nanah son da bai taɓa yi wa wata mace ba, dan ko matarsa ba ya yi wa wannan soyayyar.

Cikin kunya ta ke amsa shi har suka gama wayar.

NANAH 

Tsalle ta doka a kan gadon kafin ta dire ta fita a guje tana ƙwalawa Habiba kira.

“Wannan kiran kamar za ki cire mana kunne ga ni me aka samu ne.?”

“Ki faɗawa Baba ranar Monday za su zo.”

“Su waye?” Habiba ta tambaya tana ɗagowa daga wankin da take yi.

Ta harareta “Dallah ki gane mana Hamza nake nufi iyayensa za su zo ranar Monday.”

“Ayyyyuririri.” Habiba da Amira suka haɗa baki wajan sakin guɗa hakan ya janyo hankalin mutanen gidan aka fara tambayar me ya faru, koda suka faɗa musu ai sai Inno ta hau rawa da waƙar za ta aurar da jikoki uku lokaci guda…✍️

OUMBHANAT✍️❤️‍🔥