FreeArewaPen original
HAƊUWAR ƘADDARA
- 1views
- 21chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
🌹Hello 🥰I am a young writer Hausa novelist a story teller I want to use my talent to enlighten the society. I hope you will support me by following, liking, commenting and sharing. Thank you so much my lovers, one love!❤️🔥💔🌹
Sample · Page 1
💦HAƊUWAR ƘADDARA💦 (Hatsari da Rai)✍️Story and writing by✍️ Aisha Sufyan (Oumbhanat)❤️🔥💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️*(J.W\.A)**Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi*.✏️Follow *** channel 👇*** ♡~~~~~~~~~~~~~~♡ 💞Ina rokon Allah ya bani ikon faɗakar da Al’umma,Yahana ni gurɓata tunanin, Al'umma, kura-kuren dake ciki Allah ya yafe mana yanda nafara lafiya Allah yasa mu gama Lafiya Ameen🙏 Wannan shine Littafina Na farko dan haka sabuwar marubuciya ce, idan An ga kuskure A ciki to A yi min Uzuri. 💝Sadaukar wa ga dukkan Ahalina💝TSOKACI: Ƙagaggen labarine banyi shi dan cin zarafin wani/wata ba idan yayi kama da labarin wata/wani To Arashi ne.FREE BOOK BISSMILLAHIR RAHMANUR RAHEEM PAGE 1KANO, GWALE L.GƊorayi,babbaLayin gidan me unguwa.Gidan Alhaji Umar Sabo. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆Banko ƙofar gidan tayi, A guje ta faɗa ɗaki haɗi da mako kofar da ƙarfi ta na garƙama sakata, Jingina tai a jikin ƙofar ta na sauke numfashi saboda mugun gudun da tayi. Hmmm ta yi wani huci cikin Ran ta ta na faɗin “wai yau nasha daƙyar Gaskiya Allah yana so na, yau da'ace su Duna sun kamani ai na kaɗe har buzu na wallahi” A fili kuma tace “yau na shiga uku shikenan babu ni babu yawo a gari sai an kwana biyu idan sun manta” gwaraamm aka Buga ƙofar da ƙarfi ta zabura ta na ihuu a zaton ta sune suka biyo ta har cikin gidan.Sai kuma ta ji muryar ƙanwarta tana cewa “Dallah Malama ki buɗe min ƙofa aikin banza kawai kullum Mutum baida aiki sai neman masifa ke ba ƙarfi ba Ga shegen tsoro mtssww ta ƙarashe da jan tsaki”. Daga cikin ɗakin Nanah (KHADIJA) ta buɗe muryar ta tana cewa “ina ruwan ki munafuka wallahi idan na fi to jikin ki Ne zai faɗa miki na rantse” Heeeh ƙanwar ta Amira tayi shewa tana Faɗin “ to kibuɗe mana a gwada a gani aikin banza kaw… Kafin ta kai ƙarshen maganar ta ji ƙarar buɗe ƙofar kamar an jefo ta, ta cakume ta suka kasa dambe ba ji ba gani, Matar baban su Amarya da su ke kira da Anty ta miƙe ta nufe su dan ta raba su aikuwa ta na isa ta samu rabon na ta dukan a fuska saurin matsawa baya ta yi. Mama hajara Ita ce uwar gidan Baba ta na kofar kitchen ta na tankaɗen garin tuwo ta ce “ke waye ya aike ki raba ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.