WASAN ƘADDARA 1

Chapter 2

by @asmeetahwriter

╔══════════════════════╗
        🌹 *WASAN ƘADDARA* 🌹
╚══════════════════════╝

_A Story of Love, Pain and Destiny. That Even Fate Cannot Escape_

> ✍️ BY ASMEETAH WRITER

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

🌟 Under:

THE SHIDORIA WRITERS TEAM

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

📞 ***

📚 BOOK 1

📖 CHAPTER ___3 and 4

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

Wasu soyayyar ƙaddara ce ke haɗata...
Wasu kuma ƙaddara ce ke raba su...
Amma me zai faru idan zuciya ta ƙi amincewa da hukuncin ƙaddara?

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━



Malam ya zabura a fusace, idon nan nasa ya rine ya yi jawur, yana ƙoƙarin kamo Millu.

 Millu kuwa ta yi hanzarin maƙalewa a bayan Uma, tana fitar da harshe.
Kaka ce ta yi saurin dakatar da shi, ta ɗaga murya tana faɗin,

 "A’a Malam! Barta... barta kawai! Ta ci albarkacin ita take raka ni bara. In ba don ita ba, sai dai talauci ya kashe ni a gidan nan, tunda sauran ’ya’yan naka ba su da mutuncin da za su raka ni."

Millu ta leƙo ta bayan Uma, ta ce, "Ai wallahi daga gobe ba zan ƙara raka ki ba!"

Kaka ta canja murya, ta fara lallashi,
 "Yiii Haƙuri mana ’yar Millu-Milluna... Ai kin san muna cin daɗi a waje ko?"

"Ai ba don ina cin daɗi ba, da ba zan raka ki ba!" Millu ta ba ta amsa, tana turo baki.
 Haka suka gama gumurzunsu, kowa ya ja bakinsa ya yi shiru.

Can Kaka tana zaune a kan tabarmarta, ta laluɓo kwanon bararta, ta ciro kifi irin ’yan mitsi-mitsin nan busasshu. Ta fara ƙira,

 "Zo ku karɓi ɗaɗɗaya... ba don halinku ba!"

Haka yaran suka tashi ɗaya bayan ɗaya, suna zuwa suna karɓar kifin suna mita... A’i ce ta tuna da yayarsu, ta kwalla ƙira,

 "Aunty Amiraaa! Ki zo Kaka tana raba kifi!"

Kaka ta zabura kamar wadda kunama ta harza, "Waaaa! Aniyarta ta bita! Ni zan ba ta abun hannuna? Saboda ta yaɓa min talauci ina zaman zamana? To ahir ɗinta."

Amira dake cikin ɗaki, duk tana jiyo su, amma hankalinta yana kan littattafanta. Ko da yake ba ta da tabbacin biyan kuɗin jarrabawa, hakan bai hana ta duba darasissikan ba.

Can Uma ta kalli Millu, ta ce, "Maza je ki ce wa Amira ta fito ta ci abinci."

Malam dake zaune a kan tabarma, ya yamutsa fuska, ya ce,

 "Hmmmm! Gadara kenan... Wai ta fito ta ci abinci, irin nan ita ta kawo kayan abincin?"

Uma ba ta ko kula shi ba, ta ci gaba da harkarta. Millu ta shiga ɗakin, ta iske Amira tana karatu. 

"Aunty Amira, ki fito ki ci abinci wai."

Amira ta ɗago kai, fuskarta a yamutse, ta ce, "Abinci ko tuwo?"

Millu ta ce, "Tuwo mana! Ai kinsan kullum tuwo ne da daddare.."

Amira ta sauƙe ajiyar zuciya, "Ina zuwa to... Ni ba don ina jin yunwa ba, da ba zan ci wannan tuwon da koren miyan nan ba. Ba sauyi ko da yaushe."

Millu ta fita da gudu don isar da saƙo, tana zuwa tsakar gida ta ce, 

"Uma, wai tana zuwa. Sannan wai in ba don tana jin yunwa ba, babu abin da zai sa ta ci tuwon nan da koren miya..."

Malam ya saki kwanon abincin dake hannunsa, ya kalli Uma da wani irin mugun kallo.

 "Kin ji ko? Kin ji abin da agolar taki ta ce? Yarinyar da ko sisin kwabo ba ta taɓa kawowa gidan nan ba, har tana da bakin raina tuwon da nake sawo wa da gumi na?"

Kaka ma ta dire kwanon kifin, ta fara tafa hannu.

 "Iyeee! Lallai ma Amira! Wato yanzu har kin isa ki ƙira miyarmu da koren miya dan wulakanci? To wallahi Malam, in har ka bar yarinyar nan ta ci tuwon nan yau, to baka haihu ba a cikinaa"

Malam ya miƙe tsaye yana huci, "Fito ki ji! Amira fito!"

Amira ta fito tana gyara mayafin da ta rufe kanta, ranta a ɓace.

 Malam ya fara nuna ta da yatsa, "Wato rainin ya kai har nan ko? To tun da kika ce tuwon nan ba na ajinki ba ne, to daga yau a gidan nan, duk ranar da aka yi tuwo da koren miya, to kashinki ya bushe idan kika sa hannu.."

Uma ta yi saurin cewa, "Haba Malam, yarinya ce fa..."

"Rufe min baki!" Malam ya daka mata tsawa. "Tunda ba ta so, to ta nemo mana na canjawa. Matsiyaciya kawai, tana zaune tsiya zai kashe ta  har tana neman daban?"

Kaka ta ƙara tunzura wutar, "Ai gara ma ta fita ta nemo mana gasasshen kaza tunda ita ta fi ƙarfin koren miya... Mayya kawai, kin zo kin kange mana arziƙi sannan kina raina mana abinci."

Amira ta tsaya tana kallonsu, hawaye ya cika mata ido, tana jin ɗacin yadda maganar da ta faɗa ta zama babban laifi. Ta kalli tuwon, ta kalli Malam sannan ta juya ta koma ɗaki tana kuka, yayin da Malam da Kaka suka ci gaba da jero mata tsinuwa da baƙaƙen maganganu kamar za'a biya su hajji.


Cikin daren, shiru ya ziyarci gidan... Malam na can can ɗakin sa yana minshari, Kaka ma na nata ɗakin. A dakin Uma kuwa, numfashin yara ne kawai yake tashi. Wata katuwar katifa ce a shimfide, inda Uma, Amira, da Khadija suke raba guri guda. A ƙasa kuwa, Millu ce ke baje a kan tabarma, tana shan baccin ta da ke tana fitsarin kwance... 
Su Minal da A'i kuwa, can ɗakin Kaka suka raba daki, domin nan dakin na Uma ya yi kankanta ga daukarsu duka..

Misalin ƙarfe ɗaya na dare, Uma ta idar da sallar nafila, tana zaune a kan sallaya. Ta miƙa hannu ta fara dukan ƙafar Amira. Cikin magagin bacci ta fara motsawa tana gunaguni..

"Tashi ki zauna," Uma ta faɗa murya kasa-kasa.
Amira tana mutsu-mutsu, "Haba Uma, mutum yana bacci? Ba asubanci ba ne fa..."

"Ki yi salla ki kai kukanki wurin Ubangiji!" Inji Uma..

Amira ta gyara kwanciyarta, fuskarta na nuna alamun bacci bai gama sakinta ba. "Uma, ni kam ai salla da addu'o'i ina kan yi, ba sai mutum ya yi niyya ba."

"To tashi muyi magana."

Amira ta tashi zaune gira a haɗe, ta kalli mahaifiyarta. Sai da Uma ta jira ta gama dawo wa hayyacin ta, sannan ta ce, 

"Amira, me yasa ba kya jin maganata ne? Me yasa kullum sai kin jawo an tsine miki a gidan nan? Shin ba kya gudun magana ne?"

Amira ta numfasa, ta gyara zamanta. "Uma, ke ma fa kin san halinsu... Ko na yi wani abu, ko ban yi ba, kullum a cikin zagi nake. Ba ni da mafita. Biyayya dai ina yi dai-dai gwargwado, su ne dai ba su dauke ni a matsayin 'ya ba."

Uma ta ce, "Duk da haka, kada kina shiga shirginsu. Duk abinda suka ce, ki kawar da kai, ki zamo mai kawaici. Ba daɗi a kullum suna tsinewa rayuwarki."

Kafin Uma ta ƙarasa, Amira ta tare ta da cewa, "To Uma, ke kika tsine min? Ko mahaifina wanda ya rasu ne ya tsine min? Bana damuwa da tsinuwarsu tunda ba iyayena ne suka tsine min ba. Sannan ni, hantararsu da takurarsu ba za su taɓa mayar da ni abun tausayi ba... Ko a makaranta, in ba faɗa na yi ba, babu wanda ya san halin da nake ciki. Kullum ina cikin kwarin gwiwa da motsa jiki na. Ni in dai ba gidan nan na shigo ba, har mantawa nake da akwai wasu mutane da suka tsane ni."

Uma ta zuba mata ido, tana mamakin irin wannan zuciya ta 'yarta. Ta ce, "Amira, a koda yaushe ina son kunnuwana su rinƙa jin kalaman albarka a kanki, ba tsinuwa ba."

Amira ta girgiza kai, ta ce, "Allah yana karɓar albarka ne a bakin mai albarka. Tsinuwa kuwa, sai dai a maida wa mai shi kayansa... Don haka babu tsinuwar wanda za ta kama ni haka kawai ba tare da na tare masa hanya ba. Abu ɗaya ne yake damuna a rayuwar nan shine yadda za a samu kuɗin jarrabawa ta.. Shikenan."

Tana gama faɗin haka, ta sake komawa ta kwanta, ta ja mayafi ta rufe jikinta, ta bar Uma nan zaune tana jan carbi...Uma ta ci gaba da addu'o'i, tana rokon Allah ya tsare mata yarinyar nan tata, wadda zuciyarta ta riga ta bushe daga tsoro...

★★★

Asuba ta gari ta canja gurbi da hayaniyar gari na yau da kullum. Sautin masu tallan kosai, kukan awaki, da karaf-karaf ɗin bokitan da mutane ke jigilar ruwa da su, duka sun gauraye unguwar...

A cikin gidan su Amira, tuni kowa ya tashi. Uma tana tsugune a gaban murhu, tana hura wutar itace dake ta faman fitar da ƙauri, idonta har ya yi jawur saboda hayaƙi. Khadija da kannenta suna can gefe guda suna shirin tafiya makarantar boko ta gwamnati, kowannensu sanye da tsohuwar unifom ɗinsa wacce ta fice launi saboda tsabar koɗewa...

Amira ta fito daga ɗaki, fuskarta babu annuri ko kaɗan. Tana sanye da tsohuwar doguwar riga, ta gyara ɗaurin kwallinta ta fito ta tsaya a gaban mahaifiyarta... Dake suna idar da sallar asuba suke gaisuwa kafin a koma baccin..

"Uma, barka da safe," ta faɗa cikin muryar dake nuna har yanzu tana nan murtuke da maganar su Malam..

Uma ta ɗago daga hura wutar, ta goge fuskarta da gefen zaninta..

 "Barka da safe Amira. Kin tashi lafiya? Maza miƙa min kwanon can na tankaɗe garin kulli."

Amira ta miƙa mata kwanon, sannan ta durkusa a gefen Uma.

 "Uma... maganar makarantar nan fa? Yau fa za a rufe rijistar jarrabawar NECO... Idan ban tafi da kuɗin nan yau ba, sun ce sun riga sun cire sunana a cikin kwamfuta."

Muryarta na rawa, tana ƙoƙarin danne kukan dake neman ƙwace mata. Wannan jarrabawar ita ce makami ɗaya tilo da take gani zai fito da ita daga cikin wannan kuncin da take ciki.

Kafin Uma ta ce uffan, sai ga Malam ya fito daga ɗakinsa, yana ɗaure wandonsa wanda ya tsufa, ya juyo da sauri jin kalmar kuɗi...

"Lallai ma matsiyaciyar yarinya!" Malam ya daka mata tsawa yana huci..

 "Tun sassafe ba a fito an nemi na abinci ba, kin tsare uwar taki da batun kuɗin boko? Dubu hamsin ɗan wajen uban wa zai baki?"

Amira ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta matse yatsun hannunta guri guda, tana jure baƙaƙen kalaman nasa...

Malam ya juyo kan Uma yana fari da ido, "Halima, na gaya miki, idan kika kuskura kika lale kuɗin da ya kamata a sayi garin hatsi kika ba yarinyar nan, wallahi tsakanina da ke sai Allah! Gidan da babu tabbacin abincin rana, har ana batun dubu hamsin na karatun banzan da ba zai tsinana komai ba."

Uma ta daure, ta dubi Malam da idanunta masu ban-tausayi, "Haba Malam, karatun jarabawar ƙarshe ne fa. Shekara shida tana wahala a makarantar nan, yanzu a zo kan na ƙarshe ta fasa?"

"Ta fasa dan ubanta!" Malam ya daka tsawa, ya sa kai ya yi waje yana faɗin, "Wanda bai da uba, bai da gurin gadara... Ta tafi ta nemo wanda zai biya mata, amma ba dai a aljihuna ba.."

Kaka dake zaune a jikin katangar ɗakinta, tana gyara sandarta, ta saki wata uwar dariya ta maƙirci...

 "Hahaha ahayyeee casss! Lallai Malam ka faɗi gaskiya....Mayya ai sai dai ta fasa. Tunda kika ce koren miya ba ajinki ba ne, to kuɗin dubu hamsin ma ya fi ƙarfin kanki. Gara ma ki fita ki nemo miji ki aura, ki huta, ki hutar da mu!"

Amira ta miƙe tsaye da sauri, ta kasa jure wa wannan cin mutuncin na sassafe. Hawaye ya wanke mata fuska, ta juya da gudu ta koma ɗaki....

Bayan shigarta ta goge hawayenta, ta shafa foda kaɗan a fuskarta domin ta ɓoye alamun kukan da ta sha. Already ta yi wankanta ta shirya cikin uniform ɗinta a goge tass sannan ta ɗauki tsohuwar jakar makarantarta, ta fito tsakar gida da nufin fita..

Uma dake zaune kusa da murhun ta kalle ta cikin tausayawa. "Amira, tsaya ki karya mana. Karda ki tafi da yunwa."

Amira ta tilasta wa kanta yin murmushin ƙarfin hali ta ce, "A'a Uma, na koshi kawai...Ki bar shi."

Uma ta laluɓa gefen zaninta, ta ciro naira ɗari ta miƙa mata.. 
"To gashi, karɓi naira darin nan ko kosai ne ki saya a hanya kafin ki shiga aji."

Amira ta girgiza kai, ta tura hannun mahaifiyarta baya cikin taushin murya. 

"A'a Uma, ki bari kawai. Gaba ɗaya bana jin yunwa."

Kaka dake zaune tana jiyo su, ta taɓe baki tare da tafa hannu.

 "Ahayyeee shagali...! Zuciya kwan fitila, ko ta yi ma zata fashe... Tunda kin ƙi cin tuwon gida, ai sai ki tafi da yunwar ta kashe ki."

Duk gidan babu wanda ya bi ta kanta, sai Millu kaɗai wacce ta turo baki ta kalli Kaka. 

"Ke kakan nan, matsalar idonki ma ya ishe ki wari... Kullum baki da aiki sai sa-ido."

Kaka ta zabura kamar wadda aka tsikara, 
"Kee! Dan kutan uwar ki! Kaji munafukar yarinya da iya-yin tsiya... Wallahi yaran gidan nan baku da tarbiyya!" Haka dai Kaka tai ta faman bambami, amma Amira ba ta tsaya sauraronta ba, ta juya ta fice daga gidan da hanzari...

Tafiya take a ƙasa amma takunta cike yake da kwarin gwiwa da nuna isa. Da ɗan nisa sosai tazarar ta makaranta. 

 Ta shiga cikin makarantar, dukkan wani kuncin gida barinsa take a baya. A nan makarantar, kowa ya san ta da sunan Meera..
Yarinya ce mai faran-faran, ga matukar ƙoƙari, wanda hakan ya sa malamai da dalibai duka suke ji da ita. Tana shiga filin makaranta, ta saki fuska ta biye wa kawayenta suka shiga hira da dariya, kamar babu wata damuwa dake damun zuciyarta..
yayin da masu mata hassada kuma suke can gefe suna kunkuni saboda yadda take haskawa a kowane fanni...

Bayan an shiga aji an fito, Amira ta jira sai da kowa ya baje, sannan ta nufi ofishin Shugaban Makaranta...
Ta shiga da sallama, ta durkusa a gabansa. Muryarta na rawa, ta bayyana masa halin da ake ciki da kuma fatan a ba su lokaci... Principal ɗin ya dube ta cikin yanayi na tausayawa, ya jinjina kai..

"Meera, na sani. Na san ke yarinya ce mai matukar hazaka da ilimi, kuma babu wanda zai so ya rasa ɗaliba irinki a wannan jarrabawar. Amma maganar gaskiya ita ce, kwamfuta za a rufe yau. Ko ki hakura a wannan shekarar sai wata shekarar mai zuwa."

Jin kalmar wata shekarar, sai da Amira ta ji jiri yana neman kwashe ta. Hawaye ya wanke mata fuska, ta kasa magana sai kuka dake cin ta a ɓoye.
Ganin yadda take kuka na tsantsar dacin rai, kuma Principal din yana da yakinin cewa idan Meera ta zana jarrabawar nan zata kawo abinda ake buƙata, ganin yanda take ta kuka yasa jikinsa yin sanyi...

Ya daki teburinsa, ya ce, "Shikenan Meera, share hawayenki. Zan ƙara muku lokaci zuwa sati daya duba da kokarinki. Amma ki sani, a lokacin za a fara shirin gudanar da jarrabawar, kuma idan kuɗin basu cika ba, babu yadda zan iya taimaka miki."

Amira ta goge fuskarta, ta yi masa godiya cike da girmamawa, sannan ta tashi ta fita daga ofishin. Sati ɗaya kacal ta samu. Sati daya da take tamkar dakika guda a wurin wanda ke neman dubu hamsin...
Yayin da take tafiya ta bar farfajiyar makarantar, tambaya daya ce ke yawo a ranta, A ina zata ga dubu hamsin cikin kwana bakwai?

Ta tafi ta zauna a corridor ɗin ajinsu, ta baje littafinta a kan cinyarta amma gaba ɗaya hankalinta ba ya kan karatun. Tana tsaka da wannan fafutukar tunanin, sai ga wani malaminsu ya zo wucewa. Ganin yadda ta zabge ta yi tsuru-tsuru, kuma dama ya riga ya ji abin da ya faru tsakaninta da Principal na batun rashin kuɗin jarrabawa, sai ya tsaya ya kalle ta.

"Meera, taso ki same ni a ofis ɗina yanzu," ya faɗa cikin muryar lallashi.

Amira ta miƙe ta bi bayansa har zuwa ofis ɗinsa. Bayan ta shiga, ya sa ta zauna sannan ya fara da cewa

"Meera, na ji abin da ya faru tsakaninki da Principal," ya gyara zama yana kallon fuskarta.. 
"Na san halin da kuke ciki na rashin kuɗi, kuma gaskiya ba zan so hazaƙa irinki ta tafi a banza ba... Ni a shirye nake na biya miki duka wannan dubu hamsin ɗin a yau ɗin nan."

Amira ta ɗago da sauri, idanunsa suka buɗe tsabar tsananin murna, "Da gaske kake Malam?"

Malamin ya yi wani shu'umin murmushi, ya matso kusa da ita.

 "Kwarai kuwa... Amma fa ke ma kin san babu kyauta a duniyar nan ta yanzu. Akwai sharaɗi ɗaya tilo... muna buƙatar mu fake a wani guri, ki bani kanki ba tare da kowa ya sani ba. Sirri ne tsakanina da ke."

Nan take ganinta ya ɗan canza, cikin rashin fahimta take bin sa da kallo, ya ƙara zafafa kalamansa. 

"Kada ki ji tsoro, na daɗe ina sonki. Idan kika ba ni haɗin kai, zan ci gaba da kula da duka karatunki na gaba, kuma wallahi har aurenki zan yi idan kika gama."

ta ji gabanta ya faɗi, wani irin takaici da kyamar mutumin suka cika mata zuciya. Amma da yake tana da wayo da dabara, ba ta nuna masa ɓacin ranta ba. Ta daure ta ce masa, "Na ji Malam, kuma na gode. Amma gaskiya sai na yi shawara tukunna."

Malamin ya zazzaro ido cike da fargaba, "Ke! Abin da yake sirri ne na mutum biyu, da wa zaki yi shawara? Karki kuskura ki sanya kowa a ciki!"

Amira ta kalle shi ido cikin ido cikin natsuwa, ta ce, "Da zuciyata zan yi shawara, Malam."

Malamin ya sauƙe numfashi, ya ce, "To, maza ki natsu ki yi shawarar da wuri. Kada ki bari wannan alherin ya wuce ki..."

Amira ta miƙe ba tare da ta ƙara cewa uffan ba, ta fice daga ofis ɗin. A wannan ranar, gaba ɗaya karatun da ake yi a makarantar bai shige ta ba. Kalaman malamin nan, da tarkon da yake neman ɗana mata, da kuma wannan gajeren lokaci na sati ɗaya da Principal ya ba ta, duka sun gauraye a kanta suna yi mata yawo.

Har ƙarfe biyu na rana ta yi, aka buga ƙararrawar tashi. Dalibai kowa ya miƙe ya ɗauki jakarsa ya nufi gida, Amira ma ta fito tana jan ƙafa, zuciyarta na mata nauyi yayin da take fuskantar hanyar komawa gidan su dake cike da masifar da ta bari tun sassafe...

Amira ta dawo gida cikin wata irin fargaba da firgitaccen tunani. Gaba daya kwallon kwanyarta ta ruru tsakanin daraktan lissafin kudin jarrabawa da kuma maganar da malaminsu ya jefa mata....Tana shigowa gidan ma kokari ta yi ta kauce wa idon Kaka da Malam, ta shige daki ta shiga abubuwan gabanta jiki a mace...

Daren ya raba, bayan an idar da sallar Isha. Amira tana zaune a kan tabarma riƙe da carbi, yayin da Uma ma dake gefenta ta idar da tata sallar take nannaɗe sallayar. Dakin ya yi tsit..

Anan Amira ta gyara zama, ta kalli mahaifiyarta da idanuwanta da suka kada suka yi ja.

 "Uma, ina son neman shawara a wurinki. Ba ni da wata aminiya da ta wuce ke a duniyar nan, kuma ke kadai ce zaki iya rike min sirrina..."

Uma ta tsaya da abin da take yi, ta fuskanci 'yar tata cikin natsuwa tana sauraron kowane kalma dake fita daga bakinta.

Amira ta fara da sanar mata yadda suka yi da Principal na cewa kwamfuta zata iyakance komai, amma duba da kokarinta ya bata alfarmar sati daya kacal. Uma ta sauke kanta kasa, ta kawar da fuskarta gefe domin ita kanta a wannan lokacin ba ta da amsar tambayar, kuma bata san ta ina zata fito da dubu hamsin din nan ba cikin kwana bakwai.
Ganin mahaifiyarta ta yi shiru, sai Amira ta daure, ta ci gaba da bata labarin abin da ya faru tsakaninta da malaminsu a ofis. Ta zayyana mata kalaman yaudarar da ya yi mata da kuma sharadin da ya gitta mata na cewa sai ta mika masa mutuncinta a ɓoye tukunna zai biya kuɗin.. Amira ba ta ɓoye wa mahaifiyarta ko kalma guda ba..
Tana gama faɗa, 
 Uma a ruɗe take kallon Amira, idanunwanta sun kawo kwalla, jikinta har rawa yake yi saboda tsananin ɓacin rai da fushi.

"Amira!" Uma ta furta muryarta na rawa, "Wannan abin ne har sai kinyi tunanin neman shawara a kansa kafin kiyi hukunci?"

Amira ta ɗago tana kallon mahaifiyarta cikin rashin fahimtar me yasa ta gigice haka.
Uma ta cigaba da cewa cikin ɗacin rai,

 "Amira, ko bayan raina ban yarda ki kusanci zina ba... Shin baki zuwa Islamiyya ne? Kinfi kowa sanin hukuncin wanda ya aikata zina da gangan, kuma kinsan girman laifinsa a wurin Ubangiji. Shin bayan kinsan duk waɗannan abubuwan, shi ne har sai kinyi shawara? To kenan idan aka baki shawarar cewa ki yarda masa, zaki yadda kenan? Shin talauci hauka ne?!"

Ta dafe kafadar Amira, hawaye na fita a idonta. "Duk rintsi kada ki kuskura Amira...Idan kuma kika aikata, wallahi ban yafe miki ba duniya da lahira! Burinki shi ne ki gama secondary kije ki karanci aikin likita, idan hakan bai samu ba sai kiyi auren ki ai daman ba kowa Allah ke cika masa buri a duniya ba, don Allah kada ki ɓata gobenki saboda abun yau da kullum..  Jarrabawa idan Allah ya kaddara bazaki zana a wannan shekarar ba, ba yadda kika iya, ba mutuwa zaki yi ba. Inda rai, zaki zana jarabawar nan ko da kuwa wata shekarar ce. Ki yi hakuri ki rungumi kaddararki, ba ke kaɗai kike cikin wannan halin na rashi ba."

Kalaman Uma sun ratsa jijiyoyin jikin Amira. Ta fashe da kuka mai ban tausayi, ta kama hannun mahaifiyarta. "Na sani Uma... Na san ba zaki taɓa bani shawarar da zata cutar da rayuwata ba. Na miki alkawari, na miki alkawari a yau bazan taɓa kusantar zina ba saboda kuɗi, kuma na miki alkawarin bazan taɓa satar kayan wani ba. Ina addu'a Allah ya hore min nima ta hanyar halal."

Uma ta ji sanyi a ranta, ta matse 'yarta a kirjinta, ta share mata hawaye sannan ta ce,

 "Allah ya miki albarka yarinyar kirki. Allah ya ƙara tsare min ke daga sharrin masu sharri. Duk masu son ganin zubar mutuncinki, Allah kada ya ba su nasara a kanki. Shi kuma wannan munafikin malamin can, wallahi gobe zan je har makarantar na ci mutuncinsa a gaban kowa.."

Amira ta girgiza kai da sauri, ta riƙe hannun Uma. "A'a Uma, don Allah kiyi hakuri. Gaskiya bana son wannan maganar ta fito fili... Waɗanda basu san halin da muke ciki ba ma ƙarshe sai sun sani idan abun ya zama abin surutu. Ki rufa mana asiri tunda bamu da shi a garin nan. Mu barshi da Allah kawai, idan halinsa ne, wata rana asirinsa zai tonu a idon duniya."

Uma ta daɗe tana kallon hikima irin ta 'yarta, ta saki ajiyar zuciya ta ce,
 "To, Allah ya toni asirinsa munafuki kawai."

Daga nan suka zauna suka cigaba da tattaunawa, tsakanin uwa da 'ya...Duk da cewa kudin jarrabawa bai samu ba, amma a daren nan Amira ta kwanta da wata irin nutsuwa a ranta, tana jin cewa matukar tana da uwa irin Uma, to tana da dukkan kariyar da take bukata a duniya...



 🙏🙏🙏🙏