WASAN ƘADDARA 1Free

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

WASAN ƘADDARA 1

  • 1views
  • 12chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

I'm Asmeetah Writer

More from @asmeetahwriter

Sample · Chapter 1

╔══════════════════════╗        🌹 *WASAN ƘADDARA* 🌹╚══════════════════════╝_A Story of Love, Pain and Destiny. That Even Fate Cannot Escape_> ✍️ BY ASMEETAH WRITER━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION🌟 Under:THE SHIDORIA WRITERS TEAM━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━📞 ***📚 BOOK 1📖 CHAPTER ___1 and 2━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━Wasu soyayyar ƙaddara ce ke haɗata...Wasu kuma ƙaddara ce ke raba su...Amma me zai faru idan zuciya ta ƙi amincewa da hukuncin ƙaddara?━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━"Meerash..." Muryar ta fito ne daga can ƙarƙashin maƙogaronsa,   muryar a sanyaye wanda ta ratsa ta cikin ƙashin bayanta.... Ta juyo a hankali, idanunta suka sarƙe cikin nasa..."Why do you always look at the world like it has nothing for you?..."    Ya tambaya, yatsunsa suna neman shafa fuskarta amma suka tsaya a tsakiyar iska kamar yana tsoron taɓa abin da zai iya ɓacewa."Because it never did...." Ta amsa, muryarta na rawa..A sanyaye ya ɗago da haɓarta da yatsansa ɗaya."That's where you're wrong... because you are the miracle the world never gave you, you're my miracle... Meerash."Meerah ta ji numfashinta ya ɗauke, tazarar dake tsakaninsu ta ragu ta yadda za ta iya jin zafin dake fita daga jikinsa. Kamar zai sumbace ta sai kuma ya ja numfashi, ya janye hannunsa cikin wani irin takurewa na son zuciya."You should go inside... Because if you stay any longer...I might forget the kind of man i am."       Wannan furucin ya ratsa ta kamar wutar lantarki. Ta juya ta nufi motarsa tana numfasawa, yayin da a bayanta ya tsaya yana matse hannunsa cikin damuwa. "This is dangerous..." Shi ne ƙarshen abin da ta ji kafin komai ya ɗauke..."A'uzubillahi minash-shaiɗanir-rajim!"Ameera ta tashi zaune a zabure, gumi yana kwarara a goshinta duk da cewar ɗakin babu zafi sosai. Numfashinta yana fita da ƙarfi kamar wadda ta yi tseren gudu."Lafiya kuwa Ameera? Wai ke kullum sai kin yi mafarki ne? Na sha tambayarki wani irin mafarki kike amma sai ki ce kin manta...Kar ki na addu'a idan zaki kwanta..."Muryar Uma ta katse mata tunani, cike da damuwa da bacci.Ameera ba ta iya amsawa ba, sai kallon Uma take yi a ruɗe har ta koma ta ci gaba da baccinta.Ta ɗaga kai ta kalli tsohon agogon dake rataye a sama, hasken uban sanjo ya gauraye fuskar agogon. Ƙarfe biyu na dare ne daidai...Shiru ya ratsa ɗakin, sai kawai numfashin mutanen ɗakin da kukan tsuntsayen dare. Ta dafe kanta tana maganar zuci.."Yaa Allah, waye wannan da nake yawan mafarkinsa? Ban taɓa ganinsa ba, kuma me yasa idan na farka sai in manta kamanninsa kwata-kwata? Me yasa nake jin kamar na san shi tun kafin a halicce ni?"Ta lumshe ido tana ƙoƙarin kwaso koda siffar hancinsa ne ko kwayar idonsa, amma hoto ɗaya ne yake dawo mata, shine inuwar ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters12
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play